Showing 21001 words to 24000 words out of 101092 words

Chapter 8 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37771

taba jin irin kwadayin da yake jiba yanzu,
Takawa yayi har zuwa dakin nata, ya sameta a rabe jikin kofar dakin tana maida numfashi tareda kankame jikinta saboda wani irin yanayi takeji ga wani yam yam da tsigar jikinta ke mata,,

Tunda ta shigo ta kasa sukuni, shigowar shi yasa ta zabura zata kauce, yayi saurin shan gaban ta da idanun shi da suka koma kalar na Japanese, matsawa yake tana ja baya har ta mannu da gini tana runtse idanun ta kamar zata shige cikin ginin,

"RAHAMA!!!! Ya kira sunan ta da wani irin Amo, ta dago kanta cikin tsoro da kuma firgici, domin ita bata taba tunanin yasan sunan ta ba,, "look at me, Yafada da wani salo mai cikeda sakonni da kuma, Kara runtse idanun ta tayi gam domin she can't, bazata taba iya soka idanun ta cikin nashiba,
"Please look at me, Yafada cikin lallashi da tausasa murya, taki budewa, "zancire hijabin nan Inbaki bude ba, da mugun speed ta bude Amma takasa kallon inda yakeso sai kan fadeden chest dinshi da ya rufeta rub, ta zubawa ido,

"Meyasa kika gudu kika barni? "Girgiza kai tayi "am sorry na shafa maka datti da kazamin jikina, banason inyi laifi, tafada cikin lalubo zancen dakyar, murmushi yayi mai sauti, domin yasan Maganar da yafada mata ne take tuna mai,

"Ba datti a jikinki ai ke mai tsafta ce, " tace Amma jikina bana gwal bane, kar in shafa maka talauci da datti, "no RAHAMA let bygone be bygone, let correct our relationship mu gyara rayuwar Auren mu am ready to accept you as my wife what about you?

Wani irin kallo ta watsa mai mai cikeda nuna nima macece nasan darajar kaina,
"Noo, ni zaman Aure na yarda muyi kamar yadda iyaye na sukaso inyi biyayya, nasan inayi ban tauye maka komai ba Nafita hakkin ka Allah yagani, to kaga ni na dade da karbar Aure na,
Bakinta kawai yake kallo, he really loved it when she is talking her kissable lips wow yanda take motsasu, kawai na motsa lafiyar da' namiji,
Dago kanshi yayi ya hango HAJARA dake labe tana kasa kunne ta kofar dakin nasu Amma sam batajin Abinda suke fada,
Cikin wani irin sauri yayi saurin cafkar Abinda yake kwadayin tsotsawa, wato Alawar manya,

Numfashinta tsayawa yayi cak tareda ware idanun ta domin unexpected taji bakon Al amarin wanda yasamu dama sosai kafin ma tadawo hayya cinta yayi occupying ko ina a cikin bakinta ya rike komai yasamu yanda ya kamata da dama wadda bai taba mafarkin samunta kusa kusa ba,

Wani irin makaleta ya karayi a jikin bango yafara bata wani irin salon sumba shidai tsawon rayuwar shi bai taba kissing bakin wataba haka itama shine karon farko datake experiencing wannan lamari mai kashe jiki da kuma duk wasu jijiyoyin dake kai jini a ko ina na birnin jikin D'an Adam,
Wani irin rawa kafafunta suka farayi jin yanda ya damki harshen ta yana mai shan alawar tsinke, gaba daya bayajin kanshi a cikin sokoto ya manta ma a wace Unguwar yake,
Her mouth wow yama rasa yanda zai kwatanta what he is feeling inside west dinta da ya rike kata mau yasa taji numfashinta nadawo wa domin wani sakone nadaban kuma yake aika mata,
Jitake kamar yana tsira mata Allura a kugun nata she is feeling the touch deep down, har tsakan kanin kafafun ta,

Sulalewa ta farayi domin ya sassauta mata rikon saboda shima jikin shi yayi mugun mutuwa da sakewa, ga wani Abu da ya cure ya dunkele mai a ciki, da baisan Mene ne ba, ganin zata zube yasa ya rikota, tarota yayi zuwa jikinshi, HAJARA ta banko cikin dakin, "Amma dai kai anyi tambadadde wallahi ka zo kayi ta lalube karamar yarinya saboda iskanci da nuna kai ta tacce ne, idanun shi da sukayi ja ya watsa mata tareda cira RAHAMA sama cak kamar yanda mutum ke daukar kyanwa, yafita da ita daga dakin ya ce "please munbar miki dakin zaki iya kwana a ciki,
Yayi dakin shi da ita domin baida lokacin wannan mai bakin iyayen,
Zuciyar shi naga RAHAMA gaba daya so yake yasamu dama a wannan lokacin ya dama yanda yakeso da jikinta,
Itadai bazatace ga Abinda take tunani ba saida ya direta a tsakiyar dakin shi ya koma ya kulle kofar ta sulale tareda hade kanta da guiwa, tarasa me zata yi tunani, gaba daya yagama da lafiyar jikinta ko bakinta bata iya motsawa bare yatsar ta don da zata iya da ta hanashi duk Abinda yakeyi na farko dakko ta gaban Yaya HAJARA na biyu kawota dakinshi,

Tanajin hannun shi har yanzu a kugunta ga test din bakinshi a cikin nata, she can't believe wai bakinta ya tsotsa, wani irin tashi tsigar jikinta keyi wani irin kuka taji yazo mata apart from duk cin mutuncin da ya mata yanzu yazo yana son ya lalube ta a bagas wallahi bai isaba, dole ta Aro jarumta duk inda take ta kwatar wa kanta Y'an ci, ita kanta yaya HAJARA ta kaita bango suna son mata wasa da kwakwal wa don sunganta yarinya shi yana juyata, yanzu kuma harda promotion so yake yafara moreta, da sake, tasan akwai hakkin Auren shi akanta amma bazai taba samu cikin sauki ba ai ita ba sakarya bace,
Zabura tayi cikin tattaro jarumta ta mike zata fita,
"Ina zakije? Yafada yana cire agogon hannun shi, zanfita ne tafada kai tsaye,
"Banbaki izini ba, yabata Amsa, zanje inyi salla adakina, inkwanta, "anan ma akwai filin salla dana kwanciya, nafison can dakin ni, "ni kuma banason musu ki zauna a nan , Yafada cikin tsare gida da kuma
Nuna karfin iko, gardama ba tarbiyar da aka koya mata bace don haka dole ta koma gefe ta zauna ta bata rai,
Kallon fuskar ta yakeyi tareda zuba mata ido yayi zaune yana imagining yanda gsba daya ta sauya mai rayuwa cikin Y'an kwanaki kadan, she change him completely baya ganin duk wani laifin ta a yanzu, duk wani Abu da zatayi is adorable to him,

Ganin dare nayi bakuma tason ta yi wasa da salla yasa ta mike batada zabi ta wuce bathroom, dinshi, datsewa tayi, a d'an zaman datayi yau da gobe
Ta gama iya gane komai na bayin saboda kullum tana shiga ta wanke mai,
Tubewa tayi ta Tara ruwa domin tanaji a jikin ta dole tayi wankan tsarki don tasan hukuncin komai,
Tanayi tana tuna abinda duk ya mata duk da west dinta kawai yarike Amma tanajin hannun shi har yanzu a jikin ta,
Saida ta gama ta goge jikinta ya kalli wandon ta da ta cire taga bazai maidar mataba saboda ya jike, ta rasa yazatayi dashi, kawai ta jefa toilet tayi plushing ita ba mace bace da ke iya mayarda inner wears inta cire, don haka breziyar ta ma soketa tayi cikin sket din jikinta bayan ta goge jiki ta mayarda kayan ta, ta daura Alwala, ta fito tareda kallon inda daddumai suke a jere ta ciro daya ta tada salla yana kishin gide yana kallon duk Abinda takeyi, ita kuwa kamar ma bata ganshi ba tayi, sallar ta ta tayar, shima mikewa yayi saida ya fita ya kulle gidan ya dawo ya fada wanka, domin yayi sallah,
Ya dade kafin yafito lokacin har ta idar ta haye kan sofa ta na tunanin yau yanda zatayi bacci adakin nan,


Ganin yanda ya fito yasa tayi saurin dauke kanta daga wurin shi, dagashi sai towel a kugun shi, gaba daya duk wata halitta dake jikin da namiji mai burge mace ta gama bayyana a jikin shi komai nashi abin burgewa ne, kallo daya datayi mai ta fahimci hakan, dole yaja Aji ya rika yima mata wulakanci, akaron farko taji yes namiji ne sosai komai da yayi daidai ne saboda yanada duk wani Abu da zaisa yaja aji,
Ganin yanda tayi saurin dauke kan ta yasa yace "zoki nemo min kayan da Zansa ka, yafada cikin basarwa, ta mike tareda nufar waldrop din shi, ta zuge glass din, ta zubawa kayan ido, tarasa mema zata dakko mai,
Ganin jerin jallabiyu wasu ma a ledodin su yasa ta Zaro daya ta dawo tareda dauke kai ta mika mai,
Zata juya yace "wait wannan zansa inkwanta,? Banasa kaya da dad dare kisa a kanki, kinemo min boxer kawai ko incire towel din nan gaba daya,
Waro ido takeyi domin jin irin Abinda yake fada, yama za ayi ya iya kwance tawul din a gaban ta he is jocking,


"Dont west my time, Yafada dole ta je ta duba, tafara baza ido, taji yace "na waye wannan? Ta juyo domin taji tanbayar Me yakeyi, ta hango breziyar ta dumu dumu a hannnun shi yana kallon ta kamar yaga nonon ne a bayyane, tayi wani irin zabura ta diba da gudu zuwa inda yake domin in akwai abinda ta tsana duniya shine aga iners dinta, shikuwa har wani damkar brah din taga yanayi, so kawai take ta fisge abarta daga hannun shi,........ 🖊



Ku jira na dare my vip, karku manta HAJARA Aliyu na hanya, gobe sannan me waima zai faru ne a cikin dakin nan, nifa banason ko yatsar ta ta sakemai domin har yanzu. Masara bataji wuta ba, Gareku my fans

*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*



1⃣9⃣&2⃣0⃣


Al Ameen ne yayi karfin hali yace "momy na please don't call, Aliyu is coming munyi magana akai, cikin masifa da fada momy tace "Amma dai kai anyi sakaran namiji, kanaji kana gani tazo gidan ka ta mike kafa tana ciwa matar ka mutunci Amma kasa ido, koda yake kaima basanin darajar ta kayi ba, saboda kunganta karamar yarinya, don't forget kafada min yafi cikin kwando bakason Auren don haka kaba wata fuska kuzo ku hanata sukuni, ke kuma HAJARA kike kowa, duk dibar Albarkar dakikayi inada labari malam bala bai boye mana komai ba, kuma kinci Albarkacin su, da yau Abinda zansa Ayi miki bazakiji dadin shiba,

Kai kuma kasa ruwa akasa kasha zantafi da RAHAMA, yanda ka nuna min bakason ta, nikuma na rabaka da kayan da aka dora maka bisa ga umarnin mahaifinka in yaso kayita zama karkaje kaga likita sakarai kawai, Husna wuce ku hado min kayanta, mu tafi yanzu zaka iya walawa,

Wani irin bugun zuciya tareda tsananin tsoro ne ya rufe Al Ameen, tuni yaji sauran ciwon ya sakeshi yayi saurin riko hannun momy "momy na wasa kikeyi ko?
"Akan me nake wasa fada Anji, "you are not going with her?
"Ok ni nataba wasa da kai? Ko Al Ameen ni ina wasa dakai to watch and see, ke kuma wuce ki hado min kayan ta mu tafi,
"No no no please MOMY na don't do that wallahi mun shirya ki tanbaye ta bana mata komai I even ask for her forgiveness,
Jikin shi NA rawa duk hankalin shi ya gama tashi inkaga yanda yake fitarda gumi zakasan yashiga one chance a tashin hankali,
Cikin Sauri ya matsa gefen RAHAMA da ke kuka ciki ciki saboda sam bata kaunar tashin hankali, ya rikota "please come and tell my momy mun shirya kinji wife tell her you are not going please wife kinga banda lafiya, nafada miki zamu yi tafiya tare, girgiza kai tayi kawai domin Abu hudu ya hade mata a yanzu, tsoron karon ta dasu baba, tsoron yaya Aliyu, fadan momy, zancen rabata da Al Ameen kuma yanzu, yasa gaba daya duk taji wani irin zazzabi na neman rufeta, wani irin tausayi yabata musamman data tuna yanda jiya ya kwana baida lafiya,


Amma bata isa ta bude baki gaban wannan momyn da keda masifa tayi magana ba, ita mai shegen tsoron nan,
HAJARA kuwa lamarin ya mugun faran ta mata wato duk cika bakine Al Ameen bayason RAHAMA, wani irin dariya tayi tareda yima RAHAMA mugun kallon mugunta, Sallamar Aliyu yasa suka koma kanshi tareda Amsawa tuni jikin Rahama yayi sanyi, duk da bai taba jirgar taba amma tana tsoran shi sosai don magana kawai ya musu sai sun tsorata,
HAJARA ma tuni hanjin ta suka kulle ganin Yaya Aliyu, ta fara natsa hankalin ta tareda rakubewa,

Husna dai na dakin RAHAMA domin bin umarnin momy, cikin kayan Akwatin ta ta bude ta jido kaya tareda zuba su cikin katuwar wata extra akwati dake dakin ta zuba duk Abinda tasan RAHAMA zata bukata duk da d'an Uwan ta yabata tausayi daga gani, tasan ya afaka cikin kogin son RAHAMA,
Haka ta garo akwatin falo saboda nauyin ta,
Momy na Amsa gaisuwar Aliyu tace "wuce kice driver ya shigo ya dauka yakai mun boot din mota ta, kai kuma ka tasa kanwarka kutafi gida ku Kara Sa ido kanta wannan Y'ar sai Addu'a, tafada tanayi waje tace "Husna ku taho mu wuce ta gyara zaman jakar ta ta gayu,

Wani irin kukan tausayin Al Ameen ne yazowa RAHAMA ganin yanda ya yi shiru tareda komawa kan kujera ya zauna ya dafe kai, bata iya cewa komai ba dole tabi umarnin momy, ta wuce dakin da take zama ta dauki jakar kayan ta da Littattafan ta tafito, Husna dake tsaye ta zubawa Aliyu ido, tun fitowar ta take Satar kallon shi, Amma shi kallo daya ya mata ya cire ido, jira yake dama momy ta fita, yayi magana,
Ko kallon HAJARA baiyi ba, yace "RAHAMA zo nan, yafada tareda hade fuska kamar bai dariya,
"Wato muna waya dake kullum saboda rashin wayau kika bar wanna ta zauna miki a gida batareda kinfada min ba ko?
Me yasa bakida wayau RAHAMA? Kinsan insu baba sukaji zasuyi fushi kema dake,?
Kuka tasa tareda dafe baki tace "don Allah yaya Aliyu kayi hakuri wallahi banaso ta, gudu daga nan ne ta kuma barin gida, kuma tace zata kashe kanta in ban barta ba don Allah kayi hakuri,

Wani irin tausayi kanwar tashi ta Bashi ya goge mata hawaye tareda cewa is ok you are too innocent shiyasa take miki wayau, wuce ku tafi ana jiranku, zankiraki a waya kinji my lovely sister, take care of yourself, Husna ta riko hannun ta tace muje sister inlow, suka tafi tana waigen Al Ameen da ya runtse idanun shi ba wanda zai iya fassara halinda yake ciki sai shi da zuciyar shi yana cikin wani irin rudu da tashin hankali,

Ya Y'ar da RAHAMA hasken zuciyar shi ce he love her more than words can express, ya naji a jikin shi without her by his side bayajin zai iya walwala da farin ciki bazai iya kallon fuskar ta tana barin gidan shiba, mikewa yayi ya nufi dakin shi batareda ya iya kallon ko Aliyu ba,
Yana shigewa jikin HAJARA yafara shaking, domin duk duniya ba wanda take tsoro sama ga yaya Aliyu, don haka ya bata wani irin kallo, yace good very good and well done kinji, wuce muje gida, yafada batareda nuna mata hanya,
Ko mayafi babu a jikinta tafita daga ita sai wayar ta, ya tsayarda napep suka shiga duk sai yanzu tafara raina kanta,

Ana ajiyesu kofar gidan ya biya tafito, ya nuna mata hanya tayi gaba, ta wuce da d'an gudunta ta shige, datse kofar gidan yayi bam da kwado, yana shiga tayi tsaye takasa cewa komai inna data fito da ga kitchen rikeda flask tagan ta,
"Aa yau kuma? To sannu ko, shigowar Aliyu yasa inna tace "ina kasamota?
Hmm yace tareda nufarta a zafafen da batayi tsammani ba tajita tum akasa ta buga uban ihu tareda dafe gadon bayanta, saboda ta bugu bana wasa ba,

"Wato ke tacewar ki takai ki dauki kafarki saboda kunyi hannun riga da kunya kitafi gidan kanwarki ki zabga mata karya wai ankoreki a gida, saboda kinsan ta da tausayi da hakuri sai zuba mata iskanci kikeyi a gidan ta na Aure kina matsayin yayar ta,
Wallahi da ki zubar mana da mutunci gwara inkasheki kowa ya huta da mugun iri, "salati inna tasa da salallami tace "oh ni larai yanzu HAJARA Abin kunya da zagin da zakiyi ja mana kenan? Yanzu a, Al adar bahaushe har ma dai mu sakkwatawa da mukasan yak'ana da kunya da Kara, ki dauki kafafunki kije har gidan kanwar ki ki share gindi ki zauna, innalillahi wa inna ilaihirraji un, Amma Y'ar nan kin cuce mu kin cuci Y'ar kanwarki da batasan komai ba,

"Inna da kinji dibar Albarkar da take mata ma da ranki sai yafi haka baci , Yafada ma inna komai sannan yace yanzu haka, Nasamu momyn su ta tafi da RAHAMA bansan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login