Showing 57001 words to 60000 words out of 101092 words

Chapter 20 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37791

yace su tafi,
Tareda fada musu inda zasu kaishi,


Kiran yaya HAJARA Tayi tace "yaya banganki ba? " ai ni Naganki sister kiyi hakuri I can't show my face in front of your husband, kunyar shi nakeji Rahama but kin hadu ba kinfito kun haska you look perfect and classy Mrs Al Ameen,
Kin dagawa mata hankali kanwata I feel proud of you today,
Tafada cikin sakewa da tsokana, tuni zuciyar RAHAMA tayi sanyi ta saki jiki suka d'an yi magana kafin ta kashe wayar,
Ta jingina jikin shi tana jin wani irin farin ciki,


Har saida suka isa wani kayataccen Asibiti, driver ya faka suka fito ya riketa suka shiga ciki, sanin shi waye nan da nan aka kula dasu tareda basu umarnin shiga cikin ofishin likita kai tsaye, ya mike cikeda girma mawa yamai barka da zuwa " ranka yadade kaida kanka? " eh madam nakawo batajin dadi,
Cikin rawar jiki ya kira nurse tareda bata umar nin dibar jinin RAHAMA domin yin test Domin gano matsalar, ya bawa Al Ameen wurin zama ya ce ya jira adiba jinin ta, diba akayi dakyar ta yarda aka soka mata Allura har saida ya rike ta aka diba yana dariya bai taba ganin rakin taba sai akan Allura,

Suka dan jira na minti talatin Abinka da komai a zama nan ce akeyi aka kawo mai result, ya duba Tareda mikewa cikin farin ciki ya mikawa Al Ameen hannu,
" congratulations sir madam nada juna biyu na kusan four weeks,

Yafada cikin murnar zaiyi wa A yabo Albishir na first egg din shi a duniya duk ya kosa yaga reaction dinshi, ai kuwa mikewa Al Ameen yayi tareda kallon likitan da kyau " are you sure? Tell me how is that possible doctor ciki? My son, yafada a rude yana daga Rahama, " are you feeling something in your belly? Please are you feeling my baby,?

Ya fada a rude duk yarasa inda zai tsoma ranshi, wasu irin hawaye ne duka biyo fuskar RAHAMA," cikin Al Ameen a jikin ta, Al Ameen dai he is out of his mind kara tanbayar likita tareda zaro kudin dake pocket dinshi kab ya ajiye mai " kaduba ta da kyau I can pay any price doctor just ka tanbbatar min da cikin matata don Allah don't make me dream of it in tashi inga bacci nakeyi,


"That's the truth ranka ya dade blood test ne mukayi kuma baya kuskure don haka Ina tayaka murna Allah ya inganta,
"Allahu Akbar ya fada tareda yin sujada ya godewa Allah tareda mikewa ya daga ta cak ya rungume, yana tank you tank you tank you baby kin gama min komai wallahi,
Likita sai dariyar rude war Al Ameen yakeyi,
Ya Mai godiya tareda bashi hakuri bai da cash a jikin shi sosai that's all he have ya juye mai, yace ya jira surprise,
Ya cirata sama cak suka fita,


A hankali yake Tafiya da ita duk kunya ta gama rufeta domin kowa kallon su yakeyi
Har saida ya isa wurin motar shi driver yayi saurin bude mai ya Ajiyeta kamar kwai tareda warning driver, ya tafi a hankali dasu,

Kiran momy ne ya katse mai farin ciki " kai lafiya me yasamu RAHAMA driver yace wai kuna Asibiti? Momy muna hanya yanzu zamu iso, "momy ki tanadi goron da zaki bani,
"Goron me? "Muna zuwa dai momy, ya datse call din ya janyo ta zuwa jikin shi sai lokacin ma yaga hawayen fuskar ta, jikinshi yayi sanyi,

" yace bakya farin ciki ne RAHAMA da kyautar da Allah ya bamu? Meye kike wa kuka, saboda cikina kike zubar da hawaye? Kiyayyar takai kiyi kuka bayan anfada min Albishir din da yafi komai dadi a zuciya ta? Do you no how much I suffer before I get this child? This child is a miracle to me,
Bantaba tunanin zan samu yaro nan kusa ba duk da banda lafiya Amma Allah ya gwada ikon shi only two tomes ya Azurta ni da ciki and you, kina kuka for what?....... 🖊



*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*

4⃣3⃣&4⃣4⃣

"Am not crying because I don't want it, am crying because am happy, tafada tana fitar da wasu hawaten, tareda girgiza mai kai, " wace uwa ce zata samu baiwa irin tawa tayi kuka saidai wadda batasan ciwon kanta ba, idan nayi kukan farin ciki laifine?
You have no idear how happy I am today, having your child in my belly, me yafi wannan farin ciki, ina son cikin nan kamar raina, tafada tana shafa shafaffen cikin ta, wata irin runguma ya bata tareda shafa bayan ta kamar wani kwai, "tank you baby for this wonderful gift, I love you with all my heart, ke Alkhairi ce a rayuwa ta, tun lokacin da kika shigo duniya ta I changed completely RAHAMA you have changed me,
Da farko Nadauka bakyason cikina har hankali na yatashi domin baya ga ku keda iyaye na ba wani Abu da yakai min shi muhimmnci a rayuwa ta yanzu,
My on blood, Alhmdulillah,
Yafada yana dago ta tareda kokarin daga rigar ta tayi saurin riko hannun shi tareda nuna mai driver " doguwar riga ce fa and akwai driver,
Fata fuskar shi yayi " sorry ina so inyi kissing baby na ne,
But tunda riga tahana I can kiss his mother, yafada yana fisgo ta tareda manne bakinshi kan nata ya mata kyakkywan cafka... Saida ya saki wani irin gurnani da kuma numfashi mai zafi domin yayi kewar ta,
Sosai fiyeda tunani, saida driver ya tsaya tareda saurin bude motar ya fice domin ya najin me sukeyi,
Tayi saurin janyewa ganin yanda yake kara makaleta tareda shige mata jiki kamar zai koma cikin ta,

"Munzo gida tafada tana gyara mayafin ta tareda gyara rigar ta da duk ta nannade sama, bude jajayen idanun shi yayi tareda kallon inda driver yakai su, bata rai yayi " Amma this guy is a fool yana gani na cikin yanayin nan zai kawo ni gida shida zai wuce gidan mu, yafada fuskar shi a tamke,
Ya fito batareda yabi ta kanta ba,
Ya fara bal bale driver da masifa " kai ina ka kawoni? Why zaka ka kawo mu nan? "Sorry sir naga mun dakko madam ne shiyasa na fara kawo ta nan sai mu wuce,
Wani irin kallon takaici ya mai kafin yace " ni nafada maka hakan? Now get in and drive us to my house, "ok sir yafada yana komawa cikin motar dai dai RAHAMA ta fito, ga mutane na wulgawa dai dai ku saboda duk an dawo,

Hade rai yayi yace " ki koma ciki gidan mu zamuje, "tofa, yau ma da rigimar da zasu rabu kenan, gashi ba Abinda take so irin ta kwanta, ta huta, wani irin kasala takeji,
Dafe kanta tayi tareda cewa "kayi hakuri inkoma ciki in kwanta am very tired please,
Ok muje cikin ki kwanta a side dina saboda hayaniyar mutane, riketa yayi kamar zata gudu suka shiga falon dake cike da mutane,
Da momy ya fara cin karo, ta ja ta tsaya, " Meke damun RAHAMAr? Washe fuska yayi tareda cewa "momy zakiyi jika very soon She is pregnant, yafada tareda kara mannewa a jikin ta,
Wani irin rawa bakin momy ya farayi tareda cewa "kai karka min wasa da hankali kaji Meke damun ta? " Allah momy ciki takeda shi,
Rungume ta momy tayi cikin Sauri tareda jero Hamdala, tana fitar da kwallar farin ciki, d'an Al Ameen, zatayi jika cikin wata kadan, Allah mai girma kuma mai kyau ta da kari, cikin damuwa take yanda gidan zai kasan ce ita kadai bayan tagiyar Husna, tasan RAHAMA dole ta tare gidan mijin ta, Amma yanzu tanada wani hope nan da shekaru kadan zata samu Abokan hira a gidan suna gilmawa,

"Allah ya inganta mana RAHAMA, tafada tana dagota jikin ta, itadai duk kunya ta gama rufeta su ba ruwan su, daga momy har Al Ameen din,
"Kai tafi da ita dakin ka ka kula da ita ina zuwa inkawo mata Abinci,
Tafada tareda wucewa, shikuma zuciyar shi kamar Auduga saboda taushi yau, gashi saboda wannan babyn momy bata kore shi ba har tana bashi umarnin suje part dinshi da kanta,


Don haka dagata yayi cak tareda nufar hanyar dakin nashi yana man na mata fake a kumatu, har suka shiga ciki a hankali ya direta gefen gadon, ya zauna tareda zama dirshan kasan a gaban ta ya na riko hannun ta duka,
"Me ya rage min inne ma yanzu a duniya? Alhmdulillah na gama samun komai saura gamawa lafiya da kuma fatan fitowar jini na inganshi in dauke shi, please take care of yourself Karki min ganganci da cikin nan ina jin shi kamar rai na,

Girgiza kai tayi tareda cewa "ina son insha kamu, cikin Sauri ya mike ya ce "an gama bari inje kitchen din ingani in akwai ada ma miki, inbabu ko ina ne yau sai Anne moshi,
Fita yayi cikin Sauri, ya samu momy na hado mata Abinci Kala Kala, yace " momy wai zatasha kamu,
Kallon shi tayi tareda cewa ina zamu samu kamu ni Aisha,? Gashi bamuda shi kuma mace mai ciki intaso Abu in bata samu ba sam ba dad'i, tafada duk fuskar ta dauke da damuwa,

"Bari inkai mata wannan zanfita inne mo mata momy ko a ina ne, "ok yi maza bari inje wurin baki, ka tabbata taci karta zauna da yunwa,
, daukar tray din yayi ya nufi dakin shi cikin sauri har ta mike ta cire jallabiyar ta daura towel wanka takeso tayi jikin ta na mata wani iri,
Tsayawa yayi cak yana bin ta ko ina na skin dinta dake sheki da idanu, jikin shi tuni ya saki, ya Karasa tareda ajiye tray din ya nufeta duk idanun shi sun canja,
A natse ya shige jikinta tareda sakin numfashi mai zafi, " please yaushe zan zama kamar kowa ne namiji?
Ni ma duk lokacin da naji sha'awar matata insamu biyan bukata, ina matukar dauriya RAHAMA ba karamin kokari na keyi ba, inada mace kamar ki sai dai ido tsawon satika ina kallon ki sai dai in hadiye yawu,
Please zamu tafi India cikin satin nan nagaji gaskiya, nagaji,
Rungume shi tayi itama dakyau "kayi hakuri lokaci ne very soon har sai ka gaji, tafada tana dariya,

Dagota yayi tareda zubawa kirjinta dake kyalli ta sama ido yace " um um kece zaki gaji, dani domin sai kin biya bashi duk kwalelen nan da kike min sai na fanshe kayana, Allah dai ya kaimu lokacin, kuma ki sani ni ba na wasa bane, kina ganin banda lafiya ma bugu biyu har kin cafke, I am a good player ko?
Yafada yana daga mata gira daya, sunne kanta tayi cikin wuyan shi tana dariya, wanda yanajin wata irin kasala da muguwar jiki na baibaye shi,
" stop that ko kisa in suma yanzu ba ruwa na uhm, saurin dagowa tayi tareda matsawa. " ina Kamun?
"Oh kece kika mantar dani komai wai babu amma bari inkira a nemo mana shi,
"Aje gidan Inna bata rasa gasara bare yanzu akwai taro, sunyi an ajiye,

"Ok bari inje inkarbo kici Abinci ina zuwa, " wait ina zakaje?
"Gidan Inna ma na inne mo mana Kamun, "da kanka? Fake ya manna mata tareda juyawa yace "bye sai na dawo baby take care,
Fita yayi ya leka dakin Husna yace taje ta taya ta hira yana zuwa, binshi tayi da ido tace "kaji wani sabon salo, bari ma inje in gwangwaje ta sunje sun bata min Fati kawai,

Fitar shi yayi yana fada mata ita kuwa tayi part dinshi, tasame ta har ta watso ruwa ta zauna tana bude plates din domin ganin Abinda zata iya ci,
Husna tayi Sallama,
Dago kanta tayi tareda cewa "kaga Amaryar yaya Aliyu,
Gira ta daga tana gyara taku "yes Kifada ba a fada,
Kinma sa nafasa fadan da nazoyi,
Amma sainayi complain,

"Na farko your husband ruined my party tunda ya shiga aka daina tani da my husband to be gaba daya kamar wani cele ya dauke hankalin kowa, and ke kuma kinzo ankoma kanki gaba daya like party din naku ne ba nawa ba,
"Waima ina kuka fita kuka je ne daga liki,?

"Tofa wannan irin korafi Aunty Husna, don gwara infara kafin ki shiga gidan yaya na duk da ni bakya kirana Aunty, "amma kuma bana kiran sunan ki ai, so a zauna lafiya, waima Meke damunki ne naga kinyi wani iri a hole,? "Zazzabin da nake ta fama this days a she a she kin kusa zama momy ne, tafada tana dariya,
"What? Husna tafada tareda danewa jikinta tana "da gaske ciki kikeda shi da gaske?
Dama kawata ta fada na karya tata oh my Allah, zan zama gwaggo tafada cikeda excitement,
Tana rungume ta, dariya RAHAMA tayi tace " wai yau ina shan matsa sai kace akaina aka fara ciki? " uhm dole kisha runguma irin wannan Abin farin ciki,zama tayi ta zuba musu waina da miyar sure sukaci ba laifi Amma duk zuciyar ta naga kamu ta matsu bataga ankawo mata shiba,

Shi kuwa da kanshi ya tuka mota har zuwa mabera, ya samu kofar gidan da mutane wasu Abokan Aliyu wasu kuma mutanen baba ne a gefe kasan cewar akwai haske yana hango komai duk da duhu yayi, , Aliyu ne ya fito, dai dai yana faka motar, ya nufe shi, "yadai naga dazu kunbar Hole? Madam ba lafiya dole inbar wurin kar a kara mata ciwon kai, yafada fuskar shi a sake, Kamun congrats am going to be a father very soon,
Washe baki Aliyu yayi yace "masha Allah kace na kusa zama Auncle,

"Yeah insha Allahu, yanzu dai muje ciki kamu mukazo nema, baby naso zaisha, "tofa inji Aliyu shine ka taso da daren nan? "Eh ya zanyi nidai muje in samo,
"Ai tsayawa zakayi inkawo maka domin gidan cike yake da baki bazaka iya ratsa suba, " ok yi sauri kar ya fita ranta, dariya Aliyu yayi "kai nifa yayan ku ne, " nikuma fa? Al Ameen yafada yana mai kallon ya manta kenan!? "Or haka ne yayan mu Afuwan, bari inshiga inkawo,
Inna ya samu ya mata magana a gefe, tayi dariya tareda wucewa tana ayya na yaran yanzu basuda kunya sam wallahi, ta samu penter Kara ma ta ciko da gasara ta rufe tabashi ya fita domin kai mai,

Godiya yayi ya tafi,
Saida ya sallaci isha a Unguwar su kafin ya shiga gidan, lokacin duk baki wasu sun watse sai kuma gobe, ya nufi kitchen yabawa mai aiki yace ta diba ta dama yanzu ta kawo, sai ta saka sauran a frij,
Dakin shi ya nufa,
Ya samu ita kadai ce ta kintsa kanta cikin nightie baka ta kwanta tana kallon hanyar koda ya shigo,
Zabura tayi ta mike, "an samu?
"Eh yanzu za a kawo miki, na bayar a dama,


"Ina Husna banace karta barki ke kadai ba? "Yanzu ta fita taje wurin friends dinta sunkira ta ne, " ok, yafada tareda kwabe rigar jikin shi, ya shige bathroom, saida ya watsa ruwa ya fito daure da towel,
Ruwa na diga a jikin shi, aka buga kofar,
Ya nufi hanyar zai bude tace "wait, tareda dirowa ta ce ka koma inga waye? Rikota yayi yana dariya, " why? Saboda ba kaya a jikin ka in aka ganka fa,?
Dage gira daya yayi " ke ba gani na kikeyi ba a hakan? Harara ta watsa mai tareda cewa " ni nice ai, ta nufi kofar ta budeta karbi plask da cup tayi godiya tareda komawa ta Ajiye yana ta binta da kallon, salon kishin ta na mugun burge shi, yanason yaga ana kishin shi,

Duk lokacin da ta bayyana kishin ta Abin na mai dadi sosai,
Zama tayi ta sha Kamun ta sosai har tanajin wani irin dadi shi kuwa ya zuba mata ido batareda ya damu ya nemi kaya ya saka ba kofar ya yaje ya rufe,
Ya dawo tareda dagata cak zuwa gado, kashe hasken dakin yayi ya kunna dim light,
Numfashi taja "bazaka tafi gida bane? "Um nan ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login