Showing 60001 words to 63000 words out of 84568 words

Chapter 21 - SOYAYYA DA IZZA complete hausa novel

Mrs KD   

25 Aug 2024

21468

na shirya" "wow yan mata na kinga yadda kikai kyau" sunkuyar dakai kasa kawai rayi, yanason yajuya yakalleta amma yakasa saboda izzar sa data mai yawa, itakam tana futowa taji kanshin turarensa hakan yabata cewa shine, takowa take zata wuce, wayar Mamy ce tayi ringing "yawwa gashinan ma takira ni, Zuhura dan tayashi yasa lins din, kabata ta tayaka sawa, zan dau waya" daga haka tafuce tana daga wayar "hello mom Ilham" , tsayawa kawai tayi batare data kalle shi ba, shima kuma be ce mata komai ba , amma yana satar kallonta ta gefen ido, kici niyar sakawa yake, ganin haka yasa dakyar tabude baki tace "kawo na tayaka" bece komai ba ya matsa kusa da ita sosai "jitai numfashinta na kokarin daukewa sanadiyar kanshin turarensa daya bugi hancinta sosai, lins din takarba tafara sakamai, shikuma yakura mata ido yanajin wani yanayi me dadi acikin zuciyarsa,





💞SOYAYYA DA IZZA 💞





Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)

Yar amanar jajirtattu💪💪

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




Ina masu bibiyar books dina😃to ina muku albishir da sabon book dina😁dana fara rubutawa✍️✍️ me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan😇dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu🤣zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa😍ina alfahari daku🤩 masoyana😍 kune kwarin gwuiwa ta😀i love you so much❤💔my pans😘



ina godiya da addu'o'in ku🙏🙏🙏
dayacce kuke yabon book dina💅💅 duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu😂😂

nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku😀😀






page 41




___________________Harta gama samai besani ba , ya lula cikin kallon ta yana tunanin da shi kadai yasani, matsawa tayi, kana takalle shi, shima ita yake kallo, Mamy ce tafado dakin tana fadin, "son kamaji wai ba se an tafi dashi ba, tunda dawo dashi za ai nan din" se lokacin ya dawo hayyacinsa, yayi saurin kallon Mamy yana fadin "hakan ma yayi" "Zuhura kije kiga Jummai takarasa shirya Nadra" amsawa tayi da to tana fucewa, binta da kallo yayi, harta fuce "son su Abba fa sun futo suna falour" "ok ai nima nagama" "to kasa babbar rigar mana" "ah ah Mamy bayanzuba" "tom shikenan muje" tafada tana daukan jakarta, futowa falour sukai, duk sun hadu tafiya kawai ake jira, harda amarya Ilham tana zaune taci shadda golden yellow dinkin yasha duwatsu tun daga sama har kasa, se kyalli take tana walwali, futowa Zuhura tayi ita da Nadra se Jummai da take binsu abaya, itama tayi kwalliyarta dan Mamy tayi mata dinki har kala biyu, mikewa sukai dukansu suka fuce zuwa farfajiyar gidan, Bala driver ne yakwashi su Nadra da Muhsin da Zuhura yatafi kaisu airport, shikuma Jawad yadau Ammar da Ilham da Mamy da Abba, Abba ne agaba, sukuma suna baya, "jummai idan bala driver yadawo zaku tawo" "tom Hajiya" daga haka suka wuce, Abba ne ya kalli Jawad dake waya yace "Jawad kashe wayar nan kasan dai dokan tuki ko" tom yafada yana fadin "Yasmeen ina driving idan na sauka zan kiraki" kana yakashe wayar, shikam Ammar yajuyar da kansa yana kallon gefe fuskar nan a tamke kamar an aiko mai da sakon mutuwa, Mamy na lura dashi,

harsuka isa airport be kalli Ilham ba, bayan sun isa suka isa jirgin suka shiga, ita dai Zuhura gabanta nata faduwa dan bata taba hawa jirgiba, wani iri takeji wai yau itace zata shiga jirgi, a daddare take hawa matartakalar jirgin, bayan sun shiga, taga kowa yana duba number kujerar, can baya Ilham da Mamy sukai, sukuma su Jawad suna tare da Abba, Muhsin kuma da Nadra na can gefe, shikam gogan tuni ya zauna, itama dubawa tashiga yi, setaga kusa da Ammar take, hakan yasa tazauna kusa dashi, ita dai har yanzu zuciyar ta bugawa take, har ta zauna, announcement aka fara kowa yasa belt jirgi ze tashi, sawa suka fara itama sawar tayi, bugun zuciyar ta na karuwa, lokacin da jirgin yafara tafiya kamar ta nutse saboda tsoro, jirgi yana tashi, tasaki wata razananniyar ajiyar zuciya, tana kamo damtsen hannunsa ta kamkame, tare da rumtse ido, kama hannunta yayi data zagayo dashi ta damtsensa, yana shafa hannunta a hankali dama yana taso ya taba fulawar tata, itakam bama tasan meke faruwa ba, cikin ta ya kada ya duri ruwa, kara tura kanta tayi jikinsa tana kanainaye shi sosai, seda sukai 30mint a haka, daga baya tafara bude idonta, se lokacin ta tuna wa ta rike, da sauri taci ka shi, shima hade fuska yayi yana kawar da kai gefe, tuni ta nutsu ta dawo hankalinta,


"yaya Yasmeen kifuto inji Daddy ke ake jira" "ok muje au tsaya na dau bag dita" daga haka tadauka suka futa, duk sun hallara a falourn , Inna boil les me adon orange yayi bala'in yimata kyau, shikuma yasa shadda ligh blue, Yasmeen kuma tasa atamfa, iri daya sukai da Amira dinkin riga da skirt, shikam Halifa kanan kaya yasa yasha takalmi, kamar wani saurayi se iyayi yake, "to mu tafi dan inaso nasamu daurin auren nan" daga haka suka rankaya suka tafi, driver ne yakaisu airport, suma jirgi suka bi, ita dai Inna se Alhaji Aminu ne yarige ta dan dagyar ta iya hawa jirgin, shikam Halifa a rawar kanshi yashige, Amira kam basarwa tayi tana iyayi tashige, daga haka dai har jirginsu ya tashi


bayan sun sauka driver yazo yatafi dasu, gida kam harya cika, A'isha ma kanwar Abba ta iso ita da mijinta, falour suka zauna anata gaisawa, shikam Ammar bayan yagama gaisawa ya wuce bedroom din Ahmad, dan baya san jama'a dayawa, samun Ahmad din yayi yagama shiryawa cikin shadda ashhh colour yanasa hula, beji sallamar sa ba , saboda can cikin makoshinsa yayi, sedai kawai yaganshi zaune saman kujera ta mirror, juyowa yayi yana fadin "haba ango ai seka tsora tani" be kulashi ba, yakara cewa "kace dai kun iso" "eh" abunda yafada kenan, shima bekara magana ba,

raba ido kawai Zuhura take ko zata ga Ahmad, dan a zahiri tayi kewar sa sosai, ganin bashi ba alamar sa yasa taci gaba da zaman, su Jawad kuwa dasu Muhsin tuni sun bar falourn sun wuce gurin sauran cousin dinsu, ya'yan yayyen Abba da kannensa, dan family din sunada yawa ba laifi, susu 11 ne agidansu, dan haka kowanne su nada iyali , Hajiya ce da Hajiya Zainab kadai suka rage a matan Alhaji, hira suke tayi na yaushe gamo, itakam Zuhura tayi tsamo tsamo a cikin su, aunty Aisha ce takalle ta tace "aunty Khadija ya'r taki bata magana ne" murmushi Mamy tayi tace "tanayi mana bukuji damuka shigo ta gaggaisheku ba" "naji tayi shiru ne" "ina su zakiyya suzo su tafi da ita ko tafi sakewa a cikinsu" "oh su zakiyya sunacan compound din gida suda su Aliya naga ma su Jawad da muhsin agurin" "Nadra tashi ku rakata keda Afnan" amaswa Nadra tayi tana mikewa, tashi Zuhura tayi tabi Nadra suka fuce, "aunty Aisha ce takalli Mamy tace "aunty Khadija da ina da namiji ai da nayimai mata, gatanan tabar kallah kyakkyawa" "gaskiya dai" mom din Ilham ce tafuto tana fadin "wai haryanzu yarannan basu futoba gashinan 11 saura" "ai kema dai kya fada" ku kyalesu mana angwaye ne fa kukasan mesuke tattaunawa" dariya sukai kawai mom Ilham tasamu guri tazauna,


Ilham anyi dai dai kan bed ga kawayenta zagaye da ita, sunata hira suna shewa, sai kace ba amarya ba, "yaudai Ilham zaki zama matar yaya Ammar dinan kowa ya huta" "ai jina nake kamar in zuba ruwa akasa nasha saboda dad'i" "gaskiya dai zakiji " daga haka suka cigaba da shewar su,

"Ammar queen tazo ko"? wani kallo ya wurga mai kana yamaida kansa kan wayarsa, "nidai zanje naganta kai ka zauna anan" wani irin kishi ne yataso mai wanda besan yanada shi ba se yanzu haka ya danne bece komai ba, turare Ahmad yadauka yana fesawa, wayar Ammar tayi kara, dagawa yayi yanafadin "hello abba" "yawwa Ammar ku tawo zamu wuce gurin daurin auren, kowa ya ya hallara" da to kawai ya amsa yakashe wayar, Ahmad ne yakalle shi yace "lokaci yayi ko" kadamai kai kawai yayi, lamar eh, daga haka suka mike suka fuce , yana futowa suka fara mai guda matan dake falourn, shikam ya tamke fuska kamar me, harya fuce suna mai guda, bayan sun futa, suka tarar da sauaran abokansu kokuma ma nace cousin dinsu duk sun hallara, karasowa suka fara yi suna gaggaisawa suna musabaha, masu tsokanarsa nayi, ba abokinsa ko daya, saboda be gayyaci abokansa ko daya ba, su Alhaji aminu ne suka karaso, bayan sun futo daga cikin motar, suka fara gaggaisawa, sukuma su Inna dasu Yasmeen suka shiga ciki, Zuhura na ganinsu ta tawo da gudu ta rumgume Yasmeen, se lokacin Ahmad yaganta, jiyayi kanar ya tafi inda take, sedai kuma ai maman ta tana gurin, hakan yasa kawai yacigaba da amsa gaishe gaishen mutane, bayan sun isa, Mamy ta taso tana tararsu, gurin zama tanuna mata tazauana, kana suka fara gausawa, gabatar da ita Mamy tayi amatsayin matar Alhaji Aminu, kowa kam ya yaba da kyan ta, kuma sun sakar mata fuska, Yasmeen kam janye Zuhura tayi suka koma gurinsu Aliya,
mom Ilham ce tashiga tace Ilham taje tayi wanka tasake kaya, "mom dazamu tawo fa nayi" "bansan dogon zance kije kiyi wanka kisake kaya kafun yan daurin auren su dawo" ba a san ranta ba ta tashi tayi wankan tashirya,

su Jummai suma kafun adawo daga dauro auren suka iso dan haka aka karasa girkin biki dasu, suna dawowa gida ya kaure da guda, ana angwaye sun dawo, shikam Ammar zuciyarsa kamar tafashe, haka Ilham tafuto aka dinga hotuna , duk hoton da akeyi fuskarsa a tamke, sukam Abba part din Daddy din Ahmad suka wuce gabadayansu, Yasmeen hira suke tayi, wayar ta tayi kara, Jawad ne ke kiranta, hakan yasa tamike tabar gurin saboda hayaniyar dasuke, "hello yaya Jawad" "Yasmeen dama kunzo baki neme niba" "bamu dade da zuwa ba kuka tafi daurin aure" "ok to yanzu kifuto inasan ganinki" daga haka ya kashe wayar, komawa dakin tayi tadau mayafinta, tace musu zataje ta dawo, sekin dawo kawai suka cemata, tana futowa compound din gidan ta hangoshi hakan yasa tanufe shi, harta karaso yana murmushi, seda takaraso, ya kalleta yace "wow kinyi kyau sosai fa" "na gode" hirarsu suka cigaba dayi suna dariya,

zamewa yayi daga gurin hoton dan ya gaji dama kawai dai yanayi ba a san ransaba, bedroom din Ahmad yakoma yacire babbar rigar ya hau kan bed ya kwanta,
abinci aka fara rabawa dama sundauko masu saving, dan haka suka shiga aikinsu, sunata raba abinci, mom ce tace ma da Ilham takaiwa mijinta abinci, abincin tahada mata, takarba tawuce bedroom din yaya Ahmad, tana zuwa ta tura kofar, yana kwance idonsa arufe kamar me bacci amma ba bacci yake ba, abincin ta ajiye tanufesa, hannu takai ta taba shi, bude ido yayi, yana kallonta, dasauri yamike yana hade rai, "yaya Ammar ga abinci can nakawo ma ka tashi na zubama" wani kallo ya mata kana yace "nafada miki ina bukatar abinci ne" "baka fadamun ba kawai dai naga yadace nakawoma abincin amatsayina na matarka hakinane nakula dakai" wani irin haushinta ne ya cika zuciyarsa, data kira kanta matsayin matarsa "to kwashe bana bukata" "yaya Ammar yakamata ka rage wulakancin nan daka ke yimun, saboda yanzu mu ma aurata ne, zamuyi zama wanda bashi da iyaka" "kinga jeki bana bukatarki" "dole ne ka bukace ni saboda ni matar kace yanzu" tana kaiwa nan tafuce, dafe kansa yayi yanajin wani iri azuciyarsa,

Nadra Ahmad yatura takira mai Zuhura, aikam dagudunta taje ta sanar da ita, ba jimawa tafuto tana gyara zaman mayafinta, dubashi tashigayi, bata ganshi ba, jitai anjanyota, tafada jikin mutum, tsam ya rungume ta ajikinsa, itakam tsoro ma yabata, tafara mutsu mutsu, tunawa dayayi ita farin shiga ce yasa yasake ta, yana kallonta yace "queen i miss you, nayi kewarki sosai, ina sonki, ke kam kamar ma baki damu dani ba" "yaya Ahmad nadamu mana" "to meye sa baki kara kirana ba" "namanta ne shi yasa" "ok kin manta dani ko" "no yaya Ahmad ba haka bane" "ok kinci abinci" "ah ah yanzu dai zanci" "ok idan kinci kizo zan hadaki da mom dina ku gaisa" zaro ido tayi tana fadin "yaya Ahmad kabari ba yanzu ba inajin kunya nidai" hanci ya lakace mata kana yace "to aikuwa kidena dan yau dole sekun hadu" baki tabude zata kara magana ya dakatar da ita dacewa "kije kici abinci inajiranki" daga haka yabar gurin, bayan takoma har an kawo musu abinci dayawa, hakan yasa tazauna taci kana tasha lemon, itama Yasmeen din abinci ta dawo ci tana kammalawa takara fucewa, ganin haka yasa Zuhura ma tafuce, yana zaune kan wata kujera, yana hangota yamike, yace "anya kuwa kinci abincin dayawa" dagamai kai tayi, kana yace "to muje" "amma yaya Ahmad kai kaci" "aini ganin kima ya isheni" daga haka yaja hannunta suka wuce, tabaya suka shiga, yanufi bedroom din mom dinsa, ba kowa hakan yasa yadau wayar sa ya danna kiran mom, yace da ita dan Allah ta zo bedroom dinta yanzu, amsa mai tayi kawai, batare da wani tunanin ba, "queen yanzu zatazo" bayan tazo ta tadda su zaune, cikin mamaki take kallon Zuhura kana tace "son wace wannan kuma" karaswa yayi yakamo hannun mom din ya zaunar da ita yace "mom wannan ce Zuhura wacce nabaki labari yarinyar danake so" wani kallo ta watsa mai wanda yasa shi saurin yin shiru, bude baki tayi tace "ok bamu guri zanyi magana da ita" zuciyar sa ce ta fara dukan uku uku, danyasan ba abun arziki zata fada mata ba, baki ya bude zeyi magana , ta galla mai wata uwar harara, jiki a sabule yamike ya fuce, ita kam Zuhura kanta na kasa batasan meke faruwa ba, "ke dago ki kalle ni" maganar ta daki dodon kunnenta, a hankali ta dago batare data kalle taba, "kisani ni dana baze auri yar talakawa ba, musamman ma irinki mara asali wadanda aka tsinta a titi, saboda haka ki kyale mun dana ba sa an aurenki bane, kinzo kin like mai wama yasani ko asiri kikai mai, danku baku da aiki se yiwa ya'yan masu kudi asiri ku aure su, toni dana yafi karfinki, kije can ki koma danginki kiyi aure, ki kyale mun dana, kin wani sunkuyar da kai munafukan banza, tashi kifuce mun daga daki" ita dai Zuhura harta gama hawaye kawai takeyi, jiki a sanyaye tamike tafuce, yana ganinta yayi saurin nufo ta, yana fadin "queen meya faru" hawayen datake rikewa ne ya kufce akaro na ba adadi ya zubo, kara gigicewa yayi yana fadin "queen meye meya faru" "bakomai Please ka barni kawai" daga haka tawuce tabarshi agurin, bedroom din yakoma yasami Mom din tana kokarin futowa, "haba mom me kikayi haka" "abunda yadace" "mom inasonta zaki ki iya rasani idan kika rabani da ita" "dama mana ai nasan ta riga ta asirce ka" daga haka tawuce tabarshi a tsaye, barin gurin yayi, bedroom dinsa yawuce, jin muryoyin mutane dayawa hakan yasa yajuya, yakoma yatafi dakin baki dake gidan ya kulle, zufa ce ke keto masa tako ina, yana tunanin mafutaa, zuciyar sa ce tafara rayama yaje gurin iyayensu maza ya sanar dasu, hakan yasa yatashi yabude yanufi part din Daddy inda gabadaya iyayensu maza suke, dan bayajin ze iya bacci batare daya magance matsalar nan ba, kofar yatura ya shiga, Daddy yana ganinsa yasan ba lafiya yake ba, zama yayi gabansu, kowa ido yazuba mai, yana jiran yaji me zece, Abba ne yakalle shi yace "Ahmad kana lafiya kuwa" "Abba bana lafiya mom tanaso ta rabani da farin ciki na" "kamar yaya kenan" "Daddy mom tace batasan yarinyar dana keso tace bazan aure taba, kuma Daddy indai ban aure taba zaku iya rasani" numfasawa sukai gaadaya yan falourn, "to wacce yarinya kenan kake so" "Abba Zuhura ce Daddy inasanta sosai" "Zuhura kuma" Abba ya tambaya cikin mamaki, "to ita tana sanka" "eh uncle tana sona" "wacece ita Zuhuran " "agidan Abba take" "Alhaji usman wacece ita" labari Abba yashiga basu tun farko har karshe, sun jinjina abun kana Daddy yace "ka kwantar da hankalinka ba ita zata daura ma aure ba mune nan dan haka duk yarinyar daka kawo indai kanasonta tana sonka to zamu daura muku aura" "kwarai kuwa Ahmad ka kwantar da hankalin ka nine guardian dinta, kuma nabaka ita" wani dadi ne ya ziyarci zuciyarsa nan da nan zuciyarsa tamkar an zubamai kankara, "yanzu dan dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login