Showing 45001 words to 48000 words out of 101092 words

Chapter 16 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37772

farin ciki da natsuwa,
Irin baccin da bai tabayi ba tsawon rayuwar shi, kwanciya gado daya da mace after your first night, is the best in every couples history, and yayi matukar kokari ganin bai kuma neman ta ba a daren domin yanaso ta saki jikinta dashi kafin a kuma yi,




Da safe ta tashi garau domin ba wani ciwo da tashi tareda gyara gidan ta like before ta shirya musu breakfast, ta tsantsara Adon ta tareda baza kamshi, ta sakko kasa domin tanaso ta ga inda tafara rayuwar Auren ta mai cikeda farin ciki da kuma cigaba da Alkhairi da dama datake Gani a kullum cikin farin ciki take,

Sallamar da taji ne ya mugun bata mamaki, domin tasan safiya ce Al Ameen ma ko tashi baiyi ba, and ba wanda zai zo musu gida by this time, saidai kafin ma ta gama tunani suka sawo kai tareda gyara tafiyar su cikin yanga da nuna sufa sunci dubu sai ceto,,
Sunci uwar dauri kamar tsofaffin karuwai,
Ta gyara tsayuwar ta tareda zuba musu ido ta d'an daure fuska kadan tareda cewa "yaya HAJARA kune haka gidan mutane da sassafe daga ina haka?
"Um kaji masu gida Allah mai gida, ina gidan yake? Wannan ne gidan Hmm yarinya watan kunyar ki ya kusa tsayawa insha Allahu zakiga HAJARA a gidan da ya dama wannan ya kuma shanye shi a haduwa,............ 🖊




*ku tayata wannan yakin domin yakamata yau dai ta tabuka ma kanta wani Abun, and HAJARA yara irin su duniya Kawai ke koya musu hankali su shiga taitayin su saboda fushin iyaye babban bala'i ne da kuma masifa a rayuwar ya'ya, wanda wanna labari yana nufin ribar biyayya ne a wurin iyaye da kuma illar bijirewa zabin iyaye*

*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*

3⃣5⃣&3⃣6⃣


Wani irin kallon rainin wayau suke mata, ladidi har da gyara dauri tana hango yanda, wannan gidan ne kike takama dashi har kike cika wani baki anshigo miki gida da sassafe, "banza dakikiya sakarya, miji ya nuna miki bakida wata power ko daraja tunda yakaiki ya jingine ki a gidan iyayen shi, dama kin kakkabe wannan Auren BIYAYYA da kike ikirarin kinyi kindawo gida kin taya inna zama domin ni kwanan nan zanyi hijira in koma palace dina my mension ba irin wannan akulkin ba da kike kira gida,

"Sosai kuwa domin Duk sokoto ansan da zaman Alhaji bello mai motoci, yafi mai wannan gidan komai, wani irin kallon anyi muku uzuri take binsu dashi, kafin tace " Allah sarki yaya HAJARA aini farin ciki nake tayaki Akullum zanso ganin cigaban ki nafi kowa farin ciki idan kika samu cikar burinki a rayuwa,
Don haka ku shigo ku zauna inkawo muku breakfast, "Karki raina ma mutane hankali don munzo gidan ki, ko anfada miki yunwa ta kawo mu, mundaiji labarin kin dawo da kanki ne gidan mukazo mu sheda wa idanun mu, kindaiji haushi wallahi Rahama miji ya wulakanta ki kin kama kin nace don rashin zuciya,

Dariya tayi kadan " sosai Yaya HAJARA, wanda ma ya guji Auren yadawo yana bibiyar shi daga baya saboda hango daula da kuma haduwar mijin bare ni da Nasamu damar igiyoyin Auren shi har guda uku akaina inyi wasa dasu, ai duk wadda tayi sakaci da miji irin nawa ta rako mata duniya ne Kawai, mijin da kowace mace ke mafarkin samu ni Nasamu ai dole inlike mai,
Inaji ina ganin wasu ma kamar su kawo kansu wurin shi ko ba Aure ni Nasamu na shiga daga ciki zai tsaya shirme, ku zauna in hado muku breakfast kuma ku d'an Dali arziki, ta wuce kitchen ta barsu da mugun takaici da kuma magan ganun da ta gasa musu cikin ruwan sanyi,

HAJARA wani irin zabura tayi zata bita ta maketa Ladidi tayi saurin riko ta" relax kawata bari mu d'an gwali arziki kafin muyi rashin mutunci, ai dole ma ki dauki mataki amma ki bari in Koshi yunwa nakeji sosai komawa tayi tana jijjiga, tareda kunbura,
Lafiyayyan breakfast ta hado musu harda sauran gasashen naman da yayo musu take away jiya, ta musu warming ta jera musu a kasan carpet din, ta ce ku sakko please kuci Abinci ina zuwa,
Tafada tareda juyawa tayi sama,

A kwance tasams shi idanun shi biyu ya tashi ya zubawa kofar shigowar ido. Tana shigowa ya sakar mata murmushi " ina kikaje na farka banganki ba? " ina kasa ne na hada mana breakfast ka tashi kayi wanka ka sakko muyi break " ok madam, yafada tareda tashi, bathroom din ta wuce tareda hada mai ruwa, tana kokarin fitowa ya sawo kai wata irin runguma ya bata mai zafi tareda manne wa a jikin ta,
" kijirani inyi wanka baby infito, or kizo muyi tare, ganin ki Kawai cikin wannan Adon early morning rise the man in me, kina haukata ni fa wife,


Yafada yana kara shigewa cikin jikin ta kamar zai tsagata ya shige yakeji saboda tsabar sha'awar ta da ta taso mai, ganin yanda duk yakeyi yasa tace " muna da baki a kasa kayi wanka ka fito bari inje ingansu,
" suwaye da safen nan? " yaya HAJARA ce da kawarta, " Hmmm Kawai yace tareda sakin ta ya nufi bathtub, ita kuma tayi saurin fitowa don tasan zai iya kwabewa a gaban ta,
Kasan ta dawo tareda tarar dasu har sun cinye tas Ladidi ta dora kafa daya kan daya tana sakada hakori da toothpick,
Sakin fuskar ta tayi tareda cewa " or sorry na barku ku kadai kunsan kunyi sammako oga na gida dole indan kula dashi kafin indawo kanku

" mtsssww banza sai kije kifadawa wanda baisan matsayin ki wurin mijin ba, kizo kina cikawa mutane bakin banza sakarya mara zuciya, " Hhhh haba yaya HAJARA ai ko korata yayi sai nadawo indai da igiyar Aure a tsakanin mu, "ai dama ke tunkiya ce bakida zuciya, " sosai kuwa yaya shiyasa naga ke dakeda zuciyar kike bibiyar mijin kanwar ki uwa daya uba daya har gidan ta saboda jahilci da tsana ta da kikayi saikace ba cikin mu daya ba,
Ni wallahi wani lokaci har tantama nakeyi Anya ke jinin mu ce kuwa? Saboda zuciyar ki sam batayi kama da irin zuciyar dattijon kirki irin baba na ba, duk da yaya Aliyu nada fushi amma tanada golden heart yana kaunar mu duk iskancin da kikeyi kullum zancen shi Allah yasa ki samu miji kema kiyi Aure ko hankalin su zai kwanta,

Yanzu ke kina jin dadin rayuwar ki a irin wannan gantali da kikeyi su inna sun kawo ido sun zuba miki batareda sun ce miki komai ba saboda gudun takurawar su agareki, domin yara masu zuciya irin taki idan har aka matsa musu komai zasu iya yi saboda basuda kwakwal wa mai zurfin tunani, sannan wallahi kiyiwa kanki fada iyayen nan da kike nunawa basu isa ba wata rana zaki iya neman su ki rasa ko kuma ki nemi taimakon su lokacin komai ya kure miki,

Don haka kifarka kifita hanyar kawayen da su iyayen su sunce suje sa gani.... Wani irin tsalle sukayo zasu kai kanta saboda zancen ta yafi karfin a tsaya bata Amsa saidai duka,
Sukaji tsawar Aliyu, " zakuyi kuskure mai girman gaske duk wadda ta sake yatsar ta ta taba min ko da rigar matata wallahi sai na daure ta daurin rai da rai ba kuma wanda ya isa ya fito daku,
Waima hauka kukeyi da har kuke mafarkin shigo min gida ku Dakar min mata, gaban su ya karaso yana buga kamshi da sheki ya janyota tareda rungume ta tsam a jikin shi,

Kafin ya juyo ya zuba musu idanun shi masu matukar kwarjini da kuma ladafta mace, yace " kuna mafarki ne ko? " and you, ya nuna ladidi " banyi miki warning da kar inkuma ganin mummunar fuskar ki koda a gefen katsngar gidana bane, yau saboda kinsamu hanya har cikin gida na kina kokarin kai hannun ki jikin matar Aure mai daraja da kuma kima a zuciyar Al Ameen Shuaibu Yabo,

Wani irin tsalle zuciyar ladidi keyi Asirin ta zai tonu domin ta dade tana bibiyar shi yana mata wulakanci yau gashi ya kware ta a gaban kawar ta, yazatayi ta fitar da kanta, itama HAJARA abin yabata mamaki yaushe ladidi ta bishi har ya mata wulakanci bayan basu gama hada plan din da zata shigo gidan A matsayin matar shi ba, don haka kallon tuhuma take aika mata, ta Dukar da kanta tana kame kame,
RAHAMA ce ta yi magana "oh mijina muje ka yi breakfast banason ka zauna da yunwa kasan baka gama warkewa ba, tafada cikeda kissa tareda riko hannun shi, binta yayi kamar bindi har dining table, kafin ya fisgota zuwa kan kafar shi,
" kikace ban warke ba? " yess na yarda muje ki kara min maganin my medication, yafada yana daga mata gira tareda lasar lips dinta,
Har saida tsigar jikinta ta tashi,
"Wasa fa nakeyi nasan ka warke, " noo da saura ko yanzu sai nakuma sumar miki fa ki shirya likita zai miki bayani how to handle your husband inya leka gidan dad'i,
Batasan lokacin da tayi wata irin dariya ba wadda da biyu ta yita na farko zancen shi yasa ta dariya na biyu domin su HAJARA su gane her husband loves and care for her,
Hirar su sukeyi tana feeding dinshi with full confident, har ya Koshi tana kan cinyar shi, shima yabata, saida sukayi nak kafin ya dagata kamar baby yace " muje ki kuma sumar dani baby, yayi sama da ita suka kyale su HAJARA da takaici..

HAJARA fisgar Jakarta tayi tafice domin bama tason jin wani zance daga bakin ladidi, itama mikewa tayi tabi bayanta tana zabga mata harara saida suka fita harabar gidan tasha gaban ta. " ke wai me kike nufi?
Gyara tsayuwar ta tayi tace " me kike son ki fada min, yaushe kika fara bin A yabo?
Ya mutse baki tayi irin na nafiki bariki karamar Y'ar iska, tace " kefa kika nemi Alfarmar in taimake ki to shine nafara binshi,
Kallon kin raina min wayau HAJARA tayi mata " yaushe mukayi maganar da ko tsayar da shawara bamuyi ba Amma yana maganar yasha yi miki warning, wane irin tunani kikeso inyi ladidi kefa kawata ce ta Amana me kikeso jnsa a zuciya ta,
" kisa duk uwar da zakisa banza jaka akuya tunkiya dakikiya sakarya Kawai ke inban da Abinki kece zaki min wani hanyar Auren Aliyu, in kura na maganin zawo tawa kanta. "You think a karamar kwakwal war ki ni ina sonki ne da karuwa? Banza wallahi bakin ciki nake dake HAJARA na farko duk Abinda kikeso iyayen ki suna yi miki na biyu, kinsamu miji na nunawa tsara inyarda ki Aure shi ni ina gida bazai yuwu ba,

Matsowa HAJARA tayi gaban Ladidi " kinsan tunfarko A yabo zan Aura kika zugani nabar gida? " sosai ai komai na A yabo ina bibiyar shi dake karan kanki amma ke sam bakida wayau, to saboda ni nafi kowa kyan hali sai Inbaki goyon baya ki Aure the best and the most richest prince in sokoto, ni kuma ina gida,
Hhhhhh dariyar keta tayi, kinga na fada Abinda zan iya ni nayi nan matar bello Karki manta yaufa sunkawo gaisuwa, kije ki karba kudin Auren ki kinji ni nayi gida,


Wani irin tsalle zuciyar Hajara keyi saboda shocked da kuma mamaki, yau a rayuwa Aminiyar da ka yarda da ita ce zata ci dunduniyar ka tareda nufin ka da sharri,?
Dakyar take jan kafar ta tafito tareda nufar hanyar gida mashin ta tara ta hau, duk wata irin nadama mara Amfani ce take ratsa zuciya da gangar jikin ta, a yau tayi data sanin Amincewa zancen kawa fiyeda na iyayen ta yau tana kuka da taurin kan da ta gwadawa iyayen ta. Ta gama tozarta kanta a duniya sanadin zugar kawa, Ashe bata kaunar ta bata kaunar cigaban ta, Allah ya saka mata, tsakanin ta da ladidi sai Allah ya isa,



Mashin na sauke ta taga mutane tsoffi guda uku da baba yana musu Sallama zasu tafi,
Ta gaida su a sanyaye ta shige gida, inna tasamu zaune tayi shiru tana sauraren radio, ta yi Sallama cikin sanyi tareda natsuwar da batasan daga ina tafito ba, tace inna ina kwana,
Binta tayi da ido, a matsayin ta NA uwa tana hango damuwa da kuma sanyi a tattare da ita, tace "sannu sarkin yawo da safiyar Allah har kin dauki angarar ki kinfice ko? " toh Allah yasa kigane HAJARA,
Wani irin sanyi taji jikinta ya kara yi, a karon farko tanajin muguwar nadama tareda tausayin kanta domin tariga ta hango iyayen ta basu sa damuwar ta a zuciyar su ba ita dai itace tayiwa kanta a rayuwa basu tayi wa ba,
Don haka har ta juya zata dakin su baba yace, " Ummi zo nan ya samu wuri ya zauna hannun shi rike da wata karamar bakar leda,dawowa tayi ta zauna, ya dauki wayar shi ya kira Aliyu yace in baiyi nisa ba yana jiran shi, saboda hutu yakeyi a gida a satin nan,
Cikin girma mawa ya ce gashi nan baiyi nisa ba,
Minti Biyar ya shigo gidan shima,
Tana duke a gefen inna tayi shiru kamar ba HAJARA ba,
Yace "Aliyu kafin ka zauna samo mabugi wanda idan akayi rashin kunya ka buge min ita yau sai naga tana suma tana farfadowa,
"Tofa Malam me yafaru? Inna ta fada, ya Aliyu kuwa mai jira ya ko ciro belt ya zauna, ita kuwa hukuncin ta Kawai take jira taji dalilin kiran ta, tasan dai badon yawo zaisa a bugeta ba domin baba yace kar wanda ya kuma hanata fita zata daina idan duniya ta daura mata zani mai ado, gyara zaman shi yayi inna ta kashe redion ta ta zuba kunne,


" larai Aliyu ku zama shaida yau na daurawa Hajara Aure da zabin da ta kawomin, sunzo da zancen sa rana da kayan su na nemi Alfarmar su tsaya adaura baki daya inyaso sa shirya ranar tarewar ta domin nagaji da halin ta da yawon da takemin a gari mutane nagani na da mutunci Amma tana kokarin zubar min dashi,
Don haka ga goron sa rana da kuma na daurin Aure baki daya,
Ya fitoda goro a daure a rabin farar leda da basu wuce kwara Ashirin ba sai ledar sweet guda biyu, da dubu Biyar na gaisuwa dubu goma sha Biyar na sadaki, yace to gashi sadakin ki ne wanna ya mika mata Damin cancin wanda kana ganin su kasan da kyar suka taru, ya ce ku shaida tazama matar Aure sunce ma zuwa Jibi zasu kawo kayan Auren ta tare,

Ya mike bayan ya Ajiye musu komai yayi ficewar su, kallon ta Aliyu yayi cikeda tausayawa rayuwar ta, domin yasan dai tariga ta shiga cikin jarabawa,
Mikewa shima yayi ya bar gidan jikin shi a sanyaye, domin yana hango bushewar hawaye a idanun ta ko digo ba Alamar zata yi kuka ko wani bijirewa wanda yasan badon belt din hannun shi bane akwai abinda ke cin zuciyar ta wanda ake kira nadama mara Amfani,
Suna futa inna tace ki kwashe kudinki ta ware dubu Biyar tace wanna na mu ne na gaisuwar iyaye don munada hakki akanki,

Bata iya cewa komai ba ta mike batareda ta ce komai ba ko ta dauki kudin haka ta wuce cikin dakin ta, ta Ajiye jakar ta tazauna shirim,
Yanzu ne wasu irin zafafan hawaye suka fito daga idanun ta tagama gano komai yanzu Alhaji bello ba wani Attajirin kirki bane domin magan ganun ladidi sunsa ta fuskanci bazata taba yarda taga cigaban taba ta gama sanin Alhaji bello ba kowa bane ta jona mata shi har ta kawo shi gidan su, yau mai karkab ma har andaura musu Aure,

Wani irin ihu takeso ta buga ko zataji sanyi Amma ina wane ita hauka takeyi ta kuma nuna bijirewar ta,
Bata isaba ta kuma gwada taurin kai a gidan su ba,
Haka ta danne ta cije tareda cin kukan da bazai Amfane taba,
Wazata fada mawa waye zai taimake ta waye zai lallashe ta?


********************


RAHAMA dai suna can sun kule suna shayarda juna ruwan soyayya wanda a yau ma saida tayi da gaske ya farfado da taimakon likita, wanda bata fatan yace zai kuma mai maitawa, ace mutum inhar zai samu natsuwa sai ya suma wane irin tashin hankali ne wannan,
Don haka likita yabasu shawarar su kuma komawa India domin gudun matsala kila su sutaimaka mai, akan matsalar,
Wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login