Showing 45001 words to 48000 words out of 84568 words

Chapter 16 - SOYAYYA DA IZZA complete hausa novel

Mrs KD   

25 Aug 2024

21462

kitchen tashiga , Jummai ce kitchen din tana shirya abincin dare "sannu da aiki aunty" "yawwa Zuhura sannu" abincin tahada mai kana tahadamai coffee, tanufi part dinshi, tana zuwa tayi knocking, jin shiru yasata tura tashiga, yana zaune kan kujera yana waya, 'au dama yanaji yayi shiru mutuminnan yafiye izza' tafada cikin zuciyarta, karasawa tayi ta ajiye mai kan Centre tables, kallonta yake sosai, kamar bata walwala, kuma idonta ya kumbura alamar tayi kuka, katse wayar yayi yace anjima ze kira, bata kalle shiba tafara zuba mai, kura mata ido yayi yana kallonta, seda tagama zuba mai tasa mai spoon, takoma gefe ta tsaya, saboda tasan idan ta tafi zece waye ze futar da kayan inya gama, hakan yasa ta tsaya batare data kalle shiba, kasa cin abincin yayi,yaji yama futa aransa, besan meyasa, yadamu da yarinyar ba kwana biyu, so yake yamata magana amma bayasan taga kamar yadamu sa ita ne, kuma shi yanaji da izzar shi, kafa tafara dagawa alamar tagaji da tsaiwar, kallonta yayi yace, "zaki iya tafiya in kin gaji" cikin mamaki kuwa yaga takama hanya zata tafi, dasauri yace "sorry sekin dawo namanta ba wanda ze tafi da kayan inna gama" wani takaici ne ya turnuko mata, ba yadda ta iya haka ta dawo, ta tsaya, "Please zauna karki samun ciwon kai" se lokacin ta kalle shi, shima ita take kallo, zama tayi kasan carpet, 'wai Mamy wannan mutumin take cewa nafadawa matsalara' katseta yayi tare da cewa "zoki zuba mun ruwa" mikewa tayi batare da ta amsaba, tazuba mai kana ta tsaya taga ko ya gama tadauka tafuta, shan ruwan yake kamar meshan abu me zafi, ganin haka yasa tadau tire din abincin ta tsaya, ganin haka yasa yace "zaki iya tafiya" kafun yakarasa tafuce, da ido kawai ya bita, futa tayi tanufi kitchen, cin karo tayi da Ahmad, "yawwa my queen kefa nake ta nema" batai magana ba, kallonta yakarayi, ganin fuskarta ba annushuwa yasa yace "my queen meyafaru wanene" kallon tire din hannunta yayi yakara cewa "Ammar ne"? kallonshi tayi kana tawuce, dasauri yasha gabanta yana fadin "Please kifadamun meke damunki bazan iya bacci ba ganinki cikin halin nan" jin haka yasata cewa "bana jin dadi ne yanzuma kwanciya zanje nadanyi" "ok kinsha magani" daga mai kai tayi tana wucewa, gudun kada ya takura mata yasa be kara magana ba, tana kai kayan kitchen tanufi daki, kwanciya tayi saman gado tana fashewa da kuka, Amira ce tashigo, jin kukan yayar tata yasa, tayi saurin matsawa kusa da ita, tana fadin "yaya Zuhura meke damunki kike kuka " saurin goge hawayenta tayi tana kakalo murmushi, "ba kuka nake ba" kallonta Amira kawai tayi tashige toilet




💞 SOYAYYA DA IZZA 💞



Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)

Yar amanar jajirtattu💪💪

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



page 33



_________________ Ilham ce ta shirya tsaf cikin kananun kaya, wayarta ta dauka ta duba lokaci, karfe 9:30, hakan yasa tadau jakarta, seda tafara lekowa falour taga ba kowa kana tayi sauri tafuce, motarta tashiga, get aka bude mata tafuce, marhaba hotel tanufa, tana zuwa takira feenat ta tambayeta number room din, bayan tafada mata, tashiga ciki, knocking tamusu, feenat ce tazo tabude, rungume juna sukai, kana Ilham tayi kissing libs din feenat, bombom dinnta Ilham tashafa kana ta daka mata duka, sosawa feenat tayi tana fadin, "kefa muguwa ce" "ganin nayi kin kara kiba fa" "uhmm to kwalelenki" "aikam baki isaba sekin bani" kallon feenat Ilham kawai take, tanajin wani feeling na taso mata, "ke ina mufeeda"? "taje gurin boyfriend dinta" "to lallai ne" kwalaben datai shaye shayen ta tadauka tamaidasu gurinsu, kallon Ilham tayi tace "ko kina bukata ne" "baanso nikawai kizo kibani kaya ki zauna kina jamin aji" "oh karki damu indai wannan ne jira nafuto daga toilet" tafada tana nufar hanyar toilet din , dasauri Ilham takamota tana fadin "baki isaba kicemun sekin futo daga wanka zaki ban ba" tana kai wa nan ta hade bakinsu guri daya, shafata tafarayi, nan dai zuka zube saman kujera suna shafe shafen su, suna tsotse juna,

'meke damun yarinyar nan ne' tambayar kansa, besan meyasa yadamu da ita ba, soyake yacire tunaninta amma yakasa, sako ne yashigo cikin wayarsa, dauka yayi, yaduba


hy love, ykk, ina fata kana lafiya, nasan kamanta dani ko, kana tunanin na rabu dakai, kaima kasan bazan iya rabuwa dakai ba, inasonka sosai, am relly love you,
nice sabreen

tsaki Ammar yaja, saboda shi yama manta da ita, amma ita seda takara biyoshi, tashi yayi yasa kayan bacci ya kwanta, yakashe phone dinsa,

gabadaya jitai dakin yamata girma , takasa bacci kwata kwata, tanata tunanin Innar ta, gyangyadi tafara, batasan sanda bacci barawo yasace taba,

Ilham yau fa sedai ki kwana anan, daure take da tawul ajikinta, takalli, mufeeda da idonta dasukai kanana saboda tasha ta bugu tace "ke yanzu zantafi shirya wa zanyi" "kinsan karfe nawa yanzu kuwa? 11:30 fa tayi" kanta ta kifa saman kujera bata kara sanin meke faruwa ba, kallon feenat mufeeda tayi tace "kinga ni ko tasha dayawa fa" "rabu da ita ai itace tasha daayawa"


asubar fari tafarka, tashiga wanka tayi kana tafuto tayi sallah, kwanciya tayi, tana tunane tunane, seda gari yayi haske misalin karfe 8:00 ta tashi tagyara dakinsu ta tashi su Amira, tayiwa Halifa wanka, tace Amira taje tayi, kusan 9:00 tafito daga dakin, kitchen tanufa, tana shiga ta tarar da Jummai tana hada breakfast, gaisheta tayi, ta amsa cikin fara'a, tayata tashigayi, sunayi suna hira, seda suka gama lokacin 10:30 tayi, suka jera kan dining, dakin Nadra Zuhura tanufa, tasheta tamata wanka tashurya ta, suka futo falour, lokacin Muhsin shima yafuto, break fast tazuba musu gaba dayansu, seda suka gama, suka koma falour suna hira, Jawad ne yafuto, gaidashi sukai su duka, ya amsa kana yaaklli Zuhura yace "zoki zubamun breakfast" "tom" ta amsa tana mikewa, zuba mai tayi tamika mai, kallonta yayi yace "nagode" murmushi tayi wanda yasa ya tsaya yana kallonta "yaya Jawad kafara ci mana" "ok" yafara cin abincin, seda yagama yatashi yafuce school yanufa,

se 11:00 Ilham ta tashi, toilet tafada tayi wanka, kana tafuto ta shirya, ko sallar asuba batai ba, dama se taga daam takeyi, tashin su tayi, ganin sunki tashi yasa tadau jakarta tafuce, tashiga motarta ta nufi gida, tana zuwa tayi parking kana tafuto tashiga falourn, su Zuhura ne kawai ke zaune , tana zuwa tazauna , kallon Zuhura tayi tace "ke bani breakfast" mikewa Zuhura tayi ta hado mata takawo mata, ci tafarayi, bayan tagama tadau jakarta tawuce dakinta,

Ahmad ne yafuto cikin shirinsa nafuta, kan dining yanufa, tashi Zuhura tayi, ta isa gurin "ina kwana" kallonta yayi yace "lafiya lau my queen" zubamai tayi yafara ci, "my queen inasan siya miki waya" saurin kallonshi tayi tace "ah ah yaya Ahmad bayanzuba" "no zanje Abuja kwanannan kuma baza inya jure jin muryarki ba Please ki yarda na siya miki" "kayi gakuri yaya Ahmad kabari se na gama makaranta" "ok shikenan" yafada yacigaba da cin abincinsa, kasa tafiya tayi ganin kamar yaji haushi tace "yaya Ahmad kayi fushi dani ne" kallonta yayi yana kamo hannunta, ya kalleta yace "bazan taba fushi dake ba kome kika mun" murmushi tayi tana zame hannunta, tabar gurin, bayan yagama yafuce, ta kagu Mamy tafuto tace takira mata inna a waya, Ammar ne yafuto daga part dinshi, gaisheshi sukai, ciki ciki ya amsa, yana kokarin fucewa, "Ammar futa zakai kayi breakfast ne" juyawa yayi yanacewa "Mamy good morning" "yawwa kayi breakfast ne" "no Mamy banyiba" "ok muje nazuba ma" dining suka wuce, bayan su Zuhura sun gaishe da Mamy, zama yayi tazuba mai yafara ci "am my son biki fa yana matsowa kuma banga kana shirin komai ba" "Mamy nifa bana wani shirye shirye" "saboda me" "bana bukatar yin komai Mamy" numfasawa Mamy tayi tace "to shikenan bansani ba ko Ilham tana shiri tunda befi saura 4 days ba" bakara cewa komai ba, Zuhura ce takaraso gurin , Mamy ce takalleta tace "Zuhura kina son wani abu ne" "eh Mamy" tafada tana wasa da yatsun hannunta "ok inajinki fadamun" "Mamy dama Inna nakeso ki kiramun mu gaisa" murmushi Mamy tayi tace "ki bari anjima kinga yanzu safiya ce" "tom" tafada "kije gurin Bala driver kice yaje ya karbo muku wankin da gugarku yau zakuje islamiyya" "tom daga haka ta fice" bayan yagama ya fuce,

"amarya ta kifito ku gaisa da yar taki ko" murmushi Inna tayi tace "tom" gaba yayi tabishi abaya, har suka isa babban falour, Yasmeen na zauna tana kallo, zama Mamy tayi kan kujera, shima zaman yayi, kallon Inna yayi yace "Habiba ga yar ki" kana ya kalli Yasmeen yace "Yasmeen ga auntynki" cikin murmushi Yasmeen tace "aunty ina kwana" "lafita lau kintashi lafiya" "lafiya lau aunty" "daddy ga breakfast can kan dining, ni har nayi nawa" "au biki jiramu ba" murmushi tayi tace "aunty kuje kuyi breakfast" tashi sukai suka nufi dining, Inna ce tazuba musu suka faraci "ita ce ya' ta ta biyu, yayanta yana London karatu" *masha Allah Allah ya rayasu" "ameen" ya amsa dashi




💞 SOYAYYA DA IZZA 💞



Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)

Yar amanar jajirtattu💪💪

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



page 34



_________________Yau Inna tayi kwana uku 3 gidan Alhaji Aminu, bata da wata damuwa yana bata kulawa yana mata duk abinda takeso, hakama diyarsa tana girmama ta tana nuna mata so, breakfast Inna take shiryawa saman dining, bayan tagama shirya komai ta nufi daki danta kira abban Yasmeen, tana shiga taganshi ya kammala shirya wa tsaf tace "nagama shirya karin kumallo" kallonta yayi cikin kauna yace "yawwa sannunki muje tunda nagama" fucewa sukai tare, kan dining din ya zauna, ita kuma ta shiga zuba mai, bayan yafara ci, itama ta nemi guri tazauna, itama zubawa tayi tafara ci, kallon ta abban Yasmeen yayi yace "nace wai yaushe za a kawo yarannan ne"? "senayiwa Mamy magana" "ki aika driver yau ya daukosu , saboda kinga nagama musu komai na makaranta su kawai ake jira" "tom insha Allah yau zansa akawo su next week se su fara zuwa" "yawwa ko ke fa" murmushi kawai tayi, Yasmeen ce tafuto daga dakin tana fadin "la Daddy shine kuka fara breakfast bani ko" "naje dakinki naga kina bacci shiyasa" karasowa gurin tayi tare da gaidasu, amsawa sukai su duka, kana Inna tazuba mata abinci tafara ci, Alhaji Aminu ne yamike yana fadin "zantafi office naga har na kusa makara ma" mikewa inna tayi tana daukan jakar shi, futa yayi tabishi abaya, har bakin mota ta rakashi sukai sallama yatafi, dawowa ciki tayi tare da zama taci gaba da cin abincin, "aunty wai yaushe Zuhura zatazo kince itama kamar ni take ko" "eh maan kamar ke take wata kila ma shekarunku daya" "to aunty dan Allah ta dawo nan da zama mana" "ah ah baze yiwu ba kinga tana gurin Mamyn ta ita ma" "aunty dan allah tazo ko ta kwana inason nasamu yar uwa" "karki samu sedai idan anyi hutu yanzu kinga makaranta" "aunty bata gama school ba" "eh saura jekara daya ai" "to aunty tazo ko weekend ne mana" "yau kannen tane zasu zo Amira da Halifa zasu zauna tare damu anan" "Inna dagaske" "eh mana kuma kinga Amira ma da girmanta, dan ina tunanin yanzu zatai shekara 10 ko 11" "yawwa aunty shikenan yanzu nasamu wacce zamu dinga hira" hakane kam"


" sir excuse" Zuhura tafada, "ok wakike nema" "nazo gurin kanina Muhsin" magana malamin yayiwa Muhsin, mikewa Muhsin yayi yaje, "Please Muhsin calculator dinka zaka aramaun tawa taki kamawa kuma muna math" "ok bara na dauko miki" komawa yayi yadauko yamika mata" tafiya tayi shikuma yakoma ya zauna abikin shine sake kusa dashi ya kalle shi yace "Muhsin dama wannan sister din kace" "eh" "to ai itace rannan nake cema su fahad sun takura mata" saurin kallonshi yayi "eh ita ce" malamin ne ya katse su dacewa, "ya baku fara note din ba" farawa sukai, shikuma yayi gaba

"amarya ya gida ya amarci" "kai Mamy amarci kuma" "eh mana" gaisawa sukai kana Inna tace "dama alhaji ne yace yau akawo su Amira saboda ya kammala musu komai na makaranta" "ok ai ba matsala yanzu se nasa Bala driver yakawosu" "yau ina Hajiya" "Hajiya na dakinta tana hutawa, biki tambayi Zuhura ba" "ai nasan yanzu tana makaranta shi yasa" "gaskiya kam kinga ranan da kika tafi dakyar na lallashe ta" "Zuhura ai bata da dama kawai shagwaba ce irin tata" "yanzu bara nasa Jummai tamusu wanka se a kawo su" "tom shikenan se anjima" daga haka sukai sallama, Mamy ce takira Jummai tace tayiwa Halifa wanka ta shirya sa tasa Amira ma tayi wanka ta shirya, amsawa tayi tana wucewa, wankan tamusu ta shieyasu tsaf, futowa sukai, rayiwa Bala driver kwatance dan ya kaisu, yagane kwantancen nata dan haka suka tafi,

Zaune yake kan kujerar sa, tuanin yarinyar kawai yakeyi, shikansa yanzu besan meyasa yake tunanin taba, 'ka damu da ita ne shi yasa kake tunaninta' wata zuciyar kuma tace mai 'taya za ai kadamu da wata mace kai da mata ma basa gabanka' haka dai kowanne sashe na zuciyarsa da abunda yake saka mai, yau ko aikin kirki be yiba,


su Amira na shiga falourn suka tarar da Inna zaune tana kallo, aikam da gudu suka isa gurin ta, rungume su tayi tana murmushin jin dadi, "Inna kin tafi kin barmu" Halifa yafada yana kallon Inna "ba tafiya nayi nabarku ba kuma ai yaya Zuhura tana tare daku" "eh Mamy amma yaya Zuhura kullum da daddare se tayi kuka" Amira tafada kawar da zancen Mamy tayi tana fadin "me zaku ci" dai dai lokacin Yasmeen tafuto, tana ganin su ta washe baki tana karasowa inda suke tace "ashe kannena sun iso" "kin gansunan sun zo harsun fara takuramun" "ah habadai aunty ai bazasu takura miki ba" "baku gaishe taba itace Yaya Yasmeen" gaishe ta sukai ta amsa tare da fadar sunan kowannen su "kai Inna taya tasan sunan mu" Amira tafada cike da mamaki " kamar yadda yaya Zuhura tasanku to haka itama tasanku" murmushi tayi tana fadin "me kuke so yanzu" "bakomai" suka fada atare, tashi Inna tayi dan ta duba girkin data dora, sukuma suka cigaba da hira suna dariya.

Jawad ne zaune a falour shi da Hajiya, dayake yau beje school ba, Mamy ce tashigo falourn tana cewa "Jawad zokaje kadauko su Muhsin a school" "Mamy ina Bala driver"? "na aikeshi" tashi yayi yafuce motarsa yashiga yanufi school din , yana shiga yasamu guri yayi parking, yajima kafun a tashe yan secondary, su Nadra kawai aka tasa 1:30pm dan haka Nadra har ta shige mota tana zaune , karfe 2:00 dai dai aka tashesu , kallon mutanen yake dasuke futowa daga class, su uku suka futa tana tsakiyarsu, suna tafe suna hira banda ita da dariya kawai take, kallonta yake yana wasafa abubuwa dayawa, wanda shi kadai yasan meyake tunani, bata ankara ba taga fu'ad yasha gabanta, wata uwar harara tabishi da ita, saurin dago kai Jawad yayi daga jinginar da da yayi, "ke wai ke wacce irin yarinya ce ai ta binki kina share mutane" "Please dan Allah ka kyaleni katakurawa rayuwa ta" tana kaiwa nan ta bi ta gefenshi zata wuce, hanzarin shan gabanta yayi yace "ke dallah ta ishe ki ban taba dadewa ina bin yarinya haka ba seke" bata kula shi ba takara ratsawa zata shige yakara shan gaban, tayi tayi tabata hanya tashige yaki, abunne ya fusata Jawad ya balle murfin motar yafuto, fu'ad jiyay an dafa shi, batare daya juyo ba ya dauke hannun Jawad daga kafadarsa, yana kara tare ta, sake dafa shi Jawad yayi jin ankara dafashi yasa yajuyo cike da bala'i, waani wawan mari Jawad ya sauke mai, dai-dai lokacin Muhsin yakaraso gurin, dasauri yakarasa inda suke , rufe baki Zuhura tayi da tafun hannunta, "kai kasan waye ni ka daga hannu ka mare ni" "kawaye kai namare ka kuma idan kasake maimaita abunda kayi ba iya marima zanma ba hatta jikinka se yayi tsami" "zaka ga waka nara* yafada yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login