Showing 3001 words to 6000 words out of 101092 words
ya shirya, ta fada tareda cewa " kiyi ki shirya karkiyi latti kinji? "To inna nama yi wanka saura kaya kawai zansaka,
Tafada tareda matsawa gefen fanfo ta wanke jikinta tareda nufar dakin su ta shirya cikin uniform dinta da sukasha guga riga da wando da kuma hijabinta fes, HAJARA nata juyi haka ta shirya tayi tafiyar ta, kudin mashin ta leka dakin baban su ta karba,
Tafito cikin natsuwa take takunta, a gefen titi tafiya take tana kallon titin kozata samu kabu kabu amma shiru gashi zata makara, ganin ta yi tafiya mai nisa bata samu achaba ba taja ta tsaya sai motoci ne ke wucewa da gudun gaske kowa na saurin zuwa bakin aikin shi domin kasancewar ta safiya ce,
Bata Ankara ba taji kamar anyi fatali da ita gefen titi domin wani irin iska da batasan daga ina yataso ba,
Jinta kawai tayi akasa ga kafarta datake jinta kamar ta karye saboda faduwar da tayi, ganin mutane sun nufota tareda mata sannu wani saurayi ne dake wurin ya dagata, "sannu kinji halin yaran manyan garinga kenan basuda mutunci saboda sunga sunada kuddi,
Kallon jikinta tayi sai yanzu ta fahimci fatali mota tayi da ita gefen titi,
Ga farin hijabinta ya koma brown,
Wani irin tukuki taji yataso mata yaza ayi taje school a haka?
Wajen da taka motocin sun tsaya a jere guda uku kirar Mercedes Benz bakake wuluk, a bayan su An rubuta A Yabo 3 wanda take iya gani,
Ko motsi motacin basu kuma yiba,
Matashin nan yace kije gida ko in kaiki ga mashin dina kije a dubaki ina fatan bakiji ciwoba,
Hawaye ta sharce ta girgiza kai, tareda cewa " wancan ne ya bugeni? "Eh kiyi hakuri A yabo ne baida mutunci kyale shi yanzu duk wanda ya nemi zuwa kusa dashi zai sha wulakanci,
"Saboda shi waye tafada cikeda jin haushi shine mutum na farko da taji tana burin fadawa magana domin yasan d'an Adam nada baiwa da daraja,
Jan kafarta ta farayi duk da tana mata zugI ta nufi wurin motocin, ko glass din su bakake ne wuluk baka ganin kowa a ciki ta bayan ta kwankwasa, drivern ya sauke glass "hajiya kiyi hakuri oga na wacccan motar and ki tafi kawai, tunda har yace mu tsaya aga lafiyarki tukuna kinga he care,
"Bala'i ta fada wato yafi karfin ma yafito yabada hakuri,
Nufar motar tayi ana karkije karkije ta ki sauraran driver da kuma wannan matashin,
Kwankwasa kofar bayan tayi saida aka dauki kusan minti Biyar kafin Yabawa driver damar sauke glass din,
A hakimce yake cikin gedzner sky blue tana maiko, ya kishin gida kamar wani prince ko sarki, idanun shi masu daukeda black eye glass ya rufe ruf,
Saida gaban ta ya fadi ganin irin haduwar gayen da kyanshi yayi matukar yin kyau da haduwa farine tass kamar balarabe ga kanshi nan nade da sumar da tasha gyara,
Cikin natsuwa da sanyin muryarta tafara magana bayan ta tattaro natsuwar ta da kuma jarumta,
"Bawan Allah kabi a hankali ka kiyaye hakkin mutum kadaina daukar kanka wani kai bakowa bane a wurin ubangiji bace bawa dukkan mu daya muke bawanda yafi wani A wurin ubangiji face wanda yafi tsoron shi,
Don haka kadauki duniya da sauki ka cire girman kai,
Cikin natsuwa ya cire glass din idon shi da ya bayyana idanun shi masu matukar kwarjini da cikar haiba, ya bata wani disgusting look,
"How could you, impact how dere you show your ugly face to me? Yafada yana twisting bakinshi kamar dole who is your father by the way Y'ar gidan matsiya ta,
"Alhmdulillah ni ba yar kowa bace tafada cikin dacin rai domin kalaman shi is very hurt and painful,
Amma nasan darajar d'an Adam sannan nasan mutuncin ubana Amma kai da bakasan darajar naka ba shiyasa kake kokarin tozarta nawa, bakomai kanka kayiwa bani ba zaka ga sakamako kaje zaka gani, tafada tareda juyawa ta wuce yaron nan ya dauketa ya maida ita gida,
Tsawon rayuwar shi ba wanda yataba samun damar da wannan ugly face din ta samu a wurin shi shi A yabo wata kucaka ke zagi da cima mutunci, lallai sai yagano Y'ar gidan uban waye sai ya wulakanta iyayen ta da kuma tozarta su sai ya maida ita Abin kwatance cikin zafin rai yace ma driver drive and leave this nasty Area....🖊
*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻
*By FENERH*
*Aslm ina mata masu sana'oi ko kasuwanci dake bukatar Ayi muku tallar kayan ku ta yanda zaku samu customers online, to ku garzayo domin kasuwancin ku ya bunkasa zamu tallata muku Hajarku domin samun cigaban kasuwancin ku,hajar ku zata zagaya ko ina ta fadin Arewacin Nigeria har ma da kasashen makotan mu*
*munada lases masu inganci da kuma quality munada atamfofi na yayi da kuma shaddodi domin sabunta mai gida ku fito kuyi odar cikin farashi mai rahusa,akwai masu saukin kudi akwai kuma manya, ku fito kuyi tanadin sallah mata masu Aji, ance mai kwamin ido da wuri yake fara kuka siyan nagari maida kudi gida, to place your oder just give us a call 0803 343 8895*
3⃣&4⃣
Wani irin zafafe ya fito daga cikin motar bayan anbude mai tangamemen ginin gidan na kalla, , dake cikin shahararriyar Unguwar nan ta masu hannu da shuni wato Tamaje quarters, shiga yayi yana Harbin iska saboda zuciya ji yake kamar ya kuma hada fuska da wannan yarinyar yau sai yasa an shaketa couse batada ma matsayin da zai bata hannun shi ya taba ta, ko Sallama kasan makoshi yayi shi bayan ya shiga falon, wata budurwa ce kyakkyawar gaske wadda kana ganin ta kasan kanwar shi ce, ta fara ganin shi ta ce "yaya' matar dake zaune tayi saurin dagowa tace" wane ya... Shiru tayi ganin zai wuce har yakai kofar wani part, tace "kai, ba yanzu ka fitaba? Me kadawo yi? "Momy please am hurting right now I can Answer your question please,
"Don't tell me rubbish my friend, dadyn ku na jiranka a office d'an iskan ci ka dawo,
Dawowa yayi ya zube kan royal chair din dake falon ya runtse idanun shi gam don baijin zai iya Amsa ta a yanzu,
"Ikon Allah, Husna kiramin lado inji, Meya faru?
Kafin ma ta rufe baki yayi sallama, drivern shi ne Amintacce,
"Lado Meke faruwa? Cikin natsuwa ya mata bayani tareda zube mai wayoyin shi da ya kawo mai,
Kallon shi tayi tareda zuba mai idanu, kafin ta zauna gefen shi ta dafa shi, ya bude idanun shi da ke rufe sunyi mugun ja saboda zuciya,
"I pray ka canja hali, "a haka za ayi maka Auren? Please change saboda karka cutar da Y'ar mutane Al Ameen,
Gyara zama yayi da kyau' no please momy ki roki Dady ya barni in nemi choice dina,
"A yaushe? How many times yake baka lokaci? Kodai Har yanzu baka samu lafiya ba ne? Shiru yayi bai iya bata Amsa ba ji yayi gaba daya walwalar shi ta Kara raguwa, duk da zafin da ya dakko ya ragu Amma wannan zancen Auren yafi komai daga mai hankali, wai shi za ayima Auren hadi? God wace mai tsautsayin ce?
Gyara zama yayi ya ce " momy banda lafiya kunsani me yasa kukeson cutarda Y'ar mutane, " Al Ameen baka ganin ta hanyar Auren ne zamu sama maka lafiyar baka ganin idan kayi Auren ne kawai zamu tabbatar da lafiyar ka, "momy this is selfishness, idan bansamu lafiyar ba fa?
"Zaka samu insha Allahu Kaidai kayi BIYAYYA, Hmm mikewa yayi tareda kallon kanwar shi yace " bring hot coffee, ya shige,
A kwance yake bayan yagama shan coffee din shi ya runtse idanun shi yana jin tukukin bakin ciki idan ya tuna fuskar yarinyar nan, he just pray kar ya kuma ganin ta a rayuwa, domin zai iya bi ta kanta da mota saboda duk tsanar shi da mata bai tabajin ya tsani wata kamar itaba,
Second diserster kuma Auren shi wai Aure Allah yagani he is not ready, inma ya shirya baiga kalar wadda yakeso ba har yanzu shifa matar shi ma bai tunanin tana nija, baijin zai iya tsayawa da kazaman matan kasar nan ma,
Shifa ko a turai da yayi karatu matan can ma kyamar su yakeji bare kuma na nan nija, don haka he pity for that girl da wai zasu Aura mai,
**********************
RAHAMA kuwa har gida matashin nan ya kaita ya sauketa tareda mika mata school bag dinta dake shake da littafai, tayi mai godiya tareda dingisawa ta shiga gida,
Inna na kulla sugan ta na siyar wa ta shigo,
"Subuhanallahi RAHAMA ya akayi? Saida ta zauna gefen tabar mar ta cire hijabin ta da ya zama brown tace "tsautsayi inna, anan ta mata bayani dai dai HAJARA na fitowa cikin shigar Alfarma sai yanzu zataje school Y'ar hutun, idan ka ganta sam bazaka yarda Y'ar gidan malam bala bace driver tsabar dagawa da nuna ita takai,
Wayar hannun ta Infinix hot 9 ta jefa a jaka wadda tasa baban ta a gaba ya kammala salaryn shi kab na wata ya siya mata, ta ce "to iyami garin yaya mota tayi wasan kura dake?
"Banson dibar Albarka ki mata sannu shine kike neman ki mata dariya yarinya ta hadu da tsautsayi, "Allah ya baku hakuri ni natafi,
Ta Sakai tayi waje Abinta,
Inna ta tashi ta duba mata kafar tace "ai akwai targade a idan sawun RAHAMA bari inja miki, ta je ta debo ruwan dumi da tsumma mai tsabta saida ta matsa mata kafar kafin ta ja mata, da yake batada raki ko kuka bata yiba, ta shafe mata wurin da man zafi tace ta je ta kwanta ta huta,
Dakin su ta shiga saida ta tube kayan tasaka masu saukin nauyi ta kakkabe katifar da HAJARA ta barta kaca kaca kafin ta kwanta, abinda ya faru da ita yadawo mata, fuskar mutumin take hangowa, kyakkyawa Amma ba kyan hali,
Tayi saurin kawar da zancen tasha baccin ta,
*******"***************
Yau kimanin sati biyu da faruwar Abun suna zaune bayan isha'i a tsakar d'an karamin gidan nasu harda yayan su Aliyu suna cin tuwon su da miyar guro lafiyayya, taji nama da manshanu gefe daya kuwa hakima ce ke cin indomie da kwai tana yi tana latsa wayar hannun ta tana murmushi,
Malam bala yace "yar baba ki Ajiye wayar Kici Abincin a natse kinji, to tace ta Ajiye a gefe tanayi tana kallon hoton kan screen din da wata kawar ta turo mata,
Chart sukeyi a watsp
Ta turo mota hoton Al Ameen dayake tsaye a wurin motsa jiki duk abs dinshi sun bayyana da muscles din shi, jikin shi ba riga kana ganin shi kasan yana mugun jida jikin nan saboda kula ,
So take ta tanbayeta inyanada kudi tayi following dinshi a Instagram da twitter, saboda gayen karshe ne Abin mafarkin kowacce mace,
Cikin Sauri ta kammala ci ta dauki wayar ta tayi daki domin tanason taji waye shi,
Domin ita duk friends dinta ko a Facebook ba talaka bare Instagram bata hulda da marasa aji,
Cikin sauri tayi searching sunan shi bayan kawar ta tafada mata ai duk cikin samarin dake tashe yanzu a Arewa tundaga Instagram har twitter shine yafi kowa followers saboda kyanshi da kuma kyan Aljihun shi,
Wikipedia dinshi tafara searching a Google taga d'an takaitaccen labarin shi,
Like ta taba jin sunan shi Al Ameen Shuaibu Yabo,
Ta fara duba pics dinshi wasu a kasar turai wasu Dubai wasu kuma a cikin geming din shi, sai hoton shi da Husna wanda yasa lovely sister me, wanda suna tsantsar kama da yarinyar kuma daga gani he really love and care for his sister,
Tuni taji ra Ayinta ya sauya taji kawai taji she can manage him as friend kodan kyan shi don haka zata fara tura mai friends request,
Kafin ta bishi prvt ta tura mai pics dinta masu d'an banzan kyau da kuma haduwa wanda ta dauka a studio wasu a gidan kawayen ta masu hali wasu a d'an fodio,
Saida ta tura Mai guda kusan goma domin tasan idan yaganta bazai taba kin accept dinta ba, ta kashe data ta zauna tana murmushi,
Kiran babanta yasa ta fito cikeda nishadi, ta zauna, "yauwa Y'ar baba dama zancen Auren ki ne da d'an gidan Alhaji ina muka kwana? Tuni ta gimtse tareda cewa "wallahi baba nidai banaso Kudaina ma zancen nan haka kawai ni bazan Auri naka sasshe ba,
Cikin zafi Aliyu dake gefe yace "ke wai saboda kinga Ana lallashin ki kike iskanci ko to Wallahi ba wanda zai kuma lallaba ki a gidan nan ko kinki ko kin so sai andaura miki Aure in yaso ki mutu wawuya kawai,
"Bita a a hankali Ali, "Hajara Allah yagani nabaki hakkin ki na lallasheki nabiki duk yanda kikeso inbiki don haka yanzu lokaci yayi da nakeso in nuna miki ni ne mahaifinki na kuma isa dake, don haka daga yau kifara lisaafi sati na sama za a daura miki Aure, ki shirya ki cire komai a zuciyar ki,
Hakkin ki ne nariga na sauke shi Hajara da a ce yau kinada wani tsayayye ne da zan baki dama Amma bakida kowa don haka kiyi BIYAYYA zakici ribar Abin zakiyi Alfahari kinji,
Kuka ta kwantsama tareda tashi tayi daki, RAHAMA dake zaune taji sam zuciyar ta ba dadi sam baban su bai can canci butulci daga garesu ba ubane daya tamkar da dubu, tashi tayi ta nufi dakin nasu domin lallashin Yayar tata,
Tasameta ta sakawa wayar ta idanu itafa kawai Auren ne bata shirya ba ko shi wannan gayen kawai if possible suyi friendship ya isa kawai ya tsaya as her friend, don yanada kyau but he didn't deserve her,
Ita har yanzu mijinta bai isoba,
Zama RAHAMA tayi gefen ta ta riko hannun ta "yaya don girman Allah ki yi BIYAYYA zakici riba zabin iyaye shine zabin Allah nasani is painful I can understand your pain Auren wanda Bakaso baka sanshi ba and for that reason ma baida lafiya all is something Amma ki yarda iyayen mu kullum cigaban mu sukeso ba zasu tabo son mu fadi ba, bale ke kinsan baba na sonki sosai kullum yana kokarin faran tamiki ne domin yaga ya cika miki burinki, don Allah yaya kiyi hakuri,
"Wallahi baya sona tunda zai mun Auren dole, look at me Please ni za a hada da nakasashshe wallahi baya sona yafi sonki ke meyasa bazai Aura mai keba, ni Aurena wallahi Akwati sai ankawo dozen so nake a san zanyi Aure a Unguwar nan so nake masu ganin bazan taba samun mijin da nakeso ba inyi proving dinsu wrong, amma hakan bazai samuba baby sai na hada degree lokacin zan iya shiga villa ba,
"Yaya ki dauki komai da sauki king..... Yi shiru don Allah banza bagidajiyar kauye kibari ki shiga jami'a kigasan dadin duniya har yanzu kanki na cikin duhu, you don't know anything,
Wani haushin yayar tata taji, kullum kallon Y'ar kauye take mata tana mata kallon bagidajiya, bude baki tayi tace " gwara dai ki natsu Aure ba fashi tunda baba ya fito ya ce kinsan bazai taba canjawa ba, kuma in Allah yaso nima sai nayi karatu irin naku kafin inyi Auren, wayewa irin taki ta karya bana sonta, tafada tana gyara kwanciyar ta tareda janyo hisnul Muslim dinta tafara dubawa,
Kallon zanci ubanki ta bata, " zamuga wanda za a Aurawa wani banza a gidan nan ai. Bata kuma tanka mataba, don tasan inta Kara zata iya gwabzar ta,
*************
Shiri akeyi sosai domin malam bala ya Tara kudi harda adashi ya shiga domin yima Y'ar shi gata daidai karfin shi, inna kuwa tayi iya yimta domin ganin tafara gyarata Amma taki yarda kallon su kawai takeyi, RAHAMA dai bata Y'ar da da takunta ba domin tasan she is up to something shiyasa tadaina gardama da kuka Amma tasan bazata iya mata magana ba,
Yau tunfitar ta school shiru tun safe har la'asar ba labari gashi saura kwana hudu Auren ta, wanda tanajin jiya suna zancen kawo kayan lefe don haka sam bazata tsaya tasha kunya ba, in banda su matsiyata ne ace kayan Aure har saura kwana hudu sunkasa kawo kaya wannan yakara tabbatar mata da gagaruman matsiyata ne su basu jika a kudi ba,
Shiyasa ta shirya ta dinga kwasar kayan ta daya daya tana fita dasu saida ta kwashi Kala kusan Biyar, daman ta shirya bazata dawo gidan ba sai Anfasa Auren,
Wasa wasa har dare ba labarinta tun hankalin su inna bai tashi ba har ya fara tashi Aliyu yaje school din su sau biyu yau ance bataje ba, yaga babbar kawar ta ma ya tanbaye ta tace bata ganta ba, bayan tare suka shirya komai ta na boye a hostel din school dakin kawar tata,
Da aka fadawa baba kuwa tashin hankalin da ya shiga ba acewa komai zubewa yayi yana jan numfashi sama sama saboda tashin hankali,
Gashi ta kashe wayar ta,
Ranar sam basuyi bacci ba a gidan,
Gashi ankawo akwatuna saiti uku kowanne fadin dukiyar dake ciki bata bakine harda makullin Camry new morthen, Alhaji shuaibu da kanshi ya kai akwatunan domin bayason Y'an Uwan shi su ga inda zaiyiwa d'an shi