Showing 42001 words to 45000 words out of 84568 words

Chapter 15 - SOYAYYA DA IZZA complete hausa novel

Mrs KD   

25 Aug 2024

21466

yau weekend Zuhura bata tashiba se 11:00 tana tashi tashiga neman Inna, ganin batanan yasa tashi ga toilet tayi wanka tashirya, tafuto, kitchen tanufa, tana shiga taga wayam ba Inna ba Mamy, futowa falour tayi tawuce dakin Hajiya, sallama tayi kana tashiga, amsamata Hajiya tayi tana faɗin "kintashi kenan" "eh Hajiya natashi , amma banga su Inna a kitchen ba" "eh sunje gurin gyaran jiki" "oh to bara naje nahada bteakfast" "to namaji suna zancen yau za'a kawo sabuwar yar aiki" "tom shikenan bara naje nahada" daga haka ta fice, breakfast tahada, tadawo tahada a dining, su Nadra ta taso da su Amira kana ta taso Muhsin, zama sukai kan dining din, tazuba musu abincin suka ci , seda suka gama suka tashi, Muhsin fucewa yayi, sukuma su Nadra suka tafi garden wasa, tattara kayan take, Ahmad ne yafuto daga dakinshi cikin shirinsa nafuta, inda take yanufo, zama yayi kan dining din, "ina kwana"? "lafiya lau my queen, kintashi kalau"? "lafiya lau" abincin tafara zubamai tana zuba mai tamikamai gabanshi, kallonta yake, kana yace "my queen kullum fa kara kyau kike fa" murmushi tayi ta sunkuyar da kanta "my queen kishurya fa zama amarya" zaro ido waje tayi tana kallonshi , abinci shi yake ci yace "eh mana yan watanni kadan" "to school dinfa" tafada tana fada tana wasa da yatsun hannunta "ai kafun lokacin kun gama kunyi exam" shiru kawai tayi batare data sake maganaba, wayarsa ce tayi ringing, dauka yayi yakara akunnensa, "ok karkadamu doctor yanzu zanzo" yana kaiwa nan yakashe wayar, kallonta yayi yace "my queen zanje hospital yanzu abokina yakirani" " a dawo lafiya" "Allah yasa nagode" mikewa yayi yafuce, kayan dasukai breakfast tashiga haɗawa, kana tanufi kitchen, tea tahada tanufi dakin Hajiya, sallama tayi, amsawa hajiya tayi, "Hajiya ga tea Kisha" "yawwa sannu yar albarka nagode" "bara naje nayi wanke-wanke" futa tayi, kitchen tanufa, "ke" saurin juyowa tayi, Ilham taganj tsaye, "aunty Ilham ina kwana"? "lafiya muje kihadama yaya Ammar breakfast zan kaimai" "tom" abunda tafada kenan tawuce, suna shiga Ilham tahanyo chair tazauna, itakuma tashiga hadawa kamar yadda Ilham din tace, bayan tagama tashirya kan tire , tace mata tagama, "ok mikomin" "mikamata tayi kamar yadda tafada" tana karba tafuce, binta kawai Zuhura tayi da kallo, kana takoma tafara wanke wanke, dakin Ammar Ilham tanufa, knocking tayi, seda tadan jima kana yabude, kallonta yayi tun daga sama har gasa, "ina kwana yaya Ammar" kai kawai yadaga mata alamar ya amsa, "yaya Ammar breakfast nahadama" be bata amsaba yashige ciki, binshi tayi ciki, zama yayi kan kujera, Centre table tajanyo tadaoramai tire din, takoma tazauna, kallonta yayi yace "zaki iya tafiya" "ah ah zan jira ka gama" "no bana bukata ki tashi ki tafi" mikewa tayi zumbure-zumbure, ko kallonta beyi ba, tana fucewa tanufi bedroom dinta tarufe kofa, seda yagama breakfast kana yayi wanka yashirya cikin shadda ashhh colour, yayi kyau sosai, turarenshi ya fesa yafuto falour, tire din yadauka yafuce, falour yafuta Hajiya yagani zaune, "Hajiya ina kwana"? "lafiya lau, yanaganka da tire a hannu"? "breakfast nagama shine nafuto dashi" "ok to karasa dashi kitchen mana" "kitchen kuma Hajiya, ina yarinyar nan" "au ka gama amma kaiwa kitchen ya gagareka" gudun maganar Hajiya yasa kawai yanufi hanyar kitchen din , kujera ta taka tana mayar da cup din da aka sha tea, bakin kofa ya tsaya yana kallonta, kafarta ta daga sosai tana mayar da cup din can cikin drower, seda tamayar , tana mayar da kafarta kujerar ta goce, kafarta tazame tayo kasa, da sauri ya ajiye tire din hannunsa yanufe ta, fadowa tayi saman hannunsa kamar baby, rumtse idonta tayi ta kamkameshi, seda sukai kusan minti 5 ahaka, ita idonta na rufe shikuma yakura mata ido, jin kanshin turarenshi ya ziyarci hancinta, yasa tabude idonta, ganin tabude idonsa yasa yayi saurin sauketa kasa yana gyara zaman rigarsa, kana yafuce, ajiyar zuciya tasaki, kana tadau tire din daya ajiye tashiga wankewa, bayan yafuto yayi wa Hajiya sallama yafuce, motarsa yashiga, yanufi hospital, yana shiga , yashige office dinsa zama yayi yajingina da kujerar dayake zaune, yarufe idonsa, hoton fuskarsa ta yake gani ta runtse idonta, sallamar da akai ne yasa ya bude idonsa, wata nurse ce tsaye, "yallabai persion suna jiranka" "ok jeki zanzo yanzu" "ok" fucewa tayi shikuma ya ajiye phone dinsa yafuta, bayan ta kammala aikin ta tadawo falour ta tarar da Hajiya zaune tana kallo, zama tayi kusa da kafarta, tana fadin, "Hajiya sannu da hutawa" "yawwa Zuhura sannu" "Hajiya bazaki ci komai ba" "bana bukatar cin komai Zuhura kizauna ki huta" murmushi kawai tayi tamaida kanta gurin television, Ilham ce kwance saman bed dinta, rayi rigingine, tana jallon silin, tunanin zamanta take da yaya Ammar, danta lura kamar ma yatsaneta ne, wayar tace tadau ruri, seda kiran yakatse wani yakara shigowa kana ta dauka, daga dayan bangaren aka ce "hello Ilham ykk" "ina lafiya feenat" "kalau kuwa Ilham najiki haka"? "wlh feenat yaya Ammar ne" "meya miki kuma"? "abunda yaya Ammar yakemun yafara isata, kwata-kwata ya tsaneni fa" "ai laifinki ne dakika like mai, ba dole yadinga maki abunda yaga dama ba, nifa bazan iya wahalar nan akan namiji ba" "bazaki gane ba feenat ina sonsa dayawa" "to seki tayi Allah yabada sa'a, kwana biyu bakya lekowa club meyasa"? "inasan nadan rage yawo ne kada asamu matsala" "au kina nufin haka zaki tazama yana guma miki bakin ciki bazaki futo ki shakata ba" "haba kema kinsan ai bazan dena harkar nan ba kawai dai inason idan nayi aure semu dora" "to shikenan ai yau amma zaki futo ko" "eh me bi kuna ina"? "muna marhaba hotel" "ok zankiraki amma fa se dare" "ok Allah yakaimu" daga haka sukai sallama takashe wayar, Bala driver ne ya shigo tare da sallama, amsawa sukai su duka, gaishe da Hajiya yayi, itama Zuhura tagaishe shi, amsawa yayi cikin fara'a kana yace "Hajiya anyi baki" "baki kuma"? "eh Hajiya" "ok to kace su shigo" "tom" daga haka yafuce, wasu mata ne suka shigo su biyu, dayar bazata wuce shekara 45 ba dayar kuma zatai 27, da sallama suka shigo, amsawa sukai, Hajiya tace su shigo, shigowa sukai, ta nunamusu gurin zama, zama sukai, kana suka gaisa, Hajiya ce tace "sedai bangane kuba" "eh Hajiya baki sanmu ba" "yawwa nifa ince" "dama Hajiya Khadija ce tace tana bukatar yar aiki tun wancan satin to bata samu ba se yanzu" "kwarai kuwa tafadamun" "yawwa to shine gata nakawota zata fara aiki, ni yanzu zan wuce" "ok kungama ko ta sallameki" "eh tabani mungama" "to ki gaida gida" daga haka tafuce, Hajiya ce takalle ta tace, "yasunanki"? "sunana Jummai" "to sannu, Zuhura kaita daki tayi wanka ko" "to tafada tana mikewa, binta Jummai tayi abaya, daki tanuna mata, ira kuma tanufi kitchen danta dora girkin rana, dan 1:00 tayi, dorawa tayi, gefe takoma tana tunanin mezata dafa musu, Jummai ce tashigo kitchen din da sallama, amsawa Zuhura tayi tace "kai harkin futo"? "nafuto kice harkin dora" "eh amma bansan mezan dafa ba" "karki damu bara nayi" daga haka tashiga hada kayayyakin dazata bukata, kallonta Zuhura kawai take, da alama takware bangaren girki, kallonta Zuhura tayi tace "aunty Hajiya ita tafusan abincin gargajiya" "to bara nagama wannan sena mata daban" kallon yacca take sarrafa abincin Zuhura take tana kwashewa a kwanyarta, seda tagama tas mandi rice tayi kana tayi coleslaw da pepper chicken, seda tagama kana ta shiga hadama Hajiya bura busko da miyan taushe, seda suka kammala, suka kai komai dining, duk suna falour, harda Ilham Muhsin ma yadawo, Zuhura ce tace musu, an kammala abinci, tashi sukai suka nufi dining su duka, saving dinsu Zuhura tayi, itakuma Jummai tadau abincin Hajiya takai mata, kan table din gabanta ta ajiye mata, kallonta Hajiya tayi tana mata sannu da aiki, murmushi kawai tayi, tafara zubawa Hajiya abincin , ganin burabusko Hajiya takara sakin murmushi tana fadin, "kai amma yarinyar nan Allah yamiki albarka kamar kinsan inasansa" murmushi Jummai tayi tace "Zuhura ce tace mun kinfison abincin gargajiya" abincin tadauka tafara ci, itakuma Jummai tabar gurin, Zuhura kam tana gamawa ta wuce daki dantai wanka tayi sallah, dan har karfe 2 ta wuce, wayar Hajiya ce tayi kara, kallon wayar tayi taga Abba ne ke kira, dauka tayi, sallama yayi ta amsa kana yace "Hajiya barka da gida" "yawwa barka Usman" "Hajiya su Mamyn su Muhsin basu dawo ba ko"? "kajika ta dawata magana dasun dawo ai zaka sani, amma ai nasan yanzu suna hanya" "bara nakirata naji, dan mu nan har an daura ma" "masha allahu kace har an daura" "eh Hajiya an daura" "to Allah yasanya alkhairi yabasu zaman lafiya" "ammeen" daga haka ta ajiye wayar,


💞 SOYAYYA DA IZZA 💞



Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)

Yar amanar jajirtattu💪💪

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page 32


________________Su Mamy ne cikin mota, Mamy ce ke tuki, sunsha kunshi da lalle, ga kai nata kyalli, jikinsu su nata sheki , musamman na Inna wacce akafi gyarata sosai dan Mamy ta gayamusu amarya ce, wayar Mamy ce tayi kara, ganin my husband tasa ta murmushi tana dauke, tace "angwaye ya hidima" "gashin nan muna ta fama, wai baku dawo ba haryanzu"? "ka ganmu muna hanya ma yanzu munkusa gida" "todai yakamata ku hanzarta dan mu har an daura" "har an daura to masha allah, Allah dai yasanya alkhairi" "ammeen kudai hanzarta dan yace ana magariba zezo ya dauketa" au shi zezo ma yadauketa"? "eh yace baze wani turo abokai ba dakanshi zezo yadauketa" "lallai to ai shikenan kaga ba batun rakiya" "ah ai ba rakiya" "to dai kuyi maza ku dawo" "tom kaga ma munzo bakin gate" "to shikenan sena dawo ni" gate aka bude musu, shiga sukai , parking Mamy tayi, "maman Zuhura amfa daura" "murmushi Inna kawai tayi tana bude motar tafuta, itama Mamy futa tayi suka nufi ciki, suna shiga Hajiya ce kawai a falourn dan haka suna shiga, Mamy tazube saman kujera, tana fadin "washh Allah nagaji" "sannunku " "Hajiya sannu ya gida" "lafiya lau maman Zuhura sannuku" "maman Zuhura kije ki huta kiyi wanka kiyi sallah kici abinci" "tom" daga haka Inna tawuce, itama Mamy wucewa tayi dakinta, Inna nashiga taga Zuhura kwance saman gado tanata bacci, bata bi takanta ba tashige toilet dantai wanka, bayan tayi ta dau hijabi ta tada sallah, seda ta idar ta kara kallon Zuhura tana tace, "Zuhura tashi na dawo" tasan Zuhura da shegen bacci, hakan yasa tamike ta daka mata duka "kinfiye jarabar bacci" tashi tayi tana mutsuka ido, "au Inna kin dawo"? "kinata bacci ina zakisan nadawo" ta zare tana fadin, "kai Inna naga kamar bake ba" "to da wace, ina ya'ya na " "Inna biki tambayi yanake ba kike tambayar wadancan yaran" "to ai ke kin girma, jeki zubo mun abinci" "tom nimafa banci ba" "to nina hanaki ci" "Inna ankawo sabuwar me aiki kuma ta ita girki sosai" "to maza jeki kawomun" fucewa tayi, tana zuwa tahada musu abinci, kana tacewa dasu Amira Inna ta dawo, aikam dagudu Halifa yatafi, abincin takai musu, zama sukai suka fara ci a plate daya ita da Inna , kallon ta Inna tayi tace "Zuhura yau zantafj, inaso ki kula sakanki kisan meya dace kiyi, kinga yanzu kun girma , kulamun sa yaranan kafun nazo na daukesu" "to Inna amma ganina nake bazan iya zama ni kadai ba batare dake ba" kafadarta Inna tadafa tace "yazama dole ki koyi rayuwa ke kadai saboda ko yaushe zan kasance dake ba" hawaye ne zuka zubo a idon Zuhura tana fadin "wlh Inna bazan iya zama ni kadai ba" "aikam dole ne ki zauna" kuka take sosai ,lallashinta Inna keyi tana bata hakuri, dahaka dai har tai shiru, Mamy tana shiga bedroom dinta ta watsa ruwa tayi sallah, kana tafuto falour, zama kan kujera tayi kana takalli Muhsin tace "yima Zuhura magana takawomun abinci" "dazu ankawo sabuwar me aiki dakika nema" Hajiya tafada tana kallonta "oh tazo kenan tun waccan satin nacefa akawomun amma se yau" "ita ce na tayi gurki yau, wai sunanta Jummai" "to Allah yasa tanada tsafta kai cene takawomun abinci kaduba kitchen" "tom yafada yana mikewa, abincin Jummai ta kawo wa Mamy, kan table tadora mata kana ta gaishe ta, amsawa Mamy tayi cikin fara'a, tashi Jummai tayi tana wucewa, abincin Mamy tafara ci, "ba laifi ta iya girki, kuma da alama tana da tsafta" "ah dan abinci ai ta iya nima yanzu nagama cin burabusko da miyan taushe, Ahmad yashigo da sallama, amsawa sukai su duka "sannunku da hutawa" "yawwa Ahmad kadawo" Mamy tafada "eh Mamy nadawo" "to sannunka" Hajiya tafada, "akawoma abinci ko se kayi wanka" "ah bara nafara cin abincin dai" "ok bara nasa akawoma" Jummai takira, bata dade ba tazo, "ki kawo mai abinci" da to ta amsa tawuce, kallon Mamy Ahmad yayi yace "Mamy kinyi me aiki ne" "eh mana yau tazo" daga haka be kara magana ba, abincin takawo mai kana tawuce ta tafi, ci yafarayi, sannan ita kuma Mamy ta kammala, 6:00pm yafuto daga theater room, yana dawowa office dinsa yazauna danya huta, wayarsa ce tayi kara alamar shigowar message, dauka yayi yaduba, yana karan tawa kamar haka,

Assalamu alaikum ina magana ne da Ammar, inasan nafada ma wani abu game da yarinyar dazaka aura Ilham, ba yarinyar kirki bace, lala tacciya ce, nasan cewa yar uwarkace, bazaka so laifin taba, amma ina sanar dakai ba yarinyar aure bace, idan kanason sanin komai to kazo 2 star park, yanzu zan sanar dakai komai

yana gama karan tawa yashiga, bibiyar number, amma yajita akashe, tashi yayi yafuta, ko magana beyiwa nurses dinba yafuce, motarsa yashiga, yanufi 2 Star park, bayan ya isa yayi parking, yafuto, number yashiga kira yayi sa'a kuwa tashiga, seda yakira har sau uku ba'a daukaba, seda takatse, aka turo message kamar haka,

kayi hakuri ka koma gida , tanzu na shiga wani uzurin, gobe kadawo karfe 6:00pm, zan sanar dakai komai,

yana gama karantawa yaja tsaki, yayi blocking number, yashiga mota tawuce gida, anayin sallar magariba, Mamy tasa Inna tayi wanka tayi sallah, kana tashiryata, cikin lifaya me adon fulawoyi, tayi kyau sosai se zuba gamshi take, Ammar nadawowa , be tsaya neman Mamy ba yashige part dinsa, 7:40 su Abba da Alhaji Aminu suka iso, Abba ne yakalli Alhaji Aminu yace "wai kuwa kasanar da Mahmud batun auran ka" "ban sanar dashi ba , kaga baya kasar yanacan yana karatunsa ,in ya dawo se tagani," "ok amma dai autarka tasani ko" "ah Yasmeen tasani ai, tana ta doki ma za'a kawo mata aunty" "to masha Allah bara namusu magana se ta futo" "ok kayi maza dan Allah" "dokin me kake yaudai ai a gidan ka zata kwana" murmushi kawai Alhaji Aminu yayi, Abba yashige ciki, yana shiga yanufi bedroom din Mamy dan acan suke shiryawa, yana shiga tace, "abokina fa yana jira" "ai mun gama yanzu zata fita ai" "yawwa to kuyi maza ku fita" tashi sukai suka futa, gurin Hajiya takaita, yayinda Zuhura tana dakin, sallama tayi ma Hajiya, Hajiya tamata fatan zaman lafiya, kwanciya Zuhura tayi saman bed din Hajiya tana kukan zuci, dahaka su Inna suka fuce, har bakin mota Mamy da Abba suka rakata, kana tashiga mota suka tafi, suma su Mamy suka koma ciki, shashshekar kukanta Hajiya taji, "ah ah Zuhura kuka kike"? "Hajiya Inna ta tafi fa" tafada cikin kuka "kiyi hakuri ai zaki dinga zuwa gurinta, kuma gamu zaki zo ai mu dunga hira" dakyar dai tashawo kanta tayi shiru, Mamy ce tashigo dakin, "suntafi" Hajiya tafada tana kallon Mamy "eh Hajiya sun tafi, Zuhura yadai" "kin ganta nan tana rigima wai Inna ta tafi" dafa kafadarta Mamy tayi tana cewa "haba Zuhura ta ai muna tare dake, ga kannenki su Nadra da Muhsin, zasu debe miki kewa idansu Amira sun tafi, kuma duk abunda kike so kisanar damu, ko ni ko Hajiya ko yaynki su Ammar da Ahmad harda Ilham ma ke harda Abba, duk abunda kike so zamuyi miki kinji" daga kai tayi alamar to, "yawwa Zuhura ta" wayar Mamy ce tadau kara, dauka tayi tana fadin "hello my son ya akai" "Mamy nadawo tun dazu ina bukatar abinci" "to ai bakace kadawo ba se yanzu bara nasa Zuhura takawo ma" "ok Mamy" kashe wayar tayi tace "yata ki kaiwa yayanku abinci kinji" "to tace tana mikewa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login