Showing 36001 words to 39000 words out of 84568 words

Chapter 13 - SOYAYYA DA IZZA complete hausa novel

Mrs KD   

25 Aug 2024

21478

yayi kana yafuto daga motar, Muhsin ne ya hangoshi, seda yakarso, har inda take zaune yace, gimbiya barka da hutawa, kallon su Walida tayi tace, "zamu tafi gida se gobe"ok to Allah yakaimu"Nadra muje" hannun Nadra takama su nufi gurin mota, kafun takai har yayi sauri ya isa yabude mata gidan gaba, batai musu ba tashige, Muhsin kuma yashiga baya shi da Nadra, kallonta yayi tace, gimbiyata ya school din"?"Alhamdulillah" abunda tafada kenan, "yaya Ahmad wai ina zaka kabiyo kadauke mu" kamar ya se zani wani gu zanzo in daukeku" to naga baka taba zuwa ka daukemuba" to yau gashi nazo" daga haka ba wanda yasake magana, harsukazo gida, bayan yayi parking su Muhsin suka futo shida Nadra, itama kofar tabude danta fita taji yariko hannunta, juyowa tayi takalleshi, shima kallonta yayi yace, "my queen kamar kina fushi dani ko"? "ah ah banajin haushinka to damme yasa ma zanji haushinka, kawai nagaji ne" kin tabbata"eh" kumatunta yashafa kana yabude mata murfin motar, futa tayi, shima futowa yayi shima, tana shiga falour bakowa hakan yasa tashige dakinsu, nan ma bata ga kowaba, jakarta ta ajiye tafuta, kitchen tashiga, tana shiga taga Mamy da Hajiya ne kawai a kitchen din, sallama tayi , dukansu suka juyo suka kalleta "Mamy mundawo" to sannunku da dawowa" Hajiya mundawo" sannunku ya gajiya" Hajiya aikam da gajiya" kije ki watsa ruwa kizo kici abinci" Hajiya me kike dafa mana" dan wake nake jefamana ai kinaci ko" aikam inaci sosai" yawwa to jeki kiyi wanka kizo nazuba miki kici" Mamy ina Inna"? tayi bako ne yanzu zata dawo" tom bara naje nayi wanka" daga haka tafuce, wanka tayi tashirya kana tafuto, bayan tafuto ne ta tadda Hajiya kan dining, itama zama tayi tana fadin"Hajiya harkin gama" nagama Zuhura bara nazubamiki" plate tadauka tazuba mata tasa mata komai nahadin har kwai, bayan tazubamata ne tamukamata, karba tayi tafaraci tana fadin"kai Hajiya ta kinfi kowa iya dan wake" dariya tayi tace"karfa kifadi garin santi" Allah hajiya ba santi bane" haka suka cigaba daci suna hirarsu, Ammar ne yafuto daga part dinsa, dan yanzu yafarajin yunwa, dan coffee din da Ilham takawomai yakasa sha ba daɗi ga daci, ganinsu yayi zaune kan dining sunacin abinci sunta hira suna dariya, karasowa yayi inda suke yana fadin, "Hajiya me kuke ci haka" abincin mu mana" abincinku kuma" eh mana tunda ku bakwa ciba" ah nikam banaci" to ai shikenan" ke jeki hadamun coffee nasha" yafada yana zama, mikewa tayi danta taje ta hadamai, Hajiya ce takalleta tace "zauna ki karasa ci seki hadamai" kallonshi tayi, "Hajiya banfa karya ba" to kuma se akace ka tasheta tana cin abincinta" to Hajiya in ta dawo baseta karasaba" to kai ina matar taka kaje kace mana tahadama wato ita tanacan yar hutu bat iya komai ba" Hajiya nidai kibari kawai dan Allah taje ta hadamun ta dawo" aikuwa seta gama ci zauna ki karasa" zama tayi tacigaba da cin abincinta, seda tagama tas kana ta tashi tanufi kitchen tahadamai, takawo mai, karba yayi yafara sha , Hajiya bara naje nagyara miki dakinki kafun time din islamiyya yayi" bazaki hutaba kindawo kin gaji" ah ah ai nariga na huta" daga haka tashige, tayi hakan ne sabida batasan zama a gurin,



💞 SOYAYYA DA IZZA 💞



Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)

Yar amanar jajirtattu💪💪

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

page 27

__________________Gyaran dakin hajiya tashigayi, tagyara shi tas ta kunna turaren wuta, bayan tagama ta wanke mata toilet, seda tagama tas tafuto lokacin 3:30 har tayi, tana futowa suka ci karo da Ilham , kallonta tayi tace, "ke baki da hankali ko"? "dan Allah aunty Ilham kiyi hakuri banganiba" "karya kike ai yanzu ganin kike ni dake dayane ko saboda yaya Ahmad yace yanasonki, to bara kiji nafadamiki kifuta sabgarshi dan wlh bazamu taba bari ya aurekiba idan kuwa kika ki zakisha bakar wuya" daga haka tawuce tabarta agurin, ita kam Zuhura bata bi ta kantaba itama tashige ta tafi, tana shiga dakinsu tasamu Inna da Mamy a dakin, sallama tayi, amsawa sukai, kana tashiga ciki, "Inna tundazu nadawo bangankiba"? "to sannu da dawowa " Zuhura maza ki shirya kuwuce islamiyya kinga hudu ta kusa" tom" daga haka tashige toilet, Mamy ce taci gaba da cewa, to ke aganiniki yaushe yakamata ayi" aini banida ta cewa ko yaushe ma" to bazaki sanar da yan uwanki ba" ni bani da wasu yan uwa yanzu, yaya tace kawai taragemun, idan nayi auren zanje gurinta" tom shikenan Alhaji seyamiki wakili" to Allah kasa mudace"ammen" daga haka Mamy ta futa, Zuhura ce tafuto daga toilet, kallonta Inna tayi tace Zuhura zanyi magana dake " to Inna yanzu zanyi sallah na shirya islamiyya" to inkin dawo zamui magana "tom" daga haka ta tada sallah, bayan ta idar ta dauko unifom dinta dinkin riga da wando light blue se hijabi har gasa , fotowa tayi ta tadda su Nadra sun shirya, dukansu suna falour, a zaune, Mamy ce tace kutashi ku wuce mana gatanan tashirya, tom daga haka suka tashi, futa sukai, Bala driver ne yakaisu, ajin wadanda zasuyi sauka nan gaba aka kaita, tunda ammata interview kuma ta iya , hakanne yasa aka kaita ajin, izufinsu talatin, bata sha wuya ba saboda ta iya, sababbin kawaye tayi A'isha da fatima, suma sunada kokari, tun zuwanta malamansu suka gane tana da kokari, hakan yasa dukan malaman suke sonta,

Mamy ce takalli Ilham tace, "Ilham ranar friday zamuje mu hada lefenki, seki shirya mutafi tare, ki zabi Abinda kike so" tom Mamy" Ammar ne yamike yawuce part dinsa, Hajiya ce ta kallesa tayi tsaki tace"kamar gaske waishi jan aji" dariya sukai su duka, hajiya "na'am" ranar asabar za a daura auren Innar Zuhura da Alhaji aminu" eh haka Usman yake fadamun, to Allah dai yasanya alkhairi" " Mamy Innar Zuhura aure zatai"? "eh saurama kwana 3 shiyasa ma nace miki friday zamuje hada lefenki saboda itama zan siyo mata kaya" tabbb" abunda Ilham tafada kenan, sukam su Ahmad haka sukace "Allah yasanya alkhairi" ameen" Mamy tafada,
yana shiga dakinshi yazauna ya dafe kanshi gabadaya ya tsani aurennan da zasu mai, shi yanzu ma taya zeyi rayuwa da Ilham, jiyay gaba daya rayuwar ta dena mai dadi.

"wlh gwogwgo Larai bamusan inda suke ba damunsani ai da zamu fada miki" "ba waninan idanma kunsan inda take kuki fada to wlh kusani kar nake kallonku" haba gwaggo Larai mu kanmu munasan mugansu ba neman da bimu musuba amma bamu gansu ba" "ke dallah yimin shiru ba bakinku daya da Zuhuran ba ai kawarkice" "maryam kada ki sake magana" amma umma" nace kada ki sake magana" gwaggo Larai kiyi hakuri kije mudai bamusan inda suke ba" zaku sanine idan ma kunsani kukaki fada, zanje gidan yayar Habiban yanzu ai ita tafadamun" daga haka tafuce, Maryam ce takalli ummanta tace, "kiji fa Umma tun a mutuwar da aka ce sukoma gidanta ki tayi fa" uhmm ai yanzu tunani take ko ya bar wani abu tazo takarbe tayi gaba" Allah sarki Zuhura wlh nayi kewarki Allah dai yakara hadamu kuma Allah yasa kuna hannu nagari"ammeen"

Mamy ce tafuto falour tana fadin "nikam azo a daukomun yarannan gashinan hadari ya hado kuma da alama ze zubar da ruwa" aikam Bala driver sun futa da Abba" Ilham tafada "Ina Ahmad ne"? "shima ai yafuta" bara nasa Ammar yazo ya daukosu" wayar ta tadauka takirashi "hello Ammar zo falour ina san ganinka" amsawa yayi da to, ita kuma ta kashe wayar, tashi yayi daga kwamciyar da yake, futowa yayi, tarar da ita yayi a falour, zama yayi yana fadin "Mamy gani" "yarannan zaka daukomun kaga har 6:30 tayi ga kuma hadari" shiru yayi nadan mintuna kana yace to, tashi yayi ya yanufi hanyar part dinshi, "ya zaka koma kuma" "Mamy key din zan dauko" "ok to kayi sauri dan Allah" daga haka yashige, yana shiga yadau key din yafuto" yana shiga mota aka zuge da ruwa,

suna zaune kofar makarantar ita da Nadra sun dukunkune guridaya , shikam Muhsin ya nade hannayensa a kirjinsa, "yaya Muhsin kakira Mamy kace azo a daukemu" "to nabar wayata a gida da tuni ban kirasu ba" to mujira mu gani ai zasu zo ne" bata rufe bakiba yayi parking a kofar makarantar, ruwa ake sosai, hakan yasa be futo daga motar ba saboda idan ruwa yatabashi se yayi zazzaɓi, Muhsin ne yace "ga motar yaya Ammar nan" mikewa sukai gaba daya, motar suka nufa, Muhsin ne yabude gidan gaba yashiga sukuma suka shiga gidan baya, bawanda yayi magana acikinsu, motar yaja suka tafi, suma ganin ranshi a hade yasa basuce mai kala ba har suka iso gida, lokacin ruwa yayi karfi harda ma kankara, yanayin parking, Muhsin yabude ya futa da gudu, ita da Nadra suka bude, tana tsoron ruwa yatabata hakan yasa takasa futa daga rumfar parking space din, Nadra kam tuni ta falle da gudu ta shige, itama tafiya tafarayi hakan ruwan yana sauka akanta, lema yabude boot yadauko, be budetaba har seda yazo inda take kana yabude yakara mata, dago kai tayi takalleshi, lumshe mata ido kawai yayi, shima ba laifi ruwan yatabashi, ahaka har suka isa cikin gida, seda sukazo bakin falour ya ajiye lemar suka shiga ciki, shikam har ya fara rawar sanyi, yana shiga yawuce part dinsa, itama hanyar dakinsu tanufa, tana zuwa tahau cire kayanta da suka jike, bayan tacire tadauko wasu tasa riga da wando na sanyi masu laushi, lokacin magaruba har tayi, batai sallah ba kasancewar tana period, Inna ce tashigo dakin tana fadin"ashe kun dawo" eh Inna mundawo" yawwa to zoki zauna muyi magana, zama tayi, kallonta Inna tayi tace "Zuhura Abba ne yazomun da maganar abokinshi yana sona ze aureni, kuma kinga dai ni banace musu ah ah ba, amma sena cemusu inada ya'ya bazan iya aure ba natafi nabarsu ba, seya ce ze rikeku, amma Mamy tace baza'a dauke mata ke ba ,to yanzu dai cikin satinan za a daura aure" "to Inna ai ba komai Allah yasanya alkhairi" ameen" daga haka tamike tafuce, itama Zuhura futowa tayi, kitchen tashiga Mamy ce ke hada abincin dare, "Mamy sannu da aiki" yawwa Zuhura sannu amma dai ruwa be dakekuba ko" eh Mamy be dakemuba" yawwa to haka nakeso" Mamy ina hajiya" hajiya tana dakinta" bara naje gurinta" to sekin dawo" daga haka tafuce harda gudunta, jitai taci karo da mutum, dagowa tayi takalleshi, shima kallonta yayi yana cewa"my queen gudun me kikeyi haka" zumbura baki tayi tace "dakin hajiya zani" yacca tayi maganar ne yasa takashe mai jiki, hannunta yasa yariko kugunta tahadu da kirjinshi, yana fadin "my queen bakya nemana" kara zumbura baki tayi tana fadin "yaya Ahmad kacikani kar wani yaganmu"tsoron me kike yi badai aure zamu yi ba"Please yaya Ahmad nidai kacikani" hannunsa yasa ya tallafo fuskarta yana fadin"my queen kamar fa bakya sona ko"yaya Ahmad kabarni natafi dan Allah"ok to yimun" yafada yananunamata kumatunsa alamar tamai kiss, zaro mai ido tayi tana fadin "nidai bazan iyaba"ok to shikenan" yafada yana mata kiss a goshinta"ki kula dakanki" daga haka yasaketa yawuce, binshi tayi da kallo, gaba daya se taji jikinta ba dadi, batasan taga wani yabata rai a dalilinta, kuma musamman yaya Ahmad dake son sata farinciki, da wannan tunanin tawuce dakin hajiya.



💞 SOYAYYA DA IZZA 💞



Story and writing by Hadizatu✍️✍️

Mrs (KD)

Yar amanar jajirtattu💪💪

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

page 28

____________________Gaba daya ranshi ya baci, kullum kokari yake ya farantamata rai, amma ita ko ajikinta, wayarsa yadauko yayi dialing number nafisa, yana kira tadauka, "kina ina"? "ina club ɗin hotel din danake" "ok ganinan ki koma room" yana karasa fadin haka yakashe wayar, wani tsalle tayi tana fadin "ga Ahmad nan zezo yanzu nizan wuce kawai" Allah ah to kirikeshi kam in yazo" haka za ai" daga haka tadau jakarta tafuce, tashi yayi ya shirya, futa yayi yashiga motarshi yatafi, itakuma wanka ta karayi yafeshi jikinta da turare, yana zuwa beyi knocking ba dayake kofar abude take, tana jin karar kofa tafuto, ganinsa tai a tsaye, nufarshi tayi tana rungume shi, jiki ba kwari shima ya rungumeta, suna shiga yafada kan bed yakwanta, binshi tayi tana kwanciya kan kirjinshi, "kamar baka jin dadi" kai kawai ya kada mata alamar eh, hannunsa yasa yana janye rigar jikinta, yana shafata, hade bakinsu tayi tana tsotsarsa, tuni yafara mantawa da bacin ramshi,

tana shiga dakin Hajiya ta tadda ta tana ninkin kaya, sallama tayi tashiga, amsawa Hajiya tayi tana fadin "ashe kun dawo"? "eh Hajiya mundawo" ninki kike yi"? "eh wai kayannan nake ninkewa" to kawo natayaki" daga dawowarki dakin kyaleni nayi" ah ah Hajiya kawo natayaki" mikamata tayi tana fadin "yau ko me suke dafamana iyayen naki" bansani ba Hajiya" nifa sha'awar tuwo ma nake" tuwo kuma Hajiya"eh mana kin iya ne" ban iya ba ko sanda muke gida Inna ce takeyi" to aikam yau zaki koya" tashi muje muyi" tom" daga haka suka futa, su Inna suka tarar suna shirya abinci kan dining, "ah ah yau kuma me kuka mana" Hajiya Mandi rice ce se farfesun kayan ciki" tab kuci kayanku bara naje nayi tuwo" Hajiya dakin fada ai da nayi miki" Inna Zuhura tafada" ah ah ki huta zanje nayi" "am Zuhura jeki part din Ammar kice yazo yayi dinner naga tun dazu be futo ba ko masallaci yau banga yafuto ba shida baya sallah a gida" tom" daga haka tawuce, tana zuwa tayi knocking kofar falour jitai shiru, hakan yasa ta tura ta shiga, bakowa a falourn haka yasa ta nufi bedroom dinsa tura kofar tayi ta leka, ganoshi tayi kwance kan bed yarufa da blanket, shiga tai, ta tsaya nesa da gadon tana fadin, "yaya Ammar Mamy tana kiranka" shiru be amsaba, se rawar sanyi hakorinsa na haduwa, matsawa tayi kusa da shi tana fadin, "yaya Ammar meke damunka" be bata amsaba se dai rawar sanyin dayake takaru, matsawa tayi kusa dashi tana yaye blanket din daya rufa, idonshi yayi ja sosai, hannunta takai taba kuncinsa, zafi zau kamar garwashi "inalillahi yaya Ammar baka da lafiya ai" toilet tanufa, tadauko ruwa da tawul tafuto, "yaya Ammar tashi" kada mata kai kawai yake alamar ah ah, ganin baze iya tashiba yasa ta yaye blanket din tana kokarin dagoshi, amma ina takasa "yaya Ammar katashi" dakyar ya yunkura yatashi, tawul din ta tsoma cikin ruwan ta matse tasamai a gishinsa, lumshe ido yayi, cigaba da samai tawul din tayi, har a kirjinshi, dayake ba riga daga shi se trequater, seda tasamai ruwa sosai ajikinshi, sannan jikinshi yayi sanyi, bude ido yayi yana kallonta, itama kallonshi tayi tamai murmushi, hannunta yakama yakalli cikin idonta yace, "thanks" murmushi kawai tayi wanda shima yasa yayi murmuahin, "lah namanta Mamy ta aikoni wai kaje kayi lunch" drower yanunta mata da hannunsa yace "magani" dasauri tace ok tana nufar gurin, janyowa tayi taga magunguna tadebo mai, pridge tanufa tadauko mai ruwa rakowamai, nuna mata wanda zata ballo mai yayi, ta ballo mai tabashu, tana bashi tace "bara naje se na fadama Mamy" saurin rike hannunta yayi yana fadin "no karki gaya mata zata tada gankalinta" shike nan Allah yakara sauki"ameen" daga haka tafuce, tana zuwa ta tarar da Hajiya har ta gama tuwonta aikam tazauna suka ci, Mamy ce tazo tana fadin "Zuhura ina Ammar din"? "na kira shi yana zuwa" bata idda rufe bakiba yashigo falourn, kallonshi Mamy tayi tana fadin, "kalau kuwa kake naga yau baka futoba ga dinner ma angama" bakomai Mamy kawai dai bansan futowa ne" ok to kazo kayi dinner" no Mamy bazan iya cin komai ba , coffee kawai nakeso" ok to ga Zuhura nan tahadama" tom ta amsa tamike, hado mai tayi takawomai, amsa yayi batare daya kalle taba, sha yakeyi cikin nutsuwa, tana gama cin abinci ta takwashe kayan tabar gurin, tana zuwa dakinsu ta tarar da Inna dasu Amira da halifa harsun kwanta, itama kwanciyar tayi,

yau Nafisa duk sonta da Ahmad ya kasance ta yau seda tagaji, gashi yau kamar ba feeling yake mata, hakan yasa taji jiki sosai, tunda yazo yake abudaya, bashine ya kyaketaba se 3:00 na dare, aikam dakyar tamike, tashige toilet, shikam yajuya yafara bacci, datai wanka ma bata koma kan bed din seta kwanta saman kujera,

yau dawuri suka tafi school dayake Friday ne dawuri zasu dawo, tana zuwa ajin ta tarar da kawayenta duk sun zo, zama tayi suka fara gaisawa , daya ce tace, "Zuhura wai guy dianan dayazo daukanku yayanki ne"? "eh yaya nane" amma fa ya hadu " dayar tafada, murmushi kawai tayi azuciyarta tana fadin, 'tab da yaya Ammar kuka gani ma inaga to futa hayyacinku zakuyi' "salamu alaikum" salamar da akayi ne ya dawo da ita hayyacinta, su Islam ne suka amsa, kalon Zuhura yayi yace "bakuwa biki gabatar mana dakanki bafa" bata kallesbj ba kuma batai maganaba, dariya abokansa suka fara suna nuna shi, hakan yasa yakoma inda suke, yana zuwa suka fara cewa"angayamaka bazata kulakaba amma kaki yarda" wani tsaki yaja ta daji bencin dake gabansa, Walida ce takalleta tace "kai ammafa Zuhura kinburgeni" ai irin wa'yannan ba a tanka musu sedai amusy shiru" gaskiya dai kumafa shiru yafi ciwo" malami ne ya shigo gakan tasa sukai shiru,

wai yanaso ya leka hospital dan yaga meke wakana, hakan yasa yayi wankanshi ya shirya cikin shadda ash colour ba karamin kyau yayi ba yasa hularsa kakar kayan yafuto, a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login