Showing 72001 words to 75000 words out of 110620 words
Ɓangaren Aaaryaan kuwa ko da ya isa companyn sa a jiya babu Abin da yayi face Tijara da cin mutunci wanda a da tunanin miss Lieliy ta dauka wani kyaƙyƙyawar sako zai bata , sai ta tadda tijara , duk wasu Companyn d suke neman Hadin Gwiwa yasa a fitar masa da Takardun su a cewan sa baya bukata. Tun da ya iya rasa Farin cikin sa ,So he's ready to loose everything in his life . Rasa Gane kan gadon sa suka yi ,inda miss Lieliy ta koma tunanin Anya Sir Aaryaann yana cikin natsuwar sa kuwa ? A ganinta kuma a sanin ta ,tasan yasan Benefit din da zasu samu da Wa'annan companoni amma yake wannan cin Mutumci, Tabbas bada don tasan Shi din Kawai Ƙwarto bane Sexxy boss to da tayi masa tunanin ko ya fara dan Kwalɓewa ne . Haka sai da ya wujijjiga su sannan ya baro Companyn yana nufowa Gida . Tun da ya dawo , Part ɗin Mama ya nufa tare da shigewa Bedroom din na Nan . Bai kuma ƙara fitowa ba ,don ko da mama tayi masa maganan breakfast da safe , ce mata yayi suyi babu shi kawai , yana Aiki ne . Sai da Mama tayi jimmmm kadan don taga sauyi sosai daga Tare dashi kana daga Bisani ta fito tana aika masa da Karin kumallon nasa Har inda yake .
**
Ƙarfe Goma sha daya na Rana Hajiya Kaka ta kira Daddy marshal da kuma Baba Bala , Da Abban Jos ƙannin Daddy na family , inda Ta basu shawara akan Yanda Auren zata kasance . A cewar ta a fara samun yarinyar wato A'isha Farida a tambaye ta , daga Zarar ta amince to kar a tsaya bata lokaci , a satin a san yanda za'a daura Auren ta da Naawaaz daga baya Sai ayi maganan tarewa in yaso ta kammala karatun nata sai ta bi mijin ta ayi shagali sosai .
Tun fara maganan Hajiya Kaka Daddy marshal yayi na'am da maganan wanda bayan sun gama tattaunawa ne Daddy na fita yasa aka yi masa kirar Nawaaz , Don ya kara gasgata zancen daga Bakin sa .
**
Wuraren Ƙarfe biyu na Ranan wannan Rana ne A'isha ta fito cikin shigar ta normal doguwar riga ce wacce tsadar ta ba zata haura 12k ba . Gashin kan nan nata duka babu gyara , wani irin kallo Mama Lantana tayi mata wacce take fitowa daga Kitchen . A'isha Lafiya na Ganki Haka ? Ko dai jikin ne?.. Kallon Mama Lantana tayi ƙwallah na ciko Ƙwarmin idanun ta kana tayi sauri kasa da kan ta don bata son mama ta fahimci wani Abu daga Gare ta .Mama lafiya lau . Na fito ne na saka Wani Abu a ciki na . Ayya Sannu Jeki Falo ki zauna bari yanzu ina zuwa .
Bayan mama tabi da kallo , kana ta Dan nufi Tsakiyar falon tana zama . Wani irin kanshi Taji na tashi tare da karar Sautin takalmi irin hill shoe din nan na mata yan kwalisa . A hankali ta ɗago idanun ta tana sauke su akan Fuskar Miss liliey wacce kallo ɗaya ta tuna ta , da kuma haduwar su yanda ya kaya a Companyn Aaryaan .
Sannu Yamma '. Lieliy tayi maganan cikin Wani irin sauya salo tamkar wacce bata taɓa Sanin A'isha Farida ba . Yauwa Barka da zuwa . A'isha tayi maganan tare da mata Alamun ta zauna ga Wurin nan . Zama Lieliy tayi A'isha na kallon kafar ta a sace inda Anan taga Kafar kaman na Larabawa saboda kyau . Ke ina Son nayi magana da Ogan ki . Zaki iya sanar masa da zuwa na ?.
Kallon Lieliy A'isha tayi kana ta danne Zuciyar ta tare da cewa " Ok , ta ƙare maganan tare da Kallon Hanyar da zai kaita Bedroom din Aaaryan , inda tun juya a asibiti bata ƙara saka sa a ido ba. A hankali ta miƙe jiri na ɗibar ta , tafara nufar barin falon . Yauwa idan kinje Kice masa Masoyiyar sa Lieliy tazo....Damm-dammm Ƙirjin A'isha ya buga , Sam bata san lokacin da ta Juyo tana kallon Lieliy ba idanun ta duka sun firfito . Wani irin murmushi Lieliy tayi ganin yanda Hakar ta ke shirin cimma Ruwa . A'a Sorry ƴammata ,kawai Kice masa Miss liliey ne . Juyawa A'isha tayi tana barin falon ba tare da ta kuma ce mata komai ba .
Dama Yaudara ta ne Yake yi ko mene? Amma Kuma ai Alƙawari yayi mun ? Ko don ya lalata mun rayuwa shi yasa yayi deciding haƙura dani ,saboda ina kitsen bare romon?. Lumshe ido tayi hawaye na gangaro ma Kuncin ta , tana saka hannu tare da sharewa .
Zaune yake yana bin cike ta laptop ɗin dake gaban sa . Gyefen sa Ruwan roba ne sai Sai Tarkacen sa wayoyi keys da sauran su . Shigowa A'isha tayi kan ta a ƙasa don bata lura ko taga Halin da yake ciki ba . A hankali ta tako zuwa inda yake tare da cewa ' Barka da Sfy . Wani irin kallo yayi mata mai kama da wulakantarwa dai dai tana kallon sa suna ido hudu.
Ganin sa da tayi daga shi sai t. Shirt da boxer iya gwiwa yasa ta saurin juya baya tana cewa " Wata miss Lieliy tana Falo tana jiran ka . Ok yace ba tare da ya damu da yanda tayi masa ba . Text din Da NAAWAZ ya turo masa ne yakara kallo kana ya miƙe yana biyo bayan A'isha Farida.
A falo ya tadda ta ita da miss Lieliy , inda a ya tsaya yana kallon Lieliy tare da fadin " Me ya faru ? . Kallon sa tayi kana ta kalli A'isha da yake shirin ci mata mutunci a gaban ta .wanda hakan bai ma Lieliy dadi ba . Kame kame ta hauyi tare da cewa" Amm Sir Wannan yar Aikin ka ne ko? So ya kamata ta Bamu Wuri maganan mu mai muhimmanci ne .
Kamin Aaryaan yayi magana A'isha ta mike tare da shirin barin Wurin cike da ɓacin rai da jin mizuntuwa , Wani irin dariya Suka ji An dauka daga Baya . Wanda cikin sauri suka juya banda Aaaryaan da yake kallon ko wannen su daya bayan daya . Yusrah ce ta tako tana dariya har da kyakyatawa kana tace " Ai Yar Aiki ce baki ga babu Wayewa ba ,sai rashin kunya , wai kuma a haka take jin Aaaryaan ne abun son ta .! Please kalle ta ba ,kasashe nawa kika taba fita a rayuwar ki da har kike kokarin hada kan ki da Wanda yafi ƙarfin ki tamkar sama da ƙasa . Idanun A'isha ne suka kada Jah baya tayi tana share Hawayen fuskar ta tare da barin Wurin cikin sauri . Dariya Miss liliey ta saka tare da cewa " Really?. Eh mana idan karya na faɗa ta Musa mana .!
Tab aiko iska na Wahalar da mai kayan kara Allah dai ya kyauta . Ta ƙare maganan tare da kallon Aaryaan da Har a lokacin yake tsaye bai tanka shirmen su ba ,yanda kasan bai san ma me suke fadi ba . Gyara zama Miss liliey tayi tana cewa " Yallaɓai Sir Aaryaann ." Kallon ta yayi a dake fuska babu Annuri yana furta mata " What.? . Amm dama nazo ne akan magaanan nan da hukuncin da ka zartar jiya . Wani irin kallo ya watsa mata a wulaƙance ya ce " And...? Jikin ta sosai yayi la'asar ganin yanda yake mata maganan a dake a kuma gajarce . Shine nazo na faɗa ko zamu ƙara wani sabon Zaman ne a tattauna . Lumshe idanun sa yayi yana ware su akan ta kana yace " Okay tare da juyawa Yana bata wuri .
Shiru Yusrah tayi da akayi komai a gaban ta . Haushi ne ya kamata , to me hakan ke nufi da yanda Aaaryaan yayi a yanzu ?.
**
A wannan Rana yini A'isha tayi babu karsashi , tayi kuka har ta gode Allah . Ta tsaya a gaban madubi ta ƙare ma kanta kallo ,kuma anan zuciyar ta ya bata amsan bata kai matsayin da Aaryaan zai SO ta ba , cutar da Rayuwar ta ya riga da yayi . Gwamma taso Nawaaz wanda yasan komai abun da ya faru . Da misalin Ƙarfe 7 ne Daddy marshal ya kira wo ta ,tare da tambayar ta akan Tana son Nawaaz hankali kwance kuma he's ready to idan ta nuna bata Ra'ayin sa ba zai mata dole ba . abun da ta faɗa ya ba Mama Lantana mamaki don bata kawo A'isha Farida zata iya amincewa da Wani bayan Aaaryan ba , Komai da suke yi tsakanin su a hannun ta take kallon su . Tun shigowar ta dakin A'isha da ta ganta Kwance tana kuka a jikin sa ta fahimci shine Ɓoyayyen masoyin nata , da kuma yanda shima yake yawan maganan Ɓoyayyen masoyin . Farin ciki sosai Daddy yayi kuma a wannan daren ya sanar ma Daddyn Nawaaz haka Ma Hajiya. Inda Anan take fadin " Ya kamata a gobe a daura masu Aure bayan saukowar Sallar juma'a. Don kashe Duk wata fitina da zata ɓullo .
A ranan Mama Lantana ta kasa barci , zuciyar ta na fadin Anya baki yi masu yankar Ƙauna ba . Shidai Aaryaan bai ji labarin ba sai da Safe . Zaune yake a gaban Hajiya kaka wanda yaje Gaishe ta . Mika masa Wani Jug tayi tana cewa " Amshi ka shanye yanzu tasss .wanda babu musu bai san na Meye ba ya kafa kai yana kyankyama don ya manta da ya taɓa faɗa mata wai bashi da lafiya . Tun kamin ya gama shanyewa yaji 🍌 na sama tayi cirrrrr ,sauri aje jug din yayi yana cewa " Hajiya wannan na Meye ne?. Maganin karfin maza mana . Kana Ganin yau za'a Daura Auren NAAWAZ da an sauko masallaci , Amma kai har yanzu sha'awa ma baka dashi , wannan ma na farko ne ,zuwa yamma idan ya gama bin jikin ka kazo ka amshi Wani , ina so kai ma kayi Auren ne . Innalillahi wainna ilaihir raji'un . Kalmar da ya ambata kenan .
Wanda Hajiya kaka ta tsaya tana sakin baki kamin tace " Me kake nufi?. Bai tsaya bi ta kan ta ba ,ya mike cikin sauri yana ficewa daga sashen nata baki daya tare da nufo sashen Mama Lantana .
Wuce Masu aikin yayi yana nufar Bedroom din A'isha Farida .inda ya fara jin Muryar Yusra tana cewa " na tausaya Miki shigowa rayuwar Yaya na da kika yi Naawaaz , mtswww Baki fara kuka ba yanzu zaki fara . Murdo Handle Door ɗin yayi a zafafe yana shigowa inda Ya nufo Yusra daga Hannun sa yayi yana wanke ta da Mari Tassss . Wani wal² ta gani na tartatsi kana yace " A'isha Rayuwa ta ce , ba zan lamunci cin mutunci daga wurin kowanne daga cikin ku ba .
Sauke Hannun ta Tayi daga kunci ta cikin zafi ta fara cewa " Dama Nasan ai son junan ku kuke yi , Amma sai dai ka makaro don ita din makira ce shedaniya , ta amince da Auren NAAWAZ wanda za'a daura yau da misalin 2:30pm . Sai ka Aure tan na gani . Kuma ina maka A'ishir da cewa " Daga nan sashen Hajiya kaka nayi don na faɗa mata kai nake SO kai zan kuma Aura . Sai naga Mai Dakatar dani daga auren ka .
Tana Gama faɗin haka ta juya fuuuu tana ficewa daga Dakin. Kallon sa A'isha Farida tayi da har a lokacin idanun ta na tsiyayar da Hawaye . Hannun sa yakai yana turbitsawa cikin Sumar kansa ,cike da rashin sanin mafita. Ganin Haka yasa shi fara takawa zuwa inda A'isha take ,duk da yanda yake jin sa kaman ana masa chaji . Kallon sa tayi tana ɗago Idanun ta tare da fashe masa da kuka mai ban tausayi . Rungume ta yayi yana shafa bayan ta a hankali tare da furta " I'm sorry , I'm very sorry dear . Zaki bini mu tafi.? Saurin janye jikin ta tayi tana kallon sa kamin ta girgiza masa kai alamun a'a. . Wani irin huci ya furzar mai zafi kana ya sauke Muryar sa kasa na Rarrashi tare da cewa " Pls Ki taho mu tafi , Ki share ki ɗauka a yanzu bani ne Aaaryan ba , wanda yayi Miki Laifuka da dama . Ki ɗauka a yanzu ɓoyayyen masoyi ne a gaban ki kuma yake rokon ki akan ki biyo sa . Zaki taho .? Yayi maganan yana kallon ta idanun sa duka sun kada sunyi ja na tsaban Tashin hankali .
Kallon sa tayi cike da jin narkakkiyar tausayin sa ta nufesa tare da shuge masa tana kanka nesa , ɓoyayyen masoyi na ka tafi dani Wuri mai nisa , kar ka bari na Auri Nawaaz, kai nake so nayi rayuwa da kai na har Abada . Dago Fuskar ta yayi yana faɗin " Kin tabbata.? Cikin kuka ta girgiza masa kai wanda kamin tayi magana yayi saurin Hada Fuskar shi da nata , yana kissing ɗin ko ina na fuskar ta har zuwa laɓɓa . Jikin ta ne ya hau Rawa , don ta rabu da jin Wannan Bakon al'amarin nasa wanda bata saba dashi ba . Yau zamu bar Nigeria mu tafi muyi Rayuwa mai dadi na baki kula da Farin ciki mara iyaka . Yayi maganan tare da ɗago fuskar ta yana kallon ta tare da sakin mata Murmushi . Juyawa yayi yana kallon kallabin ta , kana ya nufi Waldrop yana Fiddo mata da Hijab . Hannun ta ya riƙe yana ficewa da ita daga Falon ba tare da Mama Lantana ta sani ba ,don tana can falon ta . Moton sa ya nufa da ita yana budewa tare ds ce mata ta shiga , babu musu ta shige , Shi kuma yana saurin komawa part ɗin shi . Can kaman mintuna uku ya fito hannun sa da brief case yana shiga moton tare da barin Cikin gidan da ita dashi baki Ɗaya......!
Sorry for the late update 🙏🏻😄
```FƳAAƊE.!```
*(Erotic and Sympathetic Story)*
Ayshatou Mamanteddy
***37-38***
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*
🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....
*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN
Whatsapp:07045125150
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.
**
Kallon Aaaryan A'isha Farida tayi tana saka masa Sabon kuka tare da Kama Hannun sa ɗaya Wanda baya Driving dashi . Yah Aryaan Ka mai Dani Gida, Ka maida Ni Wurin Mama, Ka maida Ni na haƙura muyi ma Mama da Daddy biyayya akan Abun da suke SO....Ƙuuuuuuu Taji tayar moton su na jan Ƙwalta da Ƙarfi yana ƙoƙarin Haɗa masu Haɗari . Rintse Ido tayi tana saurin Ƙanƙanesa tare da manna sa da Jikin ta , tana Kwantar da kansa Bisa saman Ƙirjin , a dole kafin Wani Abu ya faru dashi to ita ya fara faruwa da ita . Har yayi parking a gyefen Hanya ba ta sani ba , Idanun ta na rufe Sai Addu'a da take yi . Kallon ta yayi yana zan Ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da raba Jikin sa da nata. Kallon ta yayi yana cewa " A'isha buɗe Idanun ki . A hankali ta Ware idanun ta tare da Kallon sa hawaye na cigaba da Kwaranya daga Ƙwarmin idanun ta . Hannun sa yakai yana Ɗago da fuskar ta Wanda yayi mata Ƙurrrr yana kallon ta , kusan na minti biyu kana ya ɗan motsa laɓɓan sa tare da cizar Laɓɓan sa na Ƙasa a hankali . A'isha Buɗe idanun ki, ki kuma kalli Cikin Idanu na yanzu .?
Jikin ta sosai yayi Sanyi A hankali ta ɗago da zagayayyun idanun ta tana Sauke su Akan Manyan idanun sa kaman na nufawa🫣 . Meyasa Kika zaɓi Auren Naawaaz a kai na? Bayan kuma kina So na ? . Motsa bakin ta tayi tana Girgiza masa kai tare da cewa " A'a Kawai dai bana So wani Abu ya same ka ne , Saboda Nima .... Enough ya isa Don Allah.' A'isha kina So na ,a ƙwayar idanun ki naga Hakan gashi nan ,idan kin ɓoye a baki to fa ba zaki iya boyewa a ƙwayar idanun ki da kuma zuciyar ki ba . Mama na ce , Nasan zata Fahimce mu , idan kuma kin nace zaki Auri Naawaaz to ki sani ba zan taba Barin ki ba Har abada . Cikin dan daga Murya na zafin zuciya yace " Kin shirya Auren mazaje biyu a lokaci guda? . Saurin kallon sa tayi tana cewa " Ban gane ba .
Huhhhh ya furzar da iska tare da kama Hannun ta yana ware yan yatsun ta tare da murzasu a hankali . Ki kayi Kuskuren Auren Nawaaz to kisani kin jefa Rayuwar ki cikin Haɗari , da fari Ni ba zan Rabu dake ba .domin ke matata ce Alƙawari kika mun ....Ya Aaaryaan ban maka Alƙawarin Aure ba , nayi Alƙawarin rayuwa da kai Har Abada dai . Dan ƙaramin tsaki yayi tare da cewa " To Meye rayuwa na Har Abada? Bashi ne Aure ba .? To idan baki Sani ba yau ki sani . Kuma a yau zamu koma America da zama ba zan taba dawowa dake ba har sai an daura mun Auren ki , don haka ki bar Wannan Asarar Hawayen naki ,Bazan taba mai daki Gidan Daddy ba , Kin bar gidan kenan .
Sannan na biyu kuma matsalar idan kika Auri Nawaaz shi matsayin mijin ki ,Nima kuma haka yake , Saboda tun da nayi mu'amala dake Ban ƙara cin karo da macen dana ji zata iya Dauka na ba kaman ki