Showing 75001 words to 78000 words out of 101092 words
da ya gudu bai jiramu ba,
"Naji kuma zaku hanani tuna uban yaya nane? "Ya'yan guda nawa ne BIYU fa kacal, suka fada suna dariya, "Alhmdulillah gasu a yau sun cika min gida daku nan gaba kuma zaku zama one big family idan kukayi Aure, yau Al Ameen yaran shi Hudu Husna uku to me yafi wannan kuma zamu samu wasu karin a wurin ku zuri'a ta yi yawa da Albarka
Meenal ce ta mike tareda kallon su tace " nidai zan tafi gida Baba zai neme ni idan yadawo gida, Nasir muje ka sauke ni, grandma zantafi tafada tana saba gyale da jakar ta ta Y'an mata mai kyau Mai cycle
"Toh Amina ki gaida Hajara tunda ke bakya iya zama gidana, " aa wallahi baba ne ko family house baya bari muna kwana, " toh Badamuwa " nasir jeka sauke ta, tashi yayi yana jin dadi domin gaskiya yana son dama su jera akoda yaushe da ita yarinyar ce akwai kyau na fitar hankali gata fara tas irin uwar ta kirar ta kuwa ba a cewa komai, da biyu take yawan son zuwa gidan kakar su sadiq din,
Saboda tasan kullum yana zuwa gidan kuma Allah ya Dora mata mugun son yaya Sadiq din duk da bawani girman ta yayi ba impact yan watanni ne ma a tsakanin su,
Tariga tasan bazai taba sonta ba don ko kallo bata ishe shiba impact bata ma tunanin zai sota domin shi miskilancin shi har ya wuce gaban kwatance, Abubuwa da yawa sunsa tana shakkar shi domin yanada kudi sosai mahaifin shi nada kudi momyn shi babbar likitace a Asibitin Uduth dake sokoto ita kuma iyayen ta a kar kashin inuwar su suka ginu domin sunada labarin komai duk da akwai zumunci mai karfi a tsakanin s, tana kokarin goge wannan tunanin a kwakwal war kanta, tanada samari da yawa domin Allah ya bata farin jini Sosai saidai zuciyar ta naga Abubakar Sadiq da baisan tanayi ba,
Tana fara tafiya Nasir na bayanta, sukaji Sallamar shi cikin wata irin murya mai Amo da kuma taushi ga wani uban kamshi mai shegen tsada da kuma tafiya da hankalin Y'an mata, ya musu sallama, jitayi jinin jikinta ya tsaya cak take takasa motsa kafafun ta tafara shakar kamshin mai tafiya da imanin Y'an mata, dakyar ta iya bude kwayar idon ta ta sauke akan kyakkyawar fuskar shi dakuma surar jikinshi, zatasha workout,
A cikin kakin custom yake wanda kana gani Kasan ba wai karami bane yataki matsayi babba kuma mai girma ya hadu karshen haduwa gaba daya haibarshi da kwarjini shi sungama cika ko ina nafalon,
Kanshi ba hula hannun shi daure da Rolex watch ga wata katuwar tab a hannun shi kana ganin fuskar shi Kasan yarone d'anye sharab sai dai kudi da suka sa ya girma a idanun mutane don yataso cikin su,
Kasa motsawa tayi har saida nasir ya taba ta, " muje ko? Saurin dawowa tayi hayyacin ta tace" toh dakyar take iya daga kafar ta Allah yasani bata son ta tafi yanzu da yashigo Gashi yau taganshi cikin kaki bata taba ganin shi a cikin shigar ba sai taga kamar donshi a aka fito da kalar kakin, wani irin bugu kirjinta keyi saboda soyayayr shi, son Sadiq zai kasheta idan ba ayi wasa ba, gashi yayi kamar bai gantaba, don haka hartasa kafar ta zata fita tace wa nasir " am coming bari mugaisa kar yace bangaida shiba, " no kizo mu wuce kinsan halin shi zai iya gwaleki, " bari dai inzo tafada tana komawa, Wanda tuni duk sauran sun watse a falon dodo ya shigo,
Muryar ta na rawa ta karasa tareda cewa "ina wuni ya sadiq, dakyar ya daga halshe kamar wani sarki ko kallon ta baiyi ba yace lafiya,
Taji muryar shi kamar wata sarewa duk da bawata doguwar magana yayi ba Amma tasani tana mugun son jin maganar shi don har recording muryar shi tayi a wayar ta tana saurare idan tasamu kebewa ita kadai,
Tsawar da ya buga mata tadawo da ita, " uban me kikeyi anan please get lost zanyi magana da grandma dina, zabura tayi tayi waje da gudu tana dafe kirji, grandma ce ta kalle shi " meye haka Sadiq bana hanaka irin mugayen halin nan ba bakyau wulakanci fa kuma inba kaiba kaida Y'ar uwar ka kuma ma ai ba wani girman Aminar kayi ba wata baifi shida ba kaga ko ba wani son girma da zaka nuna mata,
"Wallahi ima mata kallon yarinya ce kamar su Aisha dasuke kanni na, "toh naji me kadawo yi yau kuma?
"Grandma dole indawo please kifadawa Dady Aure nakeso nama fara searching mata ina son Aure nan da karshen watan nan,
Wani irin kallo take aika mai, "ikon Allah shekarar ka Ashirin da hudu fa sadiq, "aa da Biyar fa grandma, kuma ai na isa Aure gani da business ga aiki dana samu kuma Alhamdulillah nafito da matsayi mai girma, don kunga kunki yiwa Y'an matan ku Aure da wuri ni Zanne mo sweet sixteen ne dai dai dani in Aura,
Bawai katuwa Y'ar shekara Ashirin ba,
"Toh me yakawo wannan zancen? 'Kune ai kun tara yara har sun wuce misali waisu karatu nifa inyarinya ta cika wayewa I dont like her duk sungama zubarda mutuncin su a university nifa nasan me sukeyi wasu ma kokarin yimaka fyade sukeyi a school, duk mungansu ai, shiyasa I hate graduate, " toh d'an wulakanci Aure lokaci ne kuma ba duka aka taru aka zama daya ba, don haka kayi musu kyakkyawan zato,
"Hmm ayidai shuru kawai please grandma back to our conversation please kifadawa dady Aure nakeso wallahi ko infara bin yaran mutane don inada lafiya nidai,
"Toh Allah ya shiryeka d'an banza tashi katafi ko insaba maka inka fasa bin matan mudai zuri'ar mu ba wanda yayi hakan don haka da izinin ubangiji bawanda zai janyo mana tozarci,
Mikewa yayi " nakoma bakin aiki sai nadawo inji yanda kukayi , yafita yana dariya kasa kasa irin ta miskilayen maza,
Wani irin tashin hankali grandma taji, ta janyo wayarta ta fara latsawa takira d'an nata, yana dauka tace " idan kun dawo kuzo gidana kaida matar ka ina son magana daku,
Tafada tana datse kiran,
****************
Meenal meenal aketa kwala mata kira bataji ba tun shigowar ta ta fada dakin su itada kannen ta ta kulle kanta ita kadai tasan yanda takejin zuciyar ta "Sadiq bazai taba samuwa agareta ba, fadan maman su yadawo da ita ta yi saurin goge hawayen fuskar ta ta zabura ta bude kofar,
Macece da, girma yafara nunawa atareda ita ta cika wuri tana nan yanda take da kyau saidai girma da yazo mata wato Hajiya Hajara kenan, wanda kana gani Kasan hutu ya zauna gata cikin gidan Alfarma da kuma ni'ima, fada tafara yimata,
" ke don iskanci kindawo gidan ma koki leko Kifada, min gaki ishashiya ko, to sannu mandiya, idanun ta ta Kalla taga yanda sukayi wani irin ja da kunburi saboda kuka,
"Meyasame ki? Au iya shegen ne na koke koken ya motsa, zaki fada muji intayi wari, kuma kifito babanki na kiran ki kuma ki gyara fuskar ki kafin yafara tuhuma ta ehem, tafada tana juyawa tabar dakin, ............... 🖊
*korafi ya karbu masoya zanci gaba da tsara wannan labari ta wani irin salo da zai kayatar daku kuci gaba da biyoni insha Allahu zaku nishadu fiyeda salon farkon don haka muje zuwa masoya*
*Godiya agareki kawata sa adatu matar Soja ina miki fatan Alkhairi a duk inda kike Allah ya baki Abinda kike nema duniya da lahira, jinjinar bangirma ta wajena*
*Matar Soja*
🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻
*By FENERH*
6⃣1⃣&6⃣2⃣
Fita tayi tareda gyara fuskar ta ta nufi dakin iyayen nata, A zaune tasamu mahaifin nata wanda ya ke sanye shima cikin shiga ta Alfarma bazakace shine Bello bakanike ba ya zama Alhaji bello yanzu Alhmdulillah rayuwar su ta inganta sanadin Alhaji Al Ameen, ba Abinda suka rasa yanzu,
Samun gefe daya tayi ga kannen ta biyu mata sai matashin namiji wanda yake karamin su a ciki, ta gaida baban ta fuskar ta akasa, " Amina, "na am ta Amsa, " me kike jira da maganar fitarda miji? Duk kannen ki sunfito da nasu nadakatar dasu saboda banaso inyi musu Aure ke kina gida,
Nasan dai ba masoya kika rasa ba meye dalilin rsshin tsaida gwani guda daya? Wani irin faduwa taji gaban ta yayi Allah yasani ita Sadiq takeso Amma tayaya zata fito ta fadawa baban ta hakan, tsawar da mama HAJARA ta buga mata tasa ta dago cikeda tsoro, " iya shege badake ake magana ba, in kina da Abin fada ki fada inbabu tashi Kibawa mutane wuri, Alhaji samu zakayi cikin yaran ku na wurin aiki maiso yazo abashi nidai bazata zauna min a gida ba in kannin ta sunyi Aure,
"Bi a hankali maman yara A lallaba ta kawai ta tsaida mutum guda cikin mane manta, " idan kabi ta yarinyar nan bazata taba fitowa da wani tace gashi ba don mugun korar wulakanci take musu bansan dalili ba, don haka idan kaji tatawa wallahi katsayar Kawai da kanka,
Kuka tasa mai karfi tareda zabura " wallahi nidai karku hadani Aure da wani ni wallahi banason kowa ni akyale ni inkuma akayi zan kashe kaina kowa ya huta, bazan taba iya zama da wani namiji ba ku kyale ni, ta fita da gudu tabar dakin,
Wani irin tukukin bakin ciki ne ya rufe mama Hajara yau Y'ar da ta Haifa ke fadar irin wa innan Kalamai a gaban ta? Lallai duniya dama anfada komai biyadin biyadin ne Inkayi sai anyi maka, a yau tasan zafin irin bijirewar ya'ya agaban iyayen su, Alkhairin Allah yakaiwa iyayen ta a duk inda suke, ita da ya shuka rashin mutunci buhu buhu Yau gashi Y'ar ta batayi irin nataba Amma taji ciwon kalaman,
Wasu irin hawayen takaici tareda nadamar rayuwar ta ta Y'an matan ci da sam bata da riba don haka dole ta takawa Y'ar ta birki don ita batada hakuri irin nasu inna,
Kallon ta Alhaji bello yayi " kibi ta a hankali Karki ce mata komai ni zan zabo mata miji karyar shegan taka takeyi kuma kutashi ku tafi, yafadawa kannen da sukayi tsit a wurin,
Abin yayi mugun damun HAJARA don haka mikewa tayi ta nufi dakin ta ta kulle tareda daukar wayar ta ta kira Y'ar uwar ta kuma Abokiyar shawarar ta a kullum mai hangen nesa,
A zaune take a ofishin ta na likita sanye cikin lab cot dinta fara kal tareda farin glashin ido, kana ganin ta zakasan tagama samun duniya saura goben ta kawai tayi fess da ita ta waye karshen aji,
Leshin dake jikinta kawai zaka Kalla Kasan matar manya ce ita,
Daukar wayar ta tayi datayi kara tasa akunne a cikin sauri tace "yaya barka da rana,
"Barka dai RAHAMA ya aiki? Alhmdulillah, yaya lafiya najiki cikin damuwa? " Hmm Y'ar kice, a anan ta fada mata komai tareda cewa " yau ta sa na tuna irin bijirewar da nayiwa su inna Allah ya gafarta musu RAHAMA Ashe haka Abin keda ciwo, wallahi yanzu haka zuciya ta har wani irin tafasa takeyi akan ta zan iya shake Y'ar nan kowa ya huta,
"Yi hakuri yaya kibita a hankali yanzu ki zaunar da ita kibata misali da rayuwar mu ita kadai ta isheta darasi, kuma nima zankirata gobe weekend inmata Nasiha insha Allahu yaya kibi komai A hankali,
"Toh tace tareda yin Ajiyar zuciya ta kashe wayar, tanajin sanyi tareda godiya da Allah yabata Y'ar uwa irin RAHAMA,
Tashi tayi ta nufi dakin yaran nata, tace kannin sufita zatayi magana da yayar su wadda ta hada kai da guiwa tana kukan bakin ciki, zama tayi gefen ta "Meenal, kina jina, dago kanki, tafada cikin taushin murya, ta dago duk fuskar ta fara tayi ja sumar dake kwance a gefen fuskar ta dake kara mata kyau duk sun jike da zufa, meenal photo copy din maman tace sai dai tafi HAJARA kira sosai don ita Allah ya hore mata dukiyar fulani da kuma hips kamar zasuyi magana wanda duk Lafiyayyan namiji zaiso mallakar mace kamar ta, ga ta fara tass kamar kataba jini ya fito,
Kallon maman ta tayi tana share hawaye tareda shashsheka, " me kike son ki zama a rayuwar ki? "Ya' tagari ko batacciya? Ayau inaso ki kalli rayuwar mu nida Y'ar uwata kafin a sameku akwai kalubale da muka fuskanta a cikin rayuwar mu, Karki cigaba da wannan halin da kika fara nunawa yau zamanin ki ba irin namu bane halin iyayen ki daban da nawa kije kitanbayi momyn ku irin Abin da nayi a baya wanda banci ribar shi ba don haka ki gyara wallahi Karki ma fara musu da mu bazata haifar miki da da' mai ido ba,
Ta mike gobe ki shirya kije gidan Su Aishan momyn ku nason ganin ki, tafita daga dakin,
Karfe biyu momy RAHAMA ta kira mijinta lokacin ya taso shima daga bakin aikin shi, tace "Allahu ya kiyaye min kai zuciyar RAHAMA, "hhhh yayi dariya " Karki rika fasa min kai fa shiyasa na kasa kara Aure har gobe saboda inada ke Hajiya ta, " hhh yanzu dai kana ina?
" ina hanyar shigowa Asibitin ki kifito mutafi gidan momy na ko, bansan neman da take mana ba, mikewa tayi Kawai tana gyara mayafin ta tareda cire lab cot din tafita, ma aikata sai gaida ita sukeyi domin matar nada kima da sanin darajar Mutane koda nakasan tane don haka kullum rayuwar ta keci gaba ta gefen taimako ma kullum Asibitin ta mutane tururuwa sukeyi har Asibitin taimako ake kiran shi,
Tundaga nesa ta hango katotuwar motar shi tafara taku cikin natsuwa tana jin wani irin dadi, har ta isa kusa da motar ta yayi saurin fitowa tareda sakin fuska, yana nan cikin gayun shi saidai girma da ya nuna afuskar shi yayi sauri ya bude mata motar "bismilah hajiya ta, ta shiga ta gyara zama shima ya zagaya ya shiga saida ya zauna, " ina driver yau? " ai nasan bakyaso shiyasa nazo nikadai tunda convoy dina ma kinsan sundaina bina, " uhm ai baida Amfani ne mutum kamar yana nuna kanshi ne a duniya kuma fariyar tayi yawa, duk ka cika gida da motoci,
"Yazakiyi da D'an ki da yake jera mota Biyar a bayan shi kuma yanzu? " shima ima mai surutu Kasan momy goyon bayan shi takeyi don haka nakyale su, yanzu ma karkaji da wai zancen shi ne zatayi tace muzo,
Dariya yayi kawai yana kallon hanyar fita daga tangamemen Asibitin nata mai dauke da sunan Al RAHAMA private hospital,
Direct gidan momy suka nufa lokacin ita kadaice a falon ta sanye da hijabin ta da carbi sai Y'an aikin ta dake kai kawo,.
Suka shigo da Sallama, suka zauna RAHAMA ta mike tareda cewa " momy ke kadai don Allah ki koma gidan mu Kudaina zaman kadaicin nan haka kina ganin part dinki na nan kullum sainasa An gyara shi tunda aka Gina kinki yarda ki koma,
"Hmm banason inbar dakin mijina ne Y'ar nan inajin dadi na a nan da kun kyale ni kawai, "aa momy inji Al Ameen gaskiya ki shirya kawai ki koma meye Amfanin zaman naki kekadai bayan ina raye inada gida wanda zai dauke duka zuri'ar mu ba tareda takura ba ace kina zaman kadaici,
Toh yazanyi Al Ameen ya'yan kune sunki su zauna dani saidai suzo su isheni su wuce ita Husna kuwa Kasan dakyar ma Ali yake barin ya'yan gwal dinshi na fita suzo ma duk su isheni, dazu ma nan da nasir da takwaran malam da kuma na Alhaji suka Zo suka isheni saida dodon su yazo suka bar gidan,
Kitchen RAHAMA ta shiga ta hado musu Abin motsa baki ta fito, ta ajiye ga tsakiyar su, "momy Kince kina kiran mu Allah yasa lafiya? "Eh lafiya ba lafiya ba, zancen sadiq ne yazomin da wata magana dazu,
Yace infada maka yanason Aure, don haka tun wuri kayi mai tunda yafada kuma yanada Abin yi, yanada karfin rike mata hudu ma ba daya ba,
Rike baki Al Ameen yayi "yanzu momy shine sadiq din da kanshi yafito yace ayi mai Aure? Wata irin kunya ta rufe RAHAMA wai Aure lallai ma yaron nan baida kunya, "yanzu don girman Allah momy sadiq ne za ayiwa Aure? "Eh nadai fada maka sakone na isar kuyi duk Abinda kuka ga dama, "yanzu momy koni lokacina ai ku kuka sa nayi Aure bantaba fadar irin haka ba bare shi "karka hada kanka dashi inbaso kake inyi maka tone tone ba,
"Ayi hakuri zanduba yafada yana daukar juice din da Aka Ajiye mai ya kurba yana tunanin tabbas shima badon baida lafiya ba lokacin shi kila da ya nemi Auren kila irin halittar shi sadiq din yakeda,
A natse RAHAMA ta gyara zama " momy yafada miki yasamu mata ne? "Aa yace zai nema ko a