Showing 72001 words to 75000 words out of 84568 words

Chapter 25 - SOYAYYA DA IZZA complete hausa novel

Mrs KD   

25 Aug 2024

21464

asibiti" "ai abun hawa ba wuya duk gasunan kofar gida" kudi Inna taciro himili guda tamika mai tace "kadauke ta ka kaita asibiti zamu dawo mu kara ganin jikin nata a asibitin" "to angama" daga haka yafuce, suma mikewa sukai suna yima gwaggo Larai sallama, suka ce mata zasu dawo su duba jikin nata, godiya ta dunga musu har da kuka, sudai daga haka suka fuce, gidan su Maryam suka nufa kamar yadda Zuhura ta roka, bayan sun isa sukayi parking a kofar gida, kana suka futo suka shiga, Umman Maryam ce kawai tsakar tana wanki, sallama sukai, ta dago kai ta amsa, kam ta kame tana kallon su, kana tace, "Inna Zuhura" amsawa Inna tayi tana karasawa kusa da ita suma hakan sukai, Maryam Umma tashi ga kwala ma kira, amsa wa daga daki, tana futowa, tsayawa tayi tana kallonsu, aikam da gudu ta nufi Zuhura ta rungume ta tana tsalle, "wayyo Zuhura kece" "nice Maryam" "cikata ki dauko musu tabarma su zauna" "to Umma" daga haka tashiga daki ta dauko tabarma ta shimfida musu suka zauna, "kukam ina kuka shiga Innar Zuhura" labari Inna ta basu, sukai mamaki da irin karamcin su Abba da Mamy, "dama haryanzu akwai mutane masu taimako haka" Umman Maryam tafada "wlh kam yanzu yadda duniya ta baci, sedai kawai Allah ya biyasu" Asabe tafada, suka amsa da ameen, "Maryam ya karatu" "Inna munanan munayi har mun kusa gamawa ma" "kice dai tare kuke tafiya da Zuhura" "Amira kin garma dayawa harkin mafi Zuhura" Maryam tafada tana kallon Amira, "am ansa bikin Zuhura fa" kallon Inna sukai su duka, "kwarai kuwa ansa bikinta tana kammala makaranta da sati guda za ai" "to Masha Allah" "Maryam yaushe zakizo" Zuhura tafada tana kallon Maryam "zanzo inshallah kibani number ki nasa a wayar Umma sena kiraki lokacin dazanzo" "sedai kibani number Umma ni ba waya a hannu na" "to bara na rubuta miki" daga haka tamike tadauko biro da takarda ta rubuta mata tabata, basu jimaba sukai masu sallama, har bakin mota suka rakasu , seda suka tafi kana suka koma gida, "to hankali ya kwanta yau kinga Zuhura" "wlh Umma bikiji dadin danajj ba, kullum se nayi tunaninta" "Allah me iko kalli daular dasuke ciki" "wlh kuwa Umma ai na kara tabbatar wa duniya ba a bakin komai take ba" "kwarai kuwa ba irin wulakancin da basu gani ba gurin yan uwa yanzu kuwa kallesu" "ai Umma duk me hakuri yana tare da sauki


bayan sun isa gida, Inna tace da me aikinta takawo musu abincin data shirya, ita dai Asabe baki kawai tasaki tana kallon gidan da abubuwan da aka kayatashi, abinci aka fara jerewa kan dining kala kala, bayan angama, Inna tace musu suzo suci abinci, ita dai Asabe baki bude ta tashi, tana tunanin 'wai duk gidannan na kanwarta ne Habiba, ashe muma lokacin jin dadinmu yayi' Inna ce takatse ta dacewa "yaya ki zauna mama" bayan ta zauna Inna tace Zuhura tayi serving dinsu, suka fara ci, Zuhura ce takalli Inna tace "Inna wai ina Yasmeen ne" "taje makaranta yau tace se 6 zata dawo" "tab suna dadewa gaskiya" bayan sun kammala Inna takai yaya Asabe daki tace tayi wanka, tabata kaya, koda tashiga banɗakin rasa ina zata taba tayi, haka dai ta dinga jangwale jangwale harta tabo fanfo, taga ruwa yafara zuwa, aikam tayi wanka tafuto, tadau kayan da ta ajiye mata tasa, kana tafuto, kallonta sukai Zuhura tace "kai ammafa kinyi kyau" "bansan shakiyanci" tafada tana zama, haka suka cigaba da hirarsu, har Yasmeen ta dawo, ta taddasu, kallon yaya Asabe tayi tace "lah aunty me kama dake" dariya sukai su duka kana Inna tace "ai yaya tace Yasmeen" gaisheta tayi kana tawuce dakinta, nan suka cigaba da hirarsu,

7:00pm nayi Inna tace da Zuhura ta tashi ta tafi driver ya kaita, haka dai ta tashi ba'a son ranta ba, saboda sunata hira da Yasmeen, haka ta tashi, suka rakata har bakin mota, driver yatafi kaita, bayan ya ajiyeta tashiga gidan, duk suna four, da sallama tashiga, duk suka amsa mata, jikin Hajiya tafada tana fadin "washh nagaji" kallonta Hajiya tayi tace "kiji sekace wacce tayi daka" "kai Hajiya bazakicemun sannu ba" "wa, toke a haka za ai auren, karfa kidinga sa jikana aiki" kunyace tasata mikewa tana fadin "Mamy nadawo" "sannu jeki huta" hango Jummai tayi cikin kitchen hakan yasa ta nufi kitchen din, ganin ta dukufa aiki yasa Zuhura taje bayanta, ta tafa hannayenta tana fadin "ga dodo nan" juyowa Jummai tayi tace "lallai ma yarinya wannan abunne ze tsoratani" "kai aunty Jummai" "ashe kindawo" "eh yanzu nadawo" "oh to kije ki huta" daga haka Zuhura tawuce dakinta, tana zuwa tafada toilet, tayo wanka, tafuto tasa kayan bacci, a gajiye take hakan ne yasa ta kwanta yau dawuri,


karfe 8:00pm yadawo, lokacin Ilham tana falour a kwance tana chatting, sallama yayi ciki ciki, wanda ko agurin kake koda ba abunda kakeyi bazakaji ba, zama yayi kan kujera, kallonta yayi yaga bama tasan yashigo ba, jitai kamar motsin mutum hakan yasa ta dago, ganinsa tayi a zaune, aikam da sauri ta ajiye wayar, tana fadin "kadawo" kallonta yayi yace "waike biki iya yiwa mutum sannu da zuwa ba, na dade ina tara ki" baki ta zumbura gaba tace "Allah yabaka hakuri" "jeki kawomun abinci" sosa keya tafara tace "kayi hakuri banyi ba" tsaki yaja ya tashi ya haye sama, "alhamdulillah" tafada kana takoma ta kwanta, yana shiga yashiga toilet yayi wanka yafuto yayi shirin bacci, kan bed din ya kwanta, kana yadau wayarsa, yafara duba sakonnin da aka mai,












💞SOYAYYA DA IZZA 💞





Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)





Ina masu bibiyar books dina😃to ina muku albishir da sabon book dina😁dana fara rubutawa✍️✍️ me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan😇dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu🤣zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa😍ina alfahari daku🤩 masoyana😍 kune kwarin gwuiwa ta😀i love you so much❤💔my pans😘



ina godiya da addu'o'in ku🙏🙏🙏
dayacce kuke yabon book dina💅💅 duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu😂😂

nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku😀😀








DOMIN SHIGA GROUP DIN SOYAYYA DA IZZA KA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇



https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx






DUK ME BUKATAR SOYAYYA DA IZZA YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA👇👇👇👇👇



https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J







page 47






_______________________________________________________________________
_____________________________

______________Haka rayuwa tacigaba da tafiya, Zuhura nata zana exam dinta, hankalinta kwance, Inna kam tasa Alhaji Aminu yasiyawa yaya Asabe gida me kyau, harta tare aciki, mijinta kam dan Jummai kullum yana can, dakyar take korashi yatafi, Inna kam tafara harkar business, inda Alhaji Aminu yabude mata shago yamata odar na kaya atamfofi lesika mayafai jakankuna, shaddodi, da takalma, dama sauran abubuwa, hakan yasa take gudanar da kasuwancin ta ita da yayar ta Asabe, gwaggo Larai kuwa in banda nadama da takaicin abunda ta aikata ba abunda takeyi, suna yawan kaimata ziyara duk da andawo da ita gida, ta warke,
soyayyar Yasmeen da Jawad tayi karfi, dan har taje gaban iyayensu, kuma sunji dadin haka, hakan ne yasa Daddy din Yasmeen ya roki a hade bikin Yasmeen dana Zuhura ayi tare, aikam kowa ya gamsu da shawarar tasa, hakan yasa aka tsaida maganar, za a hadesu gabadaya, ayi,
shikam Ahmad jiyake ya matsu yaga an daura musu aure da Zuhura, yama manta da batun Mom dinsa batasan auren, tun ranar da Nafeesa ta fadi magana mara dadi a kan Zuhura, be kara nemanta ba, kota kirashi baya dauka, yamaida hankalinsa kan aikin sa,

Ilham ta rasa me zatayi, dan tun ranar dasukayi waya da Feenat basu karayi ba, hakan yasa gaba daya tafuta hayyacinta, dan ji take kota yaya setayi less, amma ba hanyar futa sam, hakan yasa ta hakura ta cigaba da zama, sedai kullum ta dinga kallon video na less ,

Ammar kam tunda satin bikin Zuhura yakama, yakejin faduwar gaba, shikansa ya rasa me yasa, amma seya ta'alaka shi da soyayyar dayake mata ne, dan haryanzu soyayyar yarinyar ko gezau batayi ba daga cikin zuciyarsa, sema karuwa datayi, hakan yasa kullum tunaninta yake, danshi mantawa yake da Ilham, duk da suna gida daya, tun lokacin daya gane bata iya girki ba, yama dena mata maganar tabashi abinci, banagaren gyaran gida kuwa, Mamy tasa ankawo mata yar aiki, dan har dakin sa yar aiki ce ke gyarawa,



yau kwanan Zuhura 3 da kammala secondary dinta, tana gida suna shirye-shiryen biki, dan har ankawo lefe, hakan yasa Mamy gyara yar tata tun lokacin, Hajiya ma nata yimata turaren jiki kala kala, Maryam tana zuwa gurin Zuhura sosai suna tattaunawa game da bikin, lokacin kawo lefe ma Umman Maryam tazo, dayake su Mamy ne ma suka bada lefen, dan Mom din Ahmad tace bawanda zeje a danginta, lokacin kawo lefe, Ahmad ya hado da waya iPhone 13 a ka bawa Zuhura, dan haka suna waya sosai suna chat, hakama Maryam suna waya da Zuhura kullum, soyayyar Ahmad na karuwa a zuciyar Zuhura, amma duk lokacin data tuna da Mom dinsa batasonta setaji bata sha'awar aurensa ma, haka dai aka cigaba da hidimar shirye-shiryen biki, kowa yaga Ammar seyace ya rame, yayi niyyar ya tafi kasar waje sekuma yatuna da aikinsa, dan yanajin baze iya jure ganin Zuhura a matsayin matar Ahmad ba,

Mommy din Nafeesa ta dawo daga kasar waje, Nafeesa ta gaya mata komai daya faru, hakan ne yasa suka fara shirin yadda zasu janyo hankalin Ahmad yadawo Nafeesa ta aureshi
*********************************************

yau asabar, yau ake daura auren Zuhura da Ahmad, kuma ake daura auren Jawad da Yasmeen, bayan dinner din da aka sha har na kwana biyu, a gurin daurin aure bakin Ahmad har kunne, yakasa rufeshi, shikam Ammar fuskarsa a tamke, ba annuri, danji yake kirjinsa namasa suya, sanin halin abokin nasa yasa Ahmad be damu da rashin fara'arsa ba,

a gida kam, anata gudanar da biki, Zuhura tasha, leshi fari da adon golden, kana kallonta kasan amarya ce, dan ta kara kyau, fatarta tayi subul abar sha'awa, ga gyaran jikin da aunty Aisha ke mata kullum, hakan ne yasa takoma tamkar wata sarauniya, duk inda ta gifta seta bar kamshinta agurin, haka aka dauro aure aka dawo, aka dinga hotuna, banda Ammar dayashige part dinsa, ya kulle, haka aka dinga nishadi, har akai aka gama ba kafar Mom din Ahmad, da danginta, itama Ilham dandai Mamy ta matsa mata tazo ne shi yasa tazo, amma ba a son ranta ba, haka aka gudanar da yini, inda akai agidan Mamy, har Yasmeen amarya ma nan tazo akai komai, se karfe 7:30pm aka fara shirye-shiryen kai amare gidansu, itakam Zuhura da za a kaita Abuja, Booking din jirgi Ahmad yamusu, bayan anshirya amare cikin lifaya me adon ja, se baza kamshi suke, suka futo, masu kai Yasmeen duk suka shiga mota, ita dama Zuhura daga ita se mijinta zasu tafi, sanadiyar dare, kuma jirgi ne, bayan anfuto da ita, ta kamkame Mamy tana kuka, Mamy nata rarrashinta, hakanan taje ta rungume Hajiya tana kuka, Hajiya ma rarrashinta tashigayi tana fadin "haba fadima kiyi hakuri kowa haka akaimai, kuma karki damu zanzo har inda kike kinji" bata iya magana ba sedai ta gyadamata kai, ganin Zuhura na kuka yasa Nadra ma tafara share hawaye, aikam dasauri Zuhura tanufeta tana rungume ta, cikin shashshekar kuka tace, "Mamy dan Allah mutafi tare da Nadra" "ah ah se daga baya zan kawo miki ita dakaina" hakan yasa tacikata tana share hawaye, daga mota Ahmad na kallosu, haka dai har aka sata amota, Muhsin ne yatuka su, bayan yakaisu airport, shima sukai sallama, nan ma da kuka, suka rabu, basu jima dazama cikin jirgin ba, yatashi, bata dena kuka ba, shikam se rarrashinta yake, ta kwantar da kanta kan kafadarsa,

bayan sun sauka, driver yazo yadaukesu, gida suka wuce, bayan sun isa gidan, suka futo, rike da hannun juna, cikin falourn suka shiga, Mom ce kawai a falourn se wata yar aiki dake mata tausa a kafarta, sallama sukai, ta amsa kasa kasa, karasawa sukai suka zauna kan carpet, ita dai Zuhura sunkuyar dakanta tayi, "Mom ina yini" bata amsa ba, itama Zuhura tace "ina yini" nan ma bata amsa ba, Zuhura bata damuba dama batai tsamanin zata amsa ba, "Mom ga matata yau an daura mana aure" daga mai hannu tayi kan ya idda karasawa tace "kaga tashi kadau keta ku fuce mun, kuma kada ka sake kawomun ita gidannan" jiki a sanyaye yamike, itama tamike, suka fuce, motarsa suka shiga, ya tayar suka wuce, tunda suka fara tafiya ba wanda yace komai, harseda suka zo bakin gate din gidan nasa, ya kalleta, yace "kiyi hakuri queen" "ba kamun komai ba hakama Mom banga laifin taba" numfashi yasauke, kana ya kamo hannunta ya damke cikin nashi, me gadi ne ya bude musu gate, ya shiga, ya nemi parking space, yayi parking, kana yabude mota ya futo, itama yabude mata tafuto, shiga ciki sukai, falourn ya hadu sosai, zama sukai a falourn, shima ya zauna, yana kallonta, yace "queen shikenan kin zama tawa" murmushi kawai tayi ta sunkuyar dakai, "muje muyi alwala muyi sallah ko" yafada yana mikewa, itama tamike, suka haye saman benen dake falourn, bayan sun shiga, ya fada toilet yayo alwala, ya kalleta yace "kije kiyi alwala" mikewa tayi tashiga toileta din, tun kafun su taso daga kaduna, takejin kamar period dinta yazo, kuma dama lokacin yinta yayi, hakan yasa tana dubawa taga tafara period, hakan ne yasa batai alwalar ba tafuto, kallonta yayi yace, "baki alawalar bane" sunkuyar da kai tayi tace "banayin sallah" beja maganar ba yace "ok" hakan yasa shi yayi sallarsa, tana zaune bakin gado tana kallonsa, seda yagama yayi addu'a, kana yamike, yasauka kitchen, yazubo masu kajin daya siyo a plate, yadawo yazauna kusa da ita yace "sauko kici nasan kinajin yunwa" batai musu ba ta sauko ta zauna, saitin bakinta yakaimata naman, ta kawar dakai, yace "oh bazaki bari na baki da kaina ba" gyada mai kai tayi alamar ah ah, "to ai shikenan tun da baki son nabaki" haka suka dinga ci, yana kallonta, itakam kadan taci taji ya isheta, tadauke hannu, kallonta yayi yace "mekenan" "ya isheni" "kinason namiki dura ko" "ah ah" "to ki kara" "nakoshi fa cikina namun ciwo" "ok to nima nakoshi" "saboda me" "saboda ke mana" murmushi kawai tayi, yace "nan ne dakinki" "tom" "kitashi kiyi shirin bacci, zanje dakina nima nayi wanka" mikewa tayi tashiga toilet din, shikuma yamike yafuce, dakinsa yanufa bayan ya shiga ya fada toilet yayo wanka, kana yazo yayi shirin bacci, turarrukansa ya feshe jikinsa dashi, kana yabude kofa yafuce, bayan tafuto daga wanka, tabude akwatin kayanta, tadau rigar barci doguwa, me santsi, tasa turo kofar yayi yashigo, tajuya ta kalleshi, kana ta sunkuyar dakai, saman bed din yahau ya kwanta, yakalleta yace "zonan" jitai gabanta yafadi, ta taka a hankali harta isa gurinsa, kamo hannunta yayi, tafada saman kirjinsa, ya kalleta yace "muyi bacci nasan kin gaji sosai" kokarin zamewa take, ya matse ta yaja musu blanket, ya rufe idanuwansa, hannunsa nakan mararta yana shafawa, dahaka har barci yadaukeshi, itakam ta kasa samun bacci, saboda jinta a bakon yanayin da bata taba kasancewa ba, dahaka har barawo bacci yasaceta,


se dasafe, su Mamy, suka ga Ammar yafuto daga part dinsa, kowa ya bishi da kallo, karasowa yayi yana fadin "Abba ina kwanan ku" amsawa sukai, Mamy tace "wai dama tun jiya kana ciki baka tafi gida ba" "eh Mamy bacci ne ya dauke ni" "to shikenan zokai breakfast" "no Mamy zanje office ne" "to dan zakaje office shine bazakai breakfast ba" Hajiya tafada tana kallonsa "Hajiya banajin yunwa ne" "to ai shikenan" daga haka yamusu sallama yafuce, office yanufa kai tsaye, koda yaje be iyi aiki ba, ya zauna kawai yana tunane tunane,

Yasmeen ce da Jawad cikin kitchen suna hadawa kansu breakfast, ita tana soya dankali, shikuma yana feraye dankalin, a hankali kamar me tsoronsa, kallonshi Yasmeen tayi tace "haba jarumina yada haka kake tsoron wuka" "niba tsoronta nakeba, kinsan ance komai zakayi kayi a nutse" "gaskiya kam" tafada tana dariya, tare suka kammala suka jera saman dining, kana suka zauna sunaci, cikin soyayya

da asuba daya tashi be tashe taba, sanadiyar tace mai bata sallah, seda yayi sallar sa kana yakoma ya kwanta yakara janta jikinsa, ya rufesu da blanket, hasken daya futo ta window ne yasa tabude idanunta a hankali, kallonshi tayi dayake bacci, hannayensa duka ya kamkameta, zamewa tayi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login