Showing 57001 words to 60000 words out of 84568 words

Chapter 20 - SOYAYYA DA IZZA complete hausa novel

Mrs KD   

25 Aug 2024

21473

kenan, Yasmeen ya gari" "lafiya lau Muhsin ashe kazo" "wlh nazo, yaya Zuhura kunyi kyau fa" "kai Muhsin kyau ai se ku" dariya sukai yace "bara naje kun wadancan na dawo" daga haka ya tafi, sukuma suka cigaba da kallon wayar su,


"Ahmad inasonka sosai wlh bansan abunda ze rabani dakai" tayi maganar lokacin datake kwance saman kirjin shi, tana shafa gefen fuskarsa, "wayace dama zamu rabu muna tare" yafaa yana kara manna ta jikinshi, yana jamusu blanket, yana kara shafa bayanta, tuni itama tafara shafashi rako ina, basa gajiya da junansu, yanzu suka gama amma har feeling dinsu yakara tashi, daganan suka shiga, mantawa da a wacce duniyar suke

Feenat ce takalli Ilham tace "ke dai ki gwada mana kiga kika sani ko yazo din" "uhmm bakusan halin yaya Ammar ba" "kedai bakya san kiranshine" wayarta tadauko ta danna kiransa tana fadin "bara dai kuji da kunnenku" tasa wayar a amsa kuwa yadda zasuji, seda takatse, kana takara kira, seda takusa katse wa yadauka, "hello yaya Ammar" "inajinkj ya akai" "dama haka zance maka, dan Allah inasan kazo muyi hotuna a gurin bridal shower din" "baki da hankali ko, karki kara sani a haukanki" daga haka yakashe wayar, kallonsu tayi tace "yanzu kunji da kunnenku ai" "tab gaskiya dai kina da babban aiki a gabanki" "kunga kubar wannan zancen mu tafi kunga 8:00pm har ta kusa" daga haka suka fara tafiya, ita kuma Ilham ita da kawayenta guda biyu suka shiga cikin mota,

Zuhura da Yasmeen ne suke ta fada, Yasmeen ta dage setayiwa Zuhura hoto, ita kuma taki, dakyar dai ta tsaya ta mata guda biyu, sanarwa aka fara amarya ta iso, hakan yasa kowa ya maida hankali kan gurin shigowa, waka aka samusu wai ta shigo da amarya, ba jimawa kuwa sega su sun shigo, tana tsakiyarsu, sunata rawa har ita, har suka karaso suna rawa, kana tazauna kan kujerar, tuni kowa yafara yadaukanta hoto, Yasmeen ma mikewa tayi, taje tayimata hoto ta dawo, nan kuma aka fara gudanar da komai yadda yakamata, aka fara raba abinci dasu sancks ba abunda babu, se rawar kai take kamar ba amarya ba, bayan sun kammala cin abinci, suka maida hankalinsu kan amarya dasuke ta rawa ita da kawayenta, magana sukaji ana fadin "yan mata ashe kun iso" kallonshi Zuhura tayi tace "au yaya Jawad ashe kaine" "ita kawar taki bata magana ne Zuhura" "kai yaya Jawad tanayi mana" kallon Yasmeen tayi datake ta daddana waya tace "sister wai dama yaya Jawad be sankiba" "rabu dashi sister hakan yakeson fada" "kardai Yasmeen kanwar Mahmud" "ita mana" tafada tana kallonsa "wai kece kika girma haka, ai muna waya da Mahmud din amma be fadamun kin gurmaba" dariya tayi tace "to yaya Jawad kawai kuma seya ce ma kanwarsa ta girma" "bazaki gane dilili ba yanzu dai inason yin magana dake" kallon Zuhura tayi, itama Zuhura ita ta kalla kana tace "bara naje gaba ko nafi ganin amarya da kyau Amira muje" daga haka suka tashi suka basu gurin, kallon Yasmeen yayi yace "kai gaskiya fa kinyi kyau sosai" "Allah yaya Jawad nagode" "tun daga nesa na hangoki naji bazan iya jurewa ba se nazo, ina bukatar zan samu hadin kanki" "name kuma yaya Jawad"? "kinga Yasmeen bazan boye miki ba har ga Allah inasonki, abaya naso Zuhura amma se yaya Ahmad ya rigani, to ina fata anan ba wanda ya rigani" "yaya Jawad ba a riga ka ba, amma inason kabani lokaci nayi tunani kafun" "so nabaki nan da gobe, dan inasonki sosai wlh" dariya tayi tace "alright ba damuwa zanyi tunani" daga haka suka cigaba da hirara sh, se daga baya yace suzo yamai dasu gida, Zuhura tayima magana da Amira, suka taso suka futo, Yasmeen ce ta hau gaba sukuma suka shiga baya, daga haka suka tafi







💞 SOYAYYA DA IZZA 💞



Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)

Yar amanar jajirtattu💪💪

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️





page 40



_______________Bakin gate din yayi parking, yace "Zuhura bara nakai su Yasmeen gida" "ok to sister ki gaida gida, se gobe idan mun hadu" tafada tana ɓalle murfin motar, "ok sister se goben" motar yaja suka tafi, ita kuma tashiga ciki, bayan ta isa falour ta tarar da Hajiya kawai falourn tana waya, zama tayi kusa da ita, yayin da ita take waya da yar autar ta A'isha, dake aure a London, "yanzu A'isha su kadai zaki bari bazaki tawo dasu ba" daga cikin wayar tace "Hajiya akwai yar aiki ai zata kula dasu" "to shi Jamal din zezo ne" "eh mana Hajiya tare zamu tawo ai" "to shikenan sekunzo" "amma fa Hajiya Abuja zamu wuce direct anan jirginmu ze sauka, sedai mu hadu acan" "ok to shikenan" daga haka ta kashe wayar kana ta dubi Zuhura tace "oh Zainab wannan kwalliya haka, kamar ba ke ba" "kai Hajiya" "dagaske mana, har an tashi kenan" "ah ah kawai dai muntawo naga har 9:00pm tayi ma" "gaskiya dai gara da kukau tawowar ku yafi" Mamy ce tafuto tana fadin "ah Zuhura harkun dawo" "eh Mamy mundawo" "ina su Yasmeen din" "yaya Jawad yatafi kai su gida" "ok to kije kiyi wanka ki canja kaya sekizo kici abinci" "tom Mamy" kana tamike, tana wucewa

bayan Jawad yakaisu har cikin gidan yashiga, bayan yayi parkinga Amira tabude tafuta, itama Yasmeen harta kai hannu Jawad yace "haba dai ai bamu gama ba" "to yaya Jawad me ya rage" "fira mana" murmushi tayi kana takalleshi tace "to yaya Jawad inajinka" daga haka yashiga zubo mata matanganu wadanda zasu jawo hankalinta taji tana sonshi, har fa Allah dagaske yanason Yasmeen, kuma so na aure, saboda yanzu ya rage bin matan dayake ada, tun lokacin da Ammar yadawo, gudun kada Ammar yagane ya hukunta shi yasa yadena tun kafin yagane,


tsaye take gabanshi daure da tawul, tana tayashi ɓalle bottle din rigarsa, "wai beb meyasa kamatsu katafi ne, kodai ka gaji dani ne" kugunta yakama yana fadin "kema kinsan ai ba haka bane, kawai dai banfadawa mom nafuto ba" "ok to adawo lafiya" daga haka tayi hanyar toilet, da ido kawai yabita, kana shima yayi hanyar futa, bayan yafuto, yashiga motarsa yawuce, gida yanufa, yana zuwa yayi horn me gadi yabude mai gate ya shiga, parking space yayi parking, kana yafuto yashiga ciki, da sallama , amsawa mom tayi, tayin da me kunshi ke goge mata hannu da tissue, karasowa yayi ya zauna kusa da mom din yana kama hannunta, yana fadin *wow mom yayi kyau" "to ko za ai maka ne" "da queen tananan da ita za ayiwa, se ya ma fi kyau a hannunta" "uhmm wace queen kuma" "wacce nabaki labari mana" tsaki taja kana tace "bazaka manta da yar talakawan nan ba ko" "Mom kenan barama nasa Muhsin yatura mun hotonta dan naga yau Ilham tafara biki" "eh ta turamun hotunan nagani " wayar Muhsin yashiga kira, amma be dauka ba, seda yakira har sau uku be dauka ba, "ohh Muhsin ko ina yakai wayar tashi, bara na kira Jawad" daga haka ya danna kiran Jawad,

"sorry Yasmeen bara na daga waya, yaya Ahmad ke kirana" "ok ka dauka" wayar yadauka yakara a kunnensa yace "hello yaya Ahmad" "yawwa Jawad ya kake ya biki naga kun fara" "eh yaya Ahmad anfara yau" "hakan yayi, nace kanada pics din Zuhura ne katura mun yanzu dan Allah" "ayyah yaya Ahmad bani dashi, amma bara na tambayi Yasmeen, idan an samu zanturo ma yanzu" "ok tambaya" daga haka yakashe wayar, kallon Yasmeen yayi yace "Yasmeen kinada pics din Zuhura ne" "eh nayi mata dazu dakyar" "ok turamun yanzu ta WhatsApp" "ok" turamai tayi guda biyu, shima yayi forward yatura ma Ahmad,

yanajin karar sako kuwa yayi maza yashiga, "wowww" abunda yafada kenan, yana murmushi, "Mom kalli queen fa kina ganin ta ai kinsan tanada nutsuwa gata kyakkyawa" yafada yana nunwa Mom hoton, kallon hoton tayi azuciyarta tace 'ba laifi tanada kyau' afili kuma tace "malam matsa kabani guri, kasan Allah ko me zakai bazaka auri yarinyar nan ba" bata rai yayi yana mikewa yawuce bedroom dinsa, yana shiga yafada kan bed yacigaba da kallon hoton Zuhura, tayi kyau sosai gashi tayi murmushi, seya kara mata kyau, yanata kallon hoton daga baya yasa hoton kan screen din wayarsa, yamaida sa wallpaper,

bayan tashiga , tayi wanka ta canja kaya tasa na bacci, kana tafuto, tanufi kitchen, ba kowa hakan yasa tadawao falour, Abba da Hajiya ne se Mamy da ita tama mike zata shige ciki, ganin haka yasa bata karasa ba takoma, kitchen tanufa , tabude kulolin abincin ta zuba kadan saboda a koshe take, kadan kadan ma take kamar wace akaiwa dole, seda tagama ta bude fridge tadau lemo kana tawuce dakinta,

"yaya Jawad yakamata na shiga gida kaga na dade" "korata kike kenan" "no niba korarka nake ba kawadai nasan Daddy yadawo tun dazu" "ok to se gobe ma karasa" "to seda safe" daga haka tabude motar tafuce, seda tashige, kana yatayar da motarsa, yafuce, tana shiga ta tarar dasu kan dining gaba dayansu, sun cin abinci, karasawa tayi, Daddy yakalle ta yace "se yanzu kika dawo" "am Daddy yaya Jawad ne yazo" be kara magana ba yakalli Inna yace "amma dai auntyn yara jss zan kai Amira" "yo dama ai sedai jss kalle ta fa kamar ana kara hura ta kullum" dariya Yasmeen tayi tana shigewa, ita kuma Amira ta bata rai, shima Halifa dariyar yake, Amira ce tace "Daddy kama Halifa magana yana mun dariya" "Halifa ka dena mata dariya kaji" "tom Daddy yafada yana kunshe dariyarsa,


su Ilham basu tashi ba se 11:30pm, kana kowa yawatse, itakuma tabi su feenat, hotel, ta dage se tayi harkatar ta lesbian yau, dan idan aka daura zata tafi hutu kafun ta dawo, haka suka tafi, seda suka gama iskancinsu kana tayi wanka, tasa riga da wandon wata daya daga cikin kawayenta, tayafa mayafi akai, "nidai naga ya Ammar dinan zeyi, muda bamu damu da sex ba" daya daga cikin kawayenta tafada "yaya Ammar ma girman kansa da izzar sa bazata barshi yakawo kanshi gurina na, kinga nikuma na huta nima, sedai bansan yazanyi da harkata ba, dan bazan iya 1 week banyi ba" "ke kwantar da hankalinki badai futane baze barki ba, seki kiramu mu dinga turo miki yara idan ya futa, abunda ga yara nan suna ta shiga less, dakin saki kudi tuni zasu zo kiyi abunda kike so dasu ki sallemesu kafun yadawo" "hakan kuwa za ai kinga yaje can yasha zaman sa shi ze cutu ba ni ba" takare maganar suna kwashewa da dariya kana Ilham tace "ke mikomun key na nawuce, kufa shirya dawuri mu hadu acan danni tare da dasu zan tafi" "ok baki da matsala" daga haka tafuce, tana futa tahau motar ta tanufi gida.

juyi kawai yake saman bed din yakasa rumtsawa, tunaninsa daya, ta futa da make up din fuskanta, kuma mutane zasuyi ta kallonta, zuciyarsa nafaamai 'to wai kai ina ruwanka ne' shikansa ya kasa yagane dalilin damuwarsa dahakan, kishi ne ko kulawa, amma shikansa yasan yanzu yanason yarinyar, tana burgeshi sosai, nutsuwarta, da kamalarta, yanajin kaunarta sosai, yanason ganinta ko yaushe a kusa dashi, ya tabbatarwa kansa yana son yarinyar, amma gani yake bata kai yace yana sonta ba, kamar shi da mata ke binsa, taya ze bige da son wannan tatsitsiyar yarinyar, izzar shi bazata bari ya nuna mata yana sonta ba, kuma koda ma yanasonta, ya zeyi da Ahmad daya riga ya bayyana mata, sam baya kaunar ta auri Ahmad saboda yasan halinsa kuma har yanzu be sauya ba, haka yadinga tunani kala kala, ganin tunanin baze kare ba kawai yamike ya shiga toilet, yayi alwala yazo ya tada sallah, seda yayi nafilfilu, daga baya yadaga hannu yana rokon, idan son yarinyar yake to Allah yacire mai soyayyar ta azuciyarsa, kuma yabashi ikon zama da Ilham lafiya yakula da hakin da aka dora mai, yabashi juriyar jure zama da Ilham duk da bayasonta, seda yagama addu'ar sa yakoma saman bed din yakwanta,


asuba nayi yatashi yanufi masallaci, lokacin suma su Abba Jawad da Muhsin duk sun futo, hakan yasa suka rankaya suka tafi masallacin tare, bayan an idar suka tawo, Abba na tsakiyar su, Abba ne yakalli Ammar yace "idan kashiga ciki fara shiryawa don karfe 9:00am zamu wuce saboda 11:00am za a daura" a sanyaye tace "tom Abba" "ku kuma kar wanda yakoma bacci san bazamu jira kowa ba" amsawa sukai suma, suna karasa wa falourn kowa yawuce cikin dakinsa, itama Zuhura tun asuba data tashi bata koma ba, yau da kewar kawarta Maryam ta tashi, tanata tunanin ta aranta, bayan gari ya waye, tafuto tanufi kitchen, Jummai ce kitchen din ,har ta kammala breakfast tana zuzzubawa, "aunty Jummai ina kwana" "lafiya lau Zuhura kin tashi" "eh aunty Jummai na tashi, kardai harkin gama komai" "na gama dayake Mamy tace dawuri za a futa shiyasa na kammala komai" "gaskiya ne sannu" tayata Zuhura tayi suka kai dining suka jera, ba jimawa duk suka fara futowa kan dining, harda Ilham dan ita dama a matsu taje taga mom dinta, abincin suka fara ci harda Zuhura, Ilham ce ta kalli Mamy tace "Mamy ina yaya Ammar" "yana ciki me bi besan an kammala breakfast ba" "ok bara naje nakirashi" daga haka tamike tanufi part dinsa tana zuwa tafada ciki ko knocking batai ba , kallon ta yayi yace "meye haka zaki shigomun falour ba sallama" "haba yaya Ammar meye danna shigo awa nawa ne ya rage mu zauna daki daya dakai" "meya kawoki" "dama breakfast ne angama, kuma naga baka futoba" "jeki zan futo yanzu" juyawa tayi tafuce, shikuma ya hau hada takardun daya baza yasasu cikin drower kana ya mike yafuce, karasowa yayi dining ɗin, yana gaishe dasu Hajiya da Mamy kana yakara gaishe da Abba, gaishe dashi gabadayansu sukai, itama dagowa tayi itama tace "ina kwana" "lafiya" yafada yana zama kujerar dake kusa da ita, abinci takasa ci gaba da ci, juya cokalin kawai take, yana kallonta, amma yayi kamar ma besan da wata a kusa dashi ba, ganin bazata iya karasa cin abincin ba yasa tamike, Hajiya ce takalle ta tace "Zuhura yadai" "Hajiya nakoshi" "kin koshi kuma" "eh Mamy" "kodai bakisan zama anan dinne" Abba yafada yana kallonta, murmushi kawai tayi batare data ce komai ba "to shikenan idan kin shiga ciki kiyi wanka sekije dakina kidauko kaya" "tom" tafada tana wucewa, bayan tashiga kamar yadda Mamy tace tashiga wanka, suma ba jimawa suka tashi kowa yatafi shiryawa, harda amarya da ango, yana shiga toilet yashiga yayi wanka kana yafuto, zama yayi yana shafa lotion dinsa me dadin kamshi, seda yadan jima, kana ya gama yashafeshe jikinsa da turare kafun yasa kaya, farar shadda yadauko da linkin baki ajiki, se sheki shaddar take, sawa yayi , tayimai bala'in kyau, wani turaren yadauka yakara fesawa kana yadauko hula baka tanata kyalli yasaka,
tana futowa bata tsaya wani kwalliya ba hoda kawai da kwalli tasa seta shafa lipstick, kana tafuto tanufi dakin Mamy, sarka Mamy take sawa dan ita harta gama shiryawa da alama, dan ga mayafinta nan da jakarta a ajiye, "Mamy nagama" "ok jeki kan bed zakiga kaya atamfa ki dauka kisa" "tom" daga haka tashige, tana shiga taga atamfar a kan gadon, har bra Mamy ta ajiye mata, danta lura bata sawa, ita kunya ma abun yabata, bayadda ta iya haka tadauka tasa, kuma tamata camas ajikinta, kana tasa kayan, riga da skirt ne dinkin yayi kyau skirt din ya jawo yafuto mata da dirinta dake boye, tamfar ta haskata sosai, dankwalin ta daura ta nannadeshi kan ribbon din data daure gashinta, mayafi tadauka wanda Mamy ta ajiye mafa karami kalar kayan, dauka tayi ta yafa, kana tadau sarkar data ajiye mata da dankunne harda agogo, duka ta dauka tasa,
seda yagama karewa kansa kallo a mirror, yana jaddada wai shine yau ze auri Ilham, takaici duk ya ishe shi, dahaka dai yadebi wayoyinsa kana yadau lins din dabe saba yafuce, dakin Mamy yanufa, yana shiga yatarar da ita a falour tana kiran waya, kallonshi rayi tace, "wow son kafuto a ango" fuska ba walwala yace "Mamy wa kike kira haka" "mom din Ilham nake kira naji ko da lefen za a tafi kaga senasa su Bala driver isan zasu tafi su tafi dashi" "shiru yayi bece komai ba, yafara kokarin sa lins din a hannun rigarsa, "Mamy dan taimakamun" Zuhurace tafuto tana fadin, "Mamy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login