Showing 72001 words to 75000 words out of 101092 words

Chapter 25 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37773

tareda kallon yanda yake zukar nonon, d'an cire bakin shi yayi tareda kama kan nonon yadan matsa kadan yana cewa " wai har ruwa ya fito? Ikon Allah yafada yana kallon Abin kamar zaisa baki, "baby shikenan yanzu ya zama banawa ba,

Bata kai ga bashi Amsa ba momy ta shigo da Sallama, wanda yayi saurin waskewa ya saki nonon tareda d'an matsawa, tayi dariya a kasa, ganin yan da ya yi saurin matsawa, inya gama tashi mutafi momy ta fada, saurin cire bakin tayi wanda yaron yasanya kuka saboda ana mai wasa da Abinci, saurin karbar shi yayi yana cewa sorry sorry my boy momy ne ta fisge mana Abinci kyaleta zamu raba, yafada yana zura mai halshen shi cikin baki, yakama tamau yana tsotsa yayi tsit Abinshi,

Momy tace "wannan zamani akwai kallo ikon Allah yanzu yaran zamani sai abarsu wallahi, hijabin ta mikawa RAHAMA da katuwar suwaita yaron ma aka nadeshi cikin blanket na yara mai taushi, ta rungume shi suka fita shi da kanshi ya tuka su zuwa tsadden Asibiti, aka dubasu duka lafiya ita ma ba wata karuwa tayi sosai ba, suka bata Allurai da suka kamata da magun guna, kafin suka wuce da ita gidan Inna wanda da za a tona zuciyar Al Ameen bakikirin take saboda haushi yanzu yanaji yana gani za a tafi mai da mata da yaro ya koma gauro gaskiya akwai matsala Babba gwara yayi yayi yabar kasar nan inba haka ba zasuga rashin kunyar shi,



Inna tuni ta gyara dakinsu tsab ansa tsohon gadon ta dama a ciki ta dora ruwan zafi baba yakawo kaji saboda murna yace a figesu a zabga a tukunya kafin me jego ta iso, HAJARA da tuni ta iso gidan inna domin inna ta fada mata nan za a kawo ta wanka, ita ta zage tana zabga girki da gyare gyare, isowar su kuwa murna fal cikin kowa inna tayiwa momy maraba tareda zolayar ta "gaskiya hajiya Aisha kinayin wannan miji tunda yau kika biyoshi har gidan Amaryar shi, " ai Kedai larai bari dole in taho Karki kwace min miji, toh barkan mu da samun wannan Abun Alkhairi, suka fara gaisawa kafin Al Ameen ya fara shigo da kayan da driver ya kawo, kayane birjik kafin yasa shi ya shigoda kayan Abinci harda ruwan sha cartons aka rika saukewa saida inna tafara fada


Yana gama shigowa dasu Hajara na fitowa, sukayi clashing, tayi saurin sauke kanta kasa ta kasa cewa komai domin Allah yagani batason su hadu ma da shi domin irin watsuwar da ta bugamai a farko,
Waskewa yayi da yake d'an duniya ne " aa yaya Amarya Ashe har kin iso taron d'an naki, yafada cikeda son ya sa tasaki jiki tareda manta shirmen baya, ta d'an dago kai ta gaida shi cikeda jin kunya tamai barka ta shige dakin jegon da su inna ke ciki,


Husna ma sun iso tana ta zumudin daukar baby tareda murna kowa ma bata gani a gaban ta sai d'an ta,
"Aunty RAHAMA yaya ya miki wayau wallahi, duk ya kwashe fuskar shi,
Tafada Aliyu ma shigowa yayi yaga baby sannan yafita yasamu Al Ameen a mota yayi shiru,
Dafa shi yayi " hy brother inlow, yadai? " kaidai bari wai yaushe za a daina wannan al adar daukewa mutum mata idan ta haihu?
"Sai mun koyi Unguwar zoma dakan mu inajin koda sun taso muce mun iya, amma fa ni bazan yarda Husna ts koma wankan gida ba gaskiya, "tab wallahi baka isa ba yanda aka rabani da matata kaima sai kaji yanda nakeji,

" nifa yayan matar ka ne Al Ameen, "ni kuma fa,? Yafada yana kallon shi cikeda haushin zaman nan da yake ba d'an shi da matar shi a gefen shi,........ 🖊





*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*




*Aslm zanci gaba da wannan labari kamar yanda wasu suka shawar ceni kuma insha Allahu zaku nishadantu da sabon salon da zai biyo baya, godiya gareku kawaye na, daku nake military wife's Addu'a tareda neman kariya tareda gamawa lafiya tareda mazajen ku baki daya, Aminiyar kwarai Zainab mom Abdul Allah yabar kauna, tareda ke ta hannun dama na mom sawwama, sai my Besty Mom haidar dama sauran da bankira ba Allahu yabar mu tare yakara mana hakuri da juriya da juna*




5⃣9⃣&6⃣0⃣


Mugun bakin ciki da hassada yasa ladidi taji wasu irin hawaye, shikenan dai HAJARA ta wuce ta duk kokarin da tayi na ganun ta tarwatse rayuwar ta, " bangane me kake fadi ba? "Kamar yadda kikaji, anbiya mata hajji anbani gida nasamu aiki ta dalilin HAJARA matar kwarai, ai ke kinyi kuskure, duk wanda yasha nonon Arziki to bai taba tsiya a rayuwa, iyayen HAJARA mutanen kwarai na, shiyasa Allah ya tsare ta daga duk sherin ki, nafa san komai da kike shirya mata, na shiga rayuwar ta bada nuhin incuce taba tunfarko, banma taba tunani zansame taba sai gashi cikin yardar Allah nasame ta ta zamar min makullin Arziki na, don haka tai kiyi kwanan bakin ciki don nasan yanzu jikikai kamar ki kashe kanki don bakin ciki, HAJARA dai tayi gaba sai ketaho wanke mata takalmi,

Ya fada yana juyawa tareda jin shi a sama yau, yabar ta da bakin ciki, a kofar gidan ta zube tadora hannu akai, ta fasa, ihu kamar zararriya, duk wanda ya wuce yana kallon ta saida taci ta Koshi tayi cikin gidan su, Allah ka rabamu da hassada ga wani,


Gidan su bello ma yau kamar su goya HAJARA saboda farin ciki da murna, tazamo Alkhairi ga d'an su tunda yazo musu da labari,
Koda tadawo da dare sukayi ta mata godiya, ita kanta a ranar batajin zata iya runtsawa, saboda tsabar farin ciki, ta kwana akan buzu tana kara neman dacewa wato duk wanda yabi umarnin iyaye ko ta wane gefe zai ga haske, biyayya tayi mata rana rashin biyayya ya janyo mata, shiga cikin bakin ciki da farko don haka insha Allahu ya'yan su ma zasuyi musu BIYAYYA sai ta hada wannan zumunci inda rai da Nisan kwana, zataso taga ya'yan su sun samu irin baiwar da suka samu sanadin ya' tagari irin kanwar ta Rahama Allah yabata ya'mace ta ginata akan irin tafarkin da suma aka dora su,



Akwana a tashi ba wuya, Anyi sunan Abubakar Sadiq, cikin tsananin gata da taro mai cikeda dinbin masoya da Y'an uwa, wanda suka tara Abin Arziki, wanda kowa yasan Sadiq d'an gata ne ga dalleliyar mota da kakan shi yabashi, tun a jariri, su Husna iyayen yaro ta ko ina anzage anata jida baki, harda Y'an gayyar sodi irin mu nida tawaga ta, tundaga vip har normal group ranar muncika gidan sunan, wanda sam bai mana dadi ba munso ace a gidan Al Ameen ne yanda zamu samu space, Amma bakomai zamu hadu a wani insha Allahu akwai kara'i,
Alhmdulillah an watse taron suna Lafiya kowa ya koma gidan shi sai su Husna ne kawai kekan gyaran gidan Inna tareda gyara kayan mai jego,


Tuni Al Ameen ya gama hada ina shi inashi yana kokarin barin garin domin yasan inhar yana gari akwai damuwa, don haka ya shirya barin garin washe gari bayan suna,
Tunda daren ya zo ya sallame su bayan tasha doguwar runguma da kisses, daga oga Al Ameen, ya rungume sadiq da yake ji kamar ranshi, Allah ya dora mai son yaron fiyeda tunani, gashi ya dakko komai nashi harma yafishi,
Saida ya Ajiye musu komai dazasu bukata ya musu Sallama yatafi,
Tayi mishi fatan Alkhairi, ya wuce,

Sukaci gaba da karbar kulawa a wurin inna baba inya shigo goma zaice akawo mai Abokin shi, Dady ma sai yazo sau nawa gidan saboda Sadiq momy ma takan kawo musu ziyara kai da kai, , yaron yazama d'an gatan d'an gi kowa Sadiq yaro mai farin jini tun yana karami,
Akwana atashi ba wuya a wurin Ubangiji,

RAHAMA tayi Ar'bain , kullum saidai suyi waya da Al Ameen har video call yake Kiran su saboda yaga Sadiq, da kuma momyn shi, tasha gyara tayi bulbul na masu jego ta murje duk da tana wankan ruwan zafi ta zage ta gyara kanta domin ta kara burge oga Al Ameen, Wanda ta tabbata idan yadawo za ta rikitashi duk da kullum yakira sai ya susu ce mata a waya, " baby yaushe zaki gama wankan ki koma? Kullum maganar kenan,
Zatace ai ta kusa, ranar da suka cika Arba'in kuwa Inna tace to ta shirya komawa don tasan dakyar Al Ameen yabari akayi wannan ma don haka Yaya HAJARA dake sabon gidan ta aka kira da Husna suka je suka gyara mata gida tas tareda taimakon masu aikin ta da Already suna ciki domin kula da gidan saidai sam basa zuwa sashen masu gidan,


A ranar suka rakata gidan ta cikeda guzurin kayan harka irin na sakkwatawa masu inganci bana bature ba, ita dakanta tayiwa kanta gyara na musamman, bata fada mai tadawo ba sam saida sukayi balanced ta kara gyara, jikinta tasha kunshi da su dilka kamar Amarya , ga sadiq da yayi wayau yayi bulbul dashi kullum yaron kyanshi kara bayyana yakeyi,
Har yafi ubanshi haske, don ranar da momy tazo taga yanda yakoma ta dagashi tace "wannan yaron har yafi ubanshi haske da kyau yana karami, har maganin baki aka nemo mai saboda kowa yadauka zai yi magana, don haka wannan ma dole kirika yimai Addu'a domin neman tsari daga sharrin mutum da Aljan,


Saida tagama gyaran ta tsab ta fadawa Al Ameen sundawo fa, ai kuwa ranar kamar yayi tsuntsuwa yaji yadawo gidan, yace " yaushe kuka dawo? Tace "shekaran jiya, "amma shine baki fada min ba? Me yasa zaki barni ina juye juye kinsan ba Abinda yakai ku muhimnanci a rayuwa ta, zan iya barin komai indawo a yau da dare baiyi ba Amma gobe zantaso duk da I have a lot to do zanbarwa manager na ya kammala, am missing you badly wallahi, yafada yana kara rungume wayar shi, "were is my boy? Kallon Sadiq tayi dake kwance yana wulwulga kafafu tace " gashi yana wasa, "ok gobe dadyn shi na zuwa kice karya damu, " ok dady muna jiran ka, ta fada cikeda kissa da wani irin salon kara rikita shi domin tanajin yanda yake fitar da numfashi kamar tana kusa dashi tasan a mugun matse yake don tagano bai wasa da wannan lamari, katse kiran yayi yana murna gobe zai je wurin matar shi ya sha dadi,




Bello dai ya murje yanzu cikin wata biyun nan ya d'an yi haske saboda baya aikin wahala yana cikin inuwa yana bada Umarni gashi baya son wasa a wurin ma aikatan ma suna shiga taitayin su dashi, wurin yana bunkasa bakadan ba domin akwai tsayayye a yanzu, ya toshe wa wasu hanyar cuta sosai, Ashe kaniksnci yasa yayi baki yanzu kuwa da ya shiga inuwa ai yafara canjawa,


Hajara na plat dinta mai kyau da suka zuba kayansu yanzu gata harda kitchen dinta ita kadai ba hayaniya saidai intaso zuwa gidan gandu suma suna kawo mata ziyara wani lokaci, badai tada matsala ko kadan, ga cikin ta yafara fitowa,
Belle na matukar jida ita tana samun kulawa sosai ta hanyar Auratayya kuwa a hankali take nuna mai hanyar da takeso yabi kuma Alhamdulillah ya NA daukar darasi sosai domin shi kanshi yana jin dadin Al amarin sosai don ta iya tafiya da shi a gado, wanda hudubar Sabuwar kawatar ne Hussy Ali ta bata darasi akan yanda ake sarrafa oga ko bai iyaba akoya mai, don haka mata ku motsa ku koyi sarrafa mai house ku zama queens a gidajen Auren ku,

******************
Girki Kala Kala aka shiryawa oga na tarba ta tsala ado tareda baza kamshi ta matse cikin kayan gayu, ga kitson da tasha kanana ya zubo kan kafadun ta Abin ba a cewa komai, domin tasan yana gab da isowa a lokacin, tanajin tsayuwar mota ta sunkuci yaron ta suka nufi kofar shigowar suka tsaya domin jiran shi, shima ba bata lokaci ya fito tareda daukar Y'ar karamar jakar shi ya nufo hanyar falon, ya Yi wani irin kyau da haske harda wani d'an tunbin hutu da ya kara,

Kamshin shi ya musu welcome, ta washe fuska tana "Oyoyo dadyn mu ya dawo, , ya saki jakar laptop dinshi batareda uadamu da fashewar ta ba, ya zuba musu ido, ganin yanda takara kyau Ashe baya ganin komai a waya, hannu yasa ya karbi d'an shi yakasa cewa komai saboda farin ciki da shauki,
Ta tafi dashi fiyeda tunani, ko kiftawq bayayi, ta ce "welcome back my husband, tafada tareda dukawa ta daga jakar da ya yar tace " muje daga ciki ko kagaji, tafada tana juyawa tareda kada mai Abin zaman ta, wanda kamar tana juyawa da ruwan marar shi da ya kunso wani irin hautsina mai kwanyar kai tayi, wanda baisan lokacinda yayi wani irin taku yabi taba batareda ya iya tofa komai ba don duk ta kafe mai ruwan makoshi,


Suna shiga falon saman su yayi saurin shinfide Sadiq tareda wani irin hanzari yabata wata irin kyakkyawar runguma ta baya, ya saki numfashi tareda fisgo maganar da baimasan me yake fadaba, "miss you like hell baby, juyo da ita yayi yafara bata sumba ta fitar hankali tareda bin ko ina na jikinta da laluba, saida sadiq yadan sa kara ya saketa tareda saurin juyowa ya daga yaron yana zama domin duk hankalin shi ya gama tashi da ganin ta, "ki kaishi wurin mai raino kidawo kawai ya iya cewa, murmushi tayi domin tasan yanda yake a hannu inba yasamu Abinda yakeso ba ko Abinci bazai iya ciba tasan halin kayan ta
Don haka bausu ta sauka da Sadiq taba uwale ta dawo tareda zama gefen hannun kujerar da yake idanun shi a kulle,

" na kaishi tashi muje kayi wanka ka huta, tafada cikeda tsokana kamar bata san me yake soba, wani irin fisgota yayi " Kisan yanda zakiyi dani first wa innan zasu iya jira but me um um I can't,
Don haka sunku tar ta tayi sukayi merster bedroom, aka kashe light, fadin Abinda aka buga aranar baya rubutuwa a takardar ta domin su iyaye ne don haka abarwa su sadiq masu tasowa,





******************


Akwana atashi hasarar mai rai shekaru sunja Abubuwa sun faru da yawa na farin ciki da bakin ciki kuma, domin A rayuwa tana cikeda Abubuwa guda biyu samu da rashi, don haka akowane lokaci karuwa ake samu, wani gefen kuwa rashi,

Tangamemen falon dauke yake da Y'an mata da samari kyawa wa su kusan bakwai maza Uku Y'an matasa mata guda hudu a kewaye suke da wata mata dattijuwa mai cikeda hutu da jin dadi idanun ta dauke da glass sai surutu suke zuba mata banda mutum daya datake gefe rikeda littafi tana karatu,


Dattijuwar ce tace " kunga ku tashi don Allah kuyi gidajen ku kubarni da meenal ita kadai ce zan iya zama da ita , ita rayuwar ta akwai dadin zama kamar ta gwaggon ta Rahama, Amma ku kunzo duk kun cikamin kunne da ihu, harda ku mazan da ba cefane, saidai kuzo Abinda ubanku ya siya ya Ajiye min ku cinye,

"Kai wallahi ku tashi mutafi kullum sai munsha gorin grandma a gidan nan saboda Kawai muna zuwa tayaki hira, dama munsani kinfi son yaya Sadiq miskili da baya bari mutun yasha ruwa ya Ajiye cup in yana nan,

"Ai wallahi banason gayen nan yadawo ya takuri rayuwar mutane gwara ma da yafara aiki kowa yasamu lafiya, cewar dayan, "ai kuma infada maka Dady mugun sonshi yakeyi sam baya laifi mune dai yanzu kaji dady na hakilo a kanmu,

"A kul na kumajin hakan , baban ku na sonku duka kar inkuma jin irin wannan, "dole akwaba muku saboda kuzama nagari nan gaba, don haka karku sa wani Abu a zuciyoyin ku, Sadiq da yanzu yakama aikin shi koda baya aiki ai da company shi da kakan ku ya mallaka mai tun yana raye kunga aikin da yakeyi saboda yana ra'ayi ne,

Kuma in kun dage kun kammala karatun ku zaku samu naku shear a wurin ubanku, don haka nidai kutashi kuyi gaba,
Y'an matan guda biyu ne sukace " kina korar mu grandma, bakomai zaki nemo mu ai kuma Aunty meenal baban ta bazai taba bari ta zauna a nan ba kinsani, don haka mudai mune dole kuma ki lallaba mu,

" in lallabawa kaina aiki dai kuda baku moruwa ita kuwa akwai son aiki da gyara ku sai shegiyar kuiya a wurin ku,
Zabura sukayi "ku mutafi mudai bazamu dawo ba daga yau, " kai tafi nono fari a sauka lafiya, komawa sukayi suka zauna, " mun fasa yanzu KO munkoma momy na Asibiti bakowa a gidan don Allah grandma ki koma gidan mu wai me kikeyi a nan ke kadai ko dai kina tuna mijinki matsoraci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login