Showing 9001 words to 12000 words out of 101092 words
jikinta narawa ta tura mai slm,
Lokacin yana hanyar zuwa gidan shi yana kishingide a bayan mota yana duba sakonni, yaga slm din witch yanda yabata sunan domin ya ankare inzai hau goma zaiga sakon ta, dole yau ya bata Abinda takeso don haka yace "hee please Am married so keep your ugly and your disgusting face to your future husband am not interested, ya kashe laptop dinshi tareda jan tsaki, shi duk wata mace mai cusa kai wurin namiji he hate her yafison mace da ba ruwan ta da ko kai waye he want true love a woman who will love him not because he is handsome or rich,
Hajara taji ciwon reply dinshi sosai yanzu kamar ita zai wulakanta yasan ita wacece kuwa? Ai ba son shi takeyi ba kawai taimakon shi zatayi yasamu big girl like her, I hate people who are so proud of their self,
Gidan su yafara zuwa domin ganin momy, tayi mai welcome, tace ina RAHAMA yaushe zaka kawo min ita? "Waye haka?
"What? "Yes momy please who is she? "Your mother, kaji uwarka ce yanzu Abinda zakayi kenan Al Ameen? Yanzu yagano she is talking about that girl, "oh momy ai ni bansan sunan taba and ni nan nace mufara zuwa saboda Am missing you, " yayi kyau kaji, duk namijin Arziki zaiso Aure zaiso mace a karkashin inuwar shi amma kai kasamu gata iya gata kana turewa Iri ne mai kyau muka nema maka Al Ameen karkayi wasa dashi karike damar ka tun bata kubce mska ba zan dauki mummunan matakin da bazaka ji dadin shiba, idan baka warke bane mu koma Asibiti a dora ka akan wasu medication din,
Saboda mundamu da lafiyar ka muka yima Aure Amma saboda ka raina mu shiyasa kake nuna bamu isa ba, bari babanku ya dawo zanfada mai komai shi da kake tsoro kaji Maganar shi,
Ranshi yaji ya baci" yanzu saboda Allah momy akan wannan yarinyar zan gwada lafiyar tawa ya zatayi dani? Ko fa kosawa batayi ba baby Husna ma tafita mature duk da ina mata kallon karama ni gaskiya I can't shear my body with that thing never, daga gani bagidajiya ce sai aikin jakanci sam jikinta kamar injin yanzu zaka bata aiki ta gama ni tsoro ma take bani,
"Yanzu wahalar da Y'ar mutane kakeyi Ashe Al Ameen? "No momy nifa sau daya naganta, a gidan nan nayi tafiyata, ok jeka Al Ameen zaunique u,
Tafada tana shigewar ta daki domin ya mugun bata haushi,
Fitar shi yayi tareda kudurin sai ya wahalar da ita yau saboda tajanyo mai fushin momy,
Da taimakon Husna ta gyare mata dogon gashin ta tareda, busar mata da drayer ta, kuma sata tayi wanka tareda zaunar da ita ta caba mata Ado daidai ba hayaniya tayi mata geling gaban goshinta inda suma ta kwanta, cikin akwatin Auren ta cire mata wata riga doguwa mai guntun hannu ta roba rigar ta hadu karshe jace, ta ciro wani ribbon a jikin rigar ta daure mata jelar dogon gashin kanta dake boye,
Husna kanta ta raina kanta yau domin ganin surar matar yayan nata a bayyane, tasan wannan jikin dole ya firgita namiji mai lafiya don haka har matsuwa take yayan ta ya dawo yagani Abinda ke boye cikin hijabi, ina ga RAHAMA ta waye lallai za ayi mace a nan wurin irin matan nan unique, girar ta lips dinta eyebrow dinta kalar fatar ta mai tsananin laushi da santsi ga tafin hannun ta mai wani irin taushi kamar na jariri, bazakasan hakaba sai hannun ka ya taba inji Husna a zuciyar ta, taji tanason matar yayan nata ta, waye da kyau yanda zata murda, mai kambu,
Dama tasa ta sun shiga kitchen duk da Husna is not good at cooking but she insist domin taga nata kwazon saidai tasha matukar mamakin ganin yanda take girki cikin tsari da kwarewa, anan ma saida ta Kara jinjinawa irin Damin da yayan ta ya kwasa a Kala,
Sallamar shi sukajiyo Husna ta fito domin yaga motar ta a gidan shiyasa ya saita kanshi, ta rugo tareda Rungume shi" Oyoyo my lovely brother, welcome home, " sarkin yawo naje gida banganki ba a she kina, nan? "Yes nazo wurin sister in low dina, Tabe bakin shi yayi yace ok let me fresh up and come, "to kayi sauri we are cooking special dishes for you,
Juyowa yayi tareda bata kallon you are jocking "yaushe kika fara aiki? Kai yaya zaka gani I can work sosai harda girki ka tanbayi momy, naji, yafada ya shige Abinshi ta koma kitchen,
"Yaya ya dawo baki fito ba, wani irin tsoro ke kamata dmtunda taji muryar shi she is happy when he is not Around yanzu kuma yadawo,
Don haka da sauri tafito ta nufi dakin ta ta dakko hijabin ta karami fari tasa akan rigar because she can stand ya ganta a haka gaskiya her chest is showing sosai gasu da girma kunya takeji gaskiya, dariya Husna tayi ganin ta da hijab, "I thought kinje gaida yaya ne Ashe ke hijabi zaki saka? Murmushi kawai tayi ta karasa abinda takeyi,
Pride rice ta hada lafiyayya da kuma pepper chicken dake tashin kamshi tareda coconut juice, a wani kyakkyawan jug tadaiyi ne saboda Husna tasan bazai taba ciba Amma badon tanason ta burgeshi ba, tasan bazata taba burgeshi ba a rayuwa and she don't want to impress him at all tasan yafi karfinta as he said,
Fitowa da komai sukayi kan dining suka jera ta koma ya gyara ko ina fes tareda fitowa zata wuce dakinta, ya fito da guntayen kaya a jikinshi armless riga da tree quarter, Husna ta rikoshi "let go yaya na nayi feeding dinka, "just tell me kinaso ki bata min ciki da concussion yau, "no zodai ta zaunar dashi kan dining din ta tsayarda RAHAMA dake shirin wucewa,
"Sister in low come, ta fada ta ko matso jikinta narawa tafara gaida shi, ko dago kai baiyiba, tace " kizo kiyi serving muci delicious dinki mana,
Ta ce tom ba musu tafara kokarin daukar plate, cikin sauri Husna ta mike tace " no sister yayana bayason hijab ana mai serving remove it, tafada tareda cire mata hijabin,
Tuni ta diririce tareda ajiye plate din tafara kame kame daga karshe ta zauna kan daya daga cikin kujerun don bazata iya tsayuwar yaga jikinta a haka ba,
Kanshi ya dago domin yaga shirmen da sukeyi, yayi Arba da sumar kanta datasha parking cikin wani fancy ribbon, gashi baki suduk very long daga gani nan nade shi akayi, ya d'an kalli gefen damtsen hannun ta da yanayin rigar jikin ta, tuni yaji yana so ta mike yaga how the dress is, yasamu kanshi da daka mata tsawa " come on get up and serve us duk da baisan dalili ba amma shi sam baiyi niyyar cin komai ba,
"Hasbunallah yafada tareda hadiye yawu ganin yanda rigar ta zauna tam a jikinta ga wasu shining stones dake kashe mai ido saida Husna tace yaya Anzuba ya dawo sence dinshi ya dauke kai tareda jin kunyar yanda ya zubawa surar ta idanu, don shi tunda yake da mace bayan Husna bai taba tsayawa ya kalli wata haka ba,
And she surprised him with her structure young but huge body, him dole ta rika yawo da hijab she is hiding her heavy load, haka ya baje yaja girki cikeda wani mamakin ita tayi irin wannan?
Ta wutsiyar ido yake kallon ta tareda observing dinta sam ba a sake takeba ko cokali daya batayi ba, don haka yana ganawa ya cika glass cup da coconut juice din ya wuce tsakiyar falon tareda daukar remote ya kunna TV yana sipping yana hango yanda ta natsu har yana kallon yanda karamin bakinta dake dauke da natural colour janbaki a lips dinta, bayajin me take fada amma he can see ta saki jiki sosai da Husna har suna hira,........ . 🖊
"Ikon Allah ni kaina ina rubuta wanna labarin nishadi yake sakani don haka muje zuwa masoya muga ya lamarin zai tafi, na matsu bamuje dai dai wurin ba masoya,
*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻
*By FENERH*
Free page
*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, nagode masoya sai najiku*
1⃣1⃣&1⃣2⃣
Suna kammala cin Abincin ta dauki hijabin ta tareda mayar wa ta kwashe kayan ta kai kitchen tafara wanke wanda suka bata, Husna kuwa gefen yayan ta dake kallo Amma hankalin shi da zuciyar shi na wani wuri nadaban ta zauna,
"Yaya ni zantafi tunda kadawo, "so early ki jira Anjima in mayar dake, "ai da motor nazo, I no za akai miki gobe, tom tace tareda zama sunata hirar su, RAHAMA dai tana gamawa ta shigewar ta dakin ta bata kuma fitowa ba, yana hira yana kallon ko ina na falon kamar mai neman wani Abu,
Har lokacin da Husna ta tashi tafiya ta sameta a dakin ta deba mata kayan garar da aka kawo mata da yawa irin su cin cin da su alkaki da diblan, tayi godiya ta, rakota bakin kofar ganin shi tsaye a falon yasa ta juya ciki, sukatafi,
Bayan zuwan ta gida momy ta Kara tanbayar ta ya zaman nasu yake? Tafada mata komai da tagani harma da korata dakin Y'an aiki, da yanda duk take takure, barni da d'an banza zanyi naganin shi, bari dadyn ku yadawo Nigeria,
Zaman RAHAMA zamuce batada matsalar komai domin duk yanda mutum yadauki Al amari komai tsananin shi zaiga saukin shi haka komai saukin Abu inkasawa rayuwarka damuwa saika wahala, duk ta tattara komai tana bautar Allah da zuciyar ta daya aikin gidan duk da yake tunanin zai sata har taji wahala ta gudu yaga tanayin kayanta batareda ta gajiya ba, Abun har mamaki yake Bashi yanda zai tashi yaga every ware neat ga special dishes da yake mamakin yanda ta iya hadasu she is young but hard working and very active domin duk saurin tashin shi zai tashi yaga har ta kammala gyaran gidan duk girman shi tana girki ko wani Abu daban, wanda sam bata yarda su hadu tasan lokacin da yake fita motsa jiki tayi saurin gyara mai nashi dakin, cikin sauri takeyi tafita gudun laifi,
He want her to suffer amma ya lura tanayi ne because she love it,
Ga Addini da ya lura tanada rikon shi sosai domin kusan kullum sai yaji k'ira arta na tashi da Asuba wanda yasa shima yake zama a nashi yana yi sometimes,
Her life is very simple batada hayaniya ba cusa kai, ba yanda yayi tunanin take ba da farko she is so innocent,
HAJARA rayuwa tayi mata tsauri komai ya birkice mata tarasa madafa gashi tun ranarda ta dawo washe gari ta shirya zataje school baba yace indai shi yasaka ta to ya cireta domin tuni yasa Aliyu ya dakatar da ita wanda yazamar mata dodo a gidan yanzu har Addu a take ya fita, ba mai shiga sabgar ta ga gidan yanzu aiki takeyi tunda ba RAHAMA asubar farko inna ke tashin ta,
Tagaji gaskiya dole ta nemi mafita, RAHAMA ta tuna wadda tasan kila tana can gidan miji tana shan wahala Auren dole, don haka taji tanason taje gidan koda yaune taga ya take rayuwa, Amma tasan baza a barta ba kuma kota fita batasan inda gidan ta yake ba, don haka ta dauki wayar ta da bako sisi tayi mata please call me domin bata goge number da sukayi magana ranar ba,
Lokacin RAHAMA na kishin gide tana hutawa taji karar Y'ar wayar tata Alamar sako tasan dai ba ya Aliyu bane domin yanzu suka gama waya kuma tasan dawowar Hajara wanda hakan ya mata dadi koba komai Y'ar uwar tace bata son ta da tabewa, ganin please call me dinta jiki na rawa ta kirata domin Yaya Aliyu baya barin wayarta ba kudi saboda yana sabon copers allowance da ake basu,
Jiki na rawa tace "yaya Hajara' jin muryar RAHAMA tasa kuka tace RAHAMA kowa ya tsaneni ba a sona a gida baba ya hanani zuwa school ya daina bani ko sisi yanzu haka ko kofar gida ban fita don Allah ki roki inna yau inzo inga gidanki kinji ko zanji sauki,
Abunka da Zuciya mai imani tuni taji Y'ar uwar ta tabata tausayi tace bari inyi ma inna magana,
Ta katse kiran ta kira inna, ta roketa ta bar HAJARA tazo gidan ta kusan sati biyu bataga kowaba don Allah tanason ganin ta,
Ba musu inna tace tom Y'ar Albarka,
Domin bazata iya hana RAHAMA komai ba, tako yi godiya tareda kiran HAJARA tace inna tabarta, tazo ta fada mata sunan Unguwar, wanda saida HAJARA ta Kara tanbayar ta kodai batasan inda take ba? "Tace saidai kinzo idan kibshigo kimin please call me zan kiraki infada miki gidan, tafada tareda mikewa cikeda farin cikin zataga Y'ar uwar ta, ita kuwa HAJARA mugun tanta ma takeyi Address din da RAHAMA ta bata, tako shirya cikin best dress dinta ta fito wanda ta dade batayi ado irin wannan ba, wayarta ta dauka tareda duba wayarta tana tuno last da ta hau online lokacin da A yabo ya gasa mata magana, ta fita tareda Sallamar inna tace zantafi inna, ki gaida min da ya' tagari ga kudin mashin Albarkacin ya' tagari,
Ta mika mata Dari Biyar, ta Amsa domin tana neman na data, ta kuma duba A yabo, mashin ta hau ya kaita har low cost tafara baza idanu ko zataga d'an karamin gida wanda zai dace da RAHAMA, Amma ko ina a Unguwar ba ginin banza, ta ciro wayarta tareda kuma bawa RAHAMA please call me, tako kirata tace ta Kara matsowa ciki zataga 3upstairs ta shigo tafadawa mai gadin, domin tana fada mata ta taso ta fita da katon hijabin ta a karon farko ta tanbayi mai gadin gidan ta rokeshi ya bata kwatance gidan, yace ai hajiya mai sauki ne, duk Unguwar ga babu kamar gidanga kice mata hawa uku, sai lokacin ta kalli ginin wanda ta lura Ashe suna rayuwa a dwan stairs ne, tun tuni bata taba lura hawa uku bane sai yau ta karewa ginin kallo da irin ni'imar dake zagaye da gidan, cikin Sauri ta koma cikin gidan domin tasan tsayuwar ta wurin bai dace ba,
HAJARA tayi matukar girgiza da Al amarin harma dai data matso mai gadi ya bude mata gate din yana cewa shigo hajiya yanzu ta koma ciki, baki kawai HAJARA ta sake she can't believe her eyes, yanzu wannan gidan ne RAHAMA ke ciki kamar matar minister, kodai gadi mijin ta keyi a gidan aka basu boysquters? Bata gama tunani ba taji an fado jikinta har jakar hannun ta na faduwa, domin tayi mugun matsuwa taga yar uwar ta, ta fito tareda rungume ta, cikin yak'e da hassada ta tattaro natsuwar ta tace "ke fada min nan gidan mijin kine ko na ubangidan shi?
"Mushiga ciki yaya, tafada batareda ta lura da reaction dinta ba burinta kawai su shiga tayi hira da Y'ar uwarta,
A falon ta kasa daurewa suna shiga ta fisge hannun ta tareda, cewa "ke banza ki Amsani gidan nan NA uban waye, tafara Zaro idanun ta duka waje ta matsu bataji Amsar taba wanda yayi daidai da fitowar Al Ameen daga dakin shi daman he want to see if she is ok don ya dade bai gantaba, yaga fuskar HAJARA dake facing dinshi and he no she is that annoying girl dake bibiyar shi, "what is she doing here, ganin yanda take ma RAHAMA masifa yasa yaja ya tsaya inda sam basa ganin shi,
Cikin Hajara bai kada ba saida ta hango tangamemen hoton Al Ameen dake manne a karshen falon yana miskilin murmushi a jikin Paris high tower 🗼 ta dafe kirji bakinta na rawa ta ce "shi sh sh shsh ne mijin ki???? Kallon hoton RAHAMA tayi tareda dauke kanta domin sam bata kallon hoton sau biyu saboda kwarjinin da yakeda shi ko a hoto, tace "muzauna yaya HAJARA, " bazan zauna ba don ubanki Kifada min shine mijin ki?
Gyada mata kai tayi tareda cewa " eh shine mai gidan,
"Kutumar uban can shine baki fadamin ba kafin adaura Aure Amma RAHAMA bakya kaunata namijin da nake kwakwar so saboda shi na guji Auren hadin da baba yamun nabar gida yanzu you are telling me shi ne mijin Aurenki, I hate you RAHAMA you are not my sister yanzu namijin da nake ra ayin Aure kika Aura,
Magan ganun ta sun sosa mata zuciya sosai tace dakata Yaya HAJARA, cikin muryar ta mai sanyi tace " me yasa zakiyi min haka, bayan ke kika ja komai kece sanadin komai me yasa kika kiyiwa baba BIYAYYA lokacin da yake rokon da ki