Showing 27001 words to 30000 words out of 101092 words
abin kunyar HAJARA, bin ta kawai Husna tayi domin ganin ikon Allah,
Yana kishingide a sofa ta shigo tana karairaya, har kusa dashi tana shirin zama ya daga mata hannu,
"Me kika shigo yi? "Kaifa bakasan Abun arziki ba daga shigowa gai sheka? " OK tank you you can go, "A yabo me yasa kake mun wulakanci don girman Allah,? Saboda nace ina sonka?
Shigowar Husna yasa tayi murmushi, "here comes my lovely sister, cikin dariya tace yaya wai jinya kakeyi a haka ka hada kumatu, lallai sister in low ta iya jinya, " sosai kuwa sister your sister inlow is the best, yafada da biyu, ta ko buga tsaki tareda mikewa tayi falo,
Husna ta bi bayan ta da kallo, kafin ta kalli yayan ta "yaya what is going on here? "What happen? ya fada, "why is she here kuma daga gani batada mutunci and sister inlow told me that she is her sister, really brother?
"Yeah and please be quit banason ran wife ya baci,
"What? Yaushe kafara son wife din yaya? "Just forget go and call her for me, tundazu ta fita bata dawo ba, yafada yana murmushi,
Momy ce ta shigo da sallama, daidai RAHAMA na fitowa daga kitchen, ta amsa HAJARA kuwa ko dago kanta batayi ba, bare taga waye ya shigo, cikin tsananin girma mawa RAHAMA ta nufeta tana mata sannu da zuwa domin basai anfada mata, ba tasan itace maman su Husna domin kamannin ta duk suka dakko macece wayayya gata Y'ar gayun gaske kamar ba ita ta haifi Al Ameen ba,
Ta saki fara'a tace Rahama ina mijin naki Y'ar Albarka?
Dukar da kanta tayi tace yana ciki , to ya fito ta nufi kujera ta zauna tareda kallon HAJARA da ta dora kafa daya kan daya batada niyyar gaisheta,
"RAHAMA da kunyar duniya da bacin rai ya gama rufeta ta matso cikeda takaici tace yaya HAJARA bakiga mutum bane da bazaki yi gaisuwa .. .. "Yimin shiru banza Y'ar iyayi tunda nazo gidanki dole kirika kawomin salo Kala Kala Karki dame RAHAMA lokacin kine yanzu, wata rana inuwa ta ma bazaki shaka ba......
Mikewar da momy tayi cikeda haushi da kuma masifa yasa na kauce domin momy irin matan nan ne da basa wasa da damar su kota minti daya wajen fada bata daukar nonsense ko ina ne don ko ya'yan ta saita su takeyi, "oh kece HAJARA? To uwar me kikazo yi gidan dana? Amma dai Albasa batayi halin ruwa ba, wallahi iyayen ki mutanen Arziki ne amma ke kin zama zakka, yanzu in banda tabewa me kikeyi a gidan kanwarki bayan kin guji Auren kuma ki dakko kafa fu don rashin ta ido kizo ki mike kafa kina zuba iko da rashin kunya,
Bari inkira malam bala inji ko da sanin shi kika zo gidan kanwar ki kika tare,
Tafada tana fitowa da wayarta, wanda yayi daidai da fitowar Al Ameen da Husna domin suna jin fadan momy, RAHAMA sarkin rudu tuni ta fara hawaye jikinta na rawa, domin tasan itama yau sai tayi laifi wurin baba inyaji HAJARA na, boye gidan ta....... 🖊
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻
*By FENERH*
*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*
2⃣1⃣&2⃣2⃣
A kwance take a dakin Husna, takasa bacci ba abinda take tunani sai Al Ameen da daren su na jiya, wani irin kewar shi takeji, gashi yaki zuwa ta ganshi, wani irin sanyi ke bin ko ina na jikin ta idan ta tuna da duk Abinda ya shiga tsananin su, a gaskiya rayuwar Aure na tattare da ni'imomi daban daban, domin tasan yau ma da suna tare haka zai shayar da ita madara mai wuyar mantawa, moment dinta da Al Ameen jiya was unforgettable, ya shiga cikin tarihin rayuwar su,
Tunawa tayi da ciwon shi, tuni taji wani irin tausayin shi, yanzu All this years Abinda yake fama dashi kenan,?
Tunawa tayi da lokacin da ake fama da HAJARA ta yarda da Auren shi taki, tana cewa ai nakasashshe ne, yanzu wannan ciwon ne HAJARA ke kira nakasa? Ai wanna Abun a tausaya mai ne domin kowa kallon mai lafiya yake mai ita dai bataga ciwon da zaisa ta kasa zama dashi ba koda kuwa gurgu ne, mutum ne mai halin kwarai idan ka fahimce shi,
Tunda taje gidan shi bai taba yi mata iyaka da wani Abinci ba sai dakin da ya turata wanda ita a wurin ta yafi mata saukin zama matsayin ta na Y'ar talaka,
Murmushi tayi tunawa da lokacin da yace zai horata, da aiki sai taga ma shi baiko iya shirya mugunta ba tunda bai iya daukar hannu yace zai daki mace,
Kwana tayi juyi tareda kewar Al Ameen sosai wanda batasan ta Ina takejin wani bakon Al Amari ba,
HAJARA dai wasa wasa kafarta ta kunbura saboda targadata da Aliyu yayi da duka dakyar take taka kafar ta, koda baba ma yazo yaji labari dakin ya, leka yace "ummi Allah ya shiryeki domin bamu yi miki bakiba ma kina ganin rayuwa bare kuma mun biki da mum munan lafazi, Amma kisani baki kyauta mana ba baki kyauta wa Y'ar uwar ki ba, kema baki kyautawa rayuwar kiba, kibi a hankali ummi ke ya' mace ce duk kuskuren da zakiyi zai zama cikin tarihin rayuwar ya'yan ki ne mai kyau ko mara kyau, yau bakya Alfahari da yanayin rayuwar yar uwar ki, RAHAMA ta gama dacewa, kina nan kina kokarin ruguza mata rayuwa Allah nakara daukaka ta,
Karatun nata da aka kutsire mata tana can zataci gaba saboda biyayyr iyaye, karkiga mun zuba miki ido HAJARA, wallahi ko infada ko kar infada sai duniya ta koya miki darasi ko yau ko gobe don haka Allah ya kare ki daga fadawa halaka,
Ya juya ya fita,
Wanda da kanshi ganin yanda take fama da kafar ya gyara mata cike da tausayi na mahaifi da kuma tsantsar soyayyar HAJARA da har yanzu tana nan domin soyayyar iyaye ta daban ce duk wanda ya rasa su yayi kuka wallahi duniya su din gatan mu ne jigon mune garkuwar mu ne su, duk da inna tayi fushi da ita Amma ta tausaya mata ganin yanda duk ta koma abin tausayi,
Amma Abinda basu sani ba sam rayuwar HAJARA babu nadama kudurin ta na nan na inhar bazata samu Al Ameen ba RAHAMA ma bazatayi farin ciki ba,
Daga zaune ta kira kawar ta mai zugata Ladidi wata irin yarinya ce masu irin yawon nan da son Abin duniya itama ba wai Y'ar masu kudi bace Amma tsabar son Abin duniya yasa ta zage damtse take yawon ta zubar domin ta rika karya,
Kawancen su da HAJARA ya samo Asali ne a school tunfarkon shigar su, d'an fodio, kusan halin karyar su yazo daya da HAJARA shiyasa suka dunke ko yanzu ita ta ke zuga HAJARA akan duk Abinda takeyi,
Cikin shasheka take mata magana, " ki kirani takare min,
Cikin karad'i tace "kawata ya akayi ne? " Kedai kikirani, ta katse,
Ladidi ta kirata tana dauka tace "yadai? Anan ta kwashe komai ta fada mata, ta labto Ashar "wallahi akwai kan uba kenan sha kurumin ki yanzu ki nuna komai ya wuce mu munsan ta inda zamu bullowa lamarin, tunda kikaga ta koma gidan su ba dadewa zatayi ba zata dawo by then munfito da wani salon kawata kiyi kwanton bauna kawai, inta kama ko kan dutse ne sai mun leka don da muji kunya gwara Aljihun mu ya, bushe tawan, bari inturo miki kati, tafada tana kashe kiran tareda antayo mata dubu guda kai tsaye,
HAJARA tayi farin ciki, sosai a nan ta samu na data,
Ganin sababbin hot pictures din Al Ameen a Mumbai yasa tasan baya kasar so take tasani da RAHAMA yatafi ko shi kadai,?
Wani irin murmushi tayi tunawa da yanda momyn shi ta wuce da RAHAMA tasan for sure RAHAMA na garin sokoto,
"Don't worry my little sister wasan bai kareba, ban shiga daulaba kema bazaki shiga ba ban Auri Al Ameen ba kema bazaki taba Auren shi ba, kiji dadi ba, mu zuba nidake,
**************************
Wasa wasa An kwashe wata guda ba labarin Al Ameen bai kira kowa ba saboda fushi, yaron shi ya kawowa RAHAMA Envelop da kudi cike da kuma takarda mai dauke da kalamai masu cike da soyayyar ta da kuma matsayin ta a zuciyar shi wanda saida ta koka a ranar ita kadai tareda jin kamar tayi tsuntsuwa ta bishi wanda ya fada mata zai dawo idan su momy sun dawo mai da ita gidan shi,
I can't stay in my house without you nasaba da ke nasaba da rayuwa a inuwa daya dake duk da we are not too close amma ji nake munyi shakuwa mai girma Rahama take care of my marriage and take care of your self zandawo gareki da yardar Allah I no banda matsala dake kedin mace ce ta gari ina farin ciki ina Alfahari, za akawo miki waya ki fadawa Husna ta bude miki watsp zamu rika chart kinji,
Zuciyar ta tayi matukar tsinkiyewa da karyewa saboda yanzu ne takejin dadin zama dashi yanzu ne takeji zasuyi zama mai dadi, memory dinta na dada tariyo mata rayuwar su ta daren da zasu rabu wannan daren bazai taba gogewa a zuciyar taba,
Dady ya kammala mata duk wani shirye shirye domin ta zana jarabawar ta a cikin watannin, bakaramin farin ciki tayi ba lokacin da dady ya kawo mata zancen karatun ta, koda aka kawo mata wayar momy karba tayi tace bani kar ya sauya miki ra'ayi nasan halin shi ki kyale shi inya matsu zai biyo jirgi ya dawo, wanda hakan sam baiwa RAHAMA dadi ba taso ta ji murya shi ko da sau daya ne,
Gashi tana jin kunyar Husna bazata iya tanbayar ta ba, dole ta share ta fuskanci Al amarin karatun ta, domin Allah yagani tanada burin ganin ta zama likita a rayuwar ta,
Momy kula take bata sosai har ta saki jiki da su yanzu ta rage kunshe kanta domin bakaramin fada momy ke mata ba akan rashin kama jiki, wanda dole ta saki komai na gidan yanzu sukeyi ita da Husna kullum suna kitchen tare, wanda hakan ma farin ciki yake karawa momy Domin Husna dole tayi girki da aikin gidan,
Tun tana korafin "sister inlow gaskiya ki koma gidan mijin ki nidai kinjamin aiki har ta hakura Abin yafara bin jikinta,
Idan ma fita ya kama tare sukeyi da Husna, tana kiyaye ka'idojin fitar ta wajen suturce kanta tareda kiyayewa,
Gyaran jiki duk sati sai sunje anyi musu itada Husna, tana waya da su baba da inna yaya Aliyu ma har zuwa yakeyi wanda yanzu yake aiki da first bank saboda yace bai ra ayin aiki karkashin Alhaji shuaibu kuma ko baba yanzu katon Kanti ya bude da kudin Sallamar da yasamu a wurin Alhaji, saboda shekaru sunja gashi suruki dole ya Ajiye driving,
Ganin HAJARA ta sakko tareda gyaruwa yasa baba ya barta tacigaba da karatun ta kafin Allah ya kawo mata miji su mata Aure a cewar su,
Wanda ita sam wata dama kawai take nema, ta kuma shuka tsiya wanda iyayen ta na binta da Alkhairi tana musu kudurin tsiya mujedai zuwa Zamugani,
******************
Tundaga nesa nake kallon su cikin dogayen riguna pitch colour, sun yafa mayafi mai wadata tareda maka tafka tafkan eye glass, a idanun su , dole ka kallesu ka kuma marmarin kallon su saboda kyau da murjewa wanda dayar tafi daukar ido. Tayi wani irin ja mai kyau da daukar ido ta canja canji na mamaki saida na matsa da kyau nagane wacece "RAHAMA 😲 ina hijabi da kunbiya kunbiya,? Kana ganin ta kasan wayewa ta zauna tazama big girl ba duhun kai,
Mika ma Husna key tayi tareda cewa " look I can't drive today, you drive, "aa gaskiya wannan wayau ne kawai to meye Amfanin iya motar taki nidai ki tuka,
Ashe kuwa za a fasa fitar yau, daga kafada Husna tayi tace shikenan mu koma, saboda iya shege haka suka koma cikin gidan, da momy ke zaune tana clearing oder kayan da za akawo mata daga India, taga sundawo, tace "yadai? Daga fitarku kuma kudawo? RAHAMA ce ta zauna gefen ta "momy munfasa fitar "saboda me? "Saboda ba wanda zai iya tuka motar yau, inji Husna,
"Iya shegen banza da Wofi kuntashi kuntafi ko sai na bata muku rai?
Idan bazaku iya tukiba baga driver ba kun tsaya kuna wani shirme, "ke Husna kinsan halin gwaggon ku tunda tace kuje to gwara kawai ku wuce bazan iya bayani ba,
"Wallahi momy gidan ne ba dadi komai kwarkwarori ni gaskiya gidan sarauta baiyi ba, komai doka ka ida gaskiya if possible muyi zaman mu kawai, Husna ta fada, RAHAMA tace "momy bakin ciki take min taga ina kwadayin shiga gidan sultan of sokoto, nidai muje na yarda I will drive,
Haka dole suka wuce RAHAMA ta tuka Lexus din Husna suka fita, cikin kwarewa take tukin ta kana gani kasan hannun ta ya fada
"Ina labarin Al Ameen,
Tunda yatafi ya fara karbar treatment wanda Ake samun nasara sosai, gefen zuciyar shi kuwa yagama saduda cewar dady ya raba Auren shi da RAHAMA domin tun bayan zuwan shi da wata biyu Dady ya kirashi yace ya aiko mai da takardar ta ta waya zai mata Aure, tuni ya datse waya da kowa, shidai RAHAMA is his wife ba wanda ya isa yasa ya saketa and itama yana fushi da ita sosai domin yayi iya kokarin shi domin suyi communicating Abun ya gagara yasa anbata waya abanza wanda ya nuna mai she don't care about him at all wanda shine kuma duk motsi ko fitar numfashin shi tareda sunan tane yake fita ya gama yarda RAHAMA ta gama siye birnin zuciyar shi, wanda baijin zai iya rayuwa ba tareda itaba, as fa as zai koma nija dole yasan za ayi rigima dashi don dole abashi matar shi,
Momy tun yana kiranta domin ta hadasu har itama yadai na,
Gefen lafiyar shi Alhmdulillah wanda shi kanshi yasan he is normal yanzu Domin da tunanin ranarda suka kwana tare yake kwana yake tashi, wani irin soyayyar ta da kwadayin kasancewa tareda ita yake kamashi, wanda akwanakin nan yakejin in har bai koma da kanshi ba akwai matsala don yana gab da neman dauki wurin India wa.. ........ 🖊
"Allah yasa in tsinceshi waje gobe ba typing,
*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻
*By FENERH*
*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel 200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39 03*
2⃣3⃣&2⃣4⃣
Su RAHAMA dai suna can suna jin dad'in rayuwar su gidan sultan of sokoto domin Amaryar shi ce kanwar Dady gata mace wayyaya, tana sakewa sosai cikin su tareda Kara wayar musu da kai akoda yau she, saida suka kwashe sati guda cur a cikin gidan kafin momy ta damesu su dawo domin RAHAMA ana so ta fara karbar lesson kafin takardar ta ta fito,
Ta jona school of science dinta,
Fadin canjin da rayuwar RAHAMA ta samu bata bakine domin inkaga dressing dinta zaka dauka wata ce can data taba rayuwa a kasar turai, wanda sai yanzu tafara blaming kanta tareda jinjinawa Al Ameen da har ya iya fadawa soyayyar ta a cikin gidadan cinta, ita kanta yanzu ne ta fuskanci ta yi rayuwar gidadanci a baya wanda tasan cewa duk rashin son mu amala da mutane ne ya janyo mata hakan,yanzu kuwa ko gidan gwamna zata iya kutsa kai ba ji, a yanzu ta fahimci maganar da kullum HAJARA ke fada mata na tanada duhun kai, kuma ta yarda yanzu kan mage ya waye, don ta fannin karance karance ta samu wani ci gaba sosai,
Zancen Al Ameen kuwa tana matukar damuwa da rashin dawowar shi wanda ta yarda yanzu