Showing 69001 words to 72000 words out of 101092 words

Chapter 24 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37781

shi a gefen shi,........ 🖊





*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*




5⃣7⃣&5⃣8⃣



Sundade a wajen suna hira a tsakanin su kafin ya tafi domin ganin mata sai tururuwa sukeyi suna shiga gidan wanda yasan is impossible ya iya shiga ciki again,
Momy ma sai da ta dade kafin tabar gidan kamar kar ta tafi takeji tayi ta rike d'an jikan ta,
Baba ma ya dawo yaga jikan shi bakin shi har kunne rai yagani, su HAJARA da Husna sune masu girke girke domin Y'an barka, ta saki jiki sosai domin taga yanda baba ya ji mugun dadin ganin ta saki jikin ta ta kara kyau da cikowa saboda ta kwantar da hankalin ta, ita kanta wani irin Alfahari takeyi da rayuwar ta a yau, da ta kuma bijirewa da Allah Kadai yasan Abinda zata fuskan ta yau,
Taga jarabawa saboda bijirewa iyaye da tayi a farko ilimin ta bai Amfane taba wayewar ta tatashi abanza,

Don haka Alhmdulillah yau gata cikin gatan ta kowa ya saki jiki da ita ba wani kyara ko tsana, sai dare mijinta yazo suka tafi bayan yazo yaga baby sai wani irin rawar jiki yakeyi akan HAJARAr saboda shikan shi yasan tafi karfin rayuwar shi nesa ba kusa ba tunda shi daga ilimin primary bai kara ko ina ba ita kuwa almost degree qualification takeda duk da tajawa kanta, Husna ma Aliyu yazo sun wuce, a ranar dady yazo yaga jariri harda dunkulalliyar kyauta saboda farin ciki,
Al Ameen ma sai karfe goman dare ya iya dawowa gidan domin yasan dai kowa yabar gidan yanzu,
Har dakin ta ya shiga, lokacin ta shirya kwanciya, yaron na kwance cikin kayan sanyi farare,
Ya shigo da Sallama, ta dago idanun ta tareda Amsa wa ta saki Ajiyar zuciya tareda murmushi, "welcome Abba tafada da kalar tsokana,

Saida ya sunkuci yaron ya zauna a gefen ta " bawani Abba bayan kunyi min wuyar gani, trough out tunanin ku nakeyi, hope ba a jagwal gwala min yaro da yawa ba, yafada yana kissing dinshi,
" ya kam sha dauka yau, saurin taba goshin shi yayi, " gashi har jikin shi na zafi, gaskiya gobe zanyiwa Inna magana kar wadda tazo ta daukar min yaro,
Kallon shi tayi tana dariya " zaka iya? Watch and see, zaki gani,


D'an matse fuska tayi domin ita kanta wani irin zazzabi takeji saboda cikowar nonuwan nata da sukayi,
Kallon ta yayi yaga tana dafewa, " lafiya madam maman baby?
" nono na, tafada, wanda saida yaji Kalmar har Kasan kafar shi, ya wani irin dashe murya, "me ya sameshi? "Sun ciko suna min ciwo har zazzabi nakeji,
Juyawa yayi ya ce " bashi to yasha zasu rage cikar kiji sauki, yafada yana tsurawa kirjin ido domin yana so yaga yanda sukayi,

A hankali take daga rigar tareda ciro shi, ya zubawa niple din da suka kara fitowa saboda fitowa,
Dora mata yaron yayi yace bashi yasha inyi mai huduba yafada duk idanun shi sun k'ank'ance, ya mugun dauriya yana dauke kanshi saboda yasan bai dace ya yi wani Abu a gidan surukai ba gata cikin d'an yan jego, don haka bai dade ba ya tafi bayan ya yiwa d'an shi huduba da Abubakar, suna mai daraja da girma Amini ga ma aiki S. A. W,


Ya dade a mota kafin ya wuce yana hamdala da aka dauke ta don yanaji a jikinshi in suna tare zaiyi aika aika Ashe iyaye na da tasu hikima na dauke mace a haihuwar farko, yana taimakawa ta fuskoki daban daban,

Washe gari aka kawo ragunan kauri da akwatunan kayan barka irin dai hidima ta Al adar sakkwatawa wanda kowa yasan suna kashe kudi a wanna fage bana wasa ba,
Kafin Yazo mata da Albishir mafi dadi a rayuwar ta domin jin dadin haihuwar Abubakar Sadiq da tayi, na farko Admission dinta to school of science and technology domin cikar burin ta sai kuma takardun wani d'an madai daicin gida da yace ta bawa Hajara su koma da mijin ta Wanda yasan hakan zai faran ta mata sosai,

Ai kuwa ta koka sosai saboda farin ciki ta rungume shi gam tana kara godewa Allah da ya bata miji irin shi gaba daya yagama zama gatan ta farin cikin ta miji nagari Abin Alfaharin kowace mace a rayuwa, don haka itakam tana Alfahari da Auren biyayya da tayi gashi Akullum tana ganin Alkhairi tako wane gefe, me yafi wainnan Abubuwan farin ciki a rayuwar ta cikar burin ta farin cikin Y'ar uwar ta, don tasan Hajara yau zatayi farin ciki sosai,


Tayi godiya har ta rasa bakin gode mai karshe cafke bakin shi tayi tana bashi Lafiyayyan kiss, saida ya kwace kanshi yana maida numfashi, " no madam kibar irin wannan godiyar har mu koma gidan mu Amma yanzu if you countinue zan iya loosing control, guiwar ta tasa a kasa tareda rike hannun shi tace "Allahu ya kare min kai ya kuma kara buda maka ya baka Aljannah madauwa miya mijina,


Share mata hawaye yayi tareda girgiza kai, " you no what? Girgiza kai tayi " bantaba jin wani farin ciki ba fiye da yau, saboda nayi miki Abinda ya faran tamiki Zuciya har kina kuka that's means kina son karatun nan fiyeda tunani? " yes tafada tana rungume shi, amma farin cikin biyu ne da yaya HAJARA nasan zatayi farin ciki sosai yau Wallahi,
"Umm ki ce mata ta sa me gidan ta ya neme ni a waya inbashi wani aiki ya Ajiye wannan saboda inganta rayuwar su,

And baba Dady ya biya musu hajji bana shida Hajara dasu inna dasu Husna da Aliyu ma, don haka Karki sumar min ni natafi, yafada yana barin gidan cikeda farin cikin ganin murnar matar tashi,
Wanda tazama speechless a a wurin yau su inna zasuje hajji harda yaya HAJARA dasu yaya Aliyu, Allahu Akbar,
Wani irin kabbara ta buga tareda fita a guje zuwa dakin inna da mutane ke ciki ta fada jikinta tasa kukan dad'i,

Saida ta tsorata inna da jama'ar wurin, saida taga duk sun rude tace yi hakuri inna kukan dadi nakeyi zakuje hajji kuda su baba dady ya biya muku ni kuma zanci gaba da karatuna inna ga takardun gidan yaya HAJARA kuma, ta mika mata duk ta rikice,

Ai tuni kowa yafara tayasu murna inna ma harda kwalla tace dole a kira baban ku gaskiya, wannan gida dai haka aka wuni ana murna, inna ta dauki Sadiq tana Kiran shi Mai babban suna mai goshin Alkhairi Allah ya rayaka Akan sunnah d'an nan ka tsotsa nonon Albarka d'an nan,
Wanda Kalmar saida ta taba RAHAMA, sosai wato halin mutum nabin ya'yan shi Allah yakara mana hakuri da hali na gari da juriya domin gamawa da wannan duniya lafiya,


Hajara kuwa ai kuka wiwi tayi ranar gida hajji ga wani Albishir duk a dalilin Auren da ta bijirewa, Allah na sonta da RAHAMA datayi saurin dawowa hayyacin ta da batasan irin jarabawar da zata fuskanta ba, number Al Ameen ta karba ta kirashi tareda kiran bello tafada mai, ai shima barin wurin aikin shi yayi yazo gidan, yayi wa RAHAMA godiya kafin ya karbi number Al Ameen shima yakira yafara godiya, yace yaje ya sameshi a office domin ana gama suna yanada tafiya agaban shi, don haka ba bata lokaci ya tafi, Wanda yabashi manager a wani katon farm house dinshi wanda yayi Alkawarin biyanshi Albashi mai tsoka, don haka Bello ya kira HAJARA da kyautar Allah a gareshi domin ta zama Alkhairi a tareda shi tareda shiwa ladidi Albarka data hadasu domin ta tozarta Rayuwar HAJARA saigata tazamo Alkhairi atare da shi sanadin ta zaifara murza mota duk da ta gidan gonar ce zata dawo hannun shi domin jigilar kaida kawo, don haka dole yaje yawa ladidi godiya daga nan,



Tayi matukar mamakin jin ana kiranta wani a waje domin Abinda take nema kenan yanzu miji any how Mr Available kawai yazo tabar rayuwar gidan su da take cikeda yunwa kowa ya nemo ya ciyar da kanshi, dama HAJARA ce ke d'an janyo mata farin jini insuna tare tana samun mashin shini yanzu kuwa dif na kashewa ma gagarar ta yakeyi saidai ta sata a wurin innar su wata rana,
Don haka tanajin ana kiran ladidi ta fara washe baki ta fara kwaskwarima,
Ta fito, tayi mamakin ganin bello, saidai tayi saurin natsa kanta don tsoro yake bata don ba karamin duka ya narka musu ba ranar nan,

Ganin yanda yake fara a yasa ta saki jiki, " Aa Alhaji bello kaine a gidan mu? Wani irin kara washe baki yayi yace "kai dole inkara miki tukuici don ke kirani Alhaji dut da bani zani makka ba matata zata nima Alhaji nike inda rai da Nisan kwana don haka gashi, yaciro dalleliyar dubu guda yabata,
"Wallahi da mugun takaici kika bani Amma yanzu kewanke fess, saboda keyi sanadin hadani da, mace mai kafar Arziki, Nasamu aiki Nasamu gida gata zata makka don haka kijira inasata ta kawo miki Alkyabba me cada......... 🖊




"Hassada ga mai rabo taki don haka don't worry bout your enemies, suna maka hassada kullum kana kara cigaba a rayuwar ka, kaidai ka tsarkake zuciyar ka ka kyale kowa,


*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*




5⃣5⃣&5⃣6⃣


Shigowar mai aikin ta ne ya sa ya fara dawowa cikin natsuwar shi, da yake ba yarin ya bace ta ga Alamar nakuda RAHAMA keyi don haka takasa sukuni koda ta sauka dole tasa ta dawo saman, kuma ta na shigowa taji kukan jariri, shiyasa ta karasa dakin da gudu taganshi zaune dumu dumu cikin jinin shima ga jariri a kan jikin shi duk ya rude saboda farin ciki, sai surutai yakeyi,
Da gudu ta karaso tace "masha Allah hajiya kin sauka cikin sauki akwai reza a yanke cibi?
Nuna mata drower tayi ta ruga ta ciro sabuwar reza ta dawo tareda cewa "ranka ya dade kawo jaririn mugani saika je ka gyara jikin ka, karbar yaron tayi tubarkallah dashi katoto mai hasken ubanshi ta yanke cibiya shikuwa ya matsa gaban RAHAMA ya na shafa kanta,

He is speechless, sai wasu irin kwalla da kawai suka biyo kuma tunshi, "the most happiest day ever in my life yafada cikin wani irin emotional look, kallon jikin shi tayi tana dan matse baki saboda ciwon marar ta dake d'an tsilga mata, " kaje kayi wanka ka canja kaya duk jini,
" oh common its my blood fa me zanji kyama a wurin I couse you this blood my wife, waigawa yayi yaga har ta yanke ta dakko zani ta nade shi a ciki, ta ajiyeshi a gadon kafin ta ce "ranka ya dade bari mu gyara dakin ko,


Mikewa yayi ya matsa kusa da D'anshi ya shafo fuskr shi tareda bashi kiss a kumatu ya fita yana waigen uwa da d'an duka, wayar shi ya dauka ya bar dakin yana Kiran momy, tana dagawa cikeda zumudi da murna yace " momy ta haihu fa, zabura momy tayi dake zaune tana sana'ar tata.
"Alhmdulillah Alhmdulillah, tana ina yanzu me aka samu? Duka ta jero mai, "muna gida momy ai a gidan ta haihu, yafara jefe mata yanda akayi,

Tsabar haushi kashe Kiran tayi tayi daki tareda daukar mayafi da jakar ta tana tafe tana fada, ta kira Dady tafada mai haihuwar shima farin ciki kamar yayi me sai masha Allah yake furtawa,
Kashe wayar tayi, driver ta kira ya tuka ta zuwa gidan nasu ta matsu batayi ido biyu da Al Ameen ba taci mutuncin shi,


Gefen RAHAMA kuwa mai aikin ta gyara kasan fes batareda ta taba taba domin tasan bai kamata tace zataga tsiraicin taba, tadai bata Auduga da sabon pant domin tsayar da jinin,
Koda momy ta iso Al Ameen na nan kwakume da jaririn da ko wanka ba ayi mai ba andai nade shi a zani,
"Toh shugaban mashiririta tashi ka fita inna gama Abinda nakeyi zamu gauraya dakai, ya sungimi d'an zai fita tareda matsawa zai shafa kan RAHAMA,

"Kabani yaron ka wuce ko kuwa, dariya yayi ya mika mata yana "nifa banma san me aka samu ba kawai naga jini na, "Fita nace mara kunya, ta buga mai tsawa " na wuce momy afuwan, ya fada tana juyawa ya kalli RAHAMA da ke d'an matse ciki da fuska, " baby ko akwai wani ne.... " fita nace ko ranka ya baci sakarai kawai,
Ya fice farin ciki fal zuciyar shi, ya fara Kiran Aliyu yafada. Mai kafin baba bala kowanne su kamar ya zuba ruwa akasa, Aliyu na fadawa Husna ta mike ta ce ai yanzu zata tafi , yafara dariya "haba maman baby kijira zuwa gobe mana, bata rai tayi ta zabura tana buga kafa " nidai ko bazaka kaini ba kabar ni intafi dakai na please, tafada cikeda shagwaba,
"Maida wukar hajiya muje, yafada yana rungume ta, Amma naso ace kin bari zuwa gobe kinga yau lokaci nane ko? "Sorry zanbiya I promise, "ok ma'm,


Momy ta gyara yaron tsab namiji mai kama da tsohon shi tana shirya shi fuskar shi kamar gonar Auduga saboda farin cikin ganin jikinta a duniya, bata haihu da yawa ba Amma tana fatan su RAHAMA su cika mata gida da jikoki,
Saida ta shirya su duka kafin ta fita zuwa kitchen ta nema mata Abinda zata dumama gurbin haihuwar gashi da Alamu RAHAMA na fama da ciwon mara na haihuwa,
Saida ta dage kafin ta ci Abinci sosai, tana ta fada, " kici ki rufe gurbin wannan shirgegen yaron da kika sullubo ki gama muje Asibiti a duba lafiyar ki daga nan kawai a wuce dake gida don innace zanbarki da wannan mashiriri cin rubewa zakiyi baisan komai ba bai kuma iya komai ba, tafada tana Hararar shi da ya shigo,

"Ni momy me nayi wai bayan tare mukayi nakudar, ko baby? Yafada yana kallon RAHAMA, harara ta watsa mai domin yanzu ta hadu da barnar maza wani haushi yake bata musamman lokacin da take nakuda gashi bai san ta inama zai taimake taba saboda rudewa, da tanada halin yin dariya da tayi musamman lokacin da d'an ya fado yayi kamar idanun shi zasu fado saboda shocked,

Waro idanu yayi ganin irin Hararar da ta watsa Mai, yace " I deserve it a hankali yana wata irin dariya kasa kasa, "ai dole ki harare ni nasa kin sunkuto wannan katoton yaron yafada cikin zuciyar shi, jin kanshi yake a sama yau yazama dady shima,


Saida ta ci ta Koshi momy ta miko mata yaron bude ki bashi yasha mu tafi Asibiti,
"Me zata bashi yasha inji Al Ameen dake zaune yaki fita duk fadan momy, hakura tayi ta kyale shi, " ubanka zata bashi kaji, " ke kuma ki biyewa wannan mashiriri cin wata rana zaki ji jiki ace kina jin nakuda ki kasa kirana Kifada min kika zauna tareda wannan da baisan komai bs badon uwale na kusa ba da Allah kadai yasan me zai faru,

Sosa keya yayi " ai momy nayi mugun kokari yaron na fadowa na sunkuce shi kar sanyin tiles ya taba shi, " ita kuma uwar d'an fa? Kazo ka tasa ya a gaba bakayi tunanin Kiran kowa ba don iya shege, toh ka kwashe kayan ta kabawa driver ya tafi dasu gidan nasu daga Asibiti gida zan wuce da ita don kasani,

Wani irin hade rai yayi kadan yanzu yake da ya sani da ya Amince zai bari ta tafi gida wani wanka,
Ganin yanda ta daga riga tareda zaro breast daga bra zata bawa yaron yasa ya hadiye wani irin miyau mukut na kwadayi yanzu shikenan bashi kadai keda shiba, matsawa yayi gefen ta ya zauna lokacin da yaron ya kama ta runtse idanun ta gam saboda zafi,
Abin ya mugun burgeshi, matar shi da dan shi a yau a cikin gidan shi tana breast feeding dinshi, meyafi wannan burgewa,

Ganin yana shirin zama yasa momy komawa kitchen domin duba Abinda ta dora ta basu wuri domin tasan ba wai kunyar ta Al Ameen din kejiba don haka ya sa ta kauce, zuba mata ido yayi cikeda wani irin so sa shauki jinta yake har cikin tsokar jikin shi,
"Me zan nema sama da wannan baby? Mace tagari ya'ya nagari nasani zan samesu a karkashin inuwar mace tagari da nakeda ita, yafada yana shafo fuskar kyakkyawan d'an shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login