Showing 24001 words to 27000 words out of 101092 words

Chapter 9 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37767

wane tuggu ta hada musu ba har momyn shi ke kokarin kashe Auren,
Kuka tasa Amma bana nadama ba, "wallahi yaya ni bani nasa aka dauke taba dama ba kaunar ta yakeba cusa mai kukayi yanzu dole a...... Wani irin hambari ya kaimata, tareda Zaro belt,
Inna tace tsaya Aliyu kafin ka kasheta infada mata Kalmar da bansamu fada mata ba tun a farko kar in tabka asara,

"HAJARA bamu kika cutaba kanki kika cuta a rayuwa, munfita hakkin ki koda kika gudu kika dawo gidan nan ubanki hana yayi a duke ki, Amma saboda sharri kika kwashi kafa kika tafi gidan Y'ar uwarki kika shara mata karya mu mun koreki, kalma daya kawai zanfada miki yanzu "wallahi duk Abinda ya samu RAHAMA ko rayuwar Auren ta bamu yafe miki ba HAJARA duniya da lahira banyafe miki ba kuma duniya ce gata nan ta isheki riga da wando, wanda ma bai shigota ba jiran shi takeyi,



"Kai kuma inka kasa kasheta inada fiya fiya zan kanbada ma tanbadaddiya murage ire iren ta a duniya, ta shigewar ta dakin ta ta datse tareda kunna katon redion ta,
Ai kuwa dukan kawo wuka ya mata har saida ya ji bata motsi yajata dakin su ya wurga ta ya kulle ya fice, duk da haka baiji sanyin Abin da ya mata ba bai gama gamsuwa ba, saida ta dauki dogon lokaci ta farfado bakinta idonta fuskar ta ko ina ta kunbura saboda dakuwar da tayi, Aliyu mala'ikan daukar raine na duniya baida imani kona anini don ina kallon fuskar HAJARA nace Kuth dama Soja yayi kawai don suke canja kamannin mutum cikin minti biyu, don inka ga fuskar ta bazakace wannan hajon bace bai ji da kyau da kuma kwalliya,

Dakyar ta iya motsa kugunta tana Allah ya isa a cikin zuciyar ta domin bazama ta iya magana ba saboda kunburin bakinta,
Amma ta kudurta koda zai kasheta bazata taba goge kudurin zuciyar ta ba,


*****************
Yau RAHAMA ta kuma yarda da al marin Al Ameen dole yayi girman kai ganin irin gidan iyayen shi duk da ba irin nashi bane ta san cewa shi din d'an gatane da dole yayi girman kai, momy ta zaunar da ita tabata hakuri domin tasan ta tsorata ta da fada a, farko, "RAHAMA kiyi hakuri, ni na haifi Al Ameen nasan rayuwar shi, don haka kiyimin biyayya kamar yanda kikayi wa iyayenki zakici ribar Abin kinji,
Toh tace batareda ta nuna komai ba momy ta shinfida mata hujjojin ta tace nasan ke ya'ce mai biyayya da hakuri don haka bazaki tabema dole kiyi dariya kiyi farin ciki a rayuwar ki RAHAMA kema sai kin shigo gari yanda ba macenda zata nuna miki isa,

Dole sai kin daura damarar yaki da gidan Auren ki akwai kalubale a cikin rayuwar kowane zaman Aure don haka ki zage damtse ki koyi zaman gidan miji wanda koda Aure Al Ameen yakara kizama gwarzuwar shi a zuciya,
Haka momy keta tattalin ta, daga baya suka shige dakin Husna dake zaune tayi shiru, tana ganin RAHAMA ta zabura, tace yauwa sister in low ke nake jira, ta riko hannun ta suka zauna gefen gadon, tace "tell me About your brother, "me kike sonji akan shi? Labarin budurwar shi,
Murmushi tayi tace "ai yaya baida budurwa Amma Y'an mata nabin shi sosai, yace bazaiyi Aureba sai yaga ya wadata iyayen mu,

"Allah sarki shima yanada zuciya mai kyau, Amma haka yake baya magana da mutane? "Eh haka yake, kice halinku daya da yayanki sister inlow, tafada tana dariya,
RAHAMA tana cikin damuwar halin da Al Ameen ke ciki gashi har yanzu bai zoba she thought zai biyo bayansu, she is very worried, haka ta wuni sukuku a gidan duk da momy da Husna na iya bakin kokarin su,

Al Ameen kuwa yayi matukar daukar zafi don gani yake da RAHAMA ta nuna bazata bisu ba bazasuce zasu tafi da itaba, don haka ya nuna zuciya yaki ko zuwa gidan, Baban shi ya kira da shigowar shi kenan gari yace "Dady zan tafi gobe inga doctor, "to Allah ya kiyaye zaka iya tafiya Abuja yau gobe katashi you have everything, "yes dady Amma momy ta dauki RAHAMA yafada cikeda fatan Allah yasa dadi yace yazo ya tafi da ita
"Haka nada kyau ba damuwa nima yanzu na shigo zan fara duba office kafin intafi gidan if you like zaka iya zuwa mu hadu a office din sai ka wuce, in kuma kana sauri sai ka dawo ko ince sai munyi waya, ya datse call din, batareda ya jira cewar Al Ameen din ba,

Don haka yasan cewa koma meye yasan da yardar shi momy keyi don haka yasan ba wani Amfani da zuwan zaiyi mai gidan,
Kayan shi ya hada ya tattara ya fito tareda kudurin bazai dawo ba sai sun gaji sun nemo shi,
Yaron shi Amintacce ya kira tareda damka mai komai ya mika mai wani envelope yace ya kaiwa RAHAMA ya fada mota ya dauki hanyar Abuja zuciyar shi kamar transformer saboda zafi.......... 🖊




*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



Free page

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*


Free page



1⃣7⃣&1⃣8⃣



Mayarda hannun shi baya yayi ta fada kan kirjin shi, ya saka hannun shi daya ya riketa a kirjin nashi tamau, yana kallon yanda take kokarin, karbar brah din, jin yanda ya damki kugunta yasa ta natsu tareda kokarin barin jikin shi, yayi murmushi tareda fito da brah dinta da ga gani sabuwa ce mai kyau, milk colour kamar bata sakaba, ya zubawa kokon ido yana tunanin how big they are,
"Size dinki ne wannan? Yafada yana mata wani irin murmushi, ta dunkule fuskar ta tareda cusata cikin bear chest dinshi, saboda kunya, ya yi wata irin dariya mai Kara tareda jan numfashi saboda yanda take cusa fuskar ta cikin kirjin shi, tuni ta sakashi cikin wani yanayi,


Dora bra din yayi saman hancin shi ya shaki kamshin tareda Kara shigar da muryar , "RAHAMA dago kanki please kigani, kasa dagowa tayi saboda kunya hannu yasa yadaga ta cak zuwa gadon ya direta tareda ajiye bra din ya ce ki dago kanki ko in tube ki inga nonuwan a fili inga karshen kunya, wani irin kunya taji ta Kara rufeta wanda yasa ta d'an bugi kirjin shi cikin wani irin salon da ya tafi dashi har yayi wata irin dariya Mai cike da nishadi da jin dadin yanayin,
Wani irin kukan shagwaba ta sakar mai "please kadaina tafada, "ok nadaina ki dago muyi magana,
Cikin rusunar da kai ta dago kanta batareda sun hada ido ba, ya fuskance ta tareda riko hannun ta,

"RAHAMA, batareda ta iya Amsawa ba takalle shi tareda sauke kanta, ", kiyi min Alfarma, ki taimaka ki yafewa mijin ki, I no I hurt you, nasan ban kyauta miki ba, I misunderstood you, I thought kema irin Y'an matan da ke bina ne,
Na fahimci cewa ke tadaban ce tun ranar da kika kwana gidan nan na fuskanci ke tadaban ce, bansan Allah yamin baiwa ba sai da Aliyu ya fada min komai, he tell me everything about you, kuma nagani,
Nasani am not too good, amma Allah yamin baiwa da samun mace mai Addini mai hakuri mai tausayi,
I no kina son Y'ar uwar ki ta shiryu bakyaso ta fada wani hali, and I no idan na koreta you want be happy with me, "wallahi I leave her because she is your sister, yau da ace ba Y'ar uwar ki bace I want let her stay here with us batareda na dauki mataki,
"Taci darajar ki da tasu baba, domin basuda laifi, sunyi kokari wurin baku tarbiya, wanda da ace ita na Aura da farko bazan taba ganin mutuncin su ba Amma zama dake yasa na yarda cewa that's her way haka ta zabawa rayuwar ta,
Forgive me if I hurt you,


Yafada yana karkace kai kamar wani yaro mai neman alewa a hannun maman shi,
Girgiza kai tayi tareda da cewa "I no nasan is not easy for a man like you to accept unexpected marriage, sannan kana tunanin nayi ma rashin kunya da first time da muka hadu,
And about yaya HAJARA, kayi hakuri da duk Abinda ya faru, she is my elder sister tausayi take bani saboda tana cikin fushin su baba, Abu kadan za ayi mata yanzu ta nemi barin gida wanda duk kawaicin su baba bazasuji dadin hakan ba, domin duk Abinda yaje yadawo za ace Y'ar su ce,
Magana takeyi cikin taushin murya da tsananin hangen nesa da kuma kaunar Y'ar uwar ta, wanda sam bata son ta fada halaka ta sanadin fushin iyaye,

Kara rike hannun ta yayi, "Alhmdulillah, ya furta a bayyane, " you are a good wife good daughter and a good sister too , Allah ya bani y'a kamar ki mai halinki mai zuciyar tausayi irin taki RAHAMA, but kin iya komai a rayuwar ki saura Abu daya,
"Mene? Ta fada, "kula da miji, yafada cikin rage murya,
Zanfara daga yanzu, tafada tana Dukar da kai, "kin yafemin kenan zaki zauna dani? "Yes kamar yanda nayi Alkawarin yiwa iyaye na biyayya kaima zanyi ma biyayya insha Allahu,


Ajiyar zuciya ya sauke yanajin zuciyar shi ta samu wata irin natsuwa ji yake kamar shi yafi kowa sa'a, "na gode don haka gobe ki shirya zamu fita muje gidan mu muyi musu sallama we are leaving this country cikin Satin nan zanyi miki visa dama zanje ganin doctor,
Yafada yana kallon cikin idonta, kallon shi tayi cikin ido, "bakada lafiya ne? "Eh yeah bakisan tarihin mijin kiba ko? Ta girgiza kai "am sorry baby I have to tell you everything about me, before I don't care about my health but now komai ya canja saboda ke inason in zama kamar kowane namiji, duk da Alhmdulillah because of you am getting better, amma doctor yabani advice before everything happens between us inje su dorani akan sabon medication,
"Meke maka ciwo? tafada, cikeda tausayin shi domin tasan duk ciwon da zaisa sai anfita waje is serious,
Murmushi yayi tareda cewa " kinsan machine gun?

Cikeda wauta tace" bindiga ce ai, "yes kowane namiji nada ita a jikin shi, nima inada ita saidai batada lafiya dole inje inga likita, duk da tawa saboda ke tafara aiki kadan Amma har yanzu bullet basu isheta ba, so pray in mukaje kafin mudawo tawa tayi full da bullet, tace yanzu a jikin mutum akwai bullet? 🙄 Tafada cikeda wauta da rashin gane zancen shi, "sosai akwai bullet a jikin namiji, bari ma ingani ko akwai saura a jikina, yafada yana daga hijabinta, tayi saurin rikewa,

"Inkina so mushirya let go of this hijab, saki tayi jikinta a sanyaye, ya cireshi tareda kai hannun shi saman sumar kanta dake dauke da ruwa Alamar ta jikashi, ji take kamar ta nustse kasa saboda kunyar yana kallon jikinta" baby wankan tsalki kikayi kenan? Yafada yana kallon cikin idonta, "girgiza kai tayi cikin sauri, "ok bari insa kiyi tom yafada tareda kwantar da ita ya kashe hasken wutar dakin ta hanyar dan na wani Abu a jikin gadon tareda kunna wata mai matsakaicin haske. Wanda hakan ya mata daidai domin sam batason yana ganin ta ba hijabi,

Jin hannun shi tayi akan bayan ta tana zuge zip din rigarta, ta runtse idanun ta domin batason tamai musu sam don haka tanaji tana gani ya kwabe rigar jikinta Tayi saurin kifewa saboda kunya, yayi murmushi tareda Sa hannu ya juyo da ita cikeda dauriya, domin tun daga kan fatar jikinta da yake tabawa yafara gigicewa, lokacin da ya juyo da ita kuwa confused yayi, yafara gwama numfashi tareda tattaro jarumta ya gyara kwanciya a gefen ta ya juyo da ita tareda zubawa kirjinta ido, subuhanallah, inji balarabe, shine Kalmar da yafara jerewa ganin yanda Allah ya gama tsara mata komai nata na musamman,
This is the must precious thing ever, hannun shi na trumbling ya yi saurin kai cafka, wanda kana ganin yanda ya nufesu kasan yanada yunwar taba su a cikin zuciyar shi, saida tayi wani irin yunkuri saboda zafi ta fada jikinshi, domin tsawon rayuwar ta ba hannun da yataba taba wurin she can believe yau Al Ameen Shuaibu Yabo ne ke wasa da jikinta,
Wani irin wasa yafarayi da ita naban mamaki tareda hade bakinsu yana bata wani irin karatu da sam bazata iya haddace shi a lokaci dayaba,


Wani irin feeling da strong erection ne ya taso mishi na fitar hankali wanda ya janyo ya farajin wani irin ciwo a marar shi tareda zafi, tuni jikin shi yafara, shaking yana mazari, tareda hada zufa, tuni ya saketa ya mirgina gefe yana juyi tareda jujjuya kanshi,
Ahankali take bude idanun ta domin tun lokacin da yafara ya mutsa lafiyar jikinta ta rufe idanun ta gam ta kasa budesu jin yanda yake numfashi, kuma yabar jikinta yasa ta zabura taga ya dafe ciki,
Abin ya matukar tsorata ta ta zabura ta rungume shi tana kiran shi wanda batasan daga ina ta riko sunan ba "Meke damunka? Tafara tanbayar shi cikin rudu,

Yana fisgar numfashi yace "don't worry bring water for me, yabata Amsa muryar shi na cracking, da gudu ta dira batareda ta damu da rashin rigar jikin ta ba ta bude firij din dake dakin ta dakko mai ruwan gora mai sanyi ta kawo tareda balle bakin ta mika mai, ganin yanda yakeyi yama kasa tashi da kyau yasa ta daga shi tareda sakamai yasha sosai tareda karba ya zuba a hannun shi ya shafa a saman marar shi, ya mika mata sauran, karba tayi ta mayar tareda mayarda rigarta ta koma waldrop din shi ta samo mai jallabiyar da yaki karba tunfarko,

Ta mika mai tareda boxer ganin yanda yake rawar sanyi, duk ya bata tausayi saida ta taimaka mai yasaka ta jamai bargo tace ya kwanta ta rufeshi, hannu yasa ya janyota jikinshi tareda, rungume ta domin samun dumin jikin ta,
Kasa bacci tayi domin sababbin Al amuran da suka tunkarota a yau nafarko ta cakudu na biyu wannan lamarin da taga ya shiga na d'an lokaci wanda yanzu yafara sakin shi, "kodai shine ciwon nashi,? Tuni taji yabata tausayi,
Ta juya tareda zuba mai idanu tana kare mai kallo, a gaskiya baida makusa, tanajin wani irin Yanayi na ziyartar zuciyar ta, har batasan lokacin da itama baccin ya tafi da itaba,



HAJARA dai zamuce ranar da bakin ciki ta kwana wanda, ta dauki kuduri daban daban a zuciyar ta akan RAHAMA ta dau Alwashin indai tana numfashi to dole RAHAMA ta kunshi irin bakin cikin da take Kunsa a yanzu,
A zaune ta kwana a, falon har safe wuyanta duk ya rike, saida RAHAMA ta fito shirya musu breakfast ta ganta a takure a zaune, ta matsa tareda tabata" yaya a nan kika kwana?
Buge mata hannu tayi tareda zabga mata harara ta wuce Abinta zuwa ciki domin yin wanka, wucewa RAHAMA tayi kitchen domin nema wa Al Ameen Abinda zai karya, domin har yanzu jikinshi akwai zazzabi,



Karfe Tara na safiyar ranar Husna ta iso gidan lokacin yana bacci a ciki RAHAMA na gyaran kitchen bayan ta gama Bashi break fast, Hakima na zaune a falon ta ci ado tana kallo, Husna ta yi sallama kusan sau uku ko kallon ta batayi ba sai wani irin yatsunta, fuskar da tayi tana kauda kai kamar taga kashi,

Husna tace "kan uba a zuciyar ta tana mamakin wacece ita? Saida ta iso tsakiyar falon tace "matar yaya ina kike? RAHAMA ta fito cikeda murna don ta jiyo muryar Husna, "Oyoyo tafada cikin sabo da kuma kewar ta da tayi, tace " ina brother ina jin baida lafiya na taso momy ma na hanya ta biya wani wuri ne,
Cikin kwarkwasa HAJARA ta taso tareda cewa" lah kece dama kanwar A yabo? Ai bangane kiba da farko, wow sannu da zuwa, tafada tana washe baki, RAHAMA cikin jin kunya tace "yaya tace tazo, "oh Husna tace, kawai tace ina brother yake,? RAHAMA tace yana ciki,
Yaji sauki, "muje ki rakani, no jeki ina wani aiki inna kammala zan shigo, tafada, tsumbul HAJARA tace muje nima inganshi bansani ba ai munkwana gida daya saboda mugun hali kin kasa, fadamin baida lafiya, ta buga tsaki tareda yin gaba ko ta Husna batabi ba,


Baki da hanci Husna ta saki yau tana ganin ikon Allah, RAHAMA kuwa ai ita yanzu inda sabo tasaba da ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login