Showing 48001 words to 51000 words out of 84568 words
barin gurin, figo hannun Zuhura Jawad yayi yakaita har gurin mota yabude mota yasata ya shiga Muhsin ma yashiga , tayar da motar yayi suka bar makarantar, kallonshi Zuhura take tanaso tamai magana amma ganin yanayinsa yasa takasa, daurewa tayi tace "yaya Jawad meyesa kayi haka" daga mata hannu yayi alamar ta dakata kana yace "kinsan kina fuskantar wannan matsalar a school amma kikai shiru" shiru tayi batai magana ba, yakara cewa "Muhsin kaine babban me laifi idan ita bazata iya fada ba aikai seka fada" "wlh yaya Jawad nima bansani ba se yau" "ke kuma duk ranar daya sake miki makamancin wannan ki sanar dani wlh senamai tabo" saurin kallonshi tayi kana ta sunkuyar dakai, bayan sun isa gida yayi parking, suka futo suka shige ciki, Mamy ce da Hajiya se Ahmad daya dawo yanzu yake cin abinci, shigowa sukai, Jawad be tsaya a falour ba yawuce dakinshi, "mun dawo" Muhsin yafada , Ahmad ne yakalli Zuhura gani yayi fuskarta ba walwala Hajiya ce takalle ta tace "Zuhura yadai naganki jiki ba gwari" "bakomai Hajiya" "ko kina bukatar wani abunne Zuhura" Mamy tafada tana kallonta, a sanyaye tace "bakomai Mamy" Mamy ce takalli Muhsin tace "kai meke faruwa" "Mamy zancen gaskiya wanine yatakuea mata a school shine yau yaya Jawad ya gani ya tsawatar mai" da sauri Ahmad yadago yana kallonta, itakam mamakin Muhsin take dabe fadi marin da Jawad yayiwa fu'ad ba, "to amma in banda ke ai seki fada ai" Hajiya tafada tana kallonta, "Muhsin din ma kai ai ya kamata yafada" "Mamy nima banasaniba fa se yau" kallonra Ahmad yake tayinda itama shi take kallo, "kuje kucire uniform kuzo kuci abinci, ke kuma Nadra jeki gurin jummai tacire miki" to suka amsa su duka suna wucewa.
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 35
__________________Bayan tashiga dakin tazauna gefen gado, jakarta ta ajiye se hijabi data cire, tunani tashiga yi ko ina su Amira suka shiga,
be karasa cin abincin ba yatashi yana daukan kayan Mamy ce takalle shi tace, "bara akira Jummai tadauka" "ah ah bara namika kawai tunda natashi" daga haka yawu ce, kitchen din yashiga Jummai ce kawai, saurin karbar kayan tayi, yakalle ta yace "ina ne dakin Zuhura"? kwatantamai tayi yafuce, dakin yatura ya shiga, ganinta yayi zaune tayi shiru alamar tunani take, karasawa yayi ya duka gaban ta, hannun yakama yana fadin "my queen meke damunki haka" sagowa tayi takalle shi kana tace "bakomai" "no ban yadda ba kifadamun dan Allah kinsani cikin damuwa sam banasan naganki cikin wannan halin" murmushi ta kakalo tace "ba abunda yake damuna fa" tafada tana zame hannunta daga nashi, kura mata ido yayi yana kallonta kamar meson gano wani abu, itakam sam taki hada ido dashi, kara kama hannunta yayi akaro na biyu yace "gobe zan tafi abuja karfe 10:00am" saurin dagowa tayi ta kalleshi kana tamaida kanta kasa, haka kawai setaji ba dadi aranta, amma seta dake tace "Allah ta kiyaye hanya yakaika lafiya" "ammeen my queen, amma sedai da matsala" saurin kallonsa tayi, yadaga mata kai alamar eh, "inasan jin muryarki inna tafi kuma gashi kin hana nabaki waya" "ah ah nibanason rke waya" "to wai my queen saboda me" "lokacin da baba na take a raye yacemun duk randa nagama secondary aranar ze siyamun waya, yanzu kuma baya raye bazan rike ba se lokacin sana kammala secondary inshallah" numfasawa yayi kana yace "Allah yajikanshi yamai rahama" "ammeen" kallonta yayi yace "to yanzu yazakiyi dani" "aunty Jummai nada waya zan karbi number ka senasa awayarta zan kiraka" "kina ganin ba wata matsala" kada mai kai tayi alamar eh, hannu yasa cikin aljihunsa yaciro kudi dayawa ya sa mata kan hannunta, zaro ido tayi tana kallonshi "idan kinada wata matsala ki kira dan Allah" mikamai kudin tayi tace "ni ba abunda zanyi da kudi yanzu kuma musamman ma irin wadannan dayawa" "baby kidai ajiye agurinki idan kina bukatar wani abu" kudin tasaami a hannunsa tana mikewa tace "bana bukatarsu" "ok to shikenan, idan naje gida zanyiwa Mommy na maganar aurenmu" bata kalleshiba tace "yaya Ahmad kaje inason zanyi wanka" matsawa yayi kusada ita ya rike kafadunta ta manna mata kiss a goshi kana yace "ki kula dakanki dan Allah" daga haka yafuce, komawa tayi tazauna kan bed din wani kuka ya kwace mata, a gaskiya batasan tafiyar Ahmad ko kadan dan jitake tana tsananin sonshi, ga kuma Inna ta tafi ta barta, hawaye ne suka gangaro kan kuncinta,
bayan tayi wanka tashirya tafuto, se baza ido take taga su Amira amma taji shiru bata gansu ba, zama tayi kan dining , lokacin su Nadra da Muhsin da Jawad harsun fara cin abincin, Nadra ce tajuyo takalli Mamy tace "Mamy ina su Amira bangansuba" "su Amira maman Zuhura ta aiko an daukesu" saurin juyowa Zuhura tayi ta kalli Mamy Nadra ce tasake cewa "Mamy kenan sun tafi bazasu kara dawowa ba" "eh sedai su kawo mana ziyara" kasa cin abincin tayi tamike, Mamy takula sa yanayinta, hakan yasa tabita, samun ta tayi tana kuka, karasawa Mamy tayi ta zauna kusa da ita, kallonta tayi kana tasa hannu tafara goge mata hawaye , "Zuhura bakisan zama damu ne" girgiza mata kai tayi alamar ah ah, "to meyasa kike kuka" bakomai" to kiyi shiru kije ki wanke fuskar ki ki shirya islamiyya, to ta amsa dashi, kana tamike tashiga toilet, ita kuma Mamy tafuce, bayan sun kammala shirin islamiyya suka futa Bala driver yakaisu,
misalin karfe 5:39pm su Inna ne zaune flour sunata hira suna dariya gaba dayansu, Alhaji Aminu ne yashigo da sallama, Inna ce tamike ta nufi inda yake, tana karbar jakar hannunsa, tana mai sannu da zuwa, suma suka mai, ya amsa kana yace, mutumina kace kun karaso, daga mai kai Halifa yayi yana maida hankalinsa kan cartoon din da akeyi, Inna ce takalleshi tace, muje kayi wanka, daga haka suka shige, bayan yayi wankan suka fito, kan dining ya zauna, tazuba mai abinci, yana ci yana yaba girkin nata, sukam su Amira hankalinsu nakan cartoon din da akeyi, Yasmeen kuma tana dana wayarta, yayin da Halifa yana kwance cinyarta yana kallo,
Ilham anata gyaran jiki biki ya matso, saura kwana biyu, duk abunda take bukata seta fadawa Mamy tafadawa Ammar shikuma ya bayar, ranar Alhamis tace zatai bridal shower, tace Mamy tabarta taje Abuja tayi, amma Mamy tace ai anan za ai biki, daurin aure kawai za a kai can, dan haka ta sanar wa abokanta na Abuja suzo kaduna anan za ai, tanata shan magunguna irin nasu na yan boko, saboda kar Ammar yaji ba dai-dai ba,
yau tunda taje islamiyya bata da walwala, harta malaman sun gane, kawayen ta sun tambaye ta tace musu bata jin dadi ne, haka suka kyale ta, ko da akazo fara screning gaba daya takasa karanta komai, hakanne yasa malamin cewa abar shi se zuwa gobe, to hardai aka tashi jiki ba kwari ta tafi gida, bayan sun isa gida, tashiga daki tacire uniform din ta futo ,dakin Hajiya ta tafi, da sallama tashiga, Hajiya ta amsa, shiga tai tazauna kusa da Hajiya, kallonta Hajiya tayi tace "Zuhura kina cikin damuwa ko" kallon Hajiya tayi, Hajiya takara cewa "ki dena sawa ranki damuwa kar yazo ya shafi karatun ki, yazama dole ne ki rabu sa maman ki idan batai aure ba watarana ai ke zaki, ko kuma mutuwa ta rabaku, to ki dena sawa kanki damuwa kuma ai zakije ki ganta" "Hajiya yaushe" "se angama hidimar biki se muje ki ganta" "Hajiya bikin wa akeyi" "Ilham mana" girgiza kai tayi kana takwanta, tana wasu tunanin wanda ita kadai tasan nameye,
wayar sa ce tayi ringing, da sauri yasauka kan Nafisa yadauko wayar, "hello mommy ina yini" "lafiya lau Ahmad kana lafiya dai ko" "Mommy ina lafiya" "ok yaushe zaka tawo dan yau Daddyn ku ya tambaya" "Mamy dama gobe nake shirin tawowa" "ok to sekazo" daga haka sukai sallama, rungume shi tayi ta baya tana fadin "sweet Ahmad ina zakaje ne" juyowa yayi yace "Abuja zanje ban fadamiki ba" "baka fadamun ba" "ok ki shirya tare zamu tafi karfe 10:00am jirginmu ze tashi" "ba matsala" daga haka takara rungume shi, shima ya rungume ta a jikinsa ya hade bakinsu guri guda, tuni labari yacanja, Ahmad yayi yayi yarabu da neman mata amma yakasa, sedai kawai yanzu da Nafisa yake iskancin sa yadena bin sauran yan matan, duk da son dayakewa Zuhura yakasa raba kanshi Nafisa, kodan kaf cikin yan matansa ita take dauke mai sha'warsa, baya taba yin kwana daya batare daya ziyarci mace ba, hakan ya rigada yazame mai jiki,
karfe 6:30 yadawo gida, bayan yadawo yawuce part dinsa, yayi wanka yadauro alwala, yadawo
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 36
________________Karfe 6:30 yadawo gida, bayan yadawo yawuce part dinsa, yayi wanka yadauro alwala, yawuce masallaci, bayan yadawo ne yazauna a falour, inda su Muhsin ne kawai suke buga PS, wayarsa yadauka yahau daddanawa, Mamy ce tafuto, kallonshi tayi tace "ashe kadawo" "eh Mamy nadawo" "ok kana bukatar abinci ne" "no Mamy bara kawai idan lokacin lunch yayi senayi, "ok daga haka tawuce kitchen" Jummai ce keta aikin girki se Zuhura dake yankamata albasa, sunata hira tana bawa Zuhura labarin ya'yan ta, tanata dariya, "ah ah sannunku da aiki" "yawwa Hajiya sannu da futowa" Jummai tafada tana dan russunawa, kallon Zuhura Mamy tayi tace "Zuhura kidan hadawa Ammar coffee kikaimai naga beci komai ba me be yana bukatar cofee din" amsawa tayi da to tafara hadawa tagama tazuba a cup tafuce, afalour tasameshi, gaisheshu tayi ya amsa wanda shikadai yaji, cup din ta ajiye mai, kallonta yayi kamar yamata magana wayace takawo mai, se kuma yayi shiru dan shima yana bukata, bata aune ba taji Nadra ta riko hannunta tana fadin" yaya Zuhura zomuyi game na Ps" "Nadra ban iya bafa" "dan Allah yaya Zuhura kizo muyi" tana maganar tana jan hannunta, ganin tadage yasa tace "to shikenan muje" gaban TV din suka zauna Muhsin yamika mata kallonshi tayi tace "nifa Muhsin ban iya ba" "ai keda Nadra zakuyi nikuma senai ni kadai muga waye zai cinye, duk nasan ma nine" karba tayi suka fara, shima yafara nasa, seyaga zasu wuce sa se yayi maza ya wuce su, hakan suka dinga yi, daka karshe yaga sun wuce shi sosai, se wafce remote din ya tashi, "yaya Muhsin kabamu mana" "nabaku ku wuce ni" se zagaye suke da Nadra tanason karba se ya dageshi sama tayi ta tsalle zata karba, itakam Zuhura dariya take harda rike ciki, kallonta yake yana murmushin da besan ma yanayi ba, dariyar tata tana masa matukar kyau, Mamy ce tazo tana fadin "kai wasan meye haka" se lokacin yadena kallonta yacigaba da kallon wayarsa, "Mamy wai dan yaga zamu cinyeshi game shine ya kwace mana nida yaya Zuhura" Nadra tafada cikin shagwaba, zama Mamy tayi tana fadin "ah to Muhsin baka da gaskiya" "Mamy cinye ni fa zasuyi" "Mamy kuma shine yadinga cika baki wai seya cinyemu" Zuhura tafada tana sasauta dariyar ta, Mamy taji dadin ganin Zuhura cikin walwala, "to ai shikenan seku denayi dashi ai" shikam goganka nunawa yayi bemasan me suke yiba, "kutashi kuyi lunch" Muhsin kakira Jawad Ahmad baya nan ko Zuhura kira Ilham" to suka amsa su duka suna tafiya, kallon Ammar Mamy tayi tace "muje kayi lunch din ko" amsawa yayi yana tashi, knocking tayi , seda aka dan jima Ilham tafuta tabude, "ya akai" abunda tafada kenan tana kallon Zuhura "Mamy ce tace nakiraki" "ok jeki zanzo" wucewa Zuhura tayi kitchen tanufa, lokacin Jummai bata nan, abinci tadiba, ta zauna tafara ci, ba jimawa Jummai tashigo, kallonta tayi tace, "au anan kike ci" "eh" abunda tace kenan tacigaba da cin abincin, zama Jummai tayi itama tazuba tafara ci, "Zuhura inkin gama gana Hajiya nan dan Allah kikai mata" "to ai nama gama" tashi tayi ta wanke hannu tadauka tafuce, da sallama tashiga, ta tarar da ita saman sallaya ta idar da sallar isha, shiga tai ta ajiye kulolin, tana fadin "Hajiya ga abincinki, bara nima nayi alwala nayi sallah" daga haka tashige toilet, alwala tayi tafuto lokacin Hajiya tana zuba abincin, kan sallayar tanufa tadau hijabi tada sallar,
kallonsu Mamy tayi su duka tace, "mahaifiyarta tabarmin ita a hannuna dan Allah ku kula , kasa naji kuna hantarar ta ko kuma kuna kyararta, especially kai Ammar banason wannan tsawar datakeyi, ballantana kamata, kar naji, ku dauke ta matsayin yar uwa" girgiza kai kawai yayi yana ci gaba da cin abincinsa, Mamy ce takara cewa "yawwa kabawa Ilham kudi ranar Alhamis zatai bridal shower" dagowa yayi yakalli Ilham , "ok" yafada, Mamy ce takalle ta tace "Ilham kamar nawa za a baki" "Mamy 1.5 million yayi" kallonta kawai yayi yace "dame dame zakiyi da zan baki har 1.5 million" "haba yaya Ammar ana kashe kudi fa sosai kuma friend dina na abuja zasu zo" Mamy ce takalle shi tace "kaga kabata bakai kace bazatayi dinner ba" "ok shinenan zantura miki" yafada yana tashi, part dinshi yawuce, zama yayi saman kujera yadauko laptop dinsa yafara aiki,Jawad ne takalli Mamy yace "wai Mamy saboda me yaya Ammar baze bari ayi dinner ba" "oho mai haka yazaba, amma gashinan ai zatayi bridal shower" "to ai Mamy maza basu fiye zuwa ba" "no Jawad harda maza mana namu, kowacce ma da boyfriend dinta zata zo shine getpass dinta" "wow yayi kuma kice zamusha casu" ita dai Mamy batace komai ba, Abba ne yashigo, tashi Mamy tayi ta karbi jakar hannunsa, tanamai sannu da zuwa, suma sannu da zuwa sukai mai gaba daya, kana yashige ciki Mamy tabishi, suma bayan sun gama ci duk suka watse kowa yatafi kwanciya, Mamy ce tafuto tahadawa Abba abinci kafun yafuto wanka, Jummai ce kitchen din tana shirya kayan data wanke, "Jummai kina nan kina ta aikin ko kije huta kiyi bacci" "ai Hajiya nagama" "ok nima Abbansu ne yadawo zan hadamai abinci, ina Zuhura ne"? "tana dakin Hajiya dan tundazu datakai mata abinci bata dawo ba" bayan Mamy tagama hadawa tafuce tana fadin "kina gamawa fa kije ki kwanta"
zaune suke suna ta kallo su duka a falour, shikam halifa har yayi bacci, tunda lokacin 9:00pm, wayar Daddy Yasmeen ce tayi kara, dubawa yayi , son Mahmud shike yawo kan screen din, murmushi yayi yace , yaron nan besan mu dare bane, kana yadauka, "hello son ya akai ne" "Daddy kawai fa gaisawa zamuyi" "to shikenan mu gaisa anwuni lafiya" "lafiya lau Daddy ya kowa da kowa" "kowa na lafiya" "Daddy ina auntynmu Yasmeen tafada min munyi aunty" "kace har ta gayama, wannan yarinyar" Daddy yafada yana nunata, "to Daddy meyasa baka fadamunba" "so nai seka dawo seka ganta" "kai Daddy kabani ita mu gaisa" kallon Inna Alhaji Aminu yayi yace "ga danki yanaso ku gaisa" karba tayi tana fadin "Assalamu alaikum" "wa alayki salam aunty ina wuni" "lafiya lau ya karatu" "alhamdulilah ya mutanen gidan" "kowa yana lafiya" "Masha Allah" daga haka tamika wa Alhaji Aminu, "ok son dare yayi kabari se safiya " "to Daddy mu kwana lafiya" daga haka yakashe wayar, kallon Yasmeen yayi yace "Yasmeen kuje ku kwanta amma kifara kai Halifa dakinsu" "tom Daddy" daga haka tamike, tadau Halifa takaishi dakinsu kana tace Amira ta je ta kwanta itama tawuce dakinta, suma su Inna tashi sukai suka shige,
futowa tayi dakin Hajiya tanufi dakinsu, tana shiga tasauya kaya zuwa na bacci, kashe fitilar tayi, a tsorace ta hau kan bed din ta gudun ne ciki, iska aka fara lamar hadari, gaba daya a tsorace take dan dakin yamata girma, ruwa aka fara sosai ga kabulayen dakin sunata kadawa, kara dukun kunewa tayi tana sa kuka, har tana rawar jiki,
bayan yagama aikinsa ya rufe laptop dinsa,