Showing 39001 words to 42000 words out of 84568 words
falour ya tarar da Mamy tana shirya breakfast, gasheta yayi, ta amsa," yau futa zakai dawuri haka" "eh Mamy " to yau dai zamu je hada lefen Ilham kuma kai yakamata ka kaimu" no Mamy bazan iya ba Bala driver yakaiku" ok to kayi breakfast kafun katafu" nakoshi" daga haka yafuce , hanyar hoapital din yanufa, yana zuwa yashiga office dinsa yazauna, komai natafiya akan tsari, hakan yamai dadi sosau ganin kuma yadda ake kula da marasa lafiya cikin kulawa, ya yaba sosai hakanne ma yasa yace ze kara musu albashi.
se karfe 12:00pm Ahmad yatashi, yana tashi yayi maza ya shige toilet yayi wanka yafuto yashirya, se lokacin yaduba agogo yaga, 12:15pm "kash tatafi school bangantaba" karaf a kunnen Nafisa, hakan yasata cewa "wakenan"? ba tsoro yacemata "wacce zan aura" aure kuma!" "yes meya faru" kawai hadiye maganar dazatai tayi , tayi shiru, ok zan wuce gida yanzu " bazaka bari se yamma ba" ah ah yanzu zantafi" yana fadin haka yasa hannu aljihunsa yadauko rafers din dubu daya ya ajiye mata kan bed, yabude kofa yafuce, binshi tayi da kallo har ya fuce.
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 29
________________Bayan anfuto break suka samu karkashin bishiya suka zauna , suna hira sunata dariya, wasu mazane su uku suka iso gurin, daya daga cikin su ne yakalli Zuhura yace "ke ya zandinga maki magana kina shareni" Walida ce tace "haba fu'ad waikai bazaka sauya halinka bane" daga mata hannu yayi alamar ta dakata "kibarshi kinsan seya gwada halinsa ga duk sabuwar daliba" "ku ya isheku ba gurinku nazi ba saboda haka kar na kara jin bakin kowa" "mitssss kubarshi bashi da abunyi ne shiyasa" daga haka tadau jakarta tabar gurin, suma binta sukai, suka barsunan suna binsu da kallo,
yana komawa gida ya shige dakinsa, kan bed yakwanta yana tunanin yaze bullowa auren Zuhura, so yake ana gama bikin Ammar shima yafuto danashi auren, sedai tunanin sa daya ba lallai mom dinsa ta yadda ba, musamman idan taji asalin Zuhura basu da kudi, numfasawa yayi kana yace "ko me za ai sedai ayi amma bazan fasa aurenkiba"
"Asabe Asabe Asabe" wadda aka kira da Asabe ce tafuto daga dakin girki tana goge fuska da bakin zaninta, "ah gwaggo Larai kece ashe" "eh nice bikiso zuwana ba ko" "haba gwaggo Larai akan me zance banso zuwankiba" "saboda munafunci mana da kuke kullawa keda kanwarki Habaiba" "Habiba kuma me tayi" "tunda malam Haruna ya rasu takwashe komai ta tafi da shi annemeta an rasa" "haba gwaggo Larai kinsan dai malam haruna be bar komai ba," "inji uban wa zakuce be bar komai ba duk talaucinsa ai yabar wani abu" "haba dan Allah naga agabanki aka koresu daga gidan dasuke, biki taimakesu ba amma kinzo kina wannan maganar" "to munafuka ke me yasa biki kawosu gudankiba" "ai miji na baze yadda ba amma dana kawosu" "yanzu hakama sunbaki wani abu daga cikin gadon shi yasa kike rufa musu asiri" "ke Asabe hayaniyar me nakeji a gidana Allah yasa ba baki kikaiba" yashigo yana zare ido, "nima tundazu nakeso nayi bacci amma sun hanani" wata mata tafuto daga daki dauke da katon ciki" "ai batasan zafin haihuwa ba da wahalar ciki shi yasa zata tara miki mutane agida suyita ihu dansu hanaki bacci" "gwaggo Larai cefa tazo" "to una ruwana biki iya komai ba sedai kici ki kwanta ko dan batan watannan biki taba yiba" "kai wato baka da mutunci ko ko gaisheni wato baza kayi ba" gwaggo Lari tafada tana nunasa" "ai mutane masu kima ake gaisherwa ba irinku ba matsiyata" kai ni kake cema matsiyata" to da meye daga ke har ita wlh gwara nai kiwon akuya danai kiwon Asabe akuya zata haihu ita kuwa sedai taci tayi kashi" itadai Asabe bata tankamai ba tunda yafara dan tasan halinshi yanzu seyace ta tafi gida kuma basu da gida, nan dai yagama bala'in sa yashige yabarsu agurin , ganin haka yasa gwaggo Larai cewa "ni kinga tafiyata amma fa zandawo sekin fadamin inda suke" daga tafuce tana gyara daurin zani.
seda aka tashi suka fito tare, Walida akazo dauka mom dinta, bayan ta sun isa suka gaisheta ta amsa, kana takalli Zuhura tace "kece Zuhura"? daga mata kai tayi alamar eh "Walida nabani labarinki tace kinada yankali kuma kina da kyau kuma gashinan nagani" murmushi tayi ta harari Walida, sallama Walida tamusu suka wuce, "ke nimafa nabawa brother na labarinki" harara ta galla mata tace "wato dai tallah kukeyi dani ko"? "ke shimafa yanada kyau ki yarda yarinya ku haifamana babies beauties" dukan wasa takai mata suna dariya, Bala driver ne ya iso, horn yamusu, inda Nadra nacan na lilo, shikam Muhsin yana gurin abokansa, tahowa sukai su duka suka shiga mota, tana dagawa Islam hannu,
bayan sun kammala abincin rana Mamy tace Ilham takira mata Ahmad yau be futo ba, amsawa Ilham tayi tawuce dakinshi, tana shiga taganshi kwance yana bacci, "yaya Ahmad kazo Mamy nakiranka" daga mata hannu yayi alamar yaji, itakuma tafuce, hayaniyarsu ce tasa Mamy cewa to gasunan sundawo, hala kuwa segasu sun shigo, Muhsin da Nadra ne suketa musu akan wai wayafi kyau tsakanin Walida da Ilham, itadai Zuhura kawai murmushi take, bayan sunshigo Mamy tace "yau kuma me ake tattaunawa" Mamy wai yaya Muhsin ne yace wai Islam tafi Walida kyau" to su suwaye"? Mamay kawayen aunty Zuhura ne" "to ai gaba daya Zuhura ta tafisu kyau na tabbata" "gaskiya kam hakane Mamy" Muhsin yafada yana kallon Zuhura" "aikuwa aunty Nadra duk kinfusu kyau" "to yanzu ankashe musu aje acire uniform azo ayi luch" tom Mamy" suka fada gaba dayansu, Ahmad ne yafuto daga dakinshi sanye da riga t-shert se trequater, juyawa tayi tana kallonshi, shima ita yake kallo , murmushi yamata wadda yasa taji sanyi a ranta, ta tabbatar bayajin haushinta, itama murmushin tasakarmai wadda saura kiris yafadi, dariya takaramai tana shigewa, kujera yanema yazauna yana murmushi , dakinsu ta wuce, tana shiga tadda Mamy tana sallah, uniform din jikinta tashiga cirewa, bayan tagama tafada toilet tayi wanka tadauro alwala, bayan tafuto ta tarar da Inna ta idar da sallah, "Inna mundawo" to sannu" "Inna kwanannan naga fa kyau kikeyi" rike baki Inna tayi tana fadin "oh ni wannan yar" dariyatai tana daukan hijabi tana tada sallah, bayan ta idar tadauki kaya tasa atamfa kalar green da baki dinkin riga da skirt, bakarmin kyau sukai mataba, sun mata cib , gashinta taje ta tufke da ribbom, kana ta daura dankwalinta, Inna takalla taga ta zuba tagumi, "Inna meya faru kuma" "uhmm kawai dai insan ganin yaya ta Asabe, bansan yatake ciki da rayuwar aurenta" zama Zuhura tayi tana cewa "hakane Inna yakamata tasan inda muke saboda kinga kuku biyu ne kuka rage" "insha Allah zan nemeta" "amma Inna dan Allah kidena damuwa" "shikenan yawuce je kici abinci" daga haka tafuce, tana zuwa ta tarar dasu Muhsin kan dining suna cin abinci, zama tayi tana fadin shine ko ku jirani ko"? "sorry to zauna munjiraki" Muhsin yafada yana ajiye cokali, dariya tayi tace "daga baya kenan" dariya sukai ta nemi guri tazauna, itama abincin tazuba tafara ci,
bayan sun kammala cin abincin Muhsin yafuce ball, itakuma Nadra ta tafi gurin su Amira wasa, ganin haka yasa Zuhura wucewa dakin Hajiya, tana shiga ta tadda ita akwance kan gado, bayan tayi sallama tashiga ciki tana fadin "Hajiya bacci kike ne"? "ba bacci nake ba kawai dai nagaji ne shine nadan kishin gida" "to bara nazo namiki tausa" tafada tana hawa kan bed din "yawwa da kin kyauta kuwa" tausar tafara mata tana mtsa mata kafarta, sunayi suna hurarsu , Mamy ce tashigo cikin shurin ta nafuta unguwa, sallama rayi , suka amsa su duka "Zuhura kina nan ashe" eh Mamy" "to Hajiya zamu futa hado lefen Ilham daga nan zanyiwa maman Zuhura si yayya" "to shikenan sekun dawo ke dawa zakuje "nida Iham innaga Ahmad nasa yakimu" to ai shikenan sekun dawo" "Zuhura Innarki tayi bako karki ga biki gantaba" tom adawo lafiya"Allah yasa" daga haka Mamy tafuce,
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 30
________________Bayan yafuto theater, yadawo office dinsa yazauna lokacin har 5:15pm tayi, court dinsa yadauka yasa yadau key din motar sa da wayarsa, yafuce, reception yaje yace ma da norse din yariga yafuta, ko waye yazo kar a nemeshi, amsama tayi cikin girmamawa, daga haka yafuce , yamotarsa yayi wa key ya nufi gida,
bayan ya isa gida yatarar falour ba kowa hakan yasa yawuce part dinsa dan yayi wanka, yana shiga yafada toilet, ruwa yasakarwa kanshi, seda yayi wanka yafuto, kananun kaya yadauka , farar riga da trequater yasa, bayan yagama shiryawa yafada saman bed yakwanta, gaba daya yagaji , jiyay cikinsa na kugi alamar yunwa, wayarsa yadauka yadanna kiran mom dinsa, bayan tadaga yace mata "Mamy nadawo kuma inajin yunwa" "ayyah kaga kuma nafuta bana gayama yau zamuje hado lefe ba" "lefe kuma Mamy lefen wa"? "bansaniba ai auren baya gabanka shiyasa" se lokacin yatuna yace "ok natuna Mamy yanzu dai inajin yunwa" "ok kaje dakin Hajiya Zuhura nacan kasa ta hadama" "wlh Mamy bansan ma futa" "to seka zauna da yunwarka" daga haka takashe wayarta , idonsa ya lumshe, in ya tuna da aurennan komai jagulemai yake, dawannan tunanin yamike yafuta, dakin Hajiya yanufa, Hajiya nata bawa Zuhura labarin yan matakansu dasukayi a da, shigowa yayi bakinshi dauke da sallama, amsawa sukai, bata dago ba takalleshiba , zama yayi kan kujera yana fadin "Hajiya good evening" kallonshi Hajiya tayi ta tabe baki tace "to turawa dan iyayi kadawo" jin ance dan iyayi yasa Zuhura kwashewa da dariyar da batasan sanda tazo mataba, kallonta yayi cikin mamaki, itakam kunshe dariyarta take taki kallonshi, "ke hadamun abinci kikawo mun part dina" daga haka be jira mezata ce ba yafuce, itama tashi tayi tana fadin "Hajiya bara naje nadawo " "to sekin dawo" daga haka tafuce, kitchen tanufa tahadamai abincin kan tire, tawuce part dinsa, tura kofar tayi tashiga ciki, zaune tasameshi kan kujera, karasawa tayi inda yake, ajiyemai tayi kan table din gabansa, be ko kalle taba yaci gaba da canja channel, "ga abincin" be kalle taba ballantana tasa ran ze mata magana, ganin haka yasata juyawa zata fuce, kafun takai kofa yayi maza yasawa kofar key, kallonshi tayi ido cikin ido, alamar tambaya, shima ita yake kallo, komawa yayi ya zauna inda yake, abinci yazuba yafara ci, sakeke tayi tana kallonshi, shikam cin abincin sa yake kamar ba kowa kusa dashi, ganin tsaiwar bazata kai mata ba yasa tamatsa kusa dashi tace "ina son nafuta" ko kallonta beyi ba ballantana ya bata amsa, ganin haka tasake cewa "kabudemun nafuta" be kalle taba yace "wa kike ma dariya dazu"? shiru tayi batare da tace komai ba, abinshi yagama ci kana yadau phone dinsa yana dannawa , ganin tsaiwar bazata kai mata ba yasa tace "dan Allah kayi hakuri wlh bansan sanda dariyar ta kufce mun ba" "uhmmm kinga dariya taja miki kita zama anan se sanda nagaji nabude miki" "dan Allah kayi hakuri wlh akwai abunda zanyi" "bake kin raina mutane ba ko"? yafada yana kwanciya saman kujera, matsawa tayi kusa dashi ta tsugunna tana fadin "dan Allah yaya Ammar kayi hakuri wlh bazan karaba" lumshe idonsa yayi yana jinta amma yamata banza kamar yafara bacci, ganin baze hakura ba yasa ta kifa kanta kan gwuiwar ta tana shashekar kuka, jiyayi kukan nata nataba zuciyarsa, haka kawai yaji zuciyarsa kamar tafashe saboda kukan datakeyi, still idonshi arufe yace "ke kukanki yadameni kuma inasan nayi bacci" hadiye kukanta tayi batare data dago kanta ba, tana haka bacci yakwasheta tuni tafara bacci har tana gyara kwanciya kan carpet, shima baccin yake,
Hajiya nata jiran Zuhura ta dawo, shiru har bacci yadauketa, 6:30 su Mamy suka dawo lokacin Alhaji Aminu na kokarin futa da motarsa, futowa yayi suka gaisa, har Mamy tana tsokanarsa wai ango, daga haka dai yawuce sukuma suka shigo ciki, Ahmad nayin parking , suka futo suka wuce ciki, me gadi da Bala driver sukasa su shigo musu da kayan dasuka siyo, shikuma Ahmad ganin ana kiran sallah yasa yawuce masallaci, Inna ce tashiga neman Zuhura bata gantaba, daki tawuce tanufi toilet tayi alwala, "watakila ma tana dakin Hajiya" Inna tafada tana zura hijab, ta tayar da sallah, bayan sun iso falour , Mamy bedroom tawuce dantai sallah, ita kuma ilham tawuce part din Ammar tana iyayi, knocking tayi, shiru ba'a budeba, bugu takarayi da karfi, a firgice yamike yana salati, tashi yayi yanufi kofar danya bude, yana budewa yaga Ilham tsaye, hade rai yayi yace "ya akai" "bakomai kawai dai dama cazan maka mundawo" "to na ganku" yafada yana shigewa yafada toilet dan yayi alwala ,binshi ciki tayi tana murmushi, turus tayi ta tsaya ganin Zuhura kwance kan carpet tana bacci, "kai yaya Ammar me nake gani haka" tafada lokacin dayake futowa, be kalle taba yafuce dan ya wuce masallaci, wata uwar tsawa Ilham ta daka tana kai ma Zuhura duka, afirgice tamike tana sosa gurin "ke uban me kikeyi a dakin nan iye"? hawaye Zuhura tafara, "ba tambayarki nake ba me kuka yi" "bakomai " "muna fuka kawai zoki futa" dagudu Zuhura tafuce, mamaki ne yacika Ilham tafara tambayar kanta me Zuhura keyi dakin Ammar, ganin bata da amsa yasa tafuce, dakinsu tawuce , tana shiga taga Inna zaune kan sallaya tana lazumi, toilet tawuce, kallonta Inna kawai tayi, seda tafuto Inna takaleta tace "Zuhura ina kika je ne "? "ina dakin Hajiya" tafada tana tada sallah, kallonta Inna kawai tayi ta cigaba da lazimi, bayan sundawo masallaci suka zauna a falour gaba dayansu, Ahmad kam hankalinsa baya gurin, soyake kawai yaga ta inda Zuhura zata ɓullo, so yake yaganta, zancen bikin Ammar suka shigayi, Ahmad ne yace "ai Mamy ana gama nashi nima zanyi" "ah dagaske gara ai kuyi, amma ina kasamo yrinyar"? "Mamy ai yar kice" "ya'ta kuma"? "eh Mamy" "wacce yar'tawa kenan"? "Mamy ai zamuyi magana" "ah tom seka zo" Ammar ne kadai yagane wadda yake nufi, tashi Mamy tayi danta hada lunch, kitchen tashiga Inna ta tarar da har ta kusa gamawa , tayata tayi suka karasa suka zuba cin fulas , Zuhura ce tashigo tana fadin "sannunku da aiki" "yawwa Zuhura zoki dauka mukai dining" "tom " tafada tana dauka tafuce, itama Mamy sauran tadauka tafuce, ita kuma Inna tashiga gyara kitchen din, bayan sun ajiye a dining, Mamy tamusu magana suzo suyi lunch, tasowa sukai gaba dayansu, Ahmad ne yakalli Zuhura dake tsaye yamata murmushi, itama murmushin tasakar mai, Ammar na lura dasu, haka kawai yaji zuciyarsa ba daɗi, saving dinsu tayi, seda tagama, Mamy takalleta tace "to zauna kici mana kema" "ah ah Mamy bara nasanarwa Hajiya angama abinci" to shikenan" daga haka tawuce, Ahmad ne yace "oh namanta nabar wayata a daki zanje na dauko" busuce komai ba yatashi yawuce , jitai an riko hannunta, tayi saurin juyawa, ganinshi tayi yana sakar mata murmushi, yace "my queen nayi kewarki fa yaudinnan" nima haka" tafada tana sunkuyar da kanta kasa "dagaske my queen" daga mai kai tayi alamar eh "yanzu kenan kema kina sona" murmushi tayi kanta akasa tace "eh" hamdala yafara zubowa yana daga hannunsa sama yana godewa Allah, itakam tuni tadiba da gudu tayi dakin Hajiya, komawa yayi danya cigaba dacin abincinsa, yau jiyake kamar anmai kyautar aljanna, tana shiga dakin Hajiya taganta zaune "Hajiya an kammala abincin dare fa" "oh bansaniba ai, dazu biki dawo ba"? "eh naje nayi wani aikine a dakinmu" "tom shikenan muje" daga haka suka wuce, seda suka kusa zuwa gurin dining din Zuhura tace "am Hajiya bara naje kitchen nadawo" "tom shikenan" daga haka tawuce ita kuma Hajiya tawuce dining, zuba mata abinci Mamy tayi, tazauna tafara ci, Ammar ne yamike yana fadin "se dasafenku" "toh tun yanzu " eh nagaji ne" to Allah yatashemu lafiya" Inna tafada tana kai cokalin abinci bakinta, dakinshi yawuce yana shiga ya wuce bedroom dinsa, saman bed yafada yakwanta, yana tunanin ta, kwana biyun nan besan meke damunshi ba, dahaka bacci yadaukeshi, seda suka gama gaba daya, kowa yatashi yawuce dakinshi, zama Ahmad yayi yana jiran ko ze ganta tafuto, shiru bata futoba, har ya gaji yatashi yashige dakinsa, itakam Zuhura tana gama cin abinci tayi sallar isha takwanta,
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 31
__________________Karfe 10:30 Mamy da Inna suka fuce, gurin gyaran jiki da lallle, dayake