Showing 51001 words to 54000 words out of 101092 words

Chapter 18 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37779

Biyar na yamma wanda tasan taro yayi nisa,
Ga miss call din Husna rututu,
Da yaya HAJARA,
Dialing number HAJARA tafarayi " yaya ina zuwa yanzu muna motor, "kin faya sanyi RAHAMA tundazu kowa yagama hallara, harda mijinki na nan,
Tuni taji wani irin farin ciki tace, tom ina zuwa, driver ta kalla tace yayi sauri don Allah, Suna isa harabar giginya hotel din da jerin motocin Al Ameen ta fara cin karo, murmushi tayi kawai tarasa dalilin ds yasa yake kaunar " convoy dinshi suna binshi kamar wani d'an sarki ko gwamna, duk motocin shi uku yake siya iri daya,

Ko Wacce akwai A yabo a jikin lambar jitayi kawai she wanted to feel as his wife in public don haka tuni ta gyara walk domin ta nunawa Y'an matan sokoto nata ne fa,
Aikuwa tun shigowar shi hole din gaba daya ya gama siye hankalin matan dake ciki, don ko Ango da Amarya dake ciki basa kallon su kamar shi,
Duk da cikin farar jallabiya yake shima kamar duk sauran samarin dake wurin saidai nashi ya fita daban dana kowa wankan ga wani bakin glass da ya kwama a ido labcece gaba daya he is worried, baiji dadin zuwa wurin ba as he came bata zoba and he came only because of her duk kwanakin nan kewar tace take neman kassara mai karfin jiki da kuma lafiyar ruhin shi,


Itace akan gaba lokacin da suka shigo duk da tanajin nauyin idanun mutane akansu baisa ta bada kanta ba as she no yana wurin sam so take ta nuna mai she can act like Mrs Al Ameen A yabo,
Tafiya take tana rausaya, batayi Aune ba taji mc na kodata tareda yi mata maraba,
"Barka da zuwa zuciyar Al Ameen Shuaibu Yabo muna miki barka da zuwa matar d'an gatan sakkawata, takawar ki lafiya mace mai sa'a,
Wani irin dagowa yayi tareda zare glass a idanun shi ya mike tareda nufar hanyar domin taro shi don ta gama Tafiya da ruwan kwakwal war shi, ta mugun haduwa ga wani irin haske da sheki da takara na gyaran da sukasha ga kuma kyallin sabon boyayyan Ajiyar su,


Gaba daya Y'an mata aka fara tsegumi da kuma hassada, wasu na tayi wasu na duk haduwar shi wannan ce matar shi, kowa dai da kalar nashi Amma ni nafada saidai hassada Amma RAHAMA ta hadu ga cikar hutu da shakin Ac dake ratsa fatar ta,
Ko yanzu idan ka kalleta koda a fisge tafi HAJARA kyau nesa ba kusa ba ga kira mai daukar hankali,
Duk da jallabiya ce ajikinta zaka iya hango baiwar da Allah yayi mata na suffar jiki mai kyau d'an daidai,


Isa yayi kusa da ita tareda riko hannun ta, cikeda kulawa, kowa sun burge shi a wurin, ya nufi table din da dama shi kadai ne akai ya jamata kujera tareda sata ta zauna shima yaja tashi gab da tata ya zauna, mc sai famar kirari yakeyi tareda koda A yabo da RAHAMA, shikuwa tun shigowar ta hankali da natsuwar shi kaf na tareda ita jiyake kamar ya shige jikinta ko zaiji relief amma no way mutane na wurin,


Yaya Aliyu dake tareda Amaryar shi to be wani irin dadi da farin ciki ne ya rufe shi yaji ya kara kaunar Husna sosai a cikin zuciyar shi domin yanda A yabo ya daga darajar RAHAMA a bainar jama'a tareda nuna tattalin shi batareda ya damu da kowa dake hole din ba,
Itama abin ya matukar faran ta mata zuciya ganin yanda ya nuna mata ita din tanada matsayi agaban duk zalamammun Y'an matan dake cikin hole din, yasa itama ta saki jiki tareda riko hannun shi ta rike gam cike da shagwaba tace " banda lafiya,

Kallon idanun ta yayi yace " nima banida lafiyar ai an ke baki damu da damuwa taba, ", bayan inata kiranka kaki daukar wayar ya kakeso inyi?
Kana fushi dani, zuba mata ido yayi tareda riko hannun ta duka biyu " Meke miki ciwo? I saw it in your eyes you are sick,

"Zazzabi ne da kuma ciwon kai kullum yaki sakina, yanzu ma sanyi nakeji tafada tana kankame jikinta, saboda Ac da ya cika ko ina a wurin
Anata hada hadar rabawa Al umma shayi kamar yadda al adar ceremony din take tareda biscuit masu tsada dasu snacks

Koda aka kawo nasu dauke kai tayi tareda nuna mai a wuce da snacks din sam batason warin su, ya kalle ta cikeda damuwa ya kira service din yace ya kwashe tareda kara matsawa gab da ita " Meke damun ki haka?
"Nima bansani ba tafada idanun ta na cikowa da hawaye, domin samun wuri dama ba Abinda bai sawa, wani irin shagwaba takeji da ta ganshi,
Gashi duk ya rude ya wani susuce saboda ganin ta kawai yasa ya mantar da shi fushin shi,

"Am sorry bari ankusa tashi muje Asibiti muga doctor, "no please banaso tafada fuskar ta akwabe, alamar sam dai bata son Allura, lokacin da aka gama kora shayi aka kira ango da Amarya suka fita tsakiyar filin ne, domin ayi musu kara, ta mike, ya riketa " ina zakije? "Zanje liki ne, zanje inyi miki sit down, yafada yana mikewa ya nufi filin tana kallon yanda yake kasaita da kuma taku cikin jin shifa ya kai ta ko ina, yafara ruwan kudi, Y'an mata ansamu dama tuni suka mike domin zuwa kusa dashi ko liki suyi mai sukai labari,
Ganin yanda suka rufe wurin ruf suna mai liki yasa RAHAMA taji wani irin kishi da kuma karfi, mikewa tayi tareda nufar wurin fuskar ta a murtuke, ta ratsa su har zuwa gaban shi ta fara watsa mai Y'an canjin da tayo Y'an Dari bibbiyu,
Wani irin murmushi yayi ya riko hannun ta ko tsayawa basuyi a ciki ba yayi waje da ita,
Saida suka shiga cikin motar shi yayi Dariya, " madam kishi ina key din motar ki? " yana wurin driver, tafada tana dauke kai, ya fita tareda duba driver yace inya tashi ya kwashi wasu ya tafi Asibiti da madam,
Dawowa yayi cikin motar ya ga ta dauke kai, " Hhm madam lafiya? Cikin fushi ta juyo " ba wani lafiya dama saboda kasan Y'an mata na jiranka su rufeka shiyasa ka hanani zuwa likin to wallahi gobe bazakaje Indian night din ba,
"Hhhh Allah ya baki hakuri, angama ko yau ma nazo saboda ke ne, please muje muga doctor yafada tareda ciro wayar shi ya kira driver yace su tafi,
Tareda fada musu inda zasu kaishi,


Kiran yaya HAJARA Tayi tace "yaya banganki ba? " ai ni Naganki sister kiyi hakuri I can't show my face in front of your husband, kunyar shi nakeji Rahama but kin hadu ba kinfito kun haska you look perfect and classy Mrs Al Ameen,
Kin dagawa mata hankali kanwata I feel proud of you today,
Tafada cikin sakewa da tsokana, tuni zuciyar RAHAMA tayi sanyi ta saki jiki suka d'an yi magana kafin ta kashe wayar,
Ta jingina jikin shi tana jin wani irin farin ciki,


Har saida suka isa wani kayataccen Asibiti, driver ya faka suka fito ya riketa suka shiga ciki, sanin shi waye nan da nan aka kula dasu tareda basu umarnin shiga cikin ofishin likita kai tsaye, ya mike cikeda girma mawa yamai barka da zuwa " ranka yadade kaida kanka? " eh madam nakawo batajin dadi,
Cikin rawar jiki ya kira nurse tareda bata umar nin dibar jinin RAHAMA domin yin test Domin gano matsalar, ya bawa Al Ameen wurin zama ya ce ya jira adiba jinin ta, diba akayi dakyar ta yarda aka soka mata Allura har saida ya rike ta aka diba yana dariya bai taba ganin rakin taba sai akan Allura,

Suka dan jira na minti talatin Abinka da komai a zama nan ce akeyi aka kawo mai result, ya duba Tareda mikewa cikin farin ciki ya mikawa Al Ameen hannu,
" congratulations sir madam nada juna biyu na kusan four weeks,

Yafada cikin murnar zaiyi wa A yabo Albishir na first egg din shi a duniya duk ya kosa yaga reaction dinshi, ai kuwa mikewa Al Ameen yayi tareda kallon likitan da kyau " are you sure? Tell me how is that possible doctor ciki? My son, yafada a rude yana daga Rahama, " are you feeling something in your belly? Please are you feeling my baby,?

Ya fada a rude duk yarasa inda zai tsoma ranshi, wasu irin hawaye ne duka biyo fuskar RAHAMA," cikin Al Ameen a jikin ta, Al Ameen dai he is out of his mind kara tanbayar likita tareda zaro kudin dake pocket dinshi kab ya ajiye mai " kaduba ta da kyau I can pay any price doctor just ka tanbbatar min da cikin matata don Allah don't make me dream of it in tashi inga bacci nakeyi,


"That's the truth ranka ya dade blood test ne mukayi kuma baya kuskure don haka Ina tayaka murna Allah ya inganta,
"Allahu Akbar ya fada tareda yin sujada ya godewa Allah tareda mikewa ya daga ta cak ya rungume, yana tank you tank you tank you baby kin gama min komai wallahi,
Likita sai dariyar rude war Al Ameen yakeyi,
Ya Mai godiya tareda bashi hakuri bai da cash a jikin shi sosai that's all he have ya juye mai, yace ya jira surprise,
Ya cirata sama cak suka fita,


A hankali yake Tafiya da ita duk kunya ta gama rufeta domin kowa kallon su yakeyi
Har saida ya isa wurin motar shi driver yayi saurin bude mai ya Ajiyeta kamar kwai tareda warning driver, ya tafi a hankali dasu,

Kiran momy ne ya katse mai farin ciki " kai lafiya me yasamu RAHAMA driver yace wai kuna Asibiti? Momy muna hanya yanzu zamu iso, "momy ki tanadi goron da zaki bani,
"Goron me? "Muna zuwa dai momy, ya datse call din ya janyo ta zuwa jikin shi sai lokacin ma yaga hawayen fuskar ta, jikinshi yayi sanyi,

" yace bakya farin ciki ne RAHAMA da kyautar da Allah ya bamu? Meye kike wa kuka, saboda cikina kike zubar da hawaye? Kiyayyar takai kiyi kuka bayan anfada min Albishir din da yafi komai dadi a zuciya ta? Do you no how much I suffer before I get this child? This child is a miracle to me,
Bantaba tunanin zan samu yaro nan kusa ba duk da banda lafiya Amma Allah ya gwada ikon shi only two tomes ya Azurta ni da ciki and you, kina kuka for what?....... 🖊



*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*


3⃣9⃣&4⃣0⃣


Tare suka koma Dakin inna wanda yaushe rabon ta data sake haka cikin mutane wanda taji dadin zuciyar ta sosai a ranar zuwan RAHAMA, harda girki da shirya wasu kayan na biki su sukayi, kafin baba yadawo ya samesu shima ya sake yayi farin ciki ganin ya'yan shi kansu ya hadu a yau har suna harkokin su tare cikin farin ciki,
Sun wuni cikin farin ciki har lokacin da wayar ta tayi kara ta duba tana murmushi, domin tasan waye, dagawa tayi tareda mikewa, " kifito mutafi malama ziyarar ta isa haka ko,
Zaro idanun ta tayi tareda waigawa ta kalli su inna kafin ta shige cikin Dakin su na gidan,
"Haba ranka yadade haka zakazo har kofar gidan nan kuma ka kasa shigowa ka gaida surukai, baba na nan fa, "ok am coming in,
Ya datse kiran tayi saurin gyara jikin ta tareda fesa turare ta fito, tana fadawa su baba Al Ameen yana waje zai shigo,
"Aa kaji min shirme sai ya tsaya jiran izini shida gidan su? Bari intashi inshigo da shi,
Ya mike cikeda jin dadi ya fita,
Lokacin ya fito daga cikin motar shi yana ba driver umarnin su wuce tunda yaga da mota ta taho,

Baba yamai barka da zuwa ya durkusa har kasa ya gaida shi yayi saurin rikoshi " Aminu ka tsaya a nan ai daka shigo kai tsaye kaima kazama d'an gidan, suka shiga tsakar gidan gaba daya kamshin shi da kwarjini sun gama mamaye ko ina,
HAJARA tayi saurin mikewa ta gaida shi kanta akasa kafin ta wuce cikin daki, RAHAMA kuwa fitowa tayi daga Dakin inna rikeda jug dauke da sobo da yaji Abarba da kuma cucumber yana kamshi,
Ta ajiye a gaban shi tareda kashe mai ido daya, shikuwa yana gaida inna yana kare mata kallo, yanda tayi wani haske da kyau domin sunyi kwana biyu basu hadu ba don momy bata bari saboda kiyaye lafiyar shi,
Yaga takara kyau da wani irin kyalli da cikowa don haka yakasa dauke idanun shi akanta,
Saida tayi mai signal da su inna ya d'an natsu Amma duk da haka zuciyar shi na wurin ta,
Komawa tayi ta sako hijabin ta tareda jakar ta tafito, HAJARA ma ta biyota tana mata Sallama,
Bandir din kudi ya Ajiye wa inna yace ta kara a hidima, tana mai magana ya dawo ya dauka suma sunada hidima amma fir yaki,

Yayi gaba yana ma RAHAMA magana, tayi musu Sallama tafito, ta biyo shi, ganin shi tsaye kusa da motar ta yasa taja ta tsaya, "ina motar ka? A me kazo? "Um um madam a motana nazo nace driver ya tafi am coming with my wife, a motar ki zamu tafi So ke zaki tuka mu, muje, bude motar tayi da key tana dariya, shi ya shiga itama ta shige,
" matata zata jani yau, kin san na tsani tuki shiyasa nake yawo da driver, " yeah I see domin ko lokacin da nafara ganin ka a bayan mota na ganka kamar wani sarki ana tuka ka,
Dariya yayi tareda tuna me yafaru a lokacin,
" baby lokacin kinji ciwo ne da motar mu ta tureki? Tada motar tayi tareda cewa " uhm harda targade ma,
Saida na kwana biyu ya daina min zafi har na koma school,
Juyowa yayi da kyau yana facing dinta, " Am sorry my dear, ranar Dady ya mun zancen Aure ne ina cikin jin haushin Abun ke kuma kika zo kika gasa min magana,
Do you know har neman ki nasa ayi domin inyi miki wulakanci, Amma da yake Allah ya boye wani Abu a tsakanin mu ya hana ni ganin ki,


Saida kika tare agidana, and slowly kika fara siye zuciyar Al Ameen da kyawawan dabi'un ki, wanda yazamar min Abun Alfahari akoda yaushe, yeah am proud of you as my wife, am very lucky to have such a wonderful woman in my life,
Yafada yana riko hannun ta daya dake kan giyar motar ya murza kadan tareda sunbatar bayan,

Wani irin murmushi tasaki, " tank you for the complement oga na, "nop gaskiya ne hajiya ta you are the best wife and kece maganin ciwo na, kece farin ciki na Rufin Asiri na ina Alfahari dake akoda yaushe, shiyasa nake nacin ki Nazama kamar bindi, duk da momyn ki na mun kwalele Amma ina nace,
"Sorry my miji tana son ganin ka warke ne baki daya, nikaina hankali na na matukar tashi idan ka suma to ka hakura mu koma wurin likita idan zai iya baka wani taimakon da zai hanaka dogon suma,
"Hhhhhh madam ku gane, shekarun duk da nayisu abaya bantaba fitarda ruwa ba ko a mafarki, har nakai shekara talatin da Biyar, saboda matsala ta, and likita yafada dole ne Innayi released sai hakan ya rika faruwa har zuwa lokacin da Abin zai ragu sosai, don haka nidai muje gidana ma yanzu ki kara sumar dani am ready to pent in your arms ina son jin zumar ki, naji a jikina koda lafiya kalau nake nayi nutso a gidan dad'in nan nasan dole in iya suma saboda baby akwai zuma fa a ciki ba a magana, d'an dauke kanta tayi saboda kunyar yanda yake kallon cikin idanun ta, kuma yake fadin maganar shi hankali kwance ba kunya,

Matsowa yayi ya sanya hannu ta kuibin ta har saida tayi zullo, tareda zaro idanun kamar zata saki sitiyarin motar, tace " baby kana so in zubar damu ne,?
Cire hanun shi yayi " nooo banshirya ba nida yanzu ma nake fara Amarci na, don haka nadaina muje gidan mu kinji please don't say

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login