Showing 51001 words to 54000 words out of 84568 words
yatashi yashige bedroom dinsa, kayan bacci yasa, yakwanta, wata kishirwa yaji, tashi yayi yanufi fridge din dake falour ya bude, se lokacin yatuna ruwan sa yakare kuma besa ashigo mai dashi ba, tashi yayi yafuta dan yaje kitchen yadauko, saboda yasaba tashi cikin dare yasha, gashi kuma yanzu ma yanajin kishin, kitchen yaje ya kunna light din wayarsa, yabude fridge din yadauka yafuto, wata tsawa akai wadda tasata fasa ihu, tana fadin "wayyo Allah Inna ta kitaimakeni" jin ihunta yasa yanufi inda yakejin ihun, tura kofar yayi, ya haska da wayarsa ya nemo switch din fitilar dakin, ya kunna, tana ganin haske cikin idanta yasa takara sa kuka "wayyo Allah Inna zasu kamani" kallonta yatsaya kawai yakeyi, jin shiru yasa ta leko tacikin blanket din, ganinsa tayi, aikam da gudu ta yaye ta diro daga gadon tanufeshi, rungume shi tayi tsam tana fadin "zasu kamani kataimake ni dan Allah tsoro nakeji" kokarin banbareta yake a jikinsa amma ta kamkameshi, ganin bazata sake shiba yasa yakamata suka fuce, ko da suka fara tafiya tana kankame dashi, har suka isa part dinsa, kan kujera yazauna, still dai tana jikinshi bata cika shiba, kallonta yayi , sekuma yayi shiru da tsawa zeyi mata se kuma ya tuna maganar Mamy, yace "Please cikani dan Allah kije wacce kujerar ki kwanta kiyi bacci" yafada yana nunamata kujera 3st kallonshi tayi yakara cewa "ba inda zani ina nan ba abunda ze kamaki" mikewa tayi tanufi kujerar ta kwanta, shikuma yana zaune nan, tun tana bude ido taga ko yanan har barawo bacci yasaceta, shima se can bacci yasace shi a zaune,
kiran sallar farko a kunnensa, bude ido yayi, jiyayi wuyanshi ya kage, dakyar yamike yanufi toilet, yayi alwala yafuto yawucd masallaci, seda yayi nafilfilinsa kana aka tada sallah, bayan yadawo, still tanata bacci ga rigar baccin tata duk ta yaye, matsawa yayi yagyramata kana ya wuce daninshi ya rufe dan yayi bacci, seda gari ya waye, ta farka, ganinta tayi dakinsa, tuna abunda yafaru tayi, kana ta tashi tabude kofa tafuce, daninsu tanufa tayi alwala tayi sallah tayi brush, futowa tayi kitchen, Jummai ce keta hada breakfast na masu zuwa makaranta, kallonta tayi tace "ai na dauka kin shirya makarantar" "ah ah yanzu dai zan shirya" "ok kiyi maza kinga 7 saura nayiwa Nadra wanka" "tom bara naje na shirya" daga haka tafuce
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 37
___________________Tana shiga tafada toilet tayi wanka kana rafuto ta shirya cikin uniform dinta, seda tagama kana tafuto, dining tanufa tazauna suka fara breakfast, bayan sungama suka fuce donsu wuce school, Bala driver ne yatayar da mota, suka shiga,
karfe 9:30 duk suna kan dinning suna breakfast, banda Ammar dayanacan yana bacci, dan be samu bacci ba jiya,mikewa Ahmad yayi yace, "Abba bara naje nashirya jirgunmu 10:00am ze tashi" "to shikenan gara kayi maza" daga haka yawuce, Abba Hajiya yakalla yace "am Hajiya inagafa acan abuja za ai daurin aure duk can zaku tafi" "shi mahaifin Ilham dinne yace haka" "eh Hajiya kuma kinga kuma bazeyiwu nace mai ah ah ba" "gaskiyane tunda munrike musu diyarsu anan ba" Mamy tafada tana kallon Abba, "kenan Mamy abuja za ai daurin aure" Jawad yatambaya "eh a acan za ai" ita dai Ilham batace komai ba, seda suka kammala Mamy taraka Abba yatafi, itakuma Ilham tanufi bedroom dinta danta shirya tafuce, tanata shirye shiryen biki, dayake gobe zatayi bridal shower, Friday kuma a daura aure,
bayan Ahmad yagama shirinsa tsaf, yafuto su Mamy ne da Hajiya a falour, "Hajiya Mamy zan wuce nashirya" "ok Ahmad Allah yatsare ka gaidamun da yaya na sakuna mom dinka" "okay Mamy zataji" "to Ahmad Allah yatsare semunzo, shi wancan yanacan yana bacci bemsan zaka tafi ba ko" "Hajiya yasani ai" "to shikenan ka gaishe su sosai semunzo" daga haka yafuto, Ilham ce tafuto itama cikin shirinta nafuta, Hajiya ce takalleta tace "ah amarya futa zakiyi" "eh Hajiya gurin kwaliya zanje nayi booking" "ok gobe ne ko, yatura miki kudinne" "eh Mamy yaturamun" "ok to sekin dawo" daga haka tafuce, bayan Ahmad yafuta yaga Jummai tadawo daga kaiwa me gadi karin kumallo, tareta yayi yanafadin "yawwa dama zan baki sako ki bawa Zuhura" yafada yana bude jakar hannunsa, farar takarda yadauko yamika mata, tadan rusuna ta karba yace "ki tabbata kin bata" "insha Allahu yallabai" daga haka yanufi motarsa, Ilham ce tace "am yaya Ahmad" juyowa yayi yana kallon ta, lokacin datake karasowa gurin "yaya Ahmad wai dan Allah baka rabu da wannan matsiyaciyar yarinyar" wata tsawa yadaka mata yace "kada ki kara ce mata matsiyaciya idan ba haka ba wlh ranki seya ɓaci" shiru tayi bata kara cewa komai ba, shikuma yashige mota, me gadi yabude mai gate yafuce, itama motarta tashige itama ta fuce,
"auntyn yara" kallonshi Inna tayi tace "na'am Alhaji" "ranar juma'a fa bikin Ammar, kuma a abuja za ai daurin auren, dan haka zamuje tare" "oh bikin har yazo kenan" "eh yazo Alhaji usman ke gayamun jiya" "to Allah yakaimu dai" "ameen daukomun kaya nasa kinga yau kinsa na makara office" murmushi tayi tanufi Waldrop din tabude tadauko mai kaya ta ajiye mai, "bara naje falour naga me yarannan suke" daga haka tafuce shikuma yashiga kimtsawa, Halifa ne yafado jikin Yasmeen yana fadin "yaya Yasmeen ki mata magana wai seta dakeni" kallon Amira Yasmeen tayi tace "haba Mira saboda me zaki dake shi" "yaya Yasmeen kayana ya hargitsa mun nagaam ninkewa" "haba Halifa meyasa ka hargitsa mata" "bansaniba yaya Yasmeen" "ok toke kiyi hakuri be saniba" "zakazo kasame nine" daga haka tawuce, Inna ce tafuto tana fadin "to me kuma akeyi" "aunty wasa sukeyi" "ai nasan haline yanzu se suyi fada" "yawwa aunty anata kiran wayarki tun dazu" mikamata tayi ta karba, "yaya Yasmeen ki kaimana cartoon" "ok miko remote din" tashi yayi yadauko yamikamata takarba, cartoon din takai, "Yasmeen kiramun Mamy naga itake kirana" amsa Yasmeen tayi tana fadin "kai aunty wai yaushe zaki koyi wayarnan" "ni wannan wayar ina zan iya, shi yasa nace yasiyamun me madannai yaki yasiyamun wannan yar shafen" dariya Yasmeen tayi tana mika mata wayar, amsa tayi tare da yin sallama "maman Zuhura ina kikai wayar ne inata kira" "ina daki nabar wayar a falour ne" "ok zancen bikin Ammar zanmiki ranar Friday ne daurin auren fa, a abuja za a daura sedai ku tawo keda abban su Yasmeen" "eh dazu yake fadamun" "gobe kuma Ilham zatai nata shine nace Amira da Yasmeen suzo nan gida sesu hadu da Zuhura su tafi" "to ba matsala sena fadawa daddyn su" daga haka sukai sallama, kallon Yasmeen Inna tayi tace "Yasmeen kinji gobe zakuje gidan maman Nadra zaku tafi biki tare dasu Zuhura" "aunty zamu hadu da zuhura" "eh tare ma zaku tafi ai" Halifa ne yakalli Inna yace "aunty hardani ko" dayake yanzu gaba dayansu aunty suke cemata jin Yasmeen nafada, kallonshi Inna tayi tace "banda kai autana banda yara, party din na yan mata ne ai" bata rai yayi yaci gaba da kallonsa, abban Yasmeen ne yafuto yana fadin "zan wuce ni" "yawwa yanzu Mamy takirani take cemun gobe yarannan zasuje party din Ilham gobe" "to ba komai suje" daga haka yanufi kofa itama ta bishi,
bayan yatashi a bacci yashiga toilet yayi wanka yafuto yashirya cikin kananan kaya, sumai kyau, izzar shi takara futowa, falour yafuto, yatarar dasu Mamy da Hajiya zaune, gaishe su yayi suka amsa Hajiya tace "ango me bacci" "Hajiya nagaji ne" "me kayi kai kuwa haka" "Ahmad yawuce fa kanacan kana bacci" Mamy tafada tana kallonsa "oh harya wuce to ai shikenan" "bara nasa Jummai takawo ma breakfast" kiranta tayi nanda nan sega ta, tafadamata tahadawa Ammar breakfast, amsawa tayi tana wucewa, kallonshi Mamy tayi tace, "Please kamun wani taimako mana" "Mamy taimako kuma" "eh kaje shop na sarkoki da dan kunnaye kasiyama Zuhura saboda naga bata da wanda zatasa a biki, ni bana da lokaci, zamuje kunshi da gyaran kai, kuma zanbiya nakarbo mana dinkinanmu dana bayar" shiru kawai yayi bece komai ba "idan bazakaje ba nasa Jawad" "no Mamy zanje mana sena tashi aiki" "shikenan ai" Jummai ce takawo mai abincin tana dorawa saman table, abincin yafara ci, be wani ci dayawa ba, yace yakoshi , mikewa yayi yana cemusu seya dawo, daga haka yafuce.
yana isa airport, yatarar da Nafeesa harta je, rungume shi tayi, shikuma ya manna mata kiss a kumatu, "beb nayi ta jiranka" "to yanzy ai nazo muje lokacin tashi yakusa" daga haka suka wuce, koda suka shiga jirgin gurin zamansu daya, tana manne ajikinsa, bayan jirginsu yatashi ne takalle shi tace "beb senaji dama mu aurata ne" "yi yayi kamar be jitaba "
tayi mamaki yau Fahad be takura mata ba, koda aka futa break tabayar zezo inda suke kamar yacce yasaba, kusan karfe 2:00pm Bala driver yazo yadaukar su, suna futowa tayima kawayenta sallama suka shiga mota, bayan sun isa gida, suna shiga falour suka tarar da Hajiya zaune a falour ita kadai, "Hajiya mun dawo" suka fada gaba dayansu, "to sannunku, kuje kucire uniform kuzo kuci abincu" amsawa sukai suna wucewa, tana shiga tawatsa ruwa kana tayi alwala , tafuto tayi sallah, doguwar riga tadauka ta atamfa tasa, kana tafuto dining ta nufa Jummai tafara zuba musu, bayan sun gama , Mamy tafuto cikin shirinta, doguwar riga tasa tayi rolling da mayafin rigar, "au kundawo ashe dama ku nake jira" "eh Mamy mundawo" "kunyi lunch ko" "eh munyi" "to kutashi mutafi dama zamu futa dake Zuhura da Nadra, kai kuma Muhsin kawuce islamiyya, seka bada excuse din baza su zoba" "Mamy ni kadai zanje kenan" *to meye ba namiji bane kai" "to Mamy ni senaje nikadai" "Zuhura tashi kidauko mayafi mutafi" "tom Mamy" daga haka tamike, ranufi dakinta, mayafi tadauka tafuto, "yawwa to muje hajiya semun dawo" daga haka suka fuce ,
koda suka sauka a airport din abuja, hotel yanema musu suka sauka, seda suka gama sheke ayar su, kana yashirya yatafi gida, yace mata da daddare ze dawo, gida yanufa, yana zuwa yatarar da mom na zaune, kan kujera tana danna waya, karasawa yayi ya zauna kusa da ita, kallon shi tayi a tsorace , tana fadin "son baka da mutunci meye haka zaka tsorata ni" "kai mom be kamata ki tsorata ba ai" "yanzu ba wannan ba kaje ka watsa ruwa kazo kaci abinci" "ok mom dad be dawo ba ko" "ai se dare kasani" tashi yayi yashiga dakinshi, yana shiga yafada saman bed, ya kwanta, komai na dakin fes yake, tashi yayi ya bude wadrope yadau kaya ya canja, saboda yayi wanka a hotel, bayan yafuto ya wuce dining, me aikinta mom takira ladidi rati serving dinshi, seda yaci abincin yagama, yadawo yazauna kusa da ita, "mom ya shirye-shiryen biki" " gashinan bama mu fara ba, sedai gobe za aimun kunshi, saboda Friday bayan daurin aure zamuyi dinner tamu ta iyaye" "Mamy dinner kuma to ai mu bamu sani ba" "au haka zamuyi bikin salam ba nishadi" "to ai Ammar shine yace baza suyi dinner ba" "rabu dashi ai bamu fadamai ba, nida Mamynsa mun hada dinner bayan daurin aure" "hakan ma yayi kinga shima ai dole zezo daurin aure" "to wai kai son yaushe zakayi auren ne" "ai mom nama samu ni, jira nake agama na Ammar" "wow my son yar gidan waye kasamo mana" yasan dama tambayar dazata fara mai kenan, "am am mom dama agidan Abba take" "gidan su Ammar to wace kenan, ni nasan Hajiya khadija bata da kanwa kuma nasan Abban shima kanwarsa dayace kuma tana london tana aure, to wace kenan" a nitse yafara bata labarin rayuwar Zuhura yadda zata fahimta, kura mai ido tayi , seda yagama ta ce "ban taba sanin baka da hankali ba se yau, kana nufin yar matsiya zaka kawo mun matsayin suruka, to ka canza tunanin dan baze taba yiwuwaba" "wlh mom dandai biki ganta bane tanada hankali da nutsuwa wlh mom idan kika ganta zaki sota" "rufemun baki na lura har yanzu kuruciya bata gama sakin kaba" "mom please ina sonta sosai" tsaki taja tana tashi tawuce, dafa kanshi yayi yasan dama dole wannan ranar zatazo.
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 38
_________________Se yamma su Mamy suka dawo , suna shigowa ana kiran sallar magariba' hakan yasa Mamy tace suje suyi wanka suyi sallah, se su futo suci abinci, itama bedroom dinta tawuce, Zuhura nashiga, tafada toilet tayi wanka tayi alwala tafuto tayi sallah, bayan ta idar tadau kaya tasa, gaban mudubi ta tsaya tana kallon kanta a mirror, ita kanta tasan Mamy ta gyara ta, ga kanta nata sheki, bakikikirin, an tufke mata shi a keyar ta, yazuba kafadunta, dan tanada gashi, ga kunshi baki da ja, jinta take cikin nishadi, bayan tashirya tafuto, kitchen tanufa, ta tarar da Jummai nata hada kayan abinci zata kai dining, "aunty Jummai sannu da aiki" "yawwa Zuhura sannu kun dawo" "eh aunty Jummai mundawo" kallonta tayi tace "kinga yadda kikai kyau kika zama yan mata" dariya Zuhura tayi tace "kai aunty Jummai bara natayaki nakai wannan" tayi maganar tana daukan, dayan daga cikin kulolin, "yawwa Zuhura anbani sako na baki fa" "wanne sako kuma" "yama yake da suna, Ahmad yace nabaki" tafada tana mikamata, "oh yaya Ahmad yatafi ko" "eh yatafi" kayan tadauka tafuce itama Jummai ta debi sauran tafuce, kayan suka jera saman dining, seda suka gama, dukkansu suka hadu dining din, Jawad Mamy takalla dake ta kallon Zuhura tace "Jawad yayanku yadawo ne" saurin kallon Mamy yayi yace "eh Mamy yadawo naga yaje sallar magariba" "okay Zuhura yimai magana yazo yayi dinner" amsawa tayi tana nufar part dinsa , tana zuwa tayi knocking, izinin shiga yabayar , ta tura kofar ta shiga, kallonta yayi, seyaga yau tamai kyau sosai, katse shi tayi da cewa "Mamy ce tace nama magana kazo kayi dinner" "am ki kawomun nan banajin zan iya futa" to kawai tace tana fucewa, bayan taje ta sanarwa da Mamy abunda yace, sawa Mamy tayi Jummai tahada mata komai kan tire, tabata karba tayi tawuce, bayan takoma tashige da sallama, mikewa yayi daga kwanciyar dayake, kan centre tables ta ajiye mai, tadau plate tafara zuba mai, hannunta yake ta kallo dayasha kunshi, jiyake kamar yakai hannu yataba, harta gama besani ba, seda tamika mai, kana yadawo hayyacinsa, karba yayi yafara ci a hankali cikin nutsuwa, seda ya kusa cinyewa ya kalle ta yace "ke bakya zamane, karki samun ciwon kai mana" yayi maganar ba tare daya kalleta ba, zama tayi tana kallon TV din datake a kunne, "zoki bani ruwa" tashi tayi tadauko ruwa a fridge tazubamai a cup glass, tamikamai, seda yasha ya ajiye cup din yace "zuba kici nasan baki ciba" "ah ah inna koma zanci" daga kafada yayi alamar ko ajikinsa, diban kayan tayi tana fucewa
koda ta futa ta tarar duk sun gama harsun shige, Jummai na tattare gurin tana kwashe kayan, kallon Zuhura tayi tace "Zuhura kinci abincin kuwa" "aunty Jummai bacci ba sedai yanzu" "to muje kitchen seki zuba ko" daga haka suka wuce, suna shiga Jummai tazuba mata, tana ci suna hira,
daddare yafuto ze futa, Mom dinshi yatarar a falour, sannu yamata, ta amsa kasa kasa, kana yace "zanje gurin wani abokina" "seka dawo" tafada ba tare data kalle shi ba, fucewa yayi, daya daga cikin motocin gidan yadauka ya fice, hotel din daya ajiye nafeesa yanufa, yana zuwa kuwa, yayi knocking, jimawa tazo tabude tare da rungume shi tana fadin "beb dama nagaji da zama ni kadai" batare dayace komai ba yajata suka shige,