Showing 36001 words to 39000 words out of 101092 words
zai taka gidan wanda sai yanzu yaji kunya saboda yanaso a bashi RAHAMA su tare zaije gidan, har saida yaji kamar ya fasa tafiyar amma bazai iya hakura ba dole yau yaje, da taimakon Aliyu ya isa gidan, yana mai jin kunyar hada ido da surukan nashi a karon farko,
Yana faka d'an kareriyar motar shi, Aliyu ya fito tareda taron shi, yana cikin wata bugaggiyar shadda Y'ar gaske, "barka da zuwa Aliyu ya mai suka yi musabaha, yace "ka yi sa'a baba na gida bai fita ba kuwa, muje ciki,
Ya fada yana yin gaba, shima yayi murmushi mai cikeda jin nauyin idanun surukan nashi,
Da Sallamar shi ya shiga bayan Aliyu, baba na zaune a kan wata kujerar katako, "yace maraba Aminullahi, dukawa yayi har kasa ya gaida baba, Aliyu ya miko mai wata kujerar ya ce ya zauna, zama yayi tareda Dukar da kai kasa cikeda jin kunyar dattijon da ya dade da sanin Mutumin kirki ne, don haka wani irin kwarjinin Mutumin yake Gani da ka girman shi,
Ya kwalawa inna larai kira, yace " kifito ga me gidan RAHAMA yazo,
Fitowa tayi cikin hijabin ta tareda jin dadin ganin mijin Y'ar tata yau tana hamdala tareda godiya ga ubangiji yau wanna ne mijin RAHAMA? Duk kamshin shi ya cika gidan,
Gaida ita yayi cikin girma kafin ta koma ciki, suka dade da Aliyu da baba yana musu Nasiha kafin ya fita ya ce "ina fatan ba wata matsala tsakanin ka da RAHAMA ko? "Babu baba sai dai....... Ya fara sosa keya, "um ina son ayiwa Dady magana ta koma dakin ta, sunce wai bazata koma ba sai tayi karatu, "Ashha Alhaji bai kyauta ba, duk da ni na roki Alfarmar ya sa baki ta, samu ilimin da take buri, Aminu RAHAMA yarinya ce mai matukar biyayya, tayi min BIYAYYA lokacin da nake bukatar taimakon ta shiyasa na nemi Alfarmar itama ta samu burin rayuwar ta in har tanada rabo, duk da dai baz
amuyi maka shishshigi a rayuwar Auren ka ba, tunda kai ke da iko da ita, don haka nasan RAHAMA zatayi maka biyayya a duk zabin da ka dorata, zanje in samu Alhaji yabar zancen tunda Bakaso,
Shiru yayi tareda jin RAHAMA ta Kara shiga zuciyar shi, tunda har mahaifin ta yake yabon ta yayi wani murmushi wanda ya tuna mai da baiwa da Allah ya hore mata zahiri da kuma bad'ini
Sun dade suna tattaunawa kafin baba ya fita ya barsu a cikin gidan,
Inna ta fito ta sallami baba sannan ta kawo musu zobo mai sanyi a tsabta taccen jug, da kuma danbun nama mai dad'in gaske ta Ajiye musu, tace ya ci basu san zai zoba da an shirya mai girki, yace ya gode, ta koma cikin dakin ta ta barsu ya sake sosai da Aliyu yaci danbun nama yana korawa da zobon da yaji cucumber da kayan kamshi, yaci sosai saida yaji yayi kat ya kalli ko ina nagidan yace "ina Baby tayi zama? Dakin su RAHAMA ya nuna mai, yana dariya,tareda bashi labarin yadda take aiki 24hours a gidan ba ta gajiya, Kawai ya samu kanshi da jin dadin labarin rayuwar RAHAMA fiyeda komai, tuni yaji duk wani bacin ranshi da fushin da yake da ita ya tafi,
Sallamar su Hajara da kawarta ladidi ne ya dawo dasu daga hirar tasu, wani irin farin ciki HAJARA taji ganin Al Ameen yau a gidan su zaune ya baje daga Gani yana jin dadin lokacin,
Jikinta na rawa ta karaso ciki, "A yabo yau a gidan mu? Tafada cikeda iyayi, ladidi kuwa sakin Baki tayi ta zubawa gayun dake zaune idanu don ko Aliyu bata taba ganin shi, ba Amma A yabo ai wurin kallon hotunan shi datar su ke karewa,
Yau gashi ta ganshi eye to eye wow dole ta taya kawar ta bakin cikin yin sake, wanda a yanzu dole itama ga gwada sa'ar ta wurin shi don ai tafi Hajara wayewa da sanin bariki don ita har Abuja ta leka,
Tsawar da Aliyu ya buga musu ne "me kukeyi anan kun tasa mutane kuna kallo kkamar wasu wa inda suka warke makanta, dole HAJARA taja hannun ta sukayi ciki, tareda cewa "kawata kinga my choice? Tafada tana wani irin farin ciki, "ya tsine Baki Ladidi tayi "uhm ai ni Gani nake baby kinfi karfin wannan gayen, duk haduwar ki kike hauka akan gayen nan? Gaskiya nama raina kyan shi a zahiri, tafada cikeda kokarin cusawa Hajara wani ra'ayi, saidai zancen ya zowa HAJARA wani iri domin Ladidi ce ta fara cusa mata son Al Ameen tareda gudun muwar zuga ko wace iri yanzu kuma tana fada mata wai bai hadu ba?.......... 🖊
"Alhmdulillah fans am sorry for the two days, "masu tunanin nayi yaji ne nop FENERH is not like that ba abinda zai hanani baku farin ciki masoyan Asali ance Hassada ga mai rabo taki the more you shear the more I get new customers don haka iya ruwa fidda kai, wanda ya gyara, ya sani wanda ya bata ma ya sani insha Allahu yanzu ma nafara ganin cigaba a rayuwa ta, kuma makka bana inda rabo sai fa naje da kudin littafi Y'an bakin ciki sai dai su mutu, indawo ko dabino ba mai ci ehem🙄
*Matar Soja*🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻
*By FENERH*
*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*
2⃣9⃣&3⃣0⃣
"Kai kawata ai kuwa ko makaho ya shafa yasan Al Ameen ya gama haduwa, kuma Karki manta kece kika fara turani ga soyayyar shi, tun baya burgeni har ya shiga zuciya ta, "tab wallahi yanzu nafi ganin Haduwar Alhaji bello, kibada kai Kawai kawata gayen badai motoci ba, kina ganin irin motocin da yake zuwa dasu kina Y'ar fa shi. Wallahi daga Gani yafi A yabo hutu da kudi,
Wani iri HAJARA tayi " Amma fa mummu na ne, "ke wa ya fada miki in mutum nada charas ana ganin munin shi? Ai beb ki fara sauraran shi Kawai kinga yanzu ko kinyi me bazaki taba Auren Al Ameen ba Amma zaki iya Amfani da wani ki rama, yakama ta kija ayiwa RAHAMA kishiya kota halin yaya ne, shine kadai hanyar da zaki rama, saboda bazai taba Auren ki ba koda ya saketa wahalar banza kikeyi ko kin rabasu,
Shiru tayi tareda cizon yatsa, tace "ai duk baki hango min hakan ba kawata,
Sai yanzu, "Amma ba komai, dole kuma in raba RAHAMA da farin cikin ta, bazan taba barin ta cikin farin ciki ba wanna kankanbar da takeyi sai na sa ta dawo Abar tausayi, kuma shawarar ki zanbi zan Auri bello Auren huce haushi za suga biki zasuga naira ranar zasuka kayan lefe, Amma kiyi min wata Al farma kawata,
Ke nakeso ki zamowa RAHAMA karfen kafa, ki bibiyi Al Ameen kota bala'i domin ki shiga cikin gidan ki hanata sakewa, Zanbaki taimako nima tareda fada miki komai yanda bazaki sha wahalar samun shi ba,
Wani irin mikewa ladidi tayi, kamar da gaske tace ", what? Ni in Auri wanda kikeso? Allah ya kiyaye ai bazan taba yarda in Auri masoyin aminiyata ba ina, ke nifa sam baya wani burgeni, ni Kawai ki kyale shi ko ki nemi wata cikin kawayen mu, "um um kece na yarda dake ke nakeso ki Aure shi domin kece kawar da ke share min hawaye kece Kawai ke iya bani shawara inga Amfanin ta,
Rungume ta ladidi tayi cikin matukar farin ciki harda hawayen karya, "bakomai kawata ko banaso dole in Y'ar da in Auri zabinki dole inbi Abinda kikeso,
A kasan zuciyar ta kuwa wani irin farin ciki takeji, lallai HAJARA akwai sakarya zakici ubanki, tafada a kasan zuciyar ta, domin mugun hassada da bakin cikin kyan HAJARA takeyi saboda duk inda suka fita ita ake cewa anaso, ba saurayin da zai taya su indai HAJARA na wurin don haka yasa take zugata akoda yaushe cewar duk tafi karfin su duk wanda ya fito zata nuna ina hajjo tafi karfin shi bai hadu ba,
"Al Ameen dai koda suka shige baiko daga kai ya kallesu ba, mikewa ma yayi yace wa Aliyu zai wuce, "Aliyu yace toh my in low zanbika in gida zakaje domin inga baby na nima tunda kazo naka gyaran Auren nikuma zanje inkara wanke tukunya ta,
Dariya yayi yace "ok da nayi fushi dasu bazan koma ba Amma yanzu muje inga tawa babyn nima inna larai sukayi wa sallama ya zaro kudi ya mika mata yace su sai sabulu, taki karba kuwa fir ya Ajiye yace inna kusa Albarka Kawai ba yawa ya fita batareda ya kuma jiran korafin taba , haka suka tafi kamar wasu friends ba inlows ba, hirar su sukeyi har suka isa, har ciki Al Ameen ya mai jagora, lokacin suna zaune a falon RAHAMA rike da sabuwar wayar ta da MOMY ta bata yanzu, tana murna tareda kokarin bude watsp saboda tana son itama ta Kara sanin kan duniyar da kyau, don ta lura idan ka cika zama cikin duhun kai a wannan zamanin tofa za a barka a baya,
Wata doguwar riga ce ajikin ta ta atanfa ita da husna iri daya, kanta yasha kitso kana na ba ko d'an kwali yana gefe ga dinkin ya kamata kana ganin yanda kirjinta ya kunburo sosai, tunda ya sallamo falon idanun shi da ita yafara cin karo, ya daure fuska, duk da yasan Aliyu muharramin ta ne saida yaji wani irin kishi,
Don haka tuni fuskar shi ta sauya, har ya kasa yin magana, Husna dai wani irin farin ciki taji ganin sanyin idaniyar ta,
Tsayawa RAHAMA yayi kikam a gaba yana mai zubawa kirjinta ido da su suka fara tsokale mai ido, kafin ya kalli tsalelen kitson ta,
Dago kanta tayi cikin basar wa tareda kuma jin kishin shi dake cinta har yanzu ta kalle shi kadan kafin tace " ina wuni,
Kin amsa ta yayi sai wani irin mayen kallo da yake bin ko ina na jikinta dashi,
Mikewa tayi tareda rabewa, ta gaida yaya Aliyu cikin murna tace "yaya nasan me kazoyi ai ni na shige yanzu sam baka sona ka daina damuwa dani sai Husna ni ma ba ruwana dakai yanzu ta fada zata wuce,
Wani irin adoration look yake binta dashi komai tayi is unique a wurin shi, don haka bakinta Kawai yake kallo kamar ya lashe ta, har ta wuce Husna nace mata "lallai ma ni banyi korafi ba sai ke, kina kallon yaya Al Ameen ko ganin na bayayi in kina wuri kin kwace min shi duka baiko damuwa dani sai kece mai korafi ko,?
Juyowa yayi ya d'an harareta, "zaki hada kanku damu ne? "We are Already married ku kuma, fa har yanzu ba ako tsaida zance ba kuna nan kuna I yo ne Kawai saman ruwa,
"Hhhhh yayi my in low gori ne Abin nima zanje inyi tsiya a gida yau dole azo nema min Aure kodan ku ma rama, "zadai ku rame yafada yana nufar inda tabi,
Tana zaune sai latsa wayar ta takeyi ya shigo, tareda zama gab da ita yaja numfashi, "inna na gai dake, yafada a hankali, dago kanta tayi cikin basar da mamakin shi, "me kajeyi gidan?
Kallon ta yayi tareda juyawa ya fuskance ta, "ni ma gidan mu ne so naje gaida sune tareda kai karar ki,
Saurin Ajiye wayar tayi gefe ta fuskance shi cikin damuwa, "nayi ma laifi ne? "Eh sosai, "me nayi?
"Kina min tallar kayan dadi na baby. Yafada tareda kaucewa zancen ta ya dora but hannayen shi ta saman kirjinta ya shafa tareda. Matsawa, ta d'an runtse idanun ta kadan domin kamar da gayya yakeyi, ta Sa hannuta saman nashi tana kokarin saukewa, ya mata kallon why?
"Akwai zafi stop, " Hmmmmmm laifinki ne da kinbani dama da sun daina miki zafi saboda ba a tabasu tun tuni da sundaina zafin,
" Hmmm baby kidaina fita da irin wannan shigar am very jealous fa inada zafin kishi look at your brest ko ina a cike kuma kin zauna a main falo in wani ya shigo ya ganki a haka fa,? Nifa ko Aliyu naji haushin da ya ganki a haka fa,
"Hmm Kawai tace tayi mai shiru bata ce mai komai ba saboda tana hango hoton shi tsakiyar matan India,
Sam bai gane mata ba ya kalli fuskar ta tareda dago kanta da tafin hannun shi, yace "what happen? Me yasa ki fushi? " hope you are not angry because of me?
" kaine ta fada tareda dauke kanta,
"Tofa me nayi? Yafada yana dariya,
" ina wayar ka? Gata hajiya RAHAMA ya ciro ya mika mata, budewa tayi fuskar ta a daure, ta shiga gallery tafara searching pictures din shi, saida takai wurin hoton da tagani ta mika mai tareda dauke kai,
Kallon hoton yayi, yayi dariya mai Y'ar Kara ya mika mata wayar yace "banyi kyau bane a wurin,?
Saurin dago kanta tayi tareda zabga mai harara "kayi sosai kuma ka burgesu shiyasa har sukayi hoto dakai, dama kasaba posting hotunan ka a Instagram twitter Facebook ko ina saboda ka janyo ra ayin mata kuma hakan na burgeka ko, "ok nima zanfara tura nawa idan har ka tura daya saikaga nawa goma wallahi daga yau,
D'an daure fuska yayi tareda riko kafadun ta ya kalli cikin idanun ta, ta Dukar da kanta domin tana hango bacin ranshi a bayyane, "you think is a jock? "Don't even dream of posting your pictures on social media, "you are one man woman, you are mine a lone, your body your heart is all belongs to me, inada tsananin kishin ki RAHAMA, Allah yagani inada zafin kishi sosai shiyasa ma na kasa yarda kije makaranta I can't, kiyi hakuri da karatun nan please kifito ki fadawa su dady kin janye so that su barmu mutare baby inaji a jikina da Ace tunfarko inada lafiya bazan iya kawowa haka ba Aure ba nikadai nasan how am feeling, musamman if I saw you,
"Suwaye ka dauki hoto dasu? "Hhhh nuna mata babbar yayi, she is my friend on Facebook, when I post my pics ina India she beg to meet me and her sister that's all,
"Hmmm what a friendship, saboda kuna friends a Facebook sai Kawai kuyi sabo har ta nemi ganin ka? Gaskiya I don't like you posting your pictures on media this has to stop,
"Yes ma andaina, daga yau zan yi deleting All my pictures because of you,
A gaskiya samari da Y'an matan wannan zamani akwai gyara, domin posting pictures yazama ruwan dare a social media, for what,? You are insulting your self my sister, gwara maza akan ke mace, ba duk namijin kwarai bane zaiyi sha awar Aurenki saboda kina watsa hotunan ki a media, wallahi ku gane maza ma sunfi bukatar sweet a leda ba wanda kuda yabi ba, kukan Kurciya.......
Wayar shi ta dauka ta share duka hotunan da ke kan shafunan shi ta mika mai wayar domin tasan kan waya sosai zama da husna, dariya yayi yace "are you satisfied madam??
Gyada mai kai tayi, yace "tom Alhmdulillah, yanzu ya muje ciki? "Muje gida na ne ko kuwa.......
"Aa momy baza ta barni ba, saurin riko hannun ta yayi ya matse a tsakan kanin cinyoyin shi yana mika. "Kinji baby..... Please muje in rage ruwan mara ta yau,
Wata irin uwar kunya ce ta rufe ta tareda kokarin ciro hannun ta da takejin something very strong na tabashi, wanda tasan menene, kafin ta ankare har ya zura hannun shi ta saman kirjinta yabata wani irin hurt hold a brest dinta dayasa tayi wani irin zullo tareda zamewa ta zube a gadon, yabita tareda mata rumfa ya, yafara ya mutsata,
Tuni ya mata ligi ligi saida taji motsi ta ture shi tana gyara rigar ta da ya fara cirewa ta sama,
Yace " oh nooo baby meye haka?? " some one is coming, tashi yayi tareda kallon ta cikin ido " that's enough ke matata ce ya za a rika horani nida halali na, let go to our house right now na gaji da hakuri haka I can't take it anymore,
" ba laifina bane ai, tafada " ok then let's go,
"I can't follow you without momy permission,
Mikewa yayi a zafafe " ok then bakomai idan na mutu ko ciwon mara ya rikeni is your fault dake zanyi kuka not momy saboda you have all the right to follow me ,
Inkin