Showing 93001 words to 96000 words out of 101092 words

Chapter 32 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37786

rude, binshi tayi tana " kai lafiya Meya faru kaga damar fitowa, ina Aminar?
Ko amsa daya bai iya bata ba ya gama gigicewa saida suka shiga dakin yace "taki tashi nasa mata ruwa taki tashi ki taimake ni grandma I start loving her karta tafi tabarni inta tafi bazan kuma Aure ba please help me d'an kauda kanta tayi ganin bakomai a jikin meenal din sai ganin jini datayi kwance kamar anyanka a kuya,

"Subuhanallah kai kuwa wane irin yarone wai Kwana kayi kana murza Y'ar mutane Sadiq, gadon ya haye ya dagota Yana bubbuga ta " meenal ki gashi haka please in bakyaso bazan kuma yiba please kitashi Karki tafi kibarni don Allah,

Dago kanshi yayi idanunshi sun juya yace " grandma kin tsaya ki taimake ni mana kar matata ta mutu please, " ai dole sai momyn ka tazo ni ba aiki na bane wannan, zabura yayi ya fita da gudu a falon sukaci karo ya riko ta " momy zo kigani taki tashi please, tuni RAHAMA ta rude ta bishi don zuciyar ta tabata komai,


Koma hayewa zaiyi gadon bayan shigowar su RAHAMA ta buga mai tsawa " kai zoka fita kaji ko bani wuri mara hakurin banza kawai shugaban zalamammu kana kokarin kashe min yarinya shiyasa kaki bari ta fita tundazu ace tunjiya ka hana yarinya sukuni saboda masifar jaraba, grandma dake tsaye a rude ta Kalla " momy wallahi Kifada mai in wani Abu ya samu yarinya ta sai ranshi ya baci sai nayi mugun saba mai,
Jibi irin haukarda yayi ma yarinya,

"RAHAMA ki duba yarinya ba fada ba, grandma ta fada, don haka cikin sauri ta dauki gorar ruwa saida ta shafa mata a fuska sannan ta watsa a kirjinta ta danna sau biyu kafin ta janyo numfashi tadawo duniyar da muke ciki, Yana tsaye ko motsi baya yi yana kallon ta ji yake kamar ya kurma ihu saboda damuwa,



Yana ganin ta dawo ya dafe kirjin shi ya fesar da numfashi mai zafi "Alhmdulillah, ya furta a fili, sai a lokacin grandma ta iya matsawa kusa tareda mikawa RAHAMA towel tace daura mata bari in hada mata ruwan zafi, " aa momy ja wannan yaron yabarmin dakin nan kawai zan kimtsata, tafada tana daga ta ko kuka bata iya yi saida momyn ta sakko daita ne tsayuwa ta gagara kamar mai kaciya ta runtse idanun ta tace "washhh, da sauri ya matso zai riketa RAHAMA ta buga Mai tsawa karka taba min yarinya kaji, kallon gadon yayi har zuwa inda take tsaye jini na zuba kamar wadda ta haihu,


Grandma duk ta rikice tace "RAHAMA kiduba yarinyar nan bleeding fa takeyi,
Harara ta watsa ma Sadiq " badole tayi bleeding ba momy fa period takeyi ya hauke mata , "tafa gama momy yafada Yana dukar da kai,
" kayi min shiru sakarai ba jiya tafada min ba shine don rashin kiyaye iyakokin Allah ka ketare ka afka mata saboda abin guduwa zaiyi,

"Wallahi momy ta gama yau ta tashi ba jini kuma koda nake cewa Tagaji ni ba Abinda nayi mata da dare kutanbaye ta yafada Yana kokarin kallon fuskar ta da tun da ta farfado bata ko kalli saitin shiba,
Iya ruwan azabar da za ayiwa mutum yau sadiq ya shayar da ita,


Grandma tace " yaran yanzu sai Abarku wallahi RAHAMA jida ita kyale nidashi, "momy gwara infada mai karta huce yanzu, kodan gobe, ace mace tagama Al ada ko Kwana ba ayiba ka hauke mata mahaifa na nan a bude ba dole jinin ya kuma ballewa ba wannan jinin jikinta ne ba wani ciwo duk da ciwon ma bansaniba muje Amina ingani, tafada tana riketa, dakyar take takawa har suka shiga bathroom din Yana kallon ta,

"To zo mutafi kafin su fito, grandma tafada " ni ba inda zanje gaskiya sai naga lafiyar ta, zanbarka da momyn ka kuwa ku karata, gadon ya Kalla ya matsa tareda yaye shi ya zuba ruwa jikin katifar ya sa wani towel ya goge tas jinin da yayi staining grandma na kallon shi ya ciro wani zanin ya shinfida, fadin dadin da yakeji bata bakine so yake suyi suyi subarshi da ita yafara tattala ta zaiso tayi ta koma gidan shi inda sam basa idawa,


A ciki kuwa gasa ta Rahama tayi sosai ta duba taga bawani rauni sai kunburin wahala, saida tayi mata sit bath yakai sau uku ta sata tayi wankan tsarki tana tausaya mata don ita dakanta tasan meenal nada aiki don dagani Sadiq yamafi ubanshi zalama,


Towel kato ta dauro suka fito tana cije lips domin wani irin barkono takeji akasan ta har yanzu, ganin shi a zaune yasa ran RAHAMA ya baci ta duba taga hijabin ta tace " ungo saka mubarmai dakin kinji, zurawa tayi domin ita kanta bazataso ta Kara koda second daya tareda shi a inuwa daya ba tunda yagano ita din cikakkiya ce to jikinshi zai gaya mishi,

Ga uwar wahalar da yabata ko tausayin ta baiji ba, don haka ta shirya juyashi kamar waina kafin su daidai ta sai ya mata confess saita koyarda shi soyayyar ta ko zata Bashi wata damar, don haka taji mugun dadin faruwar wannan Abun a nan gidan bazata taba nuna ta warkeba yanzu bare ace su koma gidan su,


Fita sukayi daga dakin ya saki baki yana kallon su domin tuni grandma ta tafiyar ta tabarshi, " oh no momy why yafada bayan sunfita, he want to talk to her and apologize, shi mai laifine a wurinta gata ta shsyarda shi zuma mai wuyar mantawa meenal Y'ar baiwa ce komai nata is absolutely perfect jikinta maganar ta her life style uwa uba kogin zumar ta dake cikeda ruwan dad'i,

Wani irin shauki da nishadi yakeji a kasan zuciyar shi, don haka fadawa yayi kan gadon ya na mai runtse idanun shi yana tuno moment dinsu da ya wuce jiyayi kawai zaiso ya kuma samun kanshi cikin wannan yanayi, "kai Aure yayi a rayuwa yafada yana mulmula tareda wurwurga kafafu kamar Han kaka,



A gefen Meenal kuwa kaya momy tabata tasaka ta bata pain relief tasha tasa taci Abu mai ruwa ruwa ta hada mata wasu tsimi ta mika mata tareda bata tace kafa kai kishanye Zakiji daidai kinji, karba tayi tasha sannan ta haye gadon momy ta kwanta, fitowa tayi ta barta, shiru tayi tana tuna yanda taji yake kuka dazu tareda sambatu, kodan baya cikin hayyacin shine? Koma dai meye yau yasan cewa ita din ba watsatsiya bace, bacci mai dad'i ya kwashe ta,



Shiryawa yayi ya fita domin ana kiran shi a wurin aiki, yaso yaganta amma momyn shi tasaka mai mugun takunkumi harda iyaka ta samai karya sake taganshi a kofar ta, wanda yasan is impossible bari dai yadawo dole abashi matar shi he need privacy baya bukatar wani takura,



Fita yayi cikeda nishadi har wani shekin angonci yakeyi fuskar shi a sake take a yau ba wani cin Magani goshin shi na kyallin Amarci har wani sude baki yake inya tuna, "meenal yafada yana shafo kirjin shi ai yana gama uzurin shi zai dawo su wuce inda zai sakata ya wahala yasha Amarcin shi yanda yakeso...... 🖊




*mata akwai kuloli afito a yiwa oga siyayyar Azumi akwai masu sauki da rangwame akwai nakaiwa villa munada plates harda dinner sets munad kayan kitchen Kala Kala harda su show glass akwai gas cooker masu oven akwai masu hade da electric akwai table gas cooker munada stainless steel munada pure glass karku manta duk wadda ta bada kudinta kuma kayanta yaje hannun ta ta sanar mungode*




*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*







*Domin masu son biya har yanzu hanya a bude take kubiya ku karanta cikin Aminci bawai na bati ba, kutura cikin Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb ko kuma katin Airtel ta wannan number 09011251444 sai najiku*


8⃣1⃣&8⃣2⃣


Har dare bai samu lokaci ba domin aiki ya rikeshi gashi baida number ta bare ya Kira yaji how she is? Ya Kira grandma ta ce bazata kai mata ba tunda baida tausayi yana neman halaka Y'ar mutane, dariya kawai yayi ya kashe wayar shi, a ranar kam duk yadda yaso ya dawo Abu ya gagara saboda sunje akan case din wasu illegal kaya da aka shigo dasu ba akan ka'ida ba, dole acan ya Kwana Amma duk tunanin shi na gareta kaida kai idan ya tunata murmushi yake fitarwa nishadi yakeji mara misali a zuciyar shi,


Gefen Meenal kuwa ranar bacci tasha sosai wanda koda ta tashi taji sauki sosai ga jinin ta daya dawo da gaske, Sadiq bala'i ne gaskiya ya gurjeta bana wasa ba,
Idan ta tuna dashi wani irin dad'i takeji itace yau ta mallaki sadiq dinta datake mafarki tasani koda bayason ta tasamu daraja mai girma tunda ta kaimai Abu mafi daraja, shine budurcin ta wanda tasani tayi matukar siye zuciyar shi da shi don ko irin ruwan sambatun da ya zuba mata kawai ya isa tasan shi mayen Abun ne,


Duk lokacin da ta motsa taji zafi sai yafado mata a zuciya, a hankali tafara tunanin son ganin shi a lokacin so take taga wane irin tattali zai nuna mata, saidai har dare bata ganshi ba Abun ya d'an dameta don har fitowa falon tayi ta zauna kozata ganshi Amma har karfe goma shiru, dole ta koma dakin momy ta kwanta Abinta tana tunani har bacci ya dauketa,



Karfe bakwai na safe ya iso gidan a gajiye badon yana son ganin taba gidanshi kawai zai wuce ya huta Amma idanu da gangar jikinshi na matukar kwadayin ganin ta,
Suna zaune a falon itada RAHAMA da kuma grandma, wata zuma takesha a cikin wani karamin cup da d'an mitsilin cokalin roba shanta takeyi a yangace kamar bataso nan kuwa zumar shegen dad'i take mata, domin taji hadi a cikin ta RAHAMA ce ta Ajiye mata tace tayita sha,


Sallamar shi tasa suka dago kansu baki daya tareda Amsawa, idanun shi akanta suka sauka tana cikin doguwar rigar Material ja tayi matukar yin kyau ga kanta ta daura d'an kwali sumar ta a gefe,
Wani irin sheki takeyi na Amarci, jiyayi zuciyar shi ta narke da wata irin kaunar ta, takawa yafarayi a natse,


Itama kallon shi tayi takasa cire kyawawan idanun ta akanshi domin yayi matukar tafiya da zuciyar ta cikin kakin nashi na custom ga kanshi ba hula duk da ya gaji tana ganin shi tasan he is exhausted amma bai hanata ganin kyanshi ba da kuma cikar haibar shi,


Cikin natsuwa ya karaso baya ko kyafta idanun shi gefen ta ya zauna ya d'an lumshe idanun shi domin ya shaki wani irin kamshi mai jan gangar jikinshi zuwa gareta ji yake kamar ya fisgota ya tsotsi bakin nan me lasar zuma cikin wani irin salo mai tafiya da ruwan jikinshi,



"Allah ya yi maka dawowa? Grandma ta fada, sai a lokacin ya dawo cikin natsuwar shi ya tuna akwai mutane ma afalon domin gaba daya idanun shi sun rufe baya ganin ko momyn Nashi bare grandma,
"Sorry grandma am lost ne wurin kallon wife, nadawo wallahi am very tired tunjiya ban runtsa ba, yafada yana yi yana kallon idanun meenal da taki yadda su hada ido, again,


Juyawa yayi ya gaida momyn shi " momy good morning, "morning, ya aiki? Alhmdulillah yafada, mikewa yayi "meenal bring my breakfast to my room ya wuce dakin Nashi domin mugun so yake ya kebe da ita ya kwashi wata garar he don't care koda zata kuma bleeding as far as zai samu dad'i irin na jiya,


Yana wucewa tabi bayanshi da kallo Sadiq namiji ne son kowa gashi jarumi ta shaida,
Mikewa tafarayi RAHAMA tace koma kizauna bari akai mai, mai aiki ta Kira tabata umarnin ta hada mai komai takai mai dakinshi,
To ta amsa ta wuce saida ta hada ta wuce lokacin ya mugun matsuwa bata shigoba jiyake kamar ya ruga ya dakko ta, yaji Sallama, juyawa yayi lokacin har ya tube yana daure da towel ta turo kai da tray,

Wata uwar tsawa ya buga mata "ke uban wa yabaki izinin shigowa? Go back, yafada yana nuna mata hanya yasan aikin momy ne wato meenal bazata zoba, kota kan saka riga baiyi ba haka yafito da katon kirjinshi a bude ya nufo falon,

"Ke meenal bake nace kikawo min breakfast ba? Shine don wulakanci zaki turo mai aiki, kodaga kanta batayi ba saida momy tace " nizaka Kalla kafada min ba itaba domin umarni na ne sannan don rashin kunya kafito har tsakiyar falo ba kaya,

Shiyasa ta daga kai ta kalleshi, saida taji wani iri ga Y'an mata masu aikin gidan dake kaida kawo wani irin kallo tabashi wanda yagano ma'anar kishin ta ya nuna mata da ido ta taso kin tashi tayi domin bazata iya tsallake umarnin momyn ba,

Karasowa yayi ko a jikinshi ya zauna yana facing dinta, duk fadan RAHAMA a banza karshe mikewa tayi tabar mai falon tana cewa " ka gama ruwan iya shegen ka zanyi maganin ka,
Murmushi yayi kawai yana kallon reaction din meenal kallon shi takeyi kur alamar batason me yakeyi,

"Meenal tashi ki wuce dakin momyn ku kinji, grandma tafada domin tundazu batace musu komai ba kallon labaran ta takeyi Aljazira mikewa tayi tafara tafiya a hankali domin har yanzu ciwo takeji a kasan ta, bin kafafun ta yayi da kallo kodai ya jimata ne? Gaskiya Sadiq ka buga aiki yafada yana shafa kirjin shi yanajin wani irin nishadi, har saida ta shige dakin RAHAMA yadawo da kallon shi kan grandma,

" wai me ake nufi dani ne a gidan nan? Yanzu kiri kiri kunaso ku haramta min matata, wai iyaka kukemin da ita ko me? " jeka tanbaya uwarka RAHAMA kaji,
Daure fuska yayi "wai me yasa kikeson zagin iyaye na, " ka rama kawai, "ni na isa inzagi uwargidana ya tashi zai matso " kaga wuce kayi Wanka ka karya ka huta,

"Grandma please kibari matata tazo kusa dani duk zanfi jin dadin komai, " ka taimaki yarinyar nan Abubakar karbata ta huta yanda kake zalamar nan zakaja yarinya ta nemi gudun ka, " kaji ki wace mace ta taba gudu da za afara ta kanta please nidai kubani ita mukoma gidan mu,

"Ai saikayi tafada tana kyaleshi, mikewa yayi ya wuce dakin shi a zuciye, wanka ya yi yadawo ya kwanta ko takan Abinci baibi ba saboda haushi suna so su hanashi sakewa da iyalin shi wallahi shiba dadyn shi bane, ai yaji labarin komai wurin grandma shi bazai iya Wannan hakurin ba da sake,
Murmushi yayi kawai ya kife sai bacci, Bashi ya tashi ba sai karfe shabiyu na rana a lokacin yaji yunwa na neman kaishi, dole ya kuma yin wanka yafito domin yanema Abinda zaici, kitchen ya shiga saida ya kwankwadi madara mai sanyi kafin ya nufi dining don har ankammala na rana ya ci yayi kat sannan ya fita,

Gidan shi yaje yabawa mai aikin shi umarnin ya gyara mai ko ina yau madam zata dawo kafin ya Bashi kudi yace ya siyo duk wasu kitchen stupes da babu na Amfani, bai koma family house ba sai da dare lokacin kowa ya nemi makwancin shi,
Ita kanta meenal tana kan gadon RAHAMA tagama chart da Y'an Uwan ta bacci mai dad'i ya dauketa ya shigo gidan, dakin momyn ya nufa ya tura a hankali saida ya kunna haske yasan for sure momy na wurin dadyn shi yanzu domin basa taba Kwana a rabe yasani saidai in dadyn baya gari

Nade hannun shi yayi ya zuba mata ido tana bacci cikin wata lallausar nightie pink fuskar ta tayi fayau ga wayar da tagama chart saman kirjinta, matsawa yayi ya zauna tareda sanya hannun shi ya cire wayar " you are my rival tunda kika hau wurinda nikadai nafi can can ta in haushi, Ajiyewa yayi a gefe ya zubawa kirjin ido he can see their shape harma da kansu ta cikin rigar kasan cewar ba wani kauri gareta ba, yatsanshi ya dora akan su ya zagaya, tuni yaji komai ya fara Kunce mai lissafi,

Tuni ya ware hannayen shi ya rukesu gam gam yana miysikawa tareda runtse idanun shi wani irin dadi yakeji har cikin kwakwal war kanshi,
A hankali take jin jikinta na sauyawa cikin bacci domin touching din nashi dayake mata cikin wani irin salo, jitayi har tana tsiyaya saboda ta tsumu da salon saurin zabura tayi lokacin da ta bude idanun ta taganshi a zaune yayi dumu dumu da kirjinta, jin ta janye yasa ya bude idanun shi,

'Kintashi yafada cikin basar wa kamar bawani Abu yakeyi ba, mugun mamaki yake bata yanada karfin hali, "tashi mutafi yafada yana hade fuska domin yasan inya tsaya lallashi bazata tafi ba,
Jan bargo tayi tareda rufe jikinta "ina zamuje tafada muryar ta narawa, " wow tun jiya rabon da inji muryar ki saboda kina fushi dani, " kitashi kawai ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login