Showing 6001 words to 9000 words out of 84568 words
tunda sukafara maganarsu be samusu bakiba abincinshi kawai yakeci Ammar sekuje tare da Ahmad abuja inba hakaba baze dawoba mamy sena dan huta yabari se jibi mana to Ahmad kaji kabari se jibin ko tom shikenan nadra ce tace yaya ahmad nima zanbika tom shikenan zan tafi dake dagaske gyada mata kai yayi. Seda suka gama cin abincin Ahmad yacewa da Ammar yazo yarakashi gurin wani friend dinsa ba inda zani, ba inda zaka? eh ok tom yanafadin haka yafuce motarshi yadauka ya futa. Ammar kwanciya yayi kanshi na kallon siling da haka har bacci me dadi ya daukeshi
Baradai natashi na shirya islamiyya karna makara au makarantar zakije eh inna ai naji sauki to Allah ya kiyaye daki tanufa tashirya tsaf tafito inna nagama to sekin dawo bara najira maryam tazo zamatayi, yaya zuhura ki tsayamu mutafi tare toki sauri ki shirya mutafi yaya zuhura nima zanje wlh bazani dakaiba bazama kakeba sedai ka hanani karatu dan haka ba inda zakaje kazauna a gida. autah na tawonan kaji idan yaya maryam tazo zaka bita, itama taki zuwa amira futo mutafi na biyamata gidansu tom muje inna sukaiwa sallama suka nufi kofa. halifa muje namaka wanka unguwa zamuje inna ba unguwar dazamu je shikenan se za a unguwa ake wanka muje ni suka wuce bandaki
Gidan su maryam tanufa sallama tayi aka amsa mata shiga tayi dakin su. umma inayini lpy lau zuhura ya ummanki tana gida umma ina maryam bangantaba maryam sun tafi unguwa bata fada mikiba amma shine bata fadamunba ai dayake batasan harda itaba mikewa tayi tana fadin to umma semun dawo to Allah yabada sa a ammeen ta amsa hanun amira takama suka wuce makarantar
Se kusan karfe 5 yatashi yayi wanka yayi sallar la'asar seda yagama shiryawa sannan yafuta falour mamy ce kadai a falourn. mamy ina yini anyini lpy ina Ahmad din yafuta, tundazu ai, ok muhsin ne yashigo sanye da headphone akunnenshi ganin Ammar zaune yasashi saurin cire headphone din karasowa yayi yanafadin yaya Ammar yaushe kadawo, yau sannu da zuwa yawwa ina yaya Ahmad yaje unguwa daga ina kake dama yasan dole se yayimai wannan tambayar yaya dama ball naje to yayi dayawan ai gara aje ball din bara naje nayi wanka azuciyarshi kuma yace to yanzu mun banu tsauri yadawo, wucewa yayi, Ammar ne yakalli mamy yace mamy ya maganar hospital dinane eh munyi magana da abbanku harma angama, kai kawai yake jira yawwa dan wlh nafusan nafara aiki dawuri da canaiwa da abbanku yabudema Ahmad ma tunda kaga komai tare kukeyi to mamy ai zamu iya yi da wananan duka ko da dai shima yabudemai daya fi. to kaga ka girma yanzu ka gama karatu gashi har zaka fara aiki yakamata ka nemo mata kayi aure mamy bayanzuba se dan nan gaba inane gaban bakai yanzuba se gaba kazama tsoho kaki auruwa dan ba budurwar dazata auri tsoho tafada tana dariya kai mamy tsoho kuma habadai kasan me nida zakajema gurin ilham ka daidaita danaji dadi ilham kuma mamy to meyeda ilham din kyakyawa da itah mamy bance tanada aibuba kawaidai ni bayanzu zanyiba, kai tokodai sena kaika amma rukiyane dariya yayi yana mikewa mamy barana dauko wayata nakira Ahmad yayi hakan ne kawai danya kauda zancen.part dinshi yanufa wayarsa yadauka gaban mirror yakira Ahmad waikai yaushe zaka dawone yanzu zan tawo kaffa ka shirgani asibiti zamuje ok ganinan katse wayar yayi yakoma yazauna tunanin maganar mamy yake wai ilham wata yarinya da ita kozanyi auren ma se in auri yarinya
Antashi daga islamiyya hanun amira tarike suka nufi hanyar gida tafe suke sunata hira amira nabawa zuhura labarin yan ajinsu tanata dariya . tafiya yake yana gudu dan yasan halin Ammar baya jira hangota yayi tanata dariya, dariya take sosai, wow yafada yana kallonta, saitinsu yayi parking tare da zuge glass yana fadin sannufa bata bashi amsaba, amira ya kalla yace kanwata yayarki bata magana ne? tanayi tafada tana kallon zuhura dake tafiya shikuma yana binsu kadan kadan amota to ai ni takimun magana yan mata ki dan kalleni mana in fada miki wani abu gaskiya kinada kyau saurin kallonshi tayi wow Masha Allah beautiful girl kinga bara na nafito hannun amira taja tafara sauri kokarin futowa yake wayarsa tayi ringing dauka yayi, kaifa nake jira ok ganinan Ammar kabatamun shirina amma duk yacce zanyi sena nemoki akwai kaya bana wasaba ga kyau gaskiya yarinyarnan tayimun kala tace, daga haka yaja motar yatafi
💞💞Soyayya da izza💞💞
Story and Writing by hadeexatu✍️✍️
(Mrs KD)
yar amanar jajirtattu💪💪
Typing
Page 5
Shigowa tayi da sallama innace ta amsa tanacewa harkun dawo mundawo inna sannu da aiki yawwa, autah daukomun abincinna to ya amsa ke yanzu bazakije kicire uniform dinba zaki zauna cin abinci inna yunwa nakeji aike kullum dama yunwa ga kanwarkican batace yunwaba se ke nifa inna ina bawa cikina mahimmanci ah to lallai sekicigaba
Ahmad na shiga gida part din Ammar yanufa samunshi yayi yana shiryawa cikin shadda sky blue ta karbeshi sosai hula yadauka yasaka Ammar ne yace ah lallai abokina na yarda mundawo Nigeria meka gani shigarka wayarshi yadauka yana fadin muje ko ok muje futa sukai atare dakin mamy suka nufa dan su sanar da itah, suntafi samunta sukai kan sallaya tana lazimi karasawa dakin sukai suka zauna bakin gado Ahmad ne yace mamy zamuje asibiti, to to adawo lafiya, ameen suka fada suna fucewa harabar gidan suka futa Ahmad ne yace bara nai driving dinmu ko, ok to kama hutashe dani dariya Ahmad yayi suka shiga mota, hanyar asibiti suka nufa Ahmad ne yace abokina kasan yau nayi babban gamo namefa wata yarinya nagani, tsaki Ammar yayi, kai wannan yarinyar ta dabance gata kyakykyawa ga diri ga shape gata chocolate beauty kai bazaka taba ganewaba seka ganta naso na karbi number ta kada meni da kira to ai seka koma ka karba ko, aibansan a ina takeba to seka hakura, bazan hakuraba sena nemota daga ganni zatai gardi au da iskanci kake sonta kenan kai ba iya iskanciba da zata aureni ma zan aureta ammafa sena moreta tukun semunji dadin juna dan yarinyarnan ba karamin dadi zataiba wani kallo Ammar ya watsa mai yamaida kanshi kan screen din phone dinshi
Baba ne yashigo gidan a daddafe kana ganinshi kasan yana jin jiki inna ce takaraso dasauri tana rikeshi zuhura daukomun tabarma to tace daga daki tabarma taduko tafuto ganin baba a ririke yasata sakin tabarmar tanufi gunshi baba meya sameka baka da lpy sannu duk ta rikice shimfidamun tabarmar komawa tayi ta shifuda tabarmar tashiga dauko fulo kwantar dashi inna tayi tanamai sannu malam wai meke damunka ne wlh habiba nima bansaniba kawai tafarar daya ya rufeni ciwon to sannu, sannu sukaita zubamai duk hankalinsu ya tashi
AMMAR CLINIC HOSPITAL
abunda akasa kenan a saman asibitin kana ganinshi kasan yasha kudi, ciki suka shiga duddubawa suka hauyi ko ina da ko ina yayi bawata matsala bayan sungamane suka wuce gida mamy ce zaune a falo tana waya da hajiya rukayya mahaifiyar Ahmad , daga cikin wayar naji ana fadin, oh to ai hadin yayi bawata matsala nima naji dadin hadin sosai wlh saura kuma musanar da iyayensu ko eh su Ammar ne suka shigo kingansuma sun dawo anjima mayi waya kashe wayar tayi tana fadin harkun dawo eh mamy mundawo ok kunganiko yayi, yayi sosai to kuje kuyi dinner gashican a dining tom suka amsa suka wuce dining abincin suka fara ci, jawad ne yashigo su Ammar ya hango kan dining dan haka yasaita kanshi sallama yayi amsawa sukai su duka yaya Ammar kundawo ashe batare daya kalleshiba yace eh mundawo yaya Ahmad sannu da zuwa yawwa jawad sannu wucewa yayi azuciyarsa yanafadin yaya Ammar beyi maganaba naci sa'a maganar Ammar ce ta katseshi inda yake cewa amma dai ba school kajeba nan naje yaya shine kuma se 9:00pm zaka dawo ah dama dayake munje escoution wani gari kuma garin yanada nisa ok kasandai banasan yawon dare ko gyadamai kai yayi yace eh nasani good to daga yanzu duk inda kake katabbata 8:00 agida tayima tom ya amsa yana wucewa, duk abunda suke mamy najinsu tana sane taki sa baki saboda tasan halin jawad yasaba kaiwa fiye da hakama amma yanzu tunda Ammar yadawo ze dena, mikewa Ammar yayi yana fadin mamy inajin bacci sosai kuma gobe nakeson fara aiki gobe kuma eh to ai shikenan ok good night yafada yana shigewa ciki, Ammar yamatsu yafara aiki ko dan hutawa bazeba Ahmad yafada to yariga yanace dawuri zeyi tom ai shikenan jawad ne yafuto, dining yanufa mamy ina iya lami ne mezatai maka saving dina gaskiya baza a kirataba yau tayi aiki dayawa ta gaji tana bukatar hutu mamy yakamatafa kisamo yar aiki budurwa wanna tsohuwar ta tsufa fa kaga inzakai saving din kanka kayi Ahmad ne yayi dariya yace ko dai yau bakajin yunwa ne yaya Ahmad yunwa kai amma kakejira azo ai saving dinka rabudashi dai Ahmad abincin yazuba yafara ci
Kwanasukai basuyi bacci ba saboda jikin baba yarikice numfashima dakyar yakeyi safiya nayi inna tace zuhura kawai mukaishi asibiti tana kuka tace eh inna mukaishi dan Allah shiga kidauko hijabi kikai yarannan gidansu maryam tom shigatai tadaukosu suka nufi hanyar gidansu maryam tanufa kana ganinta kasan arikice take gidan tashiga tayi sallama ta gaisheda ummansu maryam zuhura lpy babane bashi da lpy zamu kaishi asibiti toh shi baban naku eh tagyada mata kai maryam ce tafuto tanafadin zuhura naji kinacewa baba bashi da lpy eh maryam asibiti zamu kaishi yanzu shine inna tace nakawo su halifa nan tom Allah yasawwake yabashi lpy ameen suka fada su duka futa tayi gida takoma tarar da inna tayi a kofar gida tare da me adaidaita zuhura shige muje to tafada tana shigewa adaidaitar
Se karfe 11 yatashi daga bacci wanka yashiga bayan yafuto yashirya shadda yasa milk colour ta amsheshi sosai bayan yagama ne, yafuta danyayi break fast su Ahmd ne da mamy da muhsin se nadra suke zaune falo sunata hira, mamy ina kwana antashi lpy, lpy lau su muhsin ne da nadra sukace yaya inakwana lpy ya amsa yanafadin ina Jawad yatafi school mamy tafada ok wayarshice tayi kara dagawa yayi daga daya bangaren naji ance hello doctor Ammar dan Allah muna da bukatarka a asibintinmu ankawo wani mara lpy ok badamuwa ganinan katse wayar yayi yanafadin mamy bara naje asibiti ankawo mara lpy breakfast fa bazakayiba sena dawo nayi ok seka dawo futa yayi motarshi ya dauka yawuce asibitin
Zuhurace durkushe tanata kuka inna na lallashinta zuhura kiyi shiru yanzu likita zezo yadubashi inna to ai haryanzu be zoba tafada tana shashshekar kuka wata nurse ce tace baiwar Allah dan Allah kiyi shiru ankira doctor yanzu ze zo tom tace tana share hawayenta. Parking yayi yawuce cikin asibitin derect office din doctor daya kirashi, dayake abokinshi ne, wucewa yayi office din doctor, bayan yashigane sukayi musabaha yake fadamai mara lafiyan yana reception bara nasa ashigar maka dashi ok wata nurse yakira yace takaisu dakin gwaji ok sir tafada tana fucewa banyi tunanin zaka zoba dan ku ai se manyan hospital habadai ai taimakone baranaje nadubashi am doctor ina tunanin cancer cefa ok to bara na duba nagani ok fucewa yayi, dakin da aka kai baba yanufa yana ganinshi ya ce cancer ce amma dole zamuyimai gwaji dan Allah likita kataimakawa babana karya mutu tafada tana zubar da hawaye tausayi tabashi yace inshallah ze warke mungode likitita inna tafada tana rungume zuhura wucewa yayi dakin gwaji auna baba akayi, annan yagano harda ciwon zuciya kuma yaci karfinshi sawa yayi akiramai su inna bayan sunzo ne yace musu maralafiyanku na fama da ciwon zuciya haryaci karfinsa, munshiga uku inna, amma meyasa buku kawoshi dawuruba, shiru inna tayi inda yacigaba dacewa ku kwantar da hankalinku zamuyimai aiki kuma ze warke gdy suketa yimasa, threater yasa ashirya masa nurse dince tashiga dan ta futo da baba tanazuwa ido bude ta ganshi karasawa tayi inda yake dubashi tashigayi nan taga yamutu Allah yakarbi ransa lulubeshi tayi office tanufa danta gayawa, doctor Ammar yarasu. Inna Allah yasa dai baba ya warke ze warke zuhura ai za aimai magani insha Allah ze warke hankalinsune yakwanta gabaya shiru sukai gaba daya kowa da abunda yake tunani, nurse dince tashiga office din tarar dashi tayi ya shirya cikin kayan aiki doctor dagowa yayi yakalleta batareda ya amsaba mara lafiyan da za aimai threater ya rasu dagowa yayi yakara kallonta akaro na biyu ajiyar zuciya yayi yace innalilahi wa inna ilaihi raju un abunda yafada kenan yace kije kisanar da iyalinsa tom tafada zama yayi kan kujera haka kawai yaji kamar shi akaiwa mutuwar , zuwatai gurinsu ta tsaya takasa magana daga baya tace kuyi hakuri mara lafiyan da kuka kawo Allah yamasa rasuwa a razane suka mike zuhura na fadin ah ah ah ba baba bane kije kiduba dakyau tun maganar na futa harta dena futa numfashintane yafara daukewa faduwa tayi agurin sumammiya inna ce take cewa zuhura dan Allah kitashi kema karki tafi kibarni mana, nurse dince tanufi office din Ammar da gudu doctor doctor ta suma wacece yarinyar kazo ka ganta binta yake kawai seda yaje yaganta kwance karasawa yayi gurinta yama rasa me ze yimata daukanta yayi kamar baby yanufi dakin marasa lpy kwantar da itah yayi dan yatsanshi yakara kasan hancinta yaji bata numfashi saitin zuciyarta yadaura hannunshi yaji yadda take bugawa da mugun gudu gabadaya yarasa meze faramata bakinta yabude yasa nashi aciki yana hura mata iska seda yakai kusan minti 15 ahaka still bata farfadoba se can kuma taja dogon ajiyar zuciya atare suka sauke ajiyar zuciyar da ita dashi
💞💞Soyayya da izza💞💞
Story and writing by hadeexatu✍️✍️
(Mrs KD)
yar amanar jajirtattu💪💪
Typing
Page 6
Bayan tadawo hayyacinta ne tarungume inna tana sabon kuka kallonta yayi da sxy eyes dinshi yace dan Allah kiyi shiru mana kukan da kike bazefa dawo dashiba, tom tafada tanasa tafun hannunta saman bakinta fucewa yayi daga dakin office yakoma gabaya kanshi ciwo yakemai saboda wannan kukan da takeyi shi bayasan hayaniya hutawa yayi can kuma ya kimtsa yabar asibitin derect gida yayi. Gawar suka tafi da itah gida sutura akaimata akai sallah malam haruna yasamu jama a Masha Allah duk wanda yabude baki ze magana to ta yabon malam harunane kaishi akai gidanshi na gaskiya, haryanzu zuhura kuka take tanajikin inna tanafadin shikenan baba yatafi baze kara dawowaba mundena hira nadena tambayarshi kudi yadena samun albarka inna yaya zamuyi rayuwa babu baba lallashinta takeyi itama kuka takeyi gabadaya yan zaman makokin seda suka tausaya musu gwago larai ce tace toya zakuyi dole kuyi hakuri ai kowa dan hakane
Bayan yakoma gida part dinshi yanufa yawatsa ruwa kwanciya yayi yarufe idanshi ita yafara tunani ko wanne hali suke yanzu yunwa yafaraji dan haka yafuto falo mamy yatarar tana waya tanafadin kenan se jibi zaka dawo daga daya bangaren yace inshallah jibi zandawo ok to Allah yakaimu tafada tana ajiye wayar son kadawo kenan eh mamy nadan jima da dawowa to sannu ya mara laifiyannaka ai mamy ya rasu subhannallahi ba asamu nasarar aikinba ai mamy bama ashiga dashiba to Allah yajikan musulmi ameen yafada yanafadin ba a gama lunch bane eh tadai kusa gamawa ok yazauna wayarshi yadauka mamy ce tace jibi abbanku ze dawo gobe inkunje abuja zaku tawo da ilham, ilham kuma mamy mezatai anan tadawo nan da zama saboda me saboda haka naga dama ok shikenan yafada yana mayar da idansa kan screen din wayarsa
Tashi kije kiyi sallah zuhura tom ta amsa tana mikewa alwala tayi ta gabatar da sallah ta dade tanayiwa baba addu a bayan tagama tashafa tafuto kusada inna tazauna , wani yarone yashigo yanafadin wai ana sallama da inna su zuhura waye inna tafada wani ne awaje kace ina zuwa tafada tana mikewa asoro ta tadda mutumin tana ganinshi ta ganeshi gaisawa sukai yamata gaisuwa ta amsa daga baya yace nazone kan maganar gida saboda nan da kwana uku za a rabamana gadonmu saboda haka sekun tashi daga gidannan saboda hardashi za a hada aciki a raba to ta amsa kawai saboda gabadaya ta rasa me zatai to na barku lafiya yafuce, dan gidan abokin malam haruna ne wanda ya basu gida lokacin da gwago larai ta koresu babansu ya jima da mutuwa amma ba a raba gado ba se yanzu za a raba, cikin gidan tadawo guri tasamu tazauna tana tunanin mafita gashi nanda kwana uku kawai aka basu
Dining yanufa dan yayi luch zama yayi daidai da shigowar Ahmad sallama abakinshi amsawa sukai shima dining din yanufa ya zauna saving dinsu tayi iya lami bayan tagama takoma kitchen abincin suka faraci Ahmad ne yace mamy gobe inmunje ba lallai nadawoba saboda anturomun da takardar aikina a abuja zanyi to yanzu kenan tafiya zakai bazaka dawoba ah mammy ai zandinga zuwa to ai shikenan shidai abincinshi kawai yake ci beyi maganaba
Sumayyace tashigo da sallama gaisuwa tayi musu ta matsa kusada zuhura, sir mansir yazomiki gaisuwa yana waje tom tafada tana matsawa kusada inna tafadamata tashi sukai sumayyace tafuta tashigo dashi soro gaisuwa yayimusu suka amsa bayan ze tafine yaciro kudi dubu goma yamikawa inna yace gashi ayi cefane karba tayi tana godiya cikin gida suka koma tunda suka shiga gwaggo larai take kallon hannun inna daki inna tanufa tashi gwaggo larai tayi tabita tana shiga ta hau washe mata baki tana fadin habiba meza a girkane naga kamar kudi a hannunki eh gwaggo malamin su zuhura ne yabani to kawo ayo cefane ta wafta tanacewa Allah sarki Allah yabiyashi inbanda shida da ogan malam haruna daya kawo musu dubu biyar bawanda yakawo ko fucika kallonta ina tayi kawai futa tai daga dakin tadawo waje tazauna, yayartace tace mata habiba ya akaine ina gwaggo larai din, saboda tasan halinta sarai, tana ciki tafada bayan tafutone tasa aka Kira mata almajiri dubu biyar tabayar a auno shinkafa asiyo mai da barkono tasa dubu biyar a