Showing 45001 words to 48000 words out of 83661 words

Chapter 16 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11360

a garƙame.

Taja taja abin yaci tura ta buɗu ga ƙofar irin masu tsadar nan ne koka buga baza'ajiba.
Gashi babu spay key a hannunta zubewa tai a ƙasa har coffeen na ƙonata ta saka marayan kuka na baƙin cikin asarar juye maganinta datayi aciki ta jima tana kukan takaici kafin ta ɗauke kayan a zuciye tabar wajan tana jan ƙwafa aranta tana ayyana kodai ya fara dawowa hayyacin sane da alamun sesun sake upgrated na asirin su.

Ya jima yana watsawa fatar jikinsa ruwan ɗumin dayay masa daɗi sosai yaji gajiyar duk ta sake shi.
Bayan ya kammala wankan yayi brush ya fito tare da nufar wajan ƙofa ya murza key dan haka kurum yaji baya son hayaniya a wannan time ɗin,
Alwala ya ɗauro ya sanya jallabiya fara ƙal ya tayar da sallar isha'in dayay missing.
Bayan ya idar ya nufi wajan coffee machine ɗinsa ya haɗa iya wanda yake buƙata ya dawo saman sopa ya zauna yana kurɓa da zafi zafinsa gefen shi ya duba wayar shi nata ringing!
Duba yakai ga ƙaton agogon dake manne a bangon ɗakin kusan sha ɗayan dare tayi a wannan lokacin.
Duba yakai ga screen ɗin wayar hajja ɓaro ɓaro yagani nata yawo.
"Mayya ta"
Ya faɗa cike da ƙosawa a wannan karon ma bai ɗauki wayar ba harta katse sabida yana tunanin da kuɗin hajja take amfani wanda shike zuba mata duk sati cikin wayarta.
Ƙoƙarin tashi yake wani kiran ya ƙara shigowa.
Tsaki yaja kaɗan ya ƙi ɗagawa har seda ya aje cup ɗin dake hannunsa saman ɗan ƙaramin frij ɗin dake ɗakin ya komo ya kashe ƙwan ɗakin sannan ya ɗauki wayar ya ajeta saman gado.
Ya cire jallabiyan jikinsa yayi saura daga shi se singel faffaɗan kirjinshi na cikakkun maza ya bayyana kwance da baƙin gashi.
A nutse ya kwanta a saman gadon ya matse pillow a gefen shi ya tada kai da hannunshi na dama hannunshi na hagu kuma yake lalubar numbern hajja dashi.
Daga ɓangaren ummul wadda taketa juyi a saman gadon hajja ta kasa bacci hajja se mita take akan ta dameta da sukur sukur harta gaji tai bacci ta rabu da ita.
Wayar hajja ta ɗauko ta shiga kiransa har sau uku bai ɗaga ba wurgi tai da wayar tana turo bakinta gaba.
Wata zuciyar na ce mata ai yana can manne da matar sa a kirji wannan tunani seya hadda sa mata jin zazzafan kishin daya sanya ta kuka ta kife saman pillow tana faman kukan takaici.
Jin wayar na ringing! yasa ta goge hawayen ta ɗauka amman batai magana ba
"Assalamu Alaikum"
Dakakkiyar muryarshi mai cike da Amo!
Ta ratsa cikin dodon kunnenta.
Muryarta a dashe da alamun tai kuka tace.
"Amin wa'alaikassa salam"
Jimm shuru babu wanda yayi magana cikinsu tsayin daƙiƙu biyar kafin yace.
"Fisabilillahi nikam yau bazaki barni na huta ba ummi? kira de kira de wallahi kin hanani bacci me kike ke baki baccin ba?"
Yafaɗa daɗan daɗa kaɗan.
A wannan karon kuka ta saki na rashin dalili.
Shafo kwantacciyar sumar kirjinshi yayi tare da lumshe idanu yana jaddada rigimarta.
"To daman dan ki ɗagamin hankali yasa kika kirani da tsohon daren nan me akai maki kuma?"
Jin wannan furucin yasa taɗan rage sautin kukan tace masa.
"Wallahi bazaka sami kwanciyar hankali ba harse ka ɗaukeni anan in ba haka ba nikam zan ƙara gaba dan bazan zauna kusa da gidanmu ba kamaji da wai ehe"
Tafaɗa cike da rashin kunya.
"To naji ki bani nan da kwana uku sakarai"
Yafaɗa yana jimanta wautar yarinyar wani ƙululun baƙin cikin raping ɗin da wancan ɗan iskan yaron yayi mata yaji ya naushi zuciyarsa in banda rashin tausayi wannan ƴar yarinyar meta isa.
Tausayinta yaji ya kamashi cikin kwantar da murya yace.
"Kiyi addu'a ki kwanta dan Allah ba danni ba karki je ko ina ki bari har na dawo amman ki dena kirana ni zan dinga kiranki muna gaisawa"
Yafaɗa da ƙaramin sauti.
Cikin sakarcin ta na shagwaɓar data zama ado agareta tace masa.
"Amman inna jika shuru zan kira bye asuba tagari"
Tafaɗa tare da kashe wayar.
Murmushi ya sanya mai sauti tare da aje wayar agefen sa anya ma kwa a ƙuruciyar yarinyar nan tasan soyayya kodai shirmen tane

Sedai hasko girman zatin halittar jikinta dayay yasaka ya wani lashi leɓanshi tare da rungume pillow yana cewa.
"BA SON TA NAKE BA! TAUSAYI NE"
Ba jimawa da faɗim haka wani irin bacci mai cike da aminci ya kwashe shi batare daya shiryawa hakan ba...........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.


Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

33


Bai farka ba se da asubah bakinshi ɗauke da salati, tare da addu'ar farkawa daga bacci, ya sauke santala santalan ƙafafunshi Aƙasa yana jinsa saka yau duk babu wannan gajiyar ta jiya data kashe masa jikinsa.
Kai tsaye bathroom ɗinsa dake manne a cikin ɗakin ya shiga bayan ya kammala uzirin gabanshi ya ɗauro alwala jikinsa ɗaure da faffaɗan tawul se kanshi dake ɗigar da ruwa.
Ƙaramin tawul ya ɗauka ajikin ƙofa yana tsane ruwan kanshi ya ƙarasa gaban ƙaton madubin dake ɗakin ya ɗauki turare ya fesa ajikinsa kana ya nufi wadrobe ya ɗauki wani farin lallausan yadin kufta mai ɗinkin half body ya sanya ajikinsa.
Agurguje ya tayar da raka'atul fijir sannan ya fice a ɗakin ya nufi ɗakin basma ya buga mata bai jira tashin taba ya fita waje tare da mai gadinsa suka wuce cikin masallacin dake bakin layin.

Tunda tabar bakin ƙofar ɗakin Aliyu take rangaji Allah ne ya kaita ɗakinta lafiya kwalaban turaren dake shaƙe a saman madubin ta take watsar wa duk sun farfashe sun fasa mata ƙafafunta amman bata damu da jini da zafin dake zubo mata ba face ware gashin kanta datai wanda yaci uban saloon ta tsaya a gaban madubin tana maganganu ita ɗaya.
"Why Aliyu me nai maka da zakai min wannan horon tabbas jikina yana bani akwai abin da ze faru dani marar kyau sedai ko meye nasan bokana ze tare mini shi" ( wa'iyazubillahi )
Tafaɗa tana bubbuga kanta da madubin kamar zararra haka ta wanzu a wannan dare tana sumbatu gashi tana ta kiran layin hajiya mahaifiyarta yaƙi tafiya.
Haka ta koma ƙasan tiles tai zaman dirshan tana kuka kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa seda taji kanta ya fara ciwo sannan ta haƙura ta faɗa gado tai rubda ciki tana kukan dai wanda ahaka tayi bacci.
Cikin baccinta tai wani mafarki wanda ya sakata tashin dole acikin mafarkin taga wata farar mace mai tsaho amman ba can ba sedai ta saka mayafin daya rufe fuskarta wanda bata sheda kowa ce ba, seta ga matar tana nufota sedai koda tazo wajanta seta tarar da ita zaune da Aliyu gadan gadan matar wajan Aliyu ta nufa tana miƙa masa hannu da wani irin murmushi ya miƙa mata shima hannunsa ya rungumeta a zafafe basmah tai nufin shiga tsakanin su sedai wani ƙaton rami mai macizai aciki yay mata shamaki dasu domin datai yunƙurin binsu seta faɗa cikin wannan ramin wata irin ƙara ta saka wadda ita ta farkar da ita agigice duk ta haɗa uwar zufa.

Idan banda rawa babu abin da jikinta yake idanunta sunyi jajir ta sauka daga saman gadon wayar ta dake yashe a ƙasa ta ɗauka numbern sabon bokansu ta kira alokacin wajan ƙarfe uku da rabin dare, Duk da bokan bai taɓa ganin basma ba amman suna waya sosai da ita saƙone dai mamanta ke amso mata.

Ringing biyu ya ɗauka daga ɓarinsa maganganu ne da alamun aiki yake.
"Hajiya basmah sarkin kishi kece da wannan tsohon dare?"
Dayake sunan da yake gaya mata kenan sabida bata da wata buƙata a wajansa seta kar mijinta yayi mata kishiya kar mijinta yaje wajan iyayen sa ( mata aji tsoron Allah! )
"Uban ɗakina ba kanta ba wannan ba........"
Tas ta kwashe labarin mafarkin nata ta gaya masa daga karshe ta kece da kuka tana cewa.
"Dana ga ranar da Aliyu ze min kishiya gwara naga ranar mutuwar mahaifiyata" ( wa'iyazu billahi)
Taja fasali tare da ɗorawa.
"Kai min bincike wallahi idan mafarkina ya zama gaskiya sena kashe duk wadda take ƙoƙarin shiga gonata"
Tafaɗa tana jan majina.
Kecewa da dariya yayi tare da ɗaga ƙaton kaskon dake gabanshi yayi zanen sunan Aliyu wanda ada daga ya zana yake ganin hoton Aliyu muraran da halin da yake ciki sedai wannan lokacin ya zana yafi sau biyar baiga komai ba sedai yaga wani irin haske ya cika kaskon wanda har kashe masa ido hasken yake yi dan tsabar yadda ya haske shi.
Gumi ya yarfe ya kuma zaro duƙu-duƙun idanunsa hankali tashe yacewa basma.
"Nakasa ganin komai sema wani haske dake ƙoƙarin kashen idanuna, wanda nake tunanin addu'a ce wannan hasken duk yadda akai a yanzu mijin ki baya sakaci kamar da a wannan karon da wuya aiki mai ƙarfi ya shige shi a bincike ma ze kai kusan shekaru arba'in aiki bai taɓa shiba! sedai mu juya bala'in ga duk wadda tai gigin shiga rayuwarku semun salwantar semun zubda jini semun ɓatar!!!!"
Yafaɗa yana kecewa da wata jahilar dariya mai abin tsoro!.
Gaban basmah ne ya faɗi ta wani firfito da idanunta waje cikin firgici tace.
"Kana da tabbacin akwai yuwuwar ya ƙara aure?"
Tafaɗa cikin bugun zuciya!
Dariyar da yake ya taƙaita tare da ce mata.
"Ai in kinga mijin ki ya ƙara aure to sedai a ƙiyama domin mun masa aiki da mukulli wannan na gaya miki ne kawai amman banga yuwuwar auren shiba ki yarda dani domin bana ƙarya"
(Astagfirullahi)
Cikin yarda da maganar bokan nata tare da bashi gaskiya tace.
"Kana nufin mafarki ne kenan baze tabbata ba?"
Dariya yayi mai sauti.
"Baze taba aure ba! Baze taɓa Aure ba!!!
Yafaɗa yana mai katse wayar yabarta da baki sake.
Sedai maganganun daya gaya mata tare da bata tabbacin baze ƙara aure ba yasa hankalinta ya kwanta harta samu ta tattare kwalaban data yasar ta koma baccinta wanda bugun ƙofar shine ya tashe ta amai makon ta mike tai sallar.
Seta ƙara jan bargo ta rufa ta cigaba da baccinta.......


Aliyu koda ya idar da sallar asubahin zaman shi yayi cikin masallacin wanda ya cigaba da azkar da karatun alkur'ani mai girma.
Har fiddowar rana ya tashi ya bada sallar walha sannan ya fito lokacin ƙarfe wajan taran safiya.
Gidan mahaifanshi ya wuce da ƙafafunshi ya taka har can gidan a bakin gate suka gaisa da mai gadi sannan ya wuce.
Ammi tsaye tana jere kayan abinci a daining yayi sallama ya shiga cikin falon.

Fuskarta cike da annuri ta waigo tana kallon sa kafin ta amsa masa sallamar har ƙasa ya tsugunna yana gaisheta da murmushi ta amsa masa kana ta juya da sauri ta shiga wata kwana wadda ɗakunansu ke ciki mintuna biyu ta dawo hannunta ɗauke da wannan jarkar ta jiya.
Ruwan ciki ta tittulo a cup ta miƙa masa tace masa.
"Maza jeka zauna saman seater kai bisimillah kashan ye ka shafe kanka da fuskar ka"
Tura baki yayi kamar ƙaramin yaro, ya wani langwaɓar da kansa gefe tare da cewa.
"Wai nikam Ammi tun jiya ake bani tofi na minene?"
Yafaɗa kamar wani ƙaramin yaro.
Murmushi ta sauke tare da cewa.
"nidai kasha kabani cup bana son wannan tambayar taka ta lauya"
Dariya ya saki yana mai ƙarasawa saman kujerar ya zauna tare da bin umarninta dama can Ali baya musu garesu sharrin mace ne Allah ya haɗa shi da shi.
Sosai Abba yaji daɗin ganin ɗan nashi rukumi sukai wajan yin break cikin soda ƙauna.
Bayan sun kammala Suka koma falo suka zauna suna kallo.
Aliyu na sunne kai ƙasa ya dubi Abba yace masa............

*WARRRRR*💃💃💃💃
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.








Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588

*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

34

"Abba akwai wata"
Seyay shuru yana faman jan gemunsa yana murmushi yaƙi cigaba da sauran maganar.
Tsira masa ido Abba yayi cike da ganɗokin son yaji me zece masa sedai shikam Aliyu yayi gum ya kasa ƙarasa abin da ze faɗi ɗin.
"Muna jinka wannan wani irin haline Baffa tayaya zaka tsaida mu? muna magana dakai kaja baki kayi gum"
Ammi ta faɗa tana kallonsa.
Dariya ya saki kaɗan yana ƙoƙarin miƙewa ammi ta jefo masa filon kujera tace.
"Karka tashi baffa Allah ka tashi ranka zeyi mugun ɓaci"
Ammi ta faɗa tana kallonshi.
Harara ya ɓallawa su hassana waɗanda suka zuba mashi ido ganin kallon dayay musu yasa sukai wuff suka bar falon sukai cikin ɗakunan su.
Komawa yayi ya zauna kansa a ƙasa har yanzu ya kuma kasa magana kasancewar sa namiji mai tsananin alkunya.
Da zurfin ciki duk abin da kaga ya buɗi baki yayi magana akansa tofa abun mahimmi ne Aliyu akwai tsabar zurfin ciki da kunyar tsiya.
Gyaran Murya! Abba yayi cike da dattako cikin zuciyar shi kuma murna ce fal na yadda ubangiji ya amsa musu addu'arsu ya karkato musu da hankalin ɗan nasu.
Sannan Abba yace.
"Muna jinka Baffa faɗa min gani ga Ammi ko ta samu ne?"
Abba ya faɗa da barkwancin shi wanda yakewa dukkan yaranshi sabida Abba idan yana wa ƴaƴansa magana bakace mahaifinsu bane sabida yadda yake sakewa dasu sosai yake basu mahimmancin su wasa da dariya mai tsafta wanda babu raini acikinsa haka zalika Ammi waɗanda suka mayarta kamar kakarsu dan tsabar yadda take jansu ajiki.
Wannan ɗabi'a ta su Ammi da Abba tajanyo shaƙuwa mai yawa a tsakaninsu da ƴaƴansu wadda takai gaba ɗayansu basa iya ɓoyewa mahaifan nasu komai kuma duk abin da ya faru zasu masu addu'a ko shawara hatta su anty jidda da sarat dake aure a katsina suna jin ɓurin zasu kira abba ko ammi su gayawa ɗabi'ar jan ɗa ajiki ba ƙaramin alfanu take janyo wa ba domin sosai su Ammi suke da fahimta mai kyau a tsakanin su da ƴaƴan su.


Dai dai ta nutsuwar sa yayi tare da kallon ƙasan carfet yana wasa da azurfar hannun shi cikin nutsuwa yace.
"Akwai wata yarinya anan maƙotan hajja sunanta ummi khairy but abba ina jin tausayinta sosai sabida ƙaddarar data sameta........................."
Ya kwashe labarin ummul ya shaidawa mahaifan shi sedai me? ya tsinci bakinsa da rufawa ummul asirin cewar A hotel ya ganta da kuma cewar a gidan karuwai ta zauna bayan korar da mahaifinta yayi mata sam ya kasa bayyanawa mahaifansa wannan maganar dama kuma ya kwaɓi hajja.

Sannan ya cigaba.
"Tana zaune a wajan hajja fa har zuwa wannan lokaci Abba ban taɓa ganin uba irin nata ba wai daman akwai mahaifa irin su? duk girman ƙaddarar yarinyar ya kasa amsa sema korar ta dayay daga gidan yanzu bada ban hajja ba da ina zata wace rayuwa zata faɗa?"
Yafaɗa idanunshi jajir cike da ɓacin rai.
Tagumi Ammi tayi tsigar jikinta na miƙewa duk da bata da labarin yarinyar a wajan hajja kuma bata santa ba kasancewar bata yawan zuwa gidan hajja ɗin in tana son ganinta Aliyu ke zuwa kano ya ɗaukota ko a tura draver ya ɗaukota.
Tai kwanakin ta ta koma Amman wannan labari ya girgiza Ammi a matsayinta na cikakkiyar uwa! kawai ayyanawa take yaya mahaifiyar yarinyar zataji ƴarka tun tana shekara goma sha biyar ai mata fyaɗe kuma baka da kuɗin da zakaja shari'a da waɗanda sukai matan saboda suna da hannu da shuni.

Muryar Abba ce ta katse mata tunanin inda yake ta jan salati murya cike da ɓacin rai matiƙa yake furta.
"Ka tambayi Baban shin ɗan uban waye daze mata haka( daya ke sunan da yake gayawa hajja kenan baba) ka tambaya min sunan ubansa a kano na rantse da Allah ko dukiyata zata ƙare sena makasu a kotu kuma kai zaka tsaya mata ka karɓa mata hakkinta ina son wannan ya zama darasi ga masu halin akuyoyi irinsu ai in baka da kuɗi ba yana nufin baka da rayuwa ba! Abu na gaba kuma kai Aliyu zakaje ka nemi auren ta wannan babban jahadi ne sabida a rage mata zugi da zafin tunanin ƙaddarar data sameta tunda har baba ta ɗauketa ta riƙeta na tabbata mai tarbiya ce ƙaddara ce ta faɗa mata sabida haka ni zan tura iyayenka wajan sakaran ubanta sune maka auren ta ina son na inganta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login