Showing 81001 words to 84000 words out of 84568 words
miki fa, bazakiji zafi ba" noke kafada tayi yace "oh bakya son mu samu baby dawuri ko" rufe fuska tayi tana murmushi, "kodai nayi yanzu kawai" zabura tayi tana mikewa, "matsoraciya kawai" "naji" tafada tana fucewa, shima mikewa yayi yafuce,
"Mommy ganinan yanzu" "kibari se gobe mana kizo ki karba" "ah ah Mommy nama shirya ganinan kina hotel dinne" "eh amma kiyi sauri dan zanfita tare da wani costumer na" "ok Mommy karki damu ganinan" daga haka takashe wayar tana saukowa falourn, dariya ta jiyo daga kitchen, hakan yasa tanufi kitchen din, Zuhura ce da Ahmad yana tayata aiki, sunata hira yana bata dariya wai don duk yaga hankalinta ya kwanta, "to sabon salo namiji a kitchen" juyowa sukai suka kalleta gaba daya, kana tayi murmushi tace "ah kuci gaba da aikinku nizan futa ne" "ina zaki" "ina ruwanka se kaji" daga haka tafuce, shiru yayi kawai, "yaya Ahmad kayi hakuri" "no queen bakomai muci gaba" daga haka suka cigaba da aikinsu,
"wato Amira bazakizo ba ko" "yaya Yasmeen wlh laifin aunty ne tace wai bazanzo yanzu ba se an kwana biyu" "au haka aunty tace, zankirata gaskiya yakamata kuzo" "yaya Yasmeen nima inason zuwa amma kinga su Daddy bazasu barni ba, zasuce exam" "exam din me kuma" "kai yaya Yasmeen exam din gama jss mana zan shiga ss1" "wow kanwar tawa ta girma ashe" "kai aunty tun yaushe" "au Allah mara kunya" "yaya Yasmeen kunyi waya da yaya Zuhura" "eh dazu nakirata amma bata shiga ba" "oh zankirata nima" Jawad ne yashigo falourn, tana ganinshi tasan ba lafiya ba hakan yasa tace "ok Amira zan kiraki" daga haka takashe wayar tana nufarsa, "honey yadai naganka haka" tayi maganar tana kama hannunsa, "no honey bakomai muje na zauna" zama sukayi, tace "gaskiya ban yadda ba kafadamun me ne ne" "ina tunanin yaya Ammar ne wlh" "ayyah honey ka kwantar da hankalinka komai fa me wucewa ne, wataran se labari, kuma aunty Ilham ita tayiwa kanta ai" "hakane kawai dai ina tausayinsa ne" "bakomai Allah ze bashi macen da zata sauya mai rayuwarsa" "ina fatan hakan" "to muje kayi wanka" daga haka suka mike sakale da hannun juna,
LONDON
dasafe yana gama breakfast yatafi hospital din daze fara aiki, office din doctor Johnson yanufa, da murnarsa doctor Johnson ya karbe shi, yasa akawo musu coffee, dan yasan shi ma abocin shan coffe ne, "yakamata fa yau kamana aiki kafun katafi" "base gobe ba" "kodai da madam din kazo ne" "ah ah ai bani da aure" "ohh haryanzu kai yakamata kayi" murmushi kawai Ammar yayi , bayan sun gama, ya tashi, dan ya wuce, yacemai gobe inshallah zezo yafara aiki, koda yatafi gida ya wuce, duk suna zaune, banda mijin aunty Aisha da yatafi aiki, sannu da zuwa yaran sukai mai, hakama aunty Aisha, "Ammar kasan kuwa Ahmad yakara aure" "aure kuma aunty, waya fadamiki" "yanzu mukai waya da aunty Khadija tace Daddy yakira Abba yake fadamai" "to aunty wa ya aura" "wai sunanta Nafeesa" "Nafeesa kuma, anya Ahmad kanshi kalau" "kasan tane" "ah ah bansanta ba, to amma ina Zuhuran" "Allah sarki baiwar Allah wlh tausayi ma tabani, du du sati guda da auren yayo mata kishiya yarinya me nutsuwa" shidai Ammar gaba daya ji yayi abun ya daure mai kai, dan yasan Nafeesa dai abokiyar sharholiyar Ahmad ce, amma ya akai ya aureta, "ai wlh Ammar naso kai ka auri yarinyar nan dan na yaba da hankalinta" "aunty bara naje ciki nadan huta" daga haka yamike yashige ciki,
"gaskiya ban yadda da yaron nan ba anya yanason yarinyar nan kuwa" "Hajiya yanasonta mana da bayasonta baze aure ta ba ai" "to amma ko sati biyu bata rufa ba ya kara aure" "toh Hajiya nima abunda nagani kenan" Mamy tafada "kunga ku kwantar da hankalinku Zuhura fa tana lafiya" "kai inada tantama dole zanje naga yarinyar nan" Hajiya tafada tana kallon Abba "gaskiya nima nabada goyon baya kije ki ganta, dan koda mukai waya naji muryar ta kamar bata cikin walwala" "kai kudai wlh mijinta nasonta amma kudinga wani tunani daban" "Usman kasan halin yarinyar nan ba fada zatayi ba idanma batajin daɗin zaman, kasanifa sarai mahaifiyar yaron nan basonta take ba" "to Hajiya shikenan Allah yakaimu lokacin dazakije" Abba yafada ganin Hajiya nason maida fadan kanshi, dan Hajiya mace ce me zafi bata daukan raini ko kadan, shiyasa ma koda Daddy yafada mai dililin auren Ahmad be fada musu ba, dan yasan Hajiya zata iya raba auren,
"karbi ki tabbata kin saka mai a abinci yaci" "to Mommy inshallah gobe dakaina zanyi mai breakfast tunda ai a dakina yake" "au ki tabbata a cikin kwai kika zuba mai dan da kwai yayi aikin" "karkiji komai mom, ai ina zuwa zan lalabashi mu kwana tare, kinga ina tashi sena hadamai breakfast ba wancan shegiyar ba" "todai ki kula kar wani yaganki, dan duk ranar da kika bari asirin nan ya karye , to kona haukace ko ki haukace, dan maganinsa akwai hadari, ammafa akwai biyan bukata dan wlh ko kara kika ajiye kikace kar ya tsallaka wlh baze tsallaka ba" "ai Mommy zan kula sosai bazan taba bari yagane ba" "to kitashi kije zan fita ne" mikewa tayi tana fadin "to Mommy se kinji wayata" daga haka tafuce,
suna zaune a folour, a kujera daya, suna kallo, bayan sun ci abinci, film din hausa ne na barkwanci, hakan yasa sunta dariya dagashi har ita, Nafeesa ce ta turo kofar, tashigo, kallonsu ta tsaya, kana ta tabe baki, a zuciyarta tace 'daga yau ne ai' daga haka tashige, Ahmad na kallonta amma yayi kamar be ganta ba, Zuhura kam suna cikin kallon bacci yasaceta, hakan yasa yakashe tv yadauketa cak, yawuce bedroom dinta, bayan ya isa, ya kwantar da ita saman gadonta, ya zauna yana kallon fuskar ta, yanajin sonta, a zuciyarsa, blanket yaja mata, ya rufeta, ya manna mata kiss a goshi, kana yakashe mata wutar dakin yafuce, dakinsa yanufa, yana zuwa ya shiga toilet yayi wanka, bayan yafuto, daidai lokacin Nafeesa tashigo sanye da kayan bacci, wanda gabdaya net ne, yana ganinta tacikin mirror din dayake tsaye, ta bayansa tazo ta rungumeshi, tana shafa kirjinsa, da salo me rikita shi, hade rai yayi yace "Nafeesa cikani mana" zagayowa tayi ta gabansa, ta matsa sosai har tudun breast dinta na gugan kirjinsa tace "haba mana sweet ina bukatarka" ta fada da muryar data sa yakara rikicewa, nan shima ya manna ta kirjinshi yana shafata, tuni yadauketa ya nufi bed, ra yamata rumfa, wutar damin ya kashe, dan haka bana iya ganin meke faruwa, yasa dole nafuta na janyo musu kofa, a zuciyata nace yau Ahmad ka shigo hannu😂
💞SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Ina masu bibiyar books dina😃to ina muku albishir da sabon book dina😁dana fara rubutawa✍️✍️ me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan😇dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu🤣zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa😍ina alfahari daku🤩 masoyana😍 kune kwarin gwuiwa ta😀i love you so much❤💔my pans😘
ina godiya da addu'o'in ku🙏🙏🙏
dayacce kuke yabon book dina💅💅 duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu😂😂
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku😀😀
DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J
page 51
_______________________________________________________________________
_____________________________
________________Inna ce ke shirya breakfast kan dining, wayartace ta dau kara, hakan yasa tadauka tana fadin "yaya ina kwana" daga cikin wayar yaya Asabe tace "Habiba Allah yayi wa gwaggo Larai rasuwa jiya da daddare" "inalillahi wainnailaihi rajiun" abunda Inna tafada kenan, yayin da su Amira suka futo cikin shirin makaranta, Amira ce takalleta tace "aunty meya faru" "to yanzu zantafi na sameki a can" daga haka takashe wayar, Daddy ne yafuto cikin shirin futa, Inna ce tace mai "yanzu yaya Asabe takirani take fadamin Allah yayi wa gwaggo Larai rasuwa" "subuhannallahi yaushe kuma" "jiya da daddare, yanzu inason naje tunda bama a kaita ba" "to semu tafi tare ai" "aunty muma zamuje" "ah ah ku wuce school driver yakaiku" daga haka tashige ciki, shirya wa tayi kana tafuto, suka wuce, sukuma su Amira suka wuce school, a mota ta takira Zuhura, riging har uku bata dauka ba, seta kara gwadawa ko zata dauka
bayan tafuto daga wanka taji wayarta na kara, hakan yasa ta nufi gurin wayar, ganin Inna ce ke kiranta yasa tadauka da sauri tana fadin "aunty ina kwana" "lafiya lau Zuhura, gwaggo Larai ce ta rasu" "inalillahi wainna ilaihi rajiun aunty yaushe" "jiya da daddare, amma ko kaita ma ba'ayi ba yanzu nima natafi" "Allah yajikanta, bara yaya Ahmad yatashi nafadamai ko ze kawoni" "ko kuma kibari kawai se uku kya zo" "ah ah aunty nasan baze hanani ba, kuma aunty inason nazo dan muyi magana" "kinga indai maganar auren mijinki ne nasani" "oh aunty kinsani" "to menene akanki akafara kara aure" "to anty amma" katseta Inna tayi tace "kinga dan Allah ki kyale ni, sekinzo kawai" daga haka Inna takashe wayar, a gaggauce tashirya sanadiyar yau ta makara bata tashi dawuri ba, gashi har 8:00pm tayi, tana gama shirya wa tafuce, danta hadamusu breakfast kafun su tashi, saukowa tayi falourn, tsayawa tayi cak tana kallon su, Ahmad ne ke breakfast, itakuma Nafeesa tana zaune tana kallonshi, suna hira, karasawa tayi tace "ina kwanan ku" Ahmad ne kawai ya amsa yace "lafiya kintashi" "eh" tafada tana wucewa kitchen, kanta tashiga hadawa breakfast, bayan tagama taci abinta a kitchen din, seda tagama kana tafuto, basa falourn da alama yagama sun shige ciki, zama tayi kan kujera tana kallo, ba jimawa Ahmad ya sauko cikin shirin futa office, itakuma tana rike da hannunsa, kallo daya tamusu ta dauke kai, "kai Sweet kayi kyau dayawa fa" kallonta yayi yace "to ai duk kece kika sa" dariya tayi me sauti kana tace "kasan ai inaji dakai" tafada suna kokarin fucewa, mikewa Zuhura tayi tace "yaya Ahmad inason zuwa kaduna" juyowa yayi rai a hade yace "me akeyi acan din" "dazu aunty takirani take fadamun gwaggo Larai ta rasu jiya" "to se akai yaya inkinje dawo da ita zakiyi" "yaya Ahmad kaine kuwa" "oh to waye, nidai nace ba inda zaki" daga haka yafuce, Nafeesa tabishi abaya, mamaki ne yacika Zuhura tayi mutuwar tsaye, tana tunanin anya yaya Ahmad dinta ne,
LONDON
9:30pm juyi kawai yake yakasa bacci, tunanin Zuhura kawai yake, dana auren Ahmad da aka ce yayi, kenan dama soyayyar dayake ma Zuhura karya ne, haka yadinga tunane tunane tuanane, dahaka har bacci yadaukeshi,
*********************
seda aka gama aka kai gwaggo Larai sannan driver yazo yadauki Inna, kowa mamaki ne yacikashi, ganin yadda suka koma, harda ma yaya Asabe, kuma ga yadda suke futo da kudi, da ance babu kaza sesu bada kudi, hakama Alhaji Aminu bayan ankaita an dawo, yabada dubu 50 ayi abincin zaman makoki, suma su Inna sun bayar da kuɗi, karfe 4:30pm Inna ta dawo gida, lokacin su Amira na shirin islamiyya, "aunty sannu da zuwa ya hakuri" Amira tafada lokacin da Inna ke zama saman kujera, "yawwa Amira da godiya" "aunty bara muwuce islamiyya lokaci har ya kure ma" "to sekun dawo aunta na" "to aunty" Halifa yafada suna fucewa,
komawa tayi ta zauna, saman kujera tana tunanin sauyawar yaya Ahmad dinta, Nafeesa ce tashigo flourn, ta nemi guri ta zauna tana daukan remote, ta canja tasha, takai ta wakokin naija, ita dai Zuhura shiru tayi batace komai ba, kallonta Nafeesa tayi tace "ke tashi kije ki dora abincin rana" "ai na dauka ke zakiyi tunda naga ke kikayi na safe" "ke ina magana kina magana dallah malama tashi kiyi abinda nace ko yanzu nan ranki ya baci" tashi Zuhura tayi tanufi kitchen, tsayawa kawai tayi takaici duk ya isheta, haka dai tayi girkin ba'a son ranta ba, bayan tagama tajera a dining, kana tawuce bedroom dinta, tana zuwa dakinta ta dau wayarta takira Inna, "hello aunty ya hakuri" "da godiya" "aunty na tambayi yaya Ahmad yace wai bazanzo ba" "to shikenan ai basekin zoba" "to amma dan Allah" "dan Allah bansan korafi tunda yace bazakizo ba to ki hakura" "shikenan" tafada ba ason ronta ba, bayan sungama waya, ta kwanta kawai, wayarta ce tayi kara, tajanyo ta, ganin sis Yasmeen yasa tayi saurin dauka, "hello Yasmeen ykk" "lafiya lau sister ya jin dadi" "komai Lafiya ya yaya Jawad" "yananan yanzu ma yafuta" "Muhsin yazo miki kuwa" "ai Muhsin bezo ba, kinsan yafara zuwa school shiyasa anzama manya" "ah ah lallai kam nima naso nakoma school dinnan" "ke kina amarya zaki fara school" "to ai angama amarci" "ah haba dai, ke kinsan kuwa yaya Ammar yatafi London " "London kuma aunty Aisha ta tafi ne" "eh ai tare suka tafi" "harda aunty Ilham din kenan" "ah ah aisun rabu" "me tayaya" "wlh tsautsayi yakamata tana lesbian" "what Yasmeen lesbian fa" "wlh kuwa ai ta cuci kanta dai" "tab Allah ya sawwake, kuma munyi waya da Mamy harda ma Hajiya amma duk basuyimin zancen ba" "to ai kinsan ba abunda za a dinga yaya dawa bane, ina amaryarki" "amarya kuma" "eh mana ba ance yaya Ahmad yayi aure ba" "tana nan tana falour" "oh manta ban yimiki ya hakuri ba naji anyimuku mutuwa" "oh da godiya" "yaushe zakizo kuwa" "kai gaskiya banajin zanzo" "toko dai angamu ne" "me din" "ciki mana" "ohh ni fadima rufamun asiri" "bakyaso ne" "uhmm ke dai kya haifa mana" "to ai shikenan" daga haka sukai sallama
bayan Ahmad yatashi daga office, yawuce gida, dan yaji labarin Ilham na gida, koda yaje samunta yayi, tana mopping, tsayawa kawai yayi yana kallonta dan yasan ko bedroom dinta sedai a gyara mata, "yaya Ahmad ina wuni" "lafiya lau zauna muyi magana" zama tayi ya kalleta yace "yanzu dan Allah Ilham me kikayi kenan" "dan Allah yaya Ahmad kabar maganar nan, wlh bansan ana fada ni kaina inajin kunyar abunda na aikata" "shikenan ai tunda har kin gane kuskuren ki" Mom ce tafuto, "ah Ahmad kaine" "eh Mom ina wuni" lafiya lau ta amsa tana zama, "ya matan naka" "sunanan kalau Mom" "nace yaushe zaka kawomun Zuhura ne nan ta wuni" "Mom ai zasuzo harda Nafeesa ma" "kaji nama zancen Nafeesa" "toh Mom ai dole tare zasuzo" "kaga nidai kawai ka kawomun Zuhura gobe ta wuni" "to Mom zansa driver yakawo ta" "au kai bazaka kawo taba" "Mom banda lokacin kawota ne" "yaya nima inason naganta don na muzguna mata lokacin muna gidan Mamy" "Mom bara na wuce kawai" "to a sauka lafiya" daga haka yamike yafuce, kallon Ilham Mom tayi tace "nikam se nake ga kamar Ahmad ya sauya ko" "saboda me kika ce haka Mom" "naga yacca yakeson yarinyar nan Zuhura amma har ince yakawota, yace bashi da lokaci" "to Mom watakila dagaske bashi da lokaci" "to Allah ya sawwake"
bayan tayi sallar magariba, ta sauko, bakowa a falourn, amma yayi kaca kaca, ledojin alawa da chocolate birjik a falourn, gyaran falourn tashigayi, yayi tsaf ta kunna turaren wuta, bayan tagama ta nemi guri ta zauna, Ahmad ne yashigo falourn, tana ganinshi, ta mike tana nufarsa, saurin dakatar da ita yayi dacewa "kinga bana bukata" yafada fuskarsa a hade, Nafeesa ce ta futo, sanye da riga da wando, kanta ko dan kwali babu, yasha gashin doki, tanufo Ahmad tana fadin "sweet ashe kadawo" janyo ta yayi jikinsa yana fadin "nayi kewarki fa" "nima haka, muje nama wanka" "gaskiya kam ina bukata" daga haka suka wuce rungume da juna, baki sake Zuhura tabisu da ido, batai aune ba taji hawaye yafara wanke mata fuska, kukan bakin ciki tafara, tana