Showing 78001 words to 81000 words out of 84568 words
tanufi kofar danta bude, Ahmad da Nafeesa tagani, kallonshi tayi, taga kanshi a kasa, hakan yasa tace "yaya Ahmad sannu da zuwa" "yawwa" yafada yana shigewa, Nafeesa takalla tace "sannu" yatsina fuska tayi ta dage bakin glass din dake idonta tace "yawwa sannunki kema" kana tashige ciki tazauna kusa da Ahmad , ita dai Zuhura kallonsu kawai take su duka, seda ta rufe kofar kana itama ta dawo ta zauna, dagowa Ahmad yayi ya kalli Zuhura yace "ina me baki hakuri queen nayi miki laifi ki yafemun" "yaya Ahmad ai baka laifi agurina" kallonta Nafeesa tayi ta tabe baki "wannan sunanta Nafeesa kuma ayanzu matata ce abokiyar zamanki" mamaki ne yacikata, amma sam taki nunamai hakan, sema tace "toh" kallon Nafeesa yayi yace "wannan itace Zuhura matar dana aura kuma nakeso" tsaki taja tace "ni na dauka zanga wata hamshakiyar budurwa wacce ta amsa sunanta mace, se naga wannan figigiyar yarinyar" "ya isheki, koma dai menene tafiye mun ke" "aikin banza kafun dai tasanka nina fara saninka" "dakata dalla" yafada yana daga mata hannu, ita dai Zuhura tayi shiru tana kallonsu, zuciyar ta kamar ta fado kasa, bakin ciki yacika zuciyar ta, se taji tama tsani yaya Ahmad din shi kansa, "bara nadauko wayata acikin daki" tafada tana mikewa, dakallo yabita tabbas yasan zataji haushinsa, tana zuwa dakinta tarufe tafada saman gado tana kuka me tsuma zuciya, kuka take sosai har yakai takasa dakatar dakanta, tabbas tanason yaya Ahmad shiyasa kishinsa yacika mata zuciya
💞SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Ina masu bibiyar books dina😃to ina muku albishir da sabon book dina😁dana fara rubutawa✍️✍️ me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan😇dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu🤣zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa😍ina alfahari daku🤩 masoyana😍 kune kwarin gwuiwa ta😀i love you so much❤💔my pans😘
ina godiya da addu'o'in ku🙏🙏🙏
dayacce kuke yabon book dina💅💅 duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu😂😂
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku😀😀
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
page 49
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________ "What Ilham din" Daddy yafada yana mikewa, Mom ce takalleshi tana fadin, "meya faru, meya samu ya'ta" "no Alhaji Usman banga laifin Ammar ba hukuncin dayayi shine dai-dai" "batazo ba amma zanjira nagani ko tana hanya" daga haka yakashe wayar, Mom ce takalleshi tanason jin me zece "wai meke damun yaran nan ne" "meya faru ne" "kinsan kuwq me Ilham ta aikata" "me kuma tayi" "lesbian" "what Ilham din" "kwarai kuwa" "wacce irin jarabawa ce Allah ya jarabemu ne" "au baki saniba, aikam yakamata ki sani" "nikuma taya za ai nasani" "uhmm ai bata yaran mutane da kikeyi, kuma baki dauki dan adam a bakin komai ba, ke indai mutum bashi da abun hannu shine wulakanta ce a gurinki" "tabbas nayi kuskure, nagane bakayiwa mutum gorin abunda bakai kabawa kanka ba, kudi baya hana faruwar komai sedai ya lalata rayuwa, kamar yadda ya lalata rayuwar yarana, dan tabbas da bamu da kudi bazasu lalace hakaba" takarashe maganar tana kuka, "ai yanzu kin gane kuskurenki" "nagane tabbas nagane" tayi maganar cike da dana sani
Ilham kam a lokacin ta kama hanyar Abuja duk da bata son zuwa, don batason da wanne ido zata kalle suba,
tana wannan halin kiran Maryam yashigo wayarta, aikam da sauri tamike tadau wayar, "hello amarya" jinta tana shashshekar kuka yasa hankalin Maryam yatashi tana fara fadin "Zuhura lafiya meke damunki" "Maryam yaya Ahmad yayi aure" "me aure fa" "tabbas yaya Ahmad yayi aure yanzu yazo da matar daya aura" "kai to amma meyasa" "nima bansaniba, Maryam zuciya ta namun zafi ji nake tamkar zata futo daga kirjina" "ki kwantar da hankalinki, kada ki sawa kanki damuwa, kinsan dai yaya Ahmad yanasonki, banajin dan yanasonta ya aure ta, sedai dan wani dalilin sa, saboda haka yanzu ne yadace ki nunamai soyayya" "Maryam nifa jinake nama tsane shi" "ah ah Zuhura kada kiyi haka bakisan dalili ba" "Maryam ki daure kizo inda nake dan Allah" "bazanzo ba gaskiya kuma kinsan umma ma bazata barni ba, shawara daya zan baki, kitashi kiyi alwala kiyi salla raka'a biyu ko kuma ki dau qur'ani ki karanta, zakiji zuciyar ki tayi sanyi" "nagode Maryam" daga haka takashe wayar, knocking taji, kamar bazata bude ba, sekuma wata zuciyar tace 'ki danne zuciyarki Zuhura' hakan yasa tamike ta nufi toilet ta wanke fuskarta, tanufi kofar tabude, shine a tsaye, ganinta yasa yayi saurin kamo hannayenta yana fadin "queen kina lafiya" kai kawai ta girgiza mai "kinajin haushina ko" "akan me, muje nabaka abinci lokacin dinner yayi" tafada tana shigewa, saboda karya fuskanci yanayin datake ciki, 'nasan kinajin haushina kawai dai bakison nunamun' yafada cikin zuciyarsa, abincin tahada mai, tajera saman dining, kana tace mai yataso, tazuba mai, kana ta nemi gu ta zauna, kallonta yayi yace "bazakici abinci bane" "nakoshi" "me kika ci" "am bazaka kirata taci abinci bane" tafada danta kashe wancan hirar tasu "idan tamatsu tafuto" yafada dai-dai lokacin da Nafeesa take saukowa sanye da kayan bacci, wadanda dasu da babu duk daya, da kallo Zuhura tabita har takaraso inda suke "au ni baza a kirani muyi dinner tare ba" "yanzu nake cewa yakira ki" a yatsine ta kalli Zuhura tana tauna cingom din dakee bakinta yabada sauti, "to naji, zaki iya bamu guri, kinsan dai yau a gurina ze kwana, kinga ni amarya ce" mikewa Zuhura tayi da sauri zata bar gurin, Ahmad yayi saurin riko hannunta, jitai kamar garwashi yazuba mata a hannun nata, ta rumtse idanunta, mikewa yayi ya isa gabanta yace "ba inda zaki, saboda inada bukatar ki kusa dani, kinsan kece madubi na" jitai kalamansa sun dena mata daɗin ji, hakan yasa tace "inajin bacci ne yau shiyasa" "kin tabbata"? "eh" kanshi ya sunkuya ya hade bakinsa da nata, yasakar mata hot kiss, kana yacikata yana fadin "kiyi bacci me dadi" aikam dasauri tabar gurin, mikewa Nafeesa tayi tana fadin "wannan wanne irin iskanci ne, a gaban, kasan ai hakan ze mun kuna" tsaki yaja yana shigewa, aikam tabisa a baya tana bambamin bala'i, dakinsa yashige, tabisa, "yazakayi banza dani inama magana" "kinga Nafeesa kibarni na huta, idan kuma ba hakaba ga hanya nam kitafi dakinki" "au hakama zakace" toilet yashige ya barta tanata bala'in ta, bayan yayi wanka yafuto yayi shirin bacci yahau bed yakwanta, da kallo tabishi, a zuciyar ta tana fadin 'oh baya bukatata kenan' hakan yasa haushi yacikata ta bude kofa tafuce, ta nufi dakinta,
sam takasa rumtsawa, zuciyarta sai zafi take mata, ta tabbata zafin kishi ne, dama haka take da kishi, ta tambayi kanta, kai indai haka kishi yake to bashi da daɗi, haka ta dinga tunane tunane har aka kira sallar asuba, haka tamike tayi wanka ta dauro alwala tazo tayi sallah, tana idarwa, tashirya cikin atamfa doguwar riga, ta sauko, tanufi kitchen danta hada breakfast,
tun jiya Ilham ta iso Abuja, amma bataje gida ba, tana tsoron hukuncin da Daddy zeyi mata, hakan yasa ta sauka a hotel,
tunda yatashi da asuba be koma ba, shirinsa yayi tsaf, dan yau zasu wuce London shida aunty Aisha, kuma jirgin 9:00am zasu bi, hakan yasa yashirya, yadau duk wani abu na amfaninsa, dawuri Jummai ta shirya breakfast saboda Mamy tafada mata, haka sukayi breakfast tare, bayan sun gama, suka fara sallama, Mamy harda kukanta, Jawad ne takaisu airport, daga nan sukai sallama, shikansa Jawad ranshi ba dad'i beso yayan nasu yatafi ba, don yanzu yagane duk abunda yake fadamai gaskiya ne, da irin idon dayake samai, ba takura bace, yanzu Jawad yayi hankali, duk ya rabu da gurɓatattun abokai, dan yanzu harya fara aiki, a banki, kuma babba ne a bankin, haka dai seda yaga tashin jirginsu kana shima yawuce,
bayan tagama ta jare a dining, dai-dai lokacin da Nafeesa take saukowa, kayan baccin jiya ne ajikinta, gaishe ta Zuhura tayi, batare data amsa ba ta nemi guri ta zauna saman dining din, tana fadin "oya zubamun breakfast" batayi musu ba ta zuba mata, kana tawuce zata haye sama, sukaci karo da Ahmad yana saukowa, gaishe shi tayi ya amsa yana sakar mata murmushi "muje ki sallami mijinki ze futa office" "ai aunty tana nan" "wace kuma aunty" hade fuska tayi kana tace "matarka" "no karki kara ce mata aunty sunanta Nafeesa" shiru tayi batare da tace komai ba "muje" yafada yana janyota jikinsa, a haka suka karasa, kallon su Nafeesa tayi tace "kai gaskiya bazan yadda da wannan cutar ba" kujera yajama Zuhura yace ta zauna, bayan ta zauna shima ya zauna, "wai Ahmad me kake nufi ne, so kake ka nunamata baka sona" "to da ina sonki ne" "gaskiya namiji makaryaci ne, idan muna tare kaita zubamun kalmomi kana sona, kana son kasancewa dani inada daɗi" "dakata haka Nafeesa, bazeyiwu kizo har gidanmu ki takura mana ba, idan kinsan zaki takuramana zan iya sallamar ki" "what lallai ma, akan wannan banzar" wani wawan mari yasakar mata wanda yasa ta dafe kuncinta, tana fadin "Ahmad ni ka mara" "namareki kuma ki kara maimata kalmarki kiga ni" barin gurin tayi tawuce sama, kallon Zuhura yayi yace "queen zubamun breakfast" mikewa tayi ta zubamai, yakalle ta yace "ke bazaki zuba ba" "banajin yunwa" ture abincin yayi yana mikewa yace "ok nima banaci muje ki rakani" seda yakai bakin kofa, yajuyo, tana inda take yace "ok natafi" daga haka yafuce, takaici ne ya isheta tamike tabar gurin ta tafi bedroom dinta
Mom na zaune falour, abun duniya duk ya isheta, nadama duk ta cikata, Ilham ce tashigo, tana rabe rabe, harta iso gaban Mom, kallonta Mom tayi, kana tace "Ilham naganki tun shigowar ki, ashe kema kina kunyar abunda kika aikata" kuka tafara tana faɗin "Mom dan Allah kiyi hakuri ki yafemun" "Ilham kifara tunanin neman yafiya gurin ubangiji, dan kin aikta babban zunubi" kuka takara fashewa dashi tana faɗin "nayi nadamar abunda na aikata Mom bantabajin kunyar abinda nake aikatawa ba se yanzu" Daddy ne yashigo, falourn, ganin Ilham yasa yaja tsaki yana nufar bedroom dinsa, da gudu ta isa gabansa tana kama kafafuwansa tana kuka tana fadin "Daddy dan allah kayi hakuri, ka yafemun nason na aikata babban laifi dan kayafemun" "Ilham kin tozarta ni kin wulakanta ni, ki rasa me zakayi se wannan abun, haba Ilham" "kayi hakuri Daddy" zama yayi kan kujera kana yace "ki nemi yafiyar ubangijinki dan Allah yana fushi dame aikata wannan laifin" "insha Allah daddy zancigaba da istigifari kuma zan gyara rayuwata" nasiha Daddy yashiga yimata wadda tasa jikinta yayi sanyi, taji ta tsani kanta, jin azabar da aka tanadawa me aikata wannan aikin, nadama tacika zuciyar ta, kuma ta kudiri niyyar sauya rayuwar ta, "Daddy dan Allah ka kara bawa yaya Ammar hakuri dasu Mamy" "ai shi Ammar nashi yawuce, dan yatafi London yau, Mamy kuwa bata rike kiba har Abba ma" kuka takara fashewa dashi, a zuciyar ta tana fadin 'shikenan na rasa yaya Ammar a dililin lesbian' takarashe maganar cikin zuciyar ta tana sakin kukan nadama, Mom ce tashiga rarrashinta ganin ya'r tata tayi nadama, dahaka takamata takaita dakinta, taci gaba da rararshinta,
LONDON
koda suka isa, london lokacin 8:12pm wanka yayi, kwanta dan bayason futa, koda mijin aunty Aisha yazo, yace sufuta su shakata, se yacema bayajin dadi ne yanzu sedai wani zubin, haka yakyaleshi, koda ya kwanta tunanin Zuhura ne yacika mai zuciya, kokari yake yacire ta aransa, amma hakan ya gagara, hakan yasa dayaji yafara tuainta, se yayi alwala ya tada nafila, yana idarwa wayarsa tadau kara, hakan yasa yadauka, yana fadin "hello doctor Johnson" "hello Ammar ina tayaka murna kasamu aiki a babban hospital din london" "ok nagode sosai gobe zanzo" "amma dawuri zaka fara aiki dan sun samu labarin kwarewarka a harkar likitanci" "ba damuwa nima nafuson hakan" "to se na ganka" daga haka yakashe wayar, mikewa yayi, yafuto daga bedroom dinsa, zuwa falour, yaran aunty Aisha ne kawai a falourn suna homework, hakan yasa yazauna, karamar suce ta nufeshi tana fadin "Uncle koyamun homework dina" tafada cikin harshen turanci, karba yayi yafara koyamata, tanayi,
"wlh Mommy nidai bazan cigaba da zama da Ahmad ba" "aike ce duk kissar nan namata biki iya ba" "to Mommy kinga yadda yake nunamata kuwa a gabana, kiri kiri nunamata yake baya sona" "shikenan kyale shi daga shi har ita" "nifa Mommy wlh na tsani yarinyar ma" "kwantar da hankalinki daga yau baze kara kula taba ma sedai inkin bashi umarnin yakulata nida nake da boka me aiki kaman yankan wuka, rabu dasu, daga yau se abunda kikace a gidan shi za'ayi koshi be isa ya tsallake maganar ki ba" "dagaske Mommy shiyasa nakesonki" "ai a yau dinan zanje gurinsa ko nawa ne nabayar, ammafa kema sekin dinga samo mana kuɗi, dan bazan kashe kudi ba, bani da tabbacin zan samu" "ki kwantar da hankalinki Mommy indai kudi ne, ai ko be bani ba zanci gaba da harka ta kuma zan cafko kudi" dariya sukasa su duka, daga haka sukai sallama, murna kamar me gurin Nafeesa,
💞SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Ina masu bibiyar books dina😃to ina muku albishir da sabon book dina😁dana fara rubutawa✍️✍️ me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan😇dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu🤣zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa😍ina alfahari daku🤩 masoyana😍 kune kwarin gwuiwa ta😀i love you so much❤💔my pans😘
ina godiya da addu'o'in ku🙏🙏🙏
dayacce kuke yabon book dina💅💅 duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu😂😂
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku😀😀
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
page 50
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________ Da daddare bayan Ahmad yadawo, ganin bega Zuhura ba yasa yawuce bedroom dinta, tana zaune saman bed tajuya baya tana ta kuka, bama tasan yashigo ba, karasawa yayi kusa da ita, ya dafa kafadunta, da sauri tajuyo, ganin shi yasa tafara goge hawayenta, "no queen ba bukatar haka nagani" "kayi hakuri nakasa danne zuciya ta ne" zama yayi yana janyota jikinsa, itakuma ta kwantar da kanta saman kirjinsa "nasani queen da ciwo, amma wlh ban auri Nafeesa dan ina sonta ba, sedan ba yadda zanyi" "to amma meyasa ka aure ta" "Please dan Allah karki tambaye ni inajin kunyar fada miki" dago da kai tayi tana kallonsa tace "indai kam baka fadamunba tabbas zanyi fushi dakai" "bazan iya jure fushinki ba kinsani" "to ka fadamun" "Nafeesa budurwa tace, mun dade muna tare tun kafun natafi USA karatu, muke tare, kuma muna ma'amala wacce bata kamata ba, amma Nafeesa dama can ba nitsetsiyar mace bace, ha salima a club muka hadu, tun daga nan muke mu'amalar tamkar mata da miji, koda nabi wasu matan karshe dai sena dawo gurinta" "yaya Ahmad dama kana neman mata ne" tafada cikin mamaki yayin da hawaye ke kwaronyowa a idanunta, "kiyi hakuri queen, ki yafemun, a da inayi, amma tunda muka hadu na dena, sanadiyar haka ne, Nafeesa taje gurin Daddy, tayi karairayinta, Daddy yace sena aure ta" hawayene ke bin kuncinta "shikenan yaya Ahmad yawuce, amma kasan bazata taba kallo na da daraja ba, tunda tariga tasan mijina fiye dani ma" "no queen kece zaki mata kallon mara daraja, tunda ke da mutuncinki ita kuwa fa" "to ai ni inajin kamar zata kwacemun kai" "bame kwace miki mijinki, ni nakine" kara kwantar dakai a kirjinsa tayi yakara matse ta a jikinsa yana fadin "kwana 7 fa yayi kincemun 7 days kike" "to ai kana tare da amaryarka" "to ai bamu taba kwana tare ba, dan haka ki shirya zuwana" "nidai gaskiya banaso" "ke a hankali zan