Showing 54001 words to 57000 words out of 84568 words
yamayar da kofar yarufe, kallonshi take, kwata kwata baya walwala, ba kamar yadda yatafi ba, gefen fuskarsa ta shafa, tana fadin "beb yadai kamar baka yanayi me kyau" kwantar da ita yayi saman bed din ya hade bakinsu gu daya, yana kissing dinta, itama mayar mai take,
"aunty Jummai ina wayarki"? "kin gantanan saman drower" "aunty Jummai bara nayi kira kinda kati" "eh akwai ragowar kati" dauka tayi kana tadau takardar tasa number Ahmad a wayar ta danna kira,
wayarsa ce keta kara, amma yakasa kai hannu yadauka, saboda nafeesa ta kamkamaeshi tsam ajikinta, wayar ce takara shigowa a karo na biyu, seda takusan katsewa ya kai hannu yajanyo wayar yana dagawa, karawa yayi a kunnensa, shiru tayi se daga baya tayi sallama, amsawa yayi kana tace "yaya Ahmad Zuhura ce" saurin mikewa yayi yana ture nafeesa daga jikinsa, kana yadai dai ta nutsuwar sa yace "my queen kina lafiya" "lafiya na kalau yaya Ahmad ina fata kaima haka" "haba my queen ko bani da lafiya ai jin muryarki yasa na warke" "dariya tayi daga cikin wayar tace "kai yaya Ahmad" "kina mamaki ne" shiru tayi kana yakara cewa "amma ranar Friday dake za a tawo ko" "ni ai bansaniba" "inasan nahadaki da Mommy na taganki" "ah ah yaya Ahmad nidai kunya nakeji" "kunya kuma to ai ina tare dake karkiji wata kunya" "yaya Ahmad dare yayi zanje na kwanta" "kai my queen kinamun rowar muryarki ko" "bahaka bane inason na kwanta gobe da school" "to shikenan queen sena kara jinki, ku kula dakanki kinji, kyi bacci me dadi kiyi mafarki na" "to yaya Ahmad seda safe" daga haka takashe wayar, shima kashewa yayi yana murmushi, dan yanzu yaji zuciyarsa tayi fes, tabbas yanasan yarinyar, baze iya rabuwa da ita ba, dole ne mom dinsa tayi hakuri ta karbe ta aduk halin datake, Nafeesa ce takatse mai tunani tana fadin "beb wacece kuma queen" "wacce zan aura mana" "aure kuma? "to baby haka zan ta zama banyi aure ba" "nikumafa to" "nafadamiki gaskiya bazan iya aurenkiba, harkarmu dai zamu iya yi amma kicire batun aure" "wlh Ahmad baka isaba, harna fadawa Daddy na kai zan aura kazo ka anja magana no baze yiwuba" mikewa yayi yana fadin "to seki koma kifadamai kin fasa danni bazan aureki ba" "haka kace" "yes" yafada yana fucewa" da ido kawai tabishi harya fuce,
gida yanufa, yana zuwa yayi parking, kana yashga falourn, dad ne da mom dinsa suke zaune, dad nacin abinci, karasawa yayi yana zama, "Daddy sannu da dawowa" "yawwa Ahmad kadawo kenan" "eh Daddy nadawo" "to sannu yaka barosu" "kowa yana lafiya" "to masha Allah" "bara na shiga ciki" mom ce tace "basakaci abinci ba" "no mom nakoshi" daga haka yashige bedroom dinsa , girgiza kai tayi kawai tana kallon shi har ya shige, yana zuwa yafada toilet yayi wanka ya canja kaya ya kwanta, yana tunanin Zuhura, da tunaninta bacci yadauke shi,
tana gama wayar tamika ma Jummai wayar, karba Jummai tayi tana fadin "nagane dalilin dayasa yace na tabbata nabaki" murmushi kawai tayi kana tace "bara naje na kwanta naga dare yayi" daga haka tafuce, bayan taje dakin ta canja kaya tasa na bacci, gadon tahau ta kwanta, taja abun blanket ta rufa, kin kashe wutar dakin tayi, saboda tsoro batasan duhu, dahaka bacci yadauketa,
tunda ta tashi da asuba bata komaba, tadau qur'ani tana bita, san sunfara screening din sauka, be fi saura sati guda suyi sauka, bayan tagama tadau azkar tayi, seda gari yafara haske ta mike tashiga toilet tayi wanka tazo ta shirya tsaf cikin uniform, daya daga cikin turarurrukan da Mamy tasiya mata taduka ta fesa, kana tafuto rataye da jakar ta, tarar dasu tayi a dining suna breakfast, itama zama tayi, Jummai tazuba mata, bayan sun kammala, suka mike suka fuce, Bala driver yaja su suka tafi
yau dawuri yafuto, dan haka suka hadu gaba daya sukai breakfast tare, bayan sungama, ya mike, yana musu seya dawo, ba jinawa Abba Jawad suka tashi suma, Mamy taraka Abba, shikuma Jawad yashiga motarsa yatafi, itama Ilham bayan tagama, tamike takoma daki, wanka tayi ta shirya, kana tafuto, "Mamy na tafi" "ina kuma"? "Mamy kunshin mana kuma tau friend dina zasuzo na abuja zankaisu hotel din da zasu sauka" "hotel kuma a hotel kawayen naki zasu sauka su kuma" "eh Hajiya sunce sunfi son hotel din" "to shikenan sekin dawo" Mamy tafada tana kallon ta, daga haka tafuce,
bayan ya isa office, duk inda yawuce, ma aikatan suna gaishe shi tare da yimai Allah ya sanya alkhairi, mamaki ne yakamashi jin abunda suke fada, seda ya isa office yazauna kana yafara tunanin akan me suke mai, seda ya zurfafa tunani kana ya tuna gobe daurin aurensa, danshi sam yama manta dazeyi wani aure, to amma waya fadamusu, abunda yashiga tambayar kansa kenan, wata zuciyar ce tace 'to meyesa bazasu sani ba kainefa kawai bakasan auren amma kowa naso, dole za a dora shafukan sada zumunta' wayarsa ce takatse mai tunani, dauka yayi, wani doctor ne ke kiransa, dagawa yayi, tare da dayin sallama, amsawa yayi wancan yana fadin "doctor Ammar kana asibitin ka ne"? "eh ina nan" "so dan Allah zamu kawo wani mara lafiya, abun ya gagare mu ne" "ok ba damuwa" "daga haka yakashe wayar" Ammar nada kwarewa a harkar likitanci, ko wanne irin yanayi mara lafiya ke ciki yana kokarin sama masa lafiya taeda da goyon bayan Allah (S.W.A) shi yasa duk manyan likitoci sun sanshi kuma suna yabawa kwarewarsa,
se 12:00pm Ahmad yafuto daga daki, Mom ce takalle shi yayin da ake zana mata kunshi tace "wato son se yanzu ko" karasowa yayi yazauna yana fadin "nagajini sosai, mom me ake miki" kallonshi tayi tace "kunshi mana" "kamtayayi a hannun Zuhura ake kunshinan" "wata uwar harara ta galla mai tace "karna kara jin kafadi sunan yarinyar nan anan gidan" "ni wai mom narasa me ta miki haka" "yar matsiyata ce " takaici ne ya ishe shi yabar gurin jin ana ciwa masoyiyar sa mutunci, kan dining yanufa, be jira kowa yazi yayi serving dinshi ba yayi dakansa yafara ci
cikin kuka take fadin "Mommy wlh dagaske yafadamun wai aure zeyi" "kwantar da hankalinki my daughter be isaba seya aureki, ki gama bashi jikinki yace ze auri wata bayan ke" "Mommy yaushe zaki dawo to" "ki kwantar da hankalinki kwanannan zandawo daga dubai din akwai wanda nake jira ya sallame ni" "to Mommy dan allah kidawo da wuri" "zandawo fa, amma kinsan me, karki nuna mai kin damu, kidinga janshi ajiki kuci gaba da harkarku har na dawo musan mafita" "to Mommy hakan zanyi" daga haka sukai sallama takashe wayar, duk cikin turanci suke maganar, kasancewar maman ta tana jin turanci sosai, dan ba kasar da bata zauna ba, haka kuma mahaifin Nafeesa daya rasu dan Lagos ne acan suka hadu ta aureshi, har zaman saudiyya tayi, dan acan ma Nafeesa ta girma,
karfe 2:30pm Bala driver yazo yadauke su, suka wuce, bayan sun isa gida, su Mamy na zaune falour, ita da Hajiya, shigowa sukai da sallama, Nadra tafada jikin Mamy, tana fadin " Mamy mundawo" "to autata sannunku da dawowa" Zuhura da Muhsin ma abunda suka ce kenan , suma Mamy tamusu sannu, kana suka wuce ciki, bayan taje tayi wanka, tadau kaya tasa, tayi sallar azahar, kana tanufi kitchen, Jummai ce keta aikin girki, "aunty Jummai mundawo" "sannunku Zuhura" "aunty bara natayaki" "kai Zuhura keda kika dawo yanzu" "ah ah aunty bara natayki" daga haka suka shiga aikin, bayan sun kammala suka jera a dining, seda suka kammala lunch, kana suka tattare gurin suna kwashe kayan suka kai kichen.
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 39
_________________Jummai ce ke wanke-wanken itakuma Zuhura tana mayar dasu mazauninsu, Nadra ce tashigo kitchen din tana fadin "yaya Zuhura kizo inji Mamy" "to kicd ina zuwa" daga haka Nadra tafuce, "aunty Jummai bara naje Mamy tana kirana" fura tayi tanufi falour, bayan taje ta duka gaban Mamy tace "Mamy gani" "dama maamn kice takira waya tace nabaki" tafada tana mikamata wayar, amsa tayi, Mamy tace kije da wayar idan takira kika gama seki kawo mun, amsawa tayi da to tana shigewa, dakinsu tanufa, kafun takarasa kiran Inna yashigo wayar, dasauri ta dauka, tana fadin "hello Inna" "na'am Zuhura kina jina" "eh Inna ina wuni" "lafiya lau ya mutan gidan" "kowa lafiya Inna , yaushe Inna zakizo dan allah" "kinga ba wannan nake magana ba, inason fadamiki yau su Yasmeen da Amira zasu zo, dan Allah ki kula da ita, tana taso ku hadu" "toke Inna yaushe zakizo namatsu naganki" "zanzo se ranar juma'a, kina da matsala ne" "bani da matsala Inna kawai dai inaso naganki ne" daga cikin wayar taji ana fadin "aunty Zuhura ce" "eh Yasmeen itace" "bani ita mugaisa" daga haka Yasmeen takarbi waya tana fadin "hello sister ya kike" "lafiya lau kefa" "ina lafiya sister yaushe zakizo" "se randa Inna tafada, ina Amira" "kinganta nan , Amira ga sister Zuhura" karba Amira tayi tace "yaya Zuhura ya gida" "lafiya lau yan mata, ko nemana bakya yi" "kai yaya Zuhura nida bani da waya" "nima ai bani da ita amma ke ai gata Inna" "to dai zamuzo yau se muga juna" dariya sukai Inna takarbi wayar "to sesunzo jeki mayar mata wayarta" daga haka takashe wayar, falour takoma , "Mamy ga wayar" "yawwa kingama, bara nazo nakira muku me kwalliya kafun Yasmeen takaraso" karbar wayar tayi, ita kuma tajuya tanufi daki
kirane yashigo wayar sa, yayin da yake kwance saman bed, kanshi nakallon silin, wani kiran ne yashigo, seda yaktse na uku yashigo, kana yadau wayar, Nafeesa ce, batare da yayi magana ba yakara a kunnensa, cikin wata muryar ta yaudara tace "beb najika shiru kuma kasan dai bazan iya zama banji dumin jiika ba ko" yadda tayi maganar ne yasa gaba daya jikinsa ya saki, yace "to yanzu me kike so" "kazo yanzu" tafada cikin shagwaba, "ok bara nayi wanka" "no idan kazo sai muyi" "sai nayi wanka" "ok sekazo" daga haka yakashe wayar, yamike ya shiga toilet, bayan yayi wanka yashirya cikin manyan kaya, yafeshe jiki da turare, yafuto, bakowa falour hakan yasa kawai yafuce, batare daya shiga dakin mom ba,
"aunty munshirya" Yasmeen tafada tana zura kai kitchen din, "oh har kun shirya, amma dai kunyi sallah ko" "eh aunty munyi la'sar" Halifa ne yashigo yana faɗin "aunty dan Allah zan bisu" "ah ah Halifa yara basa zuwa se yan mata shiyasa, amma kaima zamuje se gobe kaji" Yasmeen ce takalli Amira tace "lah Amira namanta wayata kan mirror daukomun" amsawa tayi tana tafiya "bara nayiwa driver magana yakaiku" daga haka Inna tafuce zuwa compound din gidan, "Ado dan Allah zaka kai yarannan unguwa kaji" "to Hajiya su futo" komawa tayi tace musu "kuje yana jiranku" "Amira muje" daga haka suka fuce, ita kuma Inna takoma ciki,
"Zuhura kiyi wanka kizo me kwalliyar ta karaso" "tom Mamy" tafada tana shigewa, tana shiga ta fada toilet tayi wanka, bayan tafuto bata sha komai ba, tazura hijabin ta har ƙasa, tafuto, falourn tafuto tana fadin "Mamy nayi" "ok jeki cikin Waldrop dina zakiga ledar da muka karbo dinki jiya, zakiga wani material purple sa baki kidauka kisa" "tom Mamy" daga haka tashige part din Mamy, Ammar ne yashigo falourn da sallama, amsawa sukai, kallon Mamy yayi yace "Mamy nadawo" "sannu da zuwa to, yau naga kadawo dawuri" "Mamy nagajine shiyasa kawai nadawo" "ok zansa akawo ma abinci" "daga haka ya shige part dinsa" Jummai Mamy takira tasa takaiwa Ammar abinci,
su Yasmeen ne suka shigo, da sallama, amsawa Mamy tayi, suka karaso falourn, durkusawa sukai suka gaida Mamy ta amsa, kana suka koma kan kujera,
kallon kanta ta tsaya tanayi a mudubi, yadda kayan yazauna mata das ajikinta, street gown ce, tabi jikinta shape dinta ya futo, kayan ya dace da fatar ta, seda tagama kallon kanta, kana tafuto, Yasmeen ce tabita da kallo, aranta tana jinjina kyawun Zuhura, dan ko ba a fada mata ba tasan ita ce Zuhuran Mamy ce ta ce "wow yan matana ta futo, ga su Yasmeen nan sunzo tun dazu" zama tayi kusa da Yasmeen tana faɗin "sannu sister ashe kun karaso" "eh wlh sister tun dazu ma fa" "to sannunku, Amira ya kuke" "lafiya lau yaya Zuhura kinyi kyau sosai" "kai Amira " "dagaske fa sister kinyi kyau" "Zuhura tafara muku make up dinnan 5:00pm har tayi fa" "tom Mamy" tashi tayi takoma kan 1sit kujera tazauna me make up din tafara mata"
Make up ake tayiwa Ilham ana tsatso ta, ta dawo kamar aljanna, saboda kwalliyar da akai mata, ba laifi tayi ktau sosai, gown tasa light blue, me net, kawayenta kuma sukasa, material copee suma sunyi kyau, su Ilham se rawar kai take, sukuma kawayenta su Feena sunata zuga ta,
bayan an kammalawa Zuhura make up, tamike , Yasmeen taje aka fara mata, light make up akaiwa Zuhura ba hayaniya, ta kyau sosai, ga daurin data mata ya zauna, Yasmeen tashigayi yiwa, nan danan tagama mata, itama tayi kyau, dayake ita fara ce tas,
Mamy ce takalli Zuhura ta ce "yan mata na biki sa dankunne ba fa" se lokacin takai hannu kunnenta taji, "jeki part din Ammar shinace yasiyo, bansaniba ko yasiyo, kice injini ya baki sarka da dankunnen" amsawa tayi tana fucewa, Amira aka fara ma make up din, itama tayi kyau dan itama tafara zama yan mata, dan har tafara kirgen danki, dayake tafi Zuhura jiki, ita tanada kiba, knocking ta tsaya tanayi, amma taji shiru, hakan yasa ta tura kofar tashiga, bakowa falourn, bakin kofar bedroom din tayi Knocking, yana toilet yana alwalar magariba zeje masallaci, se ya fito ya tsaya gaban mirror yana gyara hannun rigarsa, knocking dinta yaji, yayi zaton Muhsin ne danyace zezi ya tambayeshi dan Allah yadau mota yau dayake duk key din motocin gidan suna gurinsa, banda na Abba da Mamy da Jawad se na Bala driver da shi dama ba a karba saboda kai yara school, izinin shigowa ya bayar, tura kofar tayi tana shiga, kamshinsa dana dakinne ya doki hancinta, tsayawa tayi bakin kofar taki karasowa, "ina yini" tafada a sanyaye , saurin juyowa yayi, idonshi ne kafe kanta, kamar ita kamar ba ita ba yake tunanin, katse mai tunani tayi tace "Mamy ce ta ce wai kabani sarkokin da dankunnen" "ok" drower ya janyo yadauko wasu yan box guda uku, yatako har inda take yamika mata, hannu takai takarba, ta juya zata fuce, jin muryarsa tayi daga sama yace, "kina nufin da make up dinan zaki futa" bata da amsar dazata bashi hakan yasa tayi shiru "ba magana nake miki ba" kada mai kai tayi alamar eh "ok to shiga toilet ki wanke ta yanzu ina jiranki" marairai ce fuska tayi tace "dan Allah kayi hakuri wlh duk anyiwa su Yasmeen, kuma Mamy bazata ji dadi ba idan na wanke" be kulataba ya ratsa ta kusa da ita ya wuce, itama sauri tayi tabi bayansa, tafuce, massalaci yawuce, itakuma ta kaiwa Mamy box din daya bata, "ok zo in samiki" zuwa tai ta zauna kusa da Mamy , karamin box din tabude, dankune ne da sarka siririya, tayi kyau sosai, Mamy ta makala mata, seda tasa mata, kana tamike, bakin mayafinta tadauka wanda Mamy tabata ta yafa, se 7:00pm Bala driver yadauke su ya tafi kaisu event din,
bayan sunje, mutane sun fara taruwa sosai, amma amaryar batazo ba, guri suka nema suka zauna, gurin ya hadu sosai, kana gani kasan da uwar kudi, gurin zaman amaryar se walwali take ga wani cake a kan table din gaban kujerar amaryar, shi kansa cake din wuta yake yana walwali, yan mata ne a gurin kala kala kuma yayan masu kudi, kowanne table maza hudu mata hudu, sukam basu zauna inda maza suke empty suka samu suka zauna su uku, yan matan nata hotuna, dj na ta sakar sauti, amma sedai wakokin turanci yake sawa, sukam su Zuhura idonsu nakan wayar Yasmeen, suna kallon hotunan Yasmeen dasukaje kasar Paris hutu wancan year din, sunata hirar su, Muhsin ne ya hango su yanufo inda suke, seda yakaraso yace "kai yan matan Mamy kun iso