Showing 66001 words to 69000 words out of 101092 words

Chapter 23 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37774

da tafi kowacce tashin hankali a wurin da namiji sama da rashin lafiyar mazakuta, domin inhar bakada wannan lafiyar tofa kayi mutuwar tsaye, shi kam Alhmdulillah iyayen shi sunyi iyakar kokarin su da lokacin da zai san Amfanin ta bazata yi mai aiki ba,
Sai kusan tara suka bar gidan,
Sai gidan su, ranar kam dole ya daga kafa domin yaga Alamar gajiya a tattare da ita,


******************************

Bayan wata uku lokacin Cikin Rahama yakai wata uku, zama dakyar tashi da dabara Al Ameen yagama shirya komai saboda zumudi dakin yara ma antsara shi sosai anzuba gado da kayan wasanni Kala Kala,
Anata fama yabarta zuwa wankan gida ya murzawa idanun shi toka, kuma wani lokaci ba komai iyaye kewa gudu ba, idan har baka samu wankan farko mai kyau ba to daga baya kana iya fuskantar matsala, amma fir yaki Dady ma yaki bari su hadu domin yasan neman shi yakeyi,
KO gidan momy ya yanke zuwa saboda kullum zancen ta daya ne, ita kanta RAHAMA tafison taje gidansu domin itace damar ta takarshe da zata je gidan Inna ta zauna,

Tana matukar son ta saka baki Amma tasan fushi zaiyi idan ta rokeshi yabar ta zuwa wankan zaice dama batason shi shiyasa ta ke son ta gudu tabar gidan shi, domin wannan gorin rashin so bai daina fadar shi ba har gobe,
Idan ya tuna da zancen ta da HAJARA na cewa itama bason zaman gidan shi takeyi ba, wanda a lokacin tana cikin fargabar zama a gidan shi, ga fitinar HAJARA a lokacin na son Al Ameen dole tasa ta fadi Kalmar,


A zaune take a falon ta mike kafar ta tunanin ta yayi nisa ya shigo har saida ya zauna a gefen ta ya shafo fuskar ta tayi saurin juyowa tareda Ajiyar zuciya ta sakar mai murmushi,
"Me ake tunani maman Y'an biyu? Yafada yana kai hannun shi kan katon cikin ta, bata rai tayi " kadaina yimin fatan biyu mana, ko yanzu fa a mugun tsorace nake wallahi inna tuna dole sai wannan abin ya fito,

Dariya yayi tareda zama a kasan gab da ita " sosai kuwa tunda na saka dole yafito, Amma kuma tare zamuje haihuwar zantaya ki, " ai da zaka iya taya ni mika maka zanyi saika haifeshi, "Haka Allah ya tsara mu mu saka ku ku kenkyashe,
Now fadamin me kike tunani? Nasan ba wani haihuwa kike tunani ba, " yes ina tunanin zuwa gidan Inna ne in haihu please karka fassara ni kaga kowa haka yakeso domin ba wanda zai iya tsayawa dani kuma haihuwar farko ce,


Gyara zama yayi batareda ya bata raiba yace " kina so kije? Daga mai kai tayi tareda marai rai cewa, " ok mufara hada kayan ba damuwa bayan haihuwar zanyi Tafiya zuwa China oder wasu kayan company na da na dady don haka no problem, Amma sai kin haihu zan iya daurewa na sati daya bakya tare dani Amma ana gama suna zan gudu,
Cikeda farin ciki tace godiya nakeyi,



Sun shirya komai na Tafiya wankan ya fadawa momy ya yarda taje wankan gidan momy tayi matukar mamakin canjin Al amarin, wanda sai daga baya ta gano akwai Tafiya a gaban shi shiyasa yayi saurin sakkowa,
Yau kamar anyi ma RAHAMA wahayi da yin aiki tunda safe ta tsiri sanitation din gidan ta harda gyara tsarin dakin baccin ta wanda ta dade batayi aiki irin wannan ba, saida ta gama tsab bayan ta yafara Amsawa tuni ta samu wuri daya ta zauna tana cije lebe, koda mai akin ta ta leko taga yanda take gumi taji tsoro tareda matsowa cikin rawar jiki, " hajiya dama aiki kikeyi baki kira na tayaki ba gaki da nauyi kika hau aiki irin wanna?


Dakyar ta ke daga kanta a yanzu Domin ciwon da gaske yakeyi, wani irin rikewa marar ta keyi kafin taji d'an shin wani irin ruwa na bin ta, cikin karfin hali tace bani waya ta, da sauri ta dakko tace duba min number mijina itace farko a dial call,
Kiran shi tayi yana dauka yafara magana " gani a kofar gidan ki habibty, ya datse call din domin ya shigo gidan shi,

Zamewa tayi tareda nunawa mai aiki ta fita, ta fara murkusu su tareda juyi so take ta mike tsaye Amma wani Abu ya tokare ta ya hana ta mike,
Da fara'ar shi ya shigo tareda cewa ina maman biyun..... Saurin karasowa yayi da gudu yana lafiya? Domin tun shigowar shi ya hango halin da take ciki, kokarin daga ta yakeyi, "please ka kaini Asibiti haihuwar ce ruwa na zuba tafada mai cikeda dauriya,
Saida yayi kokarin tsayar da ita yaga yanda ruwan kebin kafafun ta, tace ya cire mata pant din jikinta yana damun ta,
Saurin daga doguwar rigar tata yayi ya zame pant din da yariga ya jike ya nufi wurin da take Ajiye hijab din sallar ta, cikin tsananin rudu da tausayin yanda take cije lebe,


Yana juyowa yaga ta na kokarin durkusawa, da gudu ya wurgar da hijabin ya rugo " baby daure mu wuce Asibiti kinji Allah zai sauke ki lafiya kinji,

"Abu zai fito.... Tafada da karfi cikin fisgo da zancen domin tanajin yanda Abun ke kun no kai wanda dole ta ware duk da batasan yanda akeyi ba, ganin yanda take numfashi da nishi yasa yasa duk ya furgice, kafin ma ya nemi mafita yaji kukan jariri,

Gashi tsaye kamar gunki, kasan ya Kalla yaga katon jariri yayi saurin zubewa gaban ta yana ware ido, tareda sungumar dan da cibiya da jini da komai bakin shi na rawa " kin haihu baby????? Allahu Akbar yafara jerowa batareda sanin Abinda zaiyi ba, Allah ya taimake ta mabiya ma tafado ta baje a wurin tana maida numfashi,
"Ka kira momy kafada mata kaga yanke cibi bamu iya ba,
Shi ina ma yasan inda hankalin shi yake yana cikin farin ciki........... 🖊





*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*




5⃣5⃣&5⃣6⃣


Shigowar mai aikin ta ne ya sa ya fara dawowa cikin natsuwar shi, da yake ba yarin ya bace ta ga Alamar nakuda RAHAMA keyi don haka takasa sukuni koda ta sauka dole tasa ta dawo saman, kuma ta na shigowa taji kukan jariri, shiyasa ta karasa dakin da gudu taganshi zaune dumu dumu cikin jinin shima ga jariri a kan jikin shi duk ya rude saboda farin ciki, sai surutai yakeyi,
Da gudu ta karaso tace "masha Allah hajiya kin sauka cikin sauki akwai reza a yanke cibi?
Nuna mata drower tayi ta ruga ta ciro sabuwar reza ta dawo tareda cewa "ranka ya dade kawo jaririn mugani saika je ka gyara jikin ka, karbar yaron tayi tubarkallah dashi katoto mai hasken ubanshi ta yanke cibiya shikuwa ya matsa gaban RAHAMA ya na shafa kanta,

He is speechless, sai wasu irin kwalla da kawai suka biyo kuma tunshi, "the most happiest day ever in my life yafada cikin wani irin emotional look, kallon jikin shi tayi tana dan matse baki saboda ciwon marar ta dake d'an tsilga mata, " kaje kayi wanka ka canja kaya duk jini,
" oh common its my blood fa me zanji kyama a wurin I couse you this blood my wife, waigawa yayi yaga har ta yanke ta dakko zani ta nade shi a ciki, ta ajiyeshi a gadon kafin ta ce "ranka ya dade bari mu gyara dakin ko,


Mikewa yayi ya matsa kusa da D'anshi ya shafo fuskr shi tareda bashi kiss a kumatu ya fita yana waigen uwa da d'an duka, wayar shi ya dauka ya bar dakin yana Kiran momy, tana dagawa cikeda zumudi da murna yace " momy ta haihu fa, zabura momy tayi dake zaune tana sana'ar tata.
"Alhmdulillah Alhmdulillah, tana ina yanzu me aka samu? Duka ta jero mai, "muna gida momy ai a gidan ta haihu, yafara jefe mata yanda akayi,

Tsabar haushi kashe Kiran tayi tayi daki tareda daukar mayafi da jakar ta tana tafe tana fada, ta kira Dady tafada mai haihuwar shima farin ciki kamar yayi me sai masha Allah yake furtawa,
Kashe wayar tayi, driver ta kira ya tuka ta zuwa gidan nasu ta matsu batayi ido biyu da Al Ameen ba taci mutuncin shi,


Gefen RAHAMA kuwa mai aikin ta gyara kasan fes batareda ta taba taba domin tasan bai kamata tace zataga tsiraicin taba, tadai bata Auduga da sabon pant domin tsayar da jinin,
Koda momy ta iso Al Ameen na nan kwakume da jaririn da ko wanka ba ayi mai ba andai nade shi a zani,
"Toh shugaban mashiririta tashi ka fita inna gama Abinda nakeyi zamu gauraya dakai, ya sungimi d'an zai fita tareda matsawa zai shafa kan RAHAMA,

"Kabani yaron ka wuce ko kuwa, dariya yayi ya mika mata yana "nifa banma san me aka samu ba kawai naga jini na, "Fita nace mara kunya, ta buga mai tsawa " na wuce momy afuwan, ya fada tana juyawa ya kalli RAHAMA da ke d'an matse ciki da fuska, " baby ko akwai wani ne.... " fita nace ko ranka ya baci sakarai kawai,
Ya fice farin ciki fal zuciyar shi, ya fara Kiran Aliyu yafada. Mai kafin baba bala kowanne su kamar ya zuba ruwa akasa, Aliyu na fadawa Husna ta mike ta ce ai yanzu zata tafi , yafara dariya "haba maman baby kijira zuwa gobe mana, bata rai tayi ta zabura tana buga kafa " nidai ko bazaka kaini ba kabar ni intafi dakai na please, tafada cikeda shagwaba,
"Maida wukar hajiya muje, yafada yana rungume ta, Amma naso ace kin bari zuwa gobe kinga yau lokaci nane ko? "Sorry zanbiya I promise, "ok ma'm,


Momy ta gyara yaron tsab namiji mai kama da tsohon shi tana shirya shi fuskar shi kamar gonar Auduga saboda farin cikin ganin jikinta a duniya, bata haihu da yawa ba Amma tana fatan su RAHAMA su cika mata gida da jikoki,
Saida ta shirya su duka kafin ta fita zuwa kitchen ta nema mata Abinda zata dumama gurbin haihuwar gashi da Alamu RAHAMA na fama da ciwon mara na haihuwa,
Saida ta dage kafin ta ci Abinci sosai, tana ta fada, " kici ki rufe gurbin wannan shirgegen yaron da kika sullubo ki gama muje Asibiti a duba lafiyar ki daga nan kawai a wuce dake gida don innace zanbarki da wannan mashiriri cin rubewa zakiyi baisan komai ba bai kuma iya komai ba, tafada tana Hararar shi da ya shigo,

"Ni momy me nayi wai bayan tare mukayi nakudar, ko baby? Yafada yana kallon RAHAMA, harara ta watsa mai domin yanzu ta hadu da barnar maza wani haushi yake bata musamman lokacin da take nakuda gashi bai san ta inama zai taimake taba saboda rudewa, da tanada halin yin dariya da tayi musamman lokacin da d'an ya fado yayi kamar idanun shi zasu fado saboda shocked,

Waro idanu yayi ganin irin Hararar da ta watsa Mai, yace " I deserve it a hankali yana wata irin dariya kasa kasa, "ai dole ki harare ni nasa kin sunkuto wannan katoton yaron yafada cikin zuciyar shi, jin kanshi yake a sama yau yazama dady shima,


Saida ta ci ta Koshi momy ta miko mata yaron bude ki bashi yasha mu tafi Asibiti,
"Me zata bashi yasha inji Al Ameen dake zaune yaki fita duk fadan momy, hakura tayi ta kyale shi, " ubanka zata bashi kaji, " ke kuma ki biyewa wannan mashiriri cin wata rana zaki ji jiki ace kina jin nakuda ki kasa kirana Kifada min kika zauna tareda wannan da baisan komai bs badon uwale na kusa ba da Allah kadai yasan me zai faru,

Sosa keya yayi " ai momy nayi mugun kokari yaron na fadowa na sunkuce shi kar sanyin tiles ya taba shi, " ita kuma uwar d'an fa? Kazo ka tasa ya a gaba bakayi tunanin Kiran kowa ba don iya shege, toh ka kwashe kayan ta kabawa driver ya tafi dasu gidan nasu daga Asibiti gida zan wuce da ita don kasani,

Wani irin hade rai yayi kadan yanzu yake da ya sani da ya Amince zai bari ta tafi gida wani wanka,
Ganin yanda ta daga riga tareda zaro breast daga bra zata bawa yaron yasa ya hadiye wani irin miyau mukut na kwadayi yanzu shikenan bashi kadai keda shiba, matsawa yayi gefen ta ya zauna lokacin da yaron ya kama ta runtse idanun ta gam saboda zafi,
Abin ya mugun burgeshi, matar shi da dan shi a yau a cikin gidan shi tana breast feeding dinshi, meyafi wannan burgewa,

Ganin yana shirin zama yasa momy komawa kitchen domin duba Abinda ta dora ta basu wuri domin tasan ba wai kunyar ta Al Ameen din kejiba don haka ya sa ta kauce, zuba mata ido yayi cikeda wani irin so sa shauki jinta yake har cikin tsokar jikin shi,
"Me zan nema sama da wannan baby? Mace tagari ya'ya nagari nasani zan samesu a karkashin inuwar mace tagari da nakeda ita, yafada yana shafo fuskar kyakkyawan d'an shi, tareda kallon yanda yake zukar nonon, d'an cire bakin shi yayi tareda kama kan nonon yadan matsa kadan yana cewa " wai har ruwa ya fito? Ikon Allah yafada yana kallon Abin kamar zaisa baki, "baby shikenan yanzu ya zama banawa ba,

Bata kai ga bashi Amsa ba momy ta shigo da Sallama, wanda yayi saurin waskewa ya saki nonon tareda d'an matsawa, tayi dariya a kasa, ganin yan da ya yi saurin matsawa, inya gama tashi mutafi momy ta fada, saurin cire bakin tayi wanda yaron yasanya kuka saboda ana mai wasa da Abinci, saurin karbar shi yayi yana cewa sorry sorry my boy momy ne ta fisge mana Abinci kyaleta zamu raba, yafada yana zura mai halshen shi cikin baki, yakama tamau yana tsotsa yayi tsit Abinshi,

Momy tace "wannan zamani akwai kallo ikon Allah yanzu yaran zamani sai abarsu wallahi, hijabin ta mikawa RAHAMA da katuwar suwaita yaron ma aka nadeshi cikin blanket na yara mai taushi, ta rungume shi suka fita shi da kanshi ya tuka su zuwa tsadden Asibiti, aka dubasu duka lafiya ita ma ba wata karuwa tayi sosai ba, suka bata Allurai da suka kamata da magun guna, kafin suka wuce da ita gidan Inna wanda da za a tona zuciyar Al Ameen bakikirin take saboda haushi yanzu yanaji yana gani za a tafi mai da mata da yaro ya koma gauro gaskiya akwai matsala Babba gwara yayi yayi yabar kasar nan inba haka ba zasuga rashin kunyar shi,



Inna tuni ta gyara dakinsu tsab ansa tsohon gadon ta dama a ciki ta dora ruwan zafi baba yakawo kaji saboda murna yace a figesu a zabga a tukunya kafin me jego ta iso, HAJARA da tuni ta iso gidan inna domin inna ta fada mata nan za a kawo ta wanka, ita ta zage tana zabga girki da gyare gyare, isowar su kuwa murna fal cikin kowa inna tayiwa momy maraba tareda zolayar ta "gaskiya hajiya Aisha kinayin wannan miji tunda yau kika biyoshi har gidan Amaryar shi, " ai Kedai larai bari dole in taho Karki kwace min miji, toh barkan mu da samun wannan Abun Alkhairi, suka fara gaisawa kafin Al Ameen ya fara shigo da kayan da driver ya kawo, kayane birjik kafin yasa shi ya shigoda kayan Abinci harda ruwan sha cartons aka rika saukewa saida inna tafara fada


Yana gama shigowa dasu Hajara na fitowa, sukayi clashing, tayi saurin sauke kanta kasa ta kasa cewa komai domin Allah yagani batason su hadu ma da shi domin irin watsuwar da ta bugamai a farko,
Waskewa yayi da yake d'an duniya ne " aa yaya Amarya Ashe har kin iso taron d'an naki, yafada cikeda son ya sa tasaki jiki tareda manta shirmen baya, ta d'an dago kai ta gaida shi cikeda jin kunya tamai barka ta shige dakin jegon da su inna ke ciki,


Husna ma sun iso tana ta zumudin daukar baby tareda murna kowa ma bata gani a gaban ta sai d'an ta,
"Aunty RAHAMA yaya ya miki wayau wallahi, duk ya kwashe fuskar shi,
Tafada Aliyu ma shigowa yayi yaga baby sannan yafita yasamu Al Ameen a mota yayi shiru,
Dafa shi yayi " hy brother inlow, yadai? " kaidai bari wai yaushe za a daina wannan al adar daukewa mutum mata idan ta haihu?
"Sai mun koyi Unguwar zoma dakan mu inajin koda sun taso muce mun iya, amma fa ni bazan yarda Husna ts koma wankan gida ba gaskiya, "tab wallahi baka isa ba yanda aka rabani da matata kaima sai kaji yanda nakeji,

" nifa yayan matar ka ne Al Ameen, "ni kuma fa,? Yafada yana kallon shi cikeda haushin zaman nan da yake ba d'an shi da matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login