Showing 48001 words to 51000 words out of 101092 words

Chapter 17 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37776

samu su momy da zancen suma sun bada goyon baya tareda bashi shawarar ya bari ayi Auren Husna sai ya wuce da matar shi baki daya daga can ma sayi hutun su,

Amma yadawo da ita gida tunda bazai iya hakura idan yana ganin taba,
Cewar momy, ya buga tsalle yace atafau ba inda zataje suna tare bazai iya zama gidan bata ciki ba, ita kanta RAHAMA zataso ya warke daga wannan matsalar domin ita kadai tasan tashin hankalin da take shiga a suman shi din nan na farko da na biyu don haka dole ta taimaka mai tayi nisa dashi gashi yazama wani irin jarabbe kullum cikin cakudata yake 24hours idan suna tare koda bazaiyi sex ba kuma ma dakyar yake iya hakura,


Don haka ta bijire tareda matsa mai ya mayarda ita wurin momy Kawai, har yayi fushi shima yace "RAHAMA bakya tausaya min ko? Sam baki damu da damuwa ta ba, kina ganin zan iya rayuwa baki ne? Kina ganin gangar jikina zata iya yin nesa dake ne koda na hour biyu, nidai ki kyale momy I will try and control myself duk da nasan is not easy for me ko yanzu banajin dadin yanda bana iya kusantar ki a duk lokacin da nakeso, " Hmmm just pray for me insamu lafiya completely baby zanzama mayen Abun sai kinyi hakuri,
Ina son hutawa dake ke dince akwai Abun hutawa a jikin ki yafada yana janyota tareda zura hannun shi ta kasan rigarta yana wasa da kayan wasan dake jikinta,


Dariya tayi tana kokarin cire hanun shi akai domin yana matukar damun su da takura musu duk akan su yake sauke gajiyar shi da maitar shi, ya jagula ya cakuda kuma ya tsotsa duk wani irin zafi suke mata,
Tasan da yana samun gamsuwa da kila bazai takurasu sosai ba,
Momy ta roka tareda sawa ta takura sai ya maidata gidan domin ta taimaka wa mijinta kodan lafiyar shi, ana gudun yawan sumar kar yajanyo matsala domin doguwar suma yakeyi,
Saida Dady yasa baki sannan ya yarda ya dauketa cikeda fushi a wata dalleliyar crv sabuwa fara dal ya kaita gida wanda tunda suka shiga take koda motar da yake yana cikin fushi ko kallon ta baiyi ba saida ta fita sannan ya mika mata key din motar yace " is your car, fuskar shi a daure ya ciro wayar shi yafara dialing phone dinshi,

Wani irin tsalle ta buga tareda Dane shi tana bashi sumba a lips dinshi mai cikeda da murna da farin ciki domin motar karshe ce wurin haduwa,
Tuni yaji wani irin dadi ya mamaye mai zuciya don bai taba tunanin zata yi farin ciki da motar har haka ba ya lura Abubuwa basu cika damun ta ba na kyale kyale wannan ma ya siya mata ne saboda yanason ganin matar shi da motoci Kala Kala koda bazata rika hawa kullum ba dai, kamar yanda ya tara nashi itama yatara mata,
Saidai farin cikin da ta nuna ya mugun faran ta mai zuciya, "Allah ya biyaka da Aljannah mijina yakara maka budi da Nisan kwana tareda lafiyar da kullum zaka kwashi gara, tafada tana sakin shi tareda rugawa cikin gidan domin nunawa Husna mukullin motar ta sabuwa,

Bin bayanta yayi da ido yana dariyar Kalmar ta ta karshe, tareda jin ko ina na jikin shi na motsawa saboda yanda jikinta ke rawa da take gudu,
"hmm zaki biya bashi yarinya Amin yafada, tareda juyawa domin drivern shu ya iso, yafada motar suka wuce bakin aikin shi,


Su momy sun tayata murna sosai Husna harda shiga da danawa tace yau zan Ara mufita yawo da ita, " bazan bayar ba malama ko tukawa banfara yiba kike so in Ara miki ita, "yayi miki kyau yarinya kin manta yadda kika gurji tawa kenan lokacin kina gida wallahi bari yayan ya dawo sai ya biyani, "oho dai bazan bayarda tawa ba, tabi bayan momy dake nufar kitchen tana cewa "momyn mu me zakiyi intaya ki?
"Aa sarkin aiki yi zamanki mijina nakewa girki kinsan bana so atayani, dariya RAHAMA tayi tace "yayi momy kina bani darasi, "sosai kuwa kema kidauka kisa a kanki inhar kin hora mijin ki da lafiyayyun dishes to duk inda yaje bazai iya cin komai ba sai yadawo gida, kotafiya dadyn ku yayi damuwa yakeyi domin baya iya cin wani abinci saidai su tea da snacks don haka kuyi koyi,
Shewa sukasa kamar wasu kawaye suna binta, "bari muje muga me ake shirya wa tsoho, "eh shakiyai munji kubarmu da tsohona bakusan tsohuwar soyayya ba yara,


Meyafi wanna dadi a rayuwa my fans samun uwar miji mai zuciya daya yanzu shine wuya, don haka duk wadda ta samu tagari irin tawa ina taya ta murna,


****************
Gaba daya Rayuwar HAJARA ta sauya ta mugun shiga taitayin ta musamman da Alhaji bello ya fito mata da ainihin shi wanene tunbata tare ba, washe garin Auren su ya zo gidan, yakirata haka ba musu ta fita, ya na washe hakora yace "Amaryar bello aa kike? Alhandulillahi andaura min Aure dake HaJaru kinzama matata don haka nittaho inganeki ga Abin karin kumallon ki wazobiya kisha kunu da kosai kega ni yanzu Andaura muna Aure hakkin ki shina bisa wuyana, yanzu ki dakace mu zuwa Jibi idan na gama gyaran wata mota ina samun kuddi in isuwa hada miki kayan akwatin ki,

Wani iri takalle shi, "gyaran mota kakeyi? " aa wai baki saniba? "Ai duk wani bakanike da aggarin sokoto yasan da zama na mota ba wadda bai iya gyarawa don haka ki jira kayan Aurenki nan da sati guda na gama ruhe miki daki kitare..... 🖊




*Matar Soja*
Pls 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*



3⃣7⃣&3⃣8⃣


Wani irin tukukin bakin ciki ne ya rufeta, musamman da ya juya ba wata kalma Mai dadi ya tafiyar shi, wazobiyar hannun ta ta kara kallo tsohuwa da ita, ta ja kafafun ta tayi cikin gidan, ko iya tsayawa batayi ba tafada Dakin su, ta saki kuka mai d'an kara, inna najin ta tace " ai dama wanda baiji maganar iyayen shiba yana tareda kuka don haka HAJARA tukuna ma Y'ar nan, tafada tana cigaba da sabgogin ta,
Bayan kwana biyu, suka kawo ganah must go din su guda uku kamar akwati da Babba da masu binta babbar ma ba katuwa can can ba, medium sai binta da Y'ar karamar cikin su,
Inna ta kira makota aka Amsa tareda godiya dasa Albarka, makota aka tafi ana tsegumi,
Bayan sun watse inna tayi guda ta ce " ina HAJARA fito ga kayan Auren ki, Abin ba acewa komai, dole ta fito, tundaga nesa tasa kuka ganin ganah must go din a tsakar gidan, " yanzu ita HAJARA ce aka kawowa wainnan kayan Auren?
Dole tayi kokarin hadiye kukan nan, inna tace zauna mugani dakyau nida ke,
Inna ta fito da zannuwa roba guda kusan goma sai kuma kamfala ta roba itama guda hudu ga takalma Y'an malabin guda biyu da wasu quality shoe irin na Y'an kauye, ta kalli kayan da ko da take gidan ubanta da ba wani Arziki sukeda shiba tanada sutura ta kece raini domin mahaifin su ba baya bane wajen share musu hawaye,

Kayan kwalliyar kuwa ko nata sunfi wainnan daraja goma sha Biyar, don yanzu haka kayan ta da takeda su duk bana banza, inna tace " kai HAJARA kinga kaya ko, to Allah kade fitina ai yayi kokari a irin sana'ar shi ya yi wannan uban kaya Allah dai ya mai Albarka, kallon inna Kawai tayi ta mike tayi daki, batajin zata kuma yin musu da kowa, bare iyayen ta, koda wannan Auren shine Ajalin ta dole ta karbeshi tayi BIYAYYA, duk da zabin tane ita takawo cikin rashin sani,


Inna tace " bari in kai daki kafin bakanku ya shigo yaga harkar Arziki, daki takoma tana kukan nadama tareda jin tausayin kanta tana hango daular da tayi wa kanta bakin ciki tunfarko gashi Y'ar uwar ta NA ciki yanzu tana fanta mawa,
Ranar tayi kuka hartaba uku lada,
Washe gari baba ya kirata da sassafe kafin ya fita, yace ta zauna,

"Ummi gaki gani ga mahaifiyar ki nan, larai ki zama sheda, in har ummi kika tare kika dakko kafar ki daidai da kwana daya kika dawo gidan nan da sunan yaji ko wani tashin hankali, banyafe miki ba duniya da lahira kuma kinfita a cikin ya'ya na, domin tun farko da kike iya shegen ki nasa miki ido banbari wani ya kyareki ba a gidan nan ga maifiyar ki nan nasha yima ta kashedi akan karta ce miki komai zaki dawo hanya,
Alhmdulillah ki godewa Allah bello yaron kirki ne duk da baiyi karatu ba Amma yasamu shedar Arziki a wurin kowa tundaga bakin aikin shi har gidan su, don haka innaji wani Abu to daga wurin ki ne,.
Kuka tasaki mai cin rai tana girgiza kai " karku yimin baki don girman Allah baba ku yafe min nagane nayiwa kaina a rayuwa ina neman yafiyar bijire muku da nayi a farko ku yafemin iyaye ne wallahi koda zanje inci tuwon kasa a gidan bello baba ZANYI BIYAYYA bazan kuma yin Abinda zai bata muku raiba insha Allahu, tafada cikin tsananin tausayi na iyaye suka ce shikenan sun yafe mata Amma duk Furucin su akan gidan Auren ta basu janye shiba,

Daki ta koma ta zabga tagumi, waye zatayi tadi dashi ko ta rage bakin ciki, RAHAMA, wata irin kunyar ta takeji me zata fada mata, wane zance zatayi da ita, ta mugun sakin damar ta tunfarko, yanzu batada wanda zata fadawa taji sanyi,

A haka aka fara shirin Auren su Aliyu da Husna wanda su baba suka roki Alfarmar Bello ya bari a yi tarewar baki daya, baiyi musu ba ya Amince don haka dole a haka inna ta fara shirya ta irin na Amare, wanda a gefen su RAHAMA dai tana gidan momy Hankalin ta kwance koda yau she Al Ameen na zarya Abin shi wata rana sai momy ta kada shi ya matsu ba a gama Auren ba su gudu India wanda yana kan shirya mata visa,
Tanason zuwa gidan su domin Abu ya kasu mata kashi biyu itace gefen Ango kuma da gefen Amarya domin yanzu husna kamar RAHAMA ce ta zamo babbar kawa a wurin ta ba matar yaya ba,
Komai RAHAMA ke tsarawa, duk da tsakan kanin satikan tanajin wani irin canji a tareda ita, ga zazzabi dake tashin mata duk dare zuwa safiya kuma tajita garau,

Ba wanda ya ankare da yanayin ta har ya rage saura sati guda Auren su Husna, ta shirya domin zuwa gidan su taga nasu shirin saidai kullum tayi waya da inna, yau so take taje taga kayan kafin akawo,
Al Ameen tafada ma zata fita, yace ta jirashi yazo suje, ta ce aa yadai barta ta tafi domin batason ya ce zai kaita anguwa zai iya kwana domin kwanan nan rigima suke tayi akan yana bukatar ta, taki yarda su hadu ko yazo gidan,
Don haka dole ya hakura ta tafi ita kadai a cikin dalleliyar motar ta ta tafi wannan karon Husna ba zuwa gidan surukai,


Tun dosowar motar ta baba ya gane ita ce ya saki fuska cikeda farin ciki yana cikin mutane, ta faka cikin Sauri ta fito cikin shigar ta ta mutunci hijabi har kasa ta dakko jakar ta, ta nufo su cikin girma mawa ta gaida su baba, ya amsa cikeda farin ciki yace ta shiga ciki yana zuwa, ta wuce cikeda dokin ganin inna itama, saidai tundaga shigar ta jikin ta yayi sanyi ganin Y'ar uwar ta tana wanke wanke duk ta kode duk da bata cikin damuwa yanzu Amma ta canja kamar ba HAJARA sarkin gayu ba, ita tafara yima RAHAMA sannu da zuwa wanda Abun ya mugun taba mata zuciya,


Tace "yaya HAJARA lafiya kalau kike kuwa? Inna ce ta fito ta tare ta tace "kalau take Amarya ai duk tare za ayi tariya dole ta rame ana fargabar Aure, tafada tareda cewa "kin tsaya nan karaso daga ciki Kiga kayan duk da gidan ku za akai,
Tafiya takeyi tana waigen yaya HAJARA, rabon da su hadu tun ranar da sukaje gidan ta da safe itada ladidi,
Dakin inna suka shiga inda taga lafiyayyun Akwatuna saiti biyu masu Biyar kaya shake masu Aji, da tsada dai dai gwargwado Yaya Aliyu yayi kokari wajen fitoda Amaryar shi, sai gefe daya taga ganah must go din Hajara suma, tace " wannan fa? "Kayan Auren Y'ar uwar kine, ki bude kigani yaron yayi kokari sosai, shiru tayi kafin tace "wai inna wane Aure? Anan ta fada mata yanda baba yayi,
Bataji dadin hukuncin baba ba Amma ya zasuyi yariga ya daura an wuce wurin don haka cikeda tausayin Y'ar uwar ta ta mike ta fita lokacin har ta gama wanke wanke ta na share tsakar gidan, tace "yaya zo muyi magana, ba musu ta Ajiye tsintsiyar tabi bayan ta zuwa Dakin su, suka zauna kamar ba HAJARA sarkin fada da kuma gudun raini ba yau ta tsaya jin maganar kanwar ta da ta raina,


"Yaya me yasa baki kirani kinfada min maganar Auren ba? Dago kanta tayi cikin wani irin sanyin halin da bansan daga ina yafito ba, tace " mezan fada miki RAHAMA meye Abin fada A ciki Aure ne dai baba ya daura kuma RAHAMA koda bana son Auren nan zanyi biyayya in zauna da bello, ina kwadayin samun RAHAMA, ina kwadayin samun dacewa irin wadda kikayi RAHAMA ke kam kingama sa'a a rayuwar ki, biyayyar ki ta janyo miki cigaba a rayuwa, wanda ni kuma taurin kai na ya janyo min koma baya Kala Kala, karatun da nake takama nayi zai kare a gidan makanike,


Wani irin tausayi RAHAMA taji na Y'ar uwar ta, tuni hawaye suka wanke mata fuska, tayi saurin matsawa ta rungume ta, "Karki damu yaya ta insha Allahu zakiyi farin ciki zakiyi Alfahari, Kawai kamar yanda kika fada ne, biyayya ga iyaye tana tattare da riba, ki godewa Allah da har kikeda da sauran damar da zaki gyaro kuskuren ki,
Don wasu zasu tafka kuskuren Amma basa taba samun damar gyarawa Har Allah ya sa su koma ga ubangiji, don haka have faith, komai zai wuce zakiyi farin ciki kema da izinin ubangiji,


"Tom tace badon tana hangowa kanta wani sauran jin dadi a duniya ba, haka ta rage murya ta nemi yafiyar Y'ar uwar ta itama........... 🖊





Kuyi min Afuwa banda Enough charge wlh mu tari gobe idan Allah ya tashe mu lfy,





*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*


4⃣1⃣&4⃣2⃣

Iya kokari tayi domin ganin ta karfafa jikinta zuwa yamma, Amma ita kadai tasan me takeji a jikinta, shirya wa sukayi cikin jallabiyu masu Aji da kuma haduwa Nata kusan iri daya da Amarya, da kuma yaya HAJARA, ta nada farin gyale akanta domin d'an kwalin baida girma,
Kuma ita matar Aure ce dole ta tsare kanta, don haka ta suturce jikinta da kyau, wanda duk da haka kana ganin irin haduwar da tayi da wani irin kyau na mai sabon shiga,
Makullin motar ta tabawa drivern momy tace shi zai kaita itada wasu friends domin Amarya Ango zaizo su tafi tare,
Kusan ma duk an wuce harda wasu Y'an Uwan momy ma, daga ita sai wasu guda biyu suka fito, takalmi da pos dinta silver suna shekin stones, ta fito cikin takun ta cikin natsuwa, ta shiga bayan motar itada dayar tana duba lokaci kusan karfe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login