Showing 108001 words to 110620 words out of 110620 words
mama tayi tana saka Hannu tare da Riƙe Hannun ta gam . Sauke Numfashi Mama Tayi tana Juya baya tare da kallon A'isha wanda idanun ta zaka kalla ka tabbatar da babu abu Ɗaya data yarda wanda suka faɗa mata a yanzu . Dafata Mama tayi tana cewa " A'isha Da gaske ne ba kowa bane iyayen ki ba face Daddyn Naawaaz da kuma Hajiya Lubna . Ki natsu a sannu zaki san gaskiyar labarin . Yanda kike zato da tunanin kan ki a rayuwar ki sam ba Haka bane ba . Ke Ɗiya ce ta sunnah Da Aure aka Haife ki sai dai Son rai irin na iyayen ki su suka jefa rayuwar ki cikin garari . Kiyi Haƙuri A'isha ki yafe mun Ni a matsayi na na Mahaifin ki . Ɗago da idanun ta A'isha tayi tana kallon Daddy da yake maganan shi kan sa cikin tashin hankali yake . Kuka Mommy Lubnah ta fashe dashi tana cewa " A'isha Yan uwan ki da mahaifin ki basuyi Miki komai ba ,nice nayi komai ba tare da sanin Ɗaya daga cikin su ba amma...... Cike da Rashin fahimta da dashewar Murya A'isha Farida ta katse Mom Lubnah da cewa " Mommy Ban gane ba , ki mun bayani yanda zan fahimta don Allah , menene ki kayi me kuma kika aika ta akai na.? .
Lumshe Ido Hajiya Lubna tayi tana tariyo labarin da ya wuce tun daga faruwar komai har rana mai irin ta yau . Karashe magaanan tayi tana faɗin " A'isha ki yafe mun na roƙi ba don Hali na ba , Don kasancewa ta ta mahaifiya a gareki . Kallon Su Mama A'isha tayi wanda suke ta aikin goge Ƙwallah . Muryar Yusraht ne ya katse su tana takowa zuwa inda A'isha farida take . Kama Hannun Farida tayi hawaye na tsiyaya daga Idanun su duka . A'isha Mommy tayi laifi kiyi Hakuri ,munyi kewar ki fiye da yanda bakya tunani . Gidan mu ya kasance tamkar gidan makoki ne na tsawon shekaru 18 . Tun a ranan da Mommy ta salwantar mana dake baby, Daddy ya daina fara'a ko raha da Mommy , magana ma sai ya zama dole sannan yake mata , shima idan muna wurin . Tun daga Wannan rana gidan mu ya dawo tamkar Gidan kiyayya ba soyayya tsakanin Daddy da Momy. Daddy ya ware Bedroom din sa ma bata isa ta shiga ba tsawon shekaru goma sha takwas muke a haka . Kuma basu taɓa sanar damu gaskiyar sanadin rikicin nasu ba sai a yanzu . Idan kin yafe ma Mommy to ki sani fushin Daddy yake yi da ita zai Kau daga Wannan Rana . Za mu ci gaba da Rayuwa cikin farin ciki tare da Soyayyar juna tamkar baya ."
Wasu irin Zafafan ƙwallah ne ke rige² n Sauka daga Ƙwarmin idanun A'isha . Juyawa tayi tana kallon inda Mom Lubnah take itama kukan take yi sosai mai tattare da nadama da danasani . Takawa tayi zuwa inda take tsaye . Cikin sanyin Muryar ta ,ta kira sunan Mommy Lubnah tana cewa " Mommy..." Ɗagowa Mom Lubna tayi cikin sauri tana kallon A'isha ido cikin Ido tana Ganin Afuwa da yafiya daga cikin idanun ta . Ware Hannayen ta tayi A'isha na Fadawa Jikin ta tare da Rungume ta ,tana fashewa da Sabon kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi a kallon duk mai gani da sauraro . Ƙanƙame ta Mommy tayi tana kuka sosai tamkar ranta zai fita . Cikin kuka Mom Lubna take fadin " A'isha ta ki yafe mun ,ki yafe ma Mommyn ki Don Allah . Mommy baki mun komai ba ,wannan ƙaddara ta ce , a rubuce take dama Allah ya hukunta hakan zai faru . Mommy na yafe Miki duniya da Lahira ."
Ɗagowa A'isha tayi tana kallon Mom Lubna da tasa Hannun ta tana goge Ƙwallahn Fuskar A'isha . Muryar Hajiya kaka ne ya katse su tana faɗin " Allahu Akbar, Kai Wannan yarinya akwai Haƙuri ,inda Nine ina zan iya wannan... Cike da Tsiwa na jika da kaka Yusrah tace " Kai Hajiya kaka , to yanzu me kike yi kenan ? Hura wutan kike yi ,wato kar A'isha ta haƙura ko.? Kar ta yafe mana duka kenan .? Eh Ƙwarai inda Nine ba fa zan yafe ba ." Haɗa ido Mom Lubna tayi dana A'isha suna sa Dariya ganin Yanda ake Yi tsakanin Yusra da Hajiya kaka . To Alhamdulillah , Allah za mu gode mawa mai kowa da ya kawo mana karshen duka wannan matsalolin cikin sauki . Alhamdulillah suka furta duka a tare ,ko wannen su ka kalla yana cikin farin ciki da annashuwa . Aaslaam ne ya fara ƙirar Numbern Mommyn shi , Wanda Ganin haka yasa Aaaryaan cewa ' Kai kuma me zaka yi ne haka kake kokarin kira.? Murmushi yayi yana cewa " Ina so na faɗa mawa Mom Daddadan Labarin A'isha Farida . Murmushi A'isha tayi yayin da su Daddy suka yi Dariya irin tasu ta manya kamin yace " Ai tun kamin mu taho nan ,na sanar ma Daddyn ka da mahaifin Sadeeq yanzu ma duka suna hanyar zuwa gidana yanzu haka .
Mommy Lubnah na ce ta kalli A'isha wacce take jin tamkar ta maida ta ciki saboda so tattali da kulawa kana tace " a'a to ai ya kamata yanzu mu koma Gidan ne Daddy kar su isa bama nan . Kallon A'isha Farida tayi tana murmushi tare da Daga mata Gira tana cewa " Yau zaki je Gidan Daddy za muyi Rayuwa mai dadi yanda muka so Allah bai nufa ba . Kin shirya mu tafi .? Gyada Mata Kai A'isha tayi tana murmushi . Yayin da Aaaryaan ke bin Su da kallon bai fahimta ba , don shi a cewan shi a yau fa Gidan sa A'isha zata sauka su Cigaba da Rayuwar su a can .!
**
Miss liliey ce ta shigo Office din Manager tana aje masa Farar envelope . Ɗagowa Managern yayi yana kallon ta cike da mamaki kamin yace " Miss liliey meke Faruwa ne.? Wannan kuma na Meye .? Kallon sa tayi tana masa kallon sama da ƙasa kamin tace " takardar Aje Aiki na ne . What me ya faru.? Manager yayi maganan tare da Miƙewa tsaye . Wani irin kallo Liliey tayi masa kamin tace " Na aje aiki , Ko baka da labarin Auren Sir Aaryaann Kareem ne.? , A'a ina dashi mana ai kusan 5 mount kenan da yin Auren . Wow ." Tayi maganan irin na Rainin hankalin nan . Good yayi Aure .? Ni kuma sai na cigaba da yin aikin banza , ina zaune yayi Aure ,shin baka da labarin Son shi nake yi ne.? Ashe nike ta dakon SO shi bai san dani ba ma . Har in rinka tunanin gamu da yan yara luku² gwanin Sha'awa ashe duk a Hauka na ne . Shi yana da wacce yake so . To ba zan yi aikin ba ,abun kuma da yayi mun Allah ya saka mun . Nima zan tafi nayi Aure na don ban rasa masu so ba . Ganin tana shirin juyawa ne tare da ficewa yasa Manager cewa " A'a Madam liliey ba'a yi haka ba ,don Allah ki Cigaba da Aikin ki ,kece da Sectary na Wannan Companyn . Mtswwwww wani uban dogon Tsaki Liliey taja kamin tace " Iskancin Banza . Wato yayi Aure ina zaune ,nan da shekara daya sai na ganshi da yara duka ina zaune Ni saboda ga mara hankali da Abun yi . Nima ba banza bace ai . Wannan envelope din saƙo ne ka basa hannu da hannu bye." Kamin yayi wata magana ta juya ta fice , yayin da Manager ya koma ya zauna yana sa Dariya tare da furta " Maganin ku kenan Matan wannan zamani .
**
Zaune take tana kallon Wani Series Film mai suna " You to me Are Everything . Sosai A'isha Farida ke jin dadin kallon Film din . Dantes And Marian Rivera . Shigowa Yusrah tayi wujajan tana nufar Akwatinan A'isha tare da sauke su tana buɗe Waldrop tana fiddo da kayan ta . AUNTY Yusra lafiya .? Hummm Baby kenan , wani lafiya Wancen mayen mijin naki ya hana mu sukuni , Yanzu fa yana kasa kaman zai sa ma Momy kuka wai a bashi matar sa . Kin ga ai gwara mu bashi tun kan ya kuma Guduwa dake a karo na biyu . ! Gintse Dariya A'isha tayi tare da cewa " a'a Aunty Yusra Ni dai Ban shirya tafiya ba , sati duka nayi anan .? Ai fa Baby mu ma don dole ne zamu bar ki ki bishi , don ya fiye damu . Kamin A'isha tayi magana ne Aaryaan ya shigo Bedroom din . Suna haɗa ido ta cuno masa ɗan mitsulin bakin ta ,don ba tason tafiyar ta koma Gidan sa a yanzu ,sosai take jin dadin zama da Familyn nata . A'a Sannu da Zuwa Ya Aaryaann ka shigo nan ne.? Kallon Yusra yayi yana cewa" Eh Waya taɓa mun Matana.? Humm Sauke Numfashi Yusra tayi tana cewa" Ai wannan kayan nata ne nake haɗa mata gwara ku tafi kawai ko ka bar mu, mu huta . Dariya yayi yana Cewa " Kai godiya nake Yusrah maza Haɗa mana kayan asa moto mu wuce. Kallon sa A'isha tayi tana cewa " A'a Nifa babu inda zani Ya Aaryaann.
Ai kuwa yau zaki tafi A'isha . Mommy na fa bari ne sai bikin Yusra . Yusrah...!!! Mommy Lubnah dake shigowa tayi maganan tana jijinawa . Murmushi Aaryaan yayi yana tuno da yanda Al'amarin suka kaya musamman Soyayya da ta kullu kaman Wasa tsakanin Aslaaam da Yusraht . A'isha bafa a tsaida watan bikin ba ma . Yusrah ne ta ce Mom rabu da ita ,rigima take ji ,kuma a yau zata tafi . Maza tashi ki s shirya . Ke da zuwa biki na ai sai kin kusa Haihuwa ko ma kin haihu lokacin kin zama Maama..... Dariya Aaaryaan yasa haka itama yusran don tsokan A'isha take yi . Juyawa A'isha tayi tana kallon Mom tare da cewa " Mommy wai idan mutum zai Haihu Alluran suma ake masa ko.? Har ya haihu bai sani ba .
Wani irin dariya suka saka mata har da Mommy Lubnah , Kamin Aaryaan yace " eh mana ai irin shi za'a yi Miki . Juyawa Yusrah tayi tana Cigaba da haɗa mata kayan tare da dan goge Hawayen da ya zubo mata ba tare da ta bari kowa ya lura ba . Tausayin ƙanwar nata ne taji ya kamata . Baby Ina Nan zuwa Gidan ki ,ki shirya mun komai da komai ." To Anty Yusra don Allah kar ki dade baki zo ba ." Kallon Aaryaan yayi tana shirin masa kuka ne yayi saurin dan Hugging din ta tare da furta " Sorry.
**
Kwance take a jikin sa suna rufe a blanket , Babu abun da kake ji sai karar fitar kiss😘 uhmm💋³ . Uhmm Uhmmm Uhmmm ni dai ya Aaryaann Yanxu fa Subahi ne , ka tashi haka kasan kace zaka leƙa companyn ka fa . Bakin sa ya daura saman Breast din ta da suka ƙara cika , don da'ala a yanzu cikin jikin ta zai kai Watanni Biyar. Kissing din Nonon ta yake yi tare da kai harshen sa da laɓɓan sa kasan Cikin jikin ta , a hankali ya fara kissing wanda yasa ta shiru tana daura Hannunan ta a saman Sumar sa tana shafa masa tare da yamutsa Sumar nasa a hankali . Baby na jiya sau nawa tayi kewar Daddyn ta .? Murmushi A'isha Farida tayi tana cewa " Babu Adadi . Shafa Cikin nata yayi yana Cewa" Yau ba zata yi ba , tare dake zamu tafi Company , don haka ki barni na ƙara one round ,zagaye daya pls . Humm Sau daya kace dai . Murmushi yake yi tare da cewa " Kwarai sau daya . Haka dazu ma kace . Ai yanzu an kusa shiga Masallaci daga Wannan shikenan . Ni dai fa duk a wajen bargo nake ji , don bana kutsa kai na ciki ba. Dariyar ta na fara ji , sai kuma can naji tana sauke nishi a hankali tana faɗin " Ahhhhh Aahhhh Ya Aaaryaan ciki Ushhhhh Ciki Sosai Ashhhh...... Danna harshen sa yake yi ciki yana karkado dadin ta yana Lumshe idanun sa...Humm Mr.&Mrss Aaryaan fatan Alheri da fatan nasara zaman Lafiya mai dorewa abadan da'iman .
**
*Final*
Moton su ne ya tsaya a Farfajiyar Companyn yayin da Aaaryaan ya fito cikin shigar sa ta suit wanda yayi masifar kyau . Zagayowa yayi ta gyefen inda take yana kallon ta itama shi take kallo Ganin yanda ya ɗan Risina ta glass din moton . A hankali ya buɗe mata Murfin Moton tana kallon sa tare da murmushi tana mai sa hannun ta tare da kama Sajen fuskar shi tana dan ja masa da karfi . Sai da ya furta " Ashhhh. dariya tayi masa tare da masa wani irin kallo mai kunshe da zallar so da kulawan juna . Jakar Hannun ta handbag ya riƙe Mata tana mai gyara zaman Mayafin ta na Jallabiyar da tasaka tsadar ta ta haura 85k .duk da cikin ta ya fito amma bai hanata saka dan takalmin ta mai karamin tudu ba . A hankali suka nufi lift don komai na Companyn ya sauya idan kana ciki zaka dauka a kasar waje kake .
Shigar su Office ke da wuya Manager ya shigo yana Gaishe su tare da bashi sakon liliey yana faɗin "sakon Na miss Lieliy ce . Ok you can Go..." Ok sir juyawa Manager yayi yana ficewa daga office din . Kallon shi A'isha Farida tayi tana murmushin yake da nuna kishi kamin tace " Tsohuwar soyayya ta motsa.? Saurin kallon ta yayi kana yace " Aaa ban fa san Meye a ciki ba . I'm sorry My luv Bara na bude a gaban ki ki gani . Aaaa nifa bai dame Ni ba . Hannun sa yakai yana Tallabo Fuskar ta yana mata kallon kaman Wanda yayi mata laifi duk ya diriri ce . Please Eashha ta bana Son fushin ki . Buɗe envelope din yayi yana Fiddo da takardan ciki tare da warwarewa .
Na gode Sir Aaryaann bisa suka Ni da kayi nayi ta dakon soyayyar ka . Sai dai naji labarin Aure . To Nima zan tafi zan yi Aure . Ina maku fatan Alheri da zuri'a dayyiba .
Your Sectary
Miss liliey.
Kallon shi A'isha tayi tana kai bakin ta tare da kissing lips ɗin shi . Lumshe ido yayi yana ware su a hankali gani yayi tasa masa dariyar nan nata dake ƙara mata kyau matuka. Ina Son ka Har Abada Ya Aaaaryaaan . Hannun sa yasa yana Rungume ta jikin sa tsam tare da furta " Nima haka Har abada abadan Abada Soyayyar ba zata gushe daga zuciya ta ba...!
*Tammat bi hamdulillah.*
Allah ya sauke su A'isha lafiya , su Nawaaz kuma da Aaslaam Sadeeq Allah yasa ayi taro a kuma watse lafiya . Taku har kullum mai maku fatan Alheri a koda yaushe Aishatou mamanteddy . Kura kuren dake cikin wannan labari Allah ka yafe mun wanda muka yi dai dai Allah ya bamu ikon aiki dashi .
Special greeting to my Husband Ina godiya da yanda kake karfafa mun gwiwa a duka harkokina . Allah ya kara haske da wadata ya kuma ƙara mana zaman lafiya .
To sai kuma Kunji Ni da sabon littafi na da zai zo maku nan kusa b da dadewa ba .
*#MAMANTEDDY*