Showing 12001 words to 15000 words out of 101092 words

Chapter 5 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37762

karbi Auren nan meyasa kika zabi ki tozartasu kibar gida saboda Auren nan, sanadinki Aka gutsure min karatuna aka kawoni nan gidan kinsani Am not ready to get marry, bayan guduwar ki baba ya mayarda Auren a kaina wanda kinsani banason Auren bana son mijin, bana bukatar duk wainnan Abubuwan kinfi kowa sanin halina Amma yanzu you are blaming me Aunty HAJARA why,


"Idan har da gaske kikeyi bakyason Auren leave this house ki barmin A yabo shine zabin zuciya ta I love him so much bazan iya rayuwa Bashi ba don't take my happiness away My sister,
Tafada tana rungume ta, wani irin mugun tausayi taji ta bata, ta fara bubbuga bayan ta, "am sorry yaya HAJARA nayiwa su baba Alkawarin komai wuya zanyi BIYAYYA bazan iya watsa musu kasa a idoba, tureta tayi ta tafi luuuu zata zube tajita fada a jikin mutum,
Wanda ya gaji da jin magan ganun HAJARA da kuma kalma mafi muni itace nima banason Auren banason mijin, shine ake wa wannan hayaniyar she suke rejecting ita har tana barin gida And now she is following him, dole ya saita ta kuwa shi A yabo,


A zabure ta gyara tsayuwar ta tareda kokarin barin jikin shi cikin Sauri domin ta gama gano komai, ya rike tafin hannun ta da yakejin shi kamar kad'a mugun karfin hali yayi ba karamin namijin kokari yayi ba lokacin da ta fado kirjin shi da bai tsaya da kyauba yanda yaji wani irin shocked da sun zube, a karkace yake kallon ta tana sanye da hijab din like always, saidai she look pretty,


"A yabo HAJARA tafada jiki na rawa ganin sam kamar baiganta ba ya kwakume Hannun RAHAMA yana bata wani irin kallo masu ma'anoni, "why are you like this? You are too cool you are good heated, you obedient, you are religious, karshe kuma she is wonderful,
RAHAMA dai a mugun tsorace take domin fargabar ta ta farko shine kar yaji magan ganun su, secondly the result,
"Are you Alright wife? Ya tanbayeta cikin wani irin salon murya tareda Kara matsowa jikin ta, batareda ya rungume taba, duk ta rude "please take care of yourself for me karkijamin Asara you no you are pregnant with my baby right? Gaskiya am happy sati biyu har doctor ya gano Ajiyar dake cikin ki, I must give you something as gift, wace kalar mota kikeso in canja miki wadda aka kai a lefe is too small for my wife, and aikin gidan nan NA hana dole kibari a kawo house girl banson ki wahala "or zandauke ki muje Paris kihut...... A yabo, HAJARA ta buga mai tsawar da saida RAHAMA ta boye bayan shi,
"Cin fuskar yayi yawa basai ka fadamin ka tale kanwata ta kwanta da itaba I can see everything kaga karamar yarinya dole ka cuceta ke kuma dakikiya jaka kinsake wannan turmusheshen ya na danneki wawuya mara wayau, and kisani sai kinyi kuka tunda kika boyemin gaskiya, yanzu kika gama fadamin bakyason shi Amma jiki munafuka kin makale a jikin shi a gabana,


Kuka Mai cin zuciya RAHAMA tasa domin tozarcin da HAJARA keyimata a gaban Al Ameen wanda ya nade hannu a kirji yana wani irin murmushin mugunta saida HAJARA tayi shiru yace "am sorry yayar mu banganki bane sannu da zuwa "sweetie kin bata drinks kuwa? nuna mata gidanki yakamata kiyi kizagaya da ita taga cikin gidanki,

A fusace ta hankade RAHAMA ta wuce fuuuu tana kuka ko zama batayi ba a gidan, RAHAMA data kusa kifewa taji ya fisgota domin All this while bai saki tafin hannun taba HAJARA na fita ya tureta tareda bata fuskar shi, yanajin wani radadi duk shirmen HAJARA bai dameshi ba what hurt him is that tana fadar bata son mijin da take Aure,

"So you are rejecting me a gaban yayar ki ni Al Ameen kike cewa you don't want to be with me, really? Who the you think of yourself, yafada yana buga mata tsawa, "how could you, how dere you reject me, yafada har jikin shi na rawa, ya dunkule hannu tareda naushin iska,
"Oh kema wani kika hango like your sister wanda yafini ko shiyasa kikeda gut ki bude baki kice wai ke bakyason mijin da kike Aure,

Cikin karaji yake Maganar kamar zai tashi sama idanun shi sunyi mugun ja his heart is burning deep down, shi ne aka jewa neman Aure har ake gudun shi, and the second one itama she don't like him, "ni Al Ameen Shuaibu Yabo kike rejecting nida mata kebibiya suna neman ko friendship muyi dasu Amma bana kula su you got me free of charge as your husband amma kina fada ma wata dakikiya wai bakyason Aure na, ni banyi rejecting dinki ba kece zakiyi rejecting dina, yafada yana matsawa gaban ta kamar zai mareta,

Saurin ja baya tayi a tsorace jikinta na rawa ga tsoron shi ga kunyar Abinda HAJARA tayi mata a gaban shi, wani irin kallo kawai yake binta dashi ganin hawayen dake zarya a kumatun ta duk tabi ta kankame jikinta saboda firgita da lamarin shi gani take kamar zai hadiyeta,
Bazama ta iya cewa komai ba, to me zama tace, sai kuka kawai,
Wanda yake shakar dashi domin zaiso ta karyata Kalmar batason Auren shi yaji Amma she is not going to talk don haka ya buga mata tsawa " if you are not going to say anything leave, kafin inyi kwallo dake,
Ai kuwa da gudu tayi dakinta, wanda he can see how her body is shacking,


Zarya yakeyi a cikin falon zuciyar shi NA Azal zalar shi, wanda yarasa dalili da ya kasa sukuni he don't care about that crazy and lunatic girl, he is worried deep down, wanda baisan me yake tunani ba, don haka ya zura key kawai yabar gidan,
Gidan su ya nufa kai tsaye, momyn shi ya samu zaune a falon tana duba wasu kayan siyar warta da aka kawo mata samples tagani a gida, Husna na tayata,
Ko sallama shi kadai yaji kayar shi,, zama yayi gefen momy tareda riko hannun Husna, kana ganin shi kasan yana cikin damuwa da kuma takaici,

"Kai lafiyarka zaka shigo min gida ba sallama? "Nayi momy, ina wuni, "lafiya, ta Amsa tareda cigaba da aikin ta, Husna tace "yadai my lovely brother? "Baby me mace take nufi intace she don't like her marriage? What was that means,
Kai tsaye batareda tunanin komai ba tace "that's means she don't love the husband at all,
Zabura yayi ya zauna kamar wanda aka watsawa barkono yace, "koda mijin irina ne? "Yeah ra ayi riga ne ai yaya daina ganin mata na binka akwai wadda sam baka gabanta ma,
Kalmar ta cimai tuwo Akwarya tamai zafi ta cakeshi idanun shi kamar wuta, ya kalli momy " wai don Allah meye dalilin daura min Aure da wadda bazata soni ba meye Amfanin Auren hadin, da Anbarni na nemi love da kaina da yafimin leaving with the person who don't care about you is unfair, wani irin mugun kallo momy ta watsa mai kafin ta bude bakinta tace " don't worry zanyi maka maganin matsalar ka baban ka kawai nake jira kuma insha Allahu Jibi zai dawo komai zai dawo normal,
"Momy wane magani zakiyi bayan is too late kunriga kun kakaba min Auren da ban shirya ba wallahi an takuramin rayuwa da zuciya kawai an hanani sakewa a cikin gidana,
"Kashh ka rage gajen hakuri zanyi maka naganin Abun tashi kaje indaina ganin ka,


Husna ya kalla" muje gidana sister please, yafada duk yayi wani irin sanyi,
"Ba inda zaka kaimin yarinya, "please momy ina bukatar ganin tane a gidana kibari muje don Allah, "kasan Allah katafi kawai Amma ba inda ya' ta zataje,
Mikewa yayi tareda cewa shikenan natafi'
"A sauka lafiya, inji momy,
Ya fita kawai, duk jikinshi ba kwari,

****************************
HAJARA da kuka ta shiga gidan lokacin baba ya shigo da kayan miya zai fita, tundaga farkon shigowar ta kurma ihun da saida inna ta fito daga daki da zani a hannu, tana Allah ya jisheni Alkhairi me yasamu ya' tagari, domin duk tunanin ta tasamu RAHAMA cikin mawuyacin haline shiyasa take kuka,
Burgima ta fara yi tana wayyo Allah ba a kauna ta ba a sona agidan nan,
An muna funceni,
Muciya inna ta dakko a kitchen mukekiya tace "yi min shiru ko in ji miki rauni don kinga ba yayanku a gida shine kike mana zanbarwar bori a gida ko, uban me akayi miki,

Baba dai kallon tababbiya yake mata,
"Eh mana ya bazan yi kuka ba An munafunce ni ance mijin da zan Aura nakasashshe ne gashi nan garau kuma yanada kudi sosai aka bari saida na gudu aka Aurawa wadda ake kauna, wallahi sai tabar min gidana na shiga ko in kashe kaina,
Baba na gane inda zancen ya nufa yace "larai natafi muna wani aikine a kamfanin Alhaji kafin yadawo Jibi, kiji da mara lafiyar nan karta sawa gidanki wuta Allah ya yaye, ya ficewar shi, inna ta garkame gida tace bude bakin inkuma jin muryar ki shasha shar banza mara kunya, "indai ilimin jami'ar haka yake to Allah ya wadaran shi, wayewar zamani ko rashin kunya da rashin tarbiya, wallahi kin cucemu kin cuci kanki HAJARA iya hakkin ku mun sauke tarbiya nayi iyakar yina nidai ba irin haihuwa ta bace ke da haihuwar Asibiti nayi zance canja min akayi, bamuda irinka a zuri'ar mu sam,

Takoyi tsit don taga Alamar zata jibgu idan tayi wasa don haka ta koma dakinsu ta ci kuka taci harta bawa uku lada "Al Ameen yanzu shine mijin data ki Aure, yanzu shine mijin RAHAMA yanzu da gaske tanada cikin shi? Wani kukan ya kuma zuwa mata ta dafe baki, ba Abinda take hangowa sai rayuwar ta cikin wannan gidan na Al Ameen, tana hangowa kanta daula tana hango kanta a cikin motoci tana murza sitiyari,

Jitayi ta tsani RAHAMA a rayuwa domin ta nuna mata bazata iya bar mata daular da take ciki ba, ita ta shiga, dole ta kirata dole ta lallaba ta tunda tanada tausayi ta zubar da cikin tabar mata gidan ita tashiga,

RAHAMA kuwa ranar a dame ta wuni aikin nata ma kasa yi tayi tana jin yunwa takasa dafa Abinci taci, ba Abinda take tunani sai Y'ar uwar ta tana tsoron karta kuma gudu tabar gidan hankalin su baba ya Kara tashi, batason tashin hankalin iyayen ta batason bakin cikin kowa a familyn su,

Al Ameen yadawo gidan saida ya kalli kofar dakin da take ciki, ya wuce dakin shi ya zauna tareda dafe kanshi, yarasa Abinda kemai dadi office ya kamata yaje Amma he can't gaskiya,
Jin shi yakeyi a matukar takure, falon ya kuma fitowa tareda zubawa kofar idanu, ya mike ya duba dining yaga ba komai tuni ya samu madafa, ya bankada kofar dakin nata lokacin ta idar da salla kenan yace "were is the food ni ne zandafawa kaina? Or girkin ma bakyason yi in fita inrika siya a waje kawai,
First time ta bude bakinta tace "yi hakuri bangirka bane naga baka gidan sannan bakoda yaushe kake ciba,
"Come on wuce kimun girki kuma daga yau tree times a day dole kibani abinci as you are the woman of the house dole kiyi girki ko bakyaso, yanzu wuce kimun tuwon shinkafa miyar da ta dace,

"Toh tace tareda gyara zaman hijabin jikinta zata fita domin wanka tayi ta saka singlet tareda daura zani a west tasaka hijab, "remove that thing oya kidaina mun Abinci kina kakkaba min datti ok,
Zaro idanun ta tayi da sukayi wani irin kyau da haske, ta rike hijabin katamau mau domin she can't remove it singlet din irin mai robar nan ce ta mugun kamata gashi hannun ta irin siririn nan ne bazata iya cireshi a gaban shiba,
So take ya fita saita saka rigar zanin ta kalli rigar, shima rigar yabi da kallo, ya kuma gane sarai me take nufi,
Don haka cikin tsawa ya buga mata da karfi "come on remove it ko inzo wurin in hada dashi in shakeki, kwaila dake sai shegen iskancin boye jiki uban meye a cikin hijabin kike boyewa,

Matsowa yayi cikin haushi ya fisge hijab din ganin batada niyyar cireshi sai faman girgiza kai takeyi,
Dunkulewa tayi da sauri tasa Kara ta tattare kirjin ta da hannayen ta, domin ita ko Yaya HAJARA bata taba bari ta ganta a haka ba bare katon namiji irin Al Ameen,
Ranshi ya mugun baci da reaction dinta wato he is right bama ta kaunar yaga koda jikinta that's means bata son shi da gaske tuni zuciyar shi ta Kara cushewa ya dagota cikin takaici ta hanyar damkar kafadunta, wanda saida yaji wani irin electric connection a jijiyoyin jikin shi domin yanajin wani irin softness a tafin hannun shi,
Kafin ta tsaya fuskar ta shabe shabe da hawaye tana girgiza kai tana kokarin mayarda hannun ta a kirjin ta,
Tuni ya saita kanshi saboda haushin ta ya ware hannun ta cikin takaici har saida taji zafi tareda bankaro kirjinta waje saboda muguntar da yake mata,
Ba Arziki ya saketa ya juya, domin yayi wani irin gani wanda zai cutarda kanshi da lafiyar jikinshi seeing her naked niple a cikin singlet and her huge boobs want to make him drip, jikin shi NA wani irin rawa yabar dakin yana jan numfashi tareda hada hanya yana blaming kanshi, "meye matsala ta da wannan yarinyar "subuhanallah ya furta tunawa da Abinda yagani, she has a perfect body structure and softer skin,

He remember the soft of her palma dazu da ya rike, meyasa komai nata is unique?
Runtse idanun shi yayi kawai yanaso ya goge komai a kwalkwal war shi,
"Come on Al Ameen delete it from your mind she is just a small girl karka janyowa kanka raini yafada yana kokarin kawar da tunanin shi baki daya bayason tuna komai, dole ya mike yabar gidan again, don baya ma kaunar zama inuwa daya da ita,
RAHAMA kuwa yana fita ta janyo rigar ta jiki na rawa ta saka ta nemi karamin mayafi ta fita domin dafa mai Abinci gudun wani laifin, bata son ta kuma ganin shi sam bata kaunar ganin fuskar shi tunda yaga jikinta. ........... 🖊




*Matar Soja*🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



Free page

*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*

1⃣3⃣&1⃣4⃣

Bai dawo gidan ba sai dare yawo kawai yayi tayi a cikin garin sokoto ranar rashin madafa, saboda sam bayason ya kasance cikin inuwa daya da ita hankalin shi bazai taba kwanciya ba, RAHAMA dai tunda rana tayi mai tuwon ta shirya mai miyar yakuwa taji kifi irin ta gargajiyar sokoto, ta zuba a warmers ta jera a dining ta shige dakin ta kulle kanta bata kuma marmarin ko lekowa ba, tana Koshi ta yi wanka ta dauki hisnul Muslim tana duba Addu'oin ta, saboda sam batason ta tsaya wani tunanin Abinda yafaru da rana,

Koda ya shigo gidan ya gama kallon ko ina kafin ya kalli kofar dakin nata dake datse, ya wuce dining domin yunwa yakeji, wani irin jan numfashi yayi tareda in healing kamshin miyar da tayi kyau ko a ido ga tuwon shinkafa dayayi fari kal ta nade shi a leda, zama yayi ya ja plate saida ya bude leda daya, yasa miya a gefe tareda kifayen ya dauki spoon yafara ci, yanayi yana lumshe idanun shi saboda dadin tuwon she is very good ta ko ina, saida yaci biyu ya tashi tareda shan drink din data Ajiye duk da yayi sanyi haka yasha, ya wuce daki yanayi yana waigon kofar ta,
Kasa bacci yayi a daren yana ta juyi tareda tunani wanda gaba daya ya cutar da lafiyar shi da gangar jikin shi a daren baisan meyasa yake jin loneliness ba,
Dakyar ya ga wayewar garin, saboda rashin bacci wanda kanshi har sarawa yakeyi, yana fitowa masallaci ya dawo falon ya zauna tareda zubawa kofar dakin ta ido kamar ya shiga yagani kota tashi,

Saboda tariga tasaba aikin ta da wuri kafin ya fito yauma hakane fitowa tayi sanye da hijabin na fama ta nadeshi a west dinta, ko ganin mutum batayi ba saboda da d'an sauran duhu sai haske kadan kadan dake fitowa cikin flowers dake falon da akayi decoration dasu, yana ganin ta tar Amma ita bata ganin shi, saida ta shiga kitchen tasa ruwan tea a jug heater ta fito, da, mopa tafara moping yana kallon yanda take komai a natse ba gajiya, he wonder wane irin training maman tayi mata haka, he really respect her mother,
Duk da HAJARA is her opposite bai hana shi jinjinawa iyayen taba yasan ita kanta HAJARA she choose that way for her self ne badan iyayen ta sunkasa bata tarbiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login