Showing 15001 words to 18000 words out of 83661 words
kusa dashi.
Ba sakewa yabar falon hajja ta take mai baya tana furta.
"To bazaka tsaya kaci abinci ba?"
Murmushi ya sauke mai ƙayatarwa.
"Haba hajja wani abincin zanci kuma bayan wanda naci?"
Ɓata rai hajja tayi kana tace.
"Ai kace bakai kalacin safiya ba to kaga akwai na rana tunda wancan na safiya kaci ay"
Zira hannayen shi yayi cikin aljihun wandonshi.
Yayi taku ɗaya zuwa biyu
'zan dawo anjima kimin sakwara miyar agushi, waccan ledar kuma maganinta ne aciki za'a sami ruwa mai ɗumi a gasa wajan sannan a shafa maganin ɗayan kuma tasha Allah ya sawaqe"
Yafaɗa tare da cigaba da tafiyar shi.
Godiya hajja tayi masa kana ta koma ciki da murna hajja ke gayawa bamu cewar wannan fa jikanta ne Aliyu ɗan wajan ɗiyarta.
Sosai suka faɗa hirar Aliyu ita da bamu wanda ita kuma ummul ta lafe jikin mahaifiyarta tana jin ƙaunarta na ratsa mata jikinta.
Seda akai la'asar sannan bamu taima hajja sallama tare da godiya ta wuce gida.
Da ƙyar ummul tayi sallah taci abinci taɗan kwanta dan wajan na mata zafi sosai.
Wajan yamma ƙannenta suka shigo a sace sukai mata sannu suka koma.
Abu kamar wasa ummul taƙi shan magani duk da irin faɗan da hajja ke mata ga uban zugin da wajan keyi mata saka makon taɓawar da likita tayi, zuwa magariba zazzaɓi da ciwon kai ya kamata har tana sheƙa amai hankalin hajja yayi masifar tashi dan ko sallar magariba ma azaune tayi ta bayan ta idar ta jibga uban bargo ta kwanta saman gadon hajja tana rawar ɗari har tana shiɗewa faɗan duniya hajja tayi shi wanda ita bata san daman ummul ciwonta haka yake ba sam bata shan magani se taji kamar zata mutu.
Shiko Aliyu ya koma hotel cikin nutsuwa yayi wanka ya shirya cikin kayan shan iska coffee yaɗan sha sannan ya kwanta bacci wanda bashi ya farka ba se wajan karfe huɗu alwalwa ya ɗauro ya tayar da sallar la'asar bayan ya idar ya ɗauko system ɗinshi yana aiki da ita.
Bai tashi daga wajan taba se magariba alwala yayi tare da sauya kaya zuwa jallabiya fara ƙal mai dogon hannu tare da baƙin 3qtr acikinta sallah ya tayar bayan ya idar ya zauna karatu wanda a kwanakin nan kusan kullum seya yi.
Seda yayi sallar isha'i wajan ƙarfe 8:30 ya miƙe tare da nade sallayar yaɗan ƙara fesa turare ya ɗauki wayarshi da keyn mota ya fita.
A hara bar hotel ɗin ya kalli sararin samaniya walkiya tana tashi hadari na haɗowa alamar ruwan sama na gab da sauka.
Yana son yanayin damuna sedai baya son dukan ruwan sama dan muddin ruwa ya taɓa shi seyayi zazzaɓi ko mura mai zafi
Da sauri ya shiga motar ya kunna ya ɗauki hanyar gidan hajja
Dayake yayi sauri yasa ya ƙarasa wajan ƙarfe 9:00pm sabida akwai tazara nesa ba kusa ba a tsakaninsu parking ya gyara a kofar gidan tare da fitowa waje bayan ya kashe motar hadarin unguwar su hajja ma har yaso yafi nacan inda ya baro ɗin tura gate ɗin yayi ya shiga daya ke hajja tasan zezo shiyasa bata rufe gate ɗinta ba.
Sallama ɗauke cikin bakinshi ya shiga falon hajja.
Da sauri hajja dake zaune tai tsuku duk al'amarin ciwon ummul ya ɗaga mata hankali ta ɗago tare da amsa mai sallamar cikin kulawa.
Tsaida kallon sa yayi a fuskar hajja yana nazarin ta kafin ya furta.
"Hajja ta lafiya na ganki cikin rashin walwala? daman nace ma ammi a yaran can wani ya dawo nan tace kinki amman zaman kaɗaicin bai da daɗi"
Yafaɗa yana mai zama a gefenta.
"Kai nifa salame na zuwa yau ma biki taje shiyasa bata zo ba,nifa duk damuwata akan ummi ne kaganta can a gado se wani abu take gudu nake kar yarinyar mutane ta mutu"
Tafaɗa tana share hawayenta.
Ɗan jimm yayi tare da cewa.
"Au hajja bata sha maganin bane wani abunne kuma?"
Yafaɗa batare da ya nuna hakan ya dame shiba.
"Babu yadda banyi da ita ba wallahi taƙi sha gaya can zazzaɓi ya kamata tana ta rawar sanyi"
Hajja ta faɗa tare da share ƙwallar dake zubo mata.
Da mamakin yake kallon hajja wannan wace irin ƙauna take ma waccan yarinyar kosu in suna ciwo bata ɗaga hankalin ta haka.
Daɗan ɓacin rai ya dubi hajja.
"Ki dena kuka! dan iskanci abata magani a asibiti sannan taƙi sha dan ta rena ki, ina maganin yake?"
Yafaɗa cikin rashin walwala.
Da hannu ta nuna masa ledar da tunda ya ajeta babu wanda ya ɗauketa.
Da matiƙar ɓacin rai ya sanya hannu ya ɗauki ledar tare da nufar bedroom ɗin hajja wanda ummul ɗin ke cikinsa a kwance............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
13
Cikin nutsuwa ya ƙarasa cikin bedroom ɗin hajja murya can ƙasa yayi sallama wadda ta tsaya a iya fatar bakinshi.
Tsaye yayi a bakin gadon ya zuba mata ido yana kallon yadda jikinta yake rawa ta cikin bargon data rufa ajikin nata.
Yafi ƙarfin mintuna goma a tsaye yana auna yadda zeyi ya tayar da ita acikin yanayin daya same ta.
A hankali yaja ƙafafunshi kamar mai tsoron ƙasa ya ƙarasa gaf da gadon ya sanya ƙafa yaɗan bugi gadon kaɗan A hankali ummul taɗan zabura tare da furta.
"Wayyo Allah! dan Allah karka kuma kayi haƙuri na dena na dena"
Muryarta ke tashi cikin wani irin ƙaraji! rintse idanu yayi alama ta nuna mafarki take wanda sautin maganar mafarkin nata ta fito fili, ɗan tsaki yaja ya kuma dukan gadon da ƙafarshi
Wannan karon ƙara tasan ya kaɗan tana jan ajiyar zuciya ƙaƙƙarfa.
"Khairy! khairy"
Yake kiran sunanta ahankali.
Cikin nutsuwa takejin saukar muryar wanda batai zato ba acikin kunnuwanta ahankali take dai dai ta nutsuwarta wadda ta rasa acikin mafarkinta.
Yun ƙurawa tayi ahankali tana rintse idanunta sannan ta tashi daga kwanciyar data yi.
Ganin yana gab da ita ya sanya taɗan ja baya ta matse jikinta acan ƙarshen gadon ta cure kamar mai jin sanyi wani irin ƙaƙƙarfan kuka ne ya tawo mata batare data shirya masa ba.
Kukan take da iyakacin ƙarfin ta tana jan ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Rasa yadda zeyi da ita yayi, se kawai ya tsaya tare da harɗe hannunsa a saman kirjinsa ya zuba mata dukkan idanunsa yana binta da kallo.
Cikin nutsuwa ya ƙarasa inda ta raɓe murya can ƙasan maƙoshi yake furta mata.
"Ke bani son sha shanci miye aka maki kike faman ɓare baki kina ma mutane kuka?"
Bata bashi amsa ba se cigaba da kukan nata data yi.
Rintse idanu yayi ko kaɗan baya son hayaniya arayuwar shi musamman kukan mace yana sanya wa jikinsa ya mutu.
Wannan karon a hankali ya bita.
Samun waje yayi can gefenta ya zauna tare da kallonta kaɗan yace.
"Ɗago fuskar ki malama ki dube ni"
Yafaɗa muryarshi adake!
A hankali ta sanya hannu ta goge hawayen dake Zubo mata.
Tare da ɗago fuskar ta data yi jajir ta dube shi batare data iya janye idanunta akan shi ba.
Wani irin sahihin kyau yayi mata wanda take jin dama zasu dauwa ma a haka tana kallon shi.
Yana da wani irin baiwa ta musamman wanda ba kowa ne ze lura da hakan ba seya zauna dashi Allah ya bashi abubuwa da dama musamman nagarta tare da kyawun zuciya da tausayi.
Baya cikin jerin maza masu mugun kyau! sedai yana daga cikin jerin nagartattun maza waɗanda kowace mace take burin taga ta mallaka! kyawunsa sassanyan kyaune mai kwanciya a zuciya.
"Sabida karki sha magani yasa kika dame ni da kuka?"
Muryar shi ta katse ta acikin tunanin data faɗa.
Janye idanunta tayi daga cikin nasa tare da ɗan turo bakinta gaba kaɗan.
"Nifa bana jin daɗi zazzaɓi ke damuna shiya hanani shan maganin"
Tafaɗa tana wani haɗe fuska kamar wadda zatai kuka!
"Hajjah zatai maki ƙarya ne?"
Yafaɗa yana ƙoƙarin saka idanun sa cikin nata.
wasa take da yatsun ta a wannan karon batai magana ba.
Ɗan sassauta fuska yayi tare da ɗan matsota kaɗan.
Duk girmanshi ya cika mata idanu da ɗakin.
Murya can ƙasan maƙoshi ya furta.
"Kiyi haƙuri kisha magani duk wani ciwo in ba'a shan magani wallahi baya tafiya ta sauƙi ki ɗaure kisha ki shafa wannan cream ɗin shima in Allah ya yarda zuwa gobe zakiji kin warke"
Yafaɗa yana wani mayar da numfashi kaɗan kamar wanda yayi gudu!
Girgiza kai tashiga yi tana zubo da hawaye tasan maganarshi gaskiya ne gareta sedai ita ko kaɗan bata ƙaunar magani.
Bata kai dayi mai magana ba taga ya miƙe tsaye ya fita daga ɗakin ba jimawa ya dawo hannunsa riƙe da cup ya dire a gabanta.
Tare da ɓallo mata maganin guda ya miƙo mata babu musu ta karɓa yana tsaye akanta ta haɗiyi maganin tana wani yamutsa fuska kamar mai shan maɗaci.
Amsar cup ɗin yayi ya fita waje mintuna kusan biyu suka dawo shida hajja abin mamaki da kanshi ya shiga toilet ya haɗo ruwan ɗumi cikin bawo ya sanya tawul aciki ya fito ya miƙawa hajja tare da furta.
"Ina falo zan ci abinci kafin ku kammala ke kuma ki mata gardama karki fasa"
Yafaɗa tare da fita falo.
Da ƙyar ummul ta yarda hajja ta taimaka mata wajan gasa wajan ta shafa mata cream ɗin wanda babu abin da ummul take se kukan shagwaɓa tana matso hawaye!
A haka suka gama hajja takai bawon bayi ta dawo tana mata dariya tana cewa.
"Ke kam ummi raguwa ce ahaka zamuyi wankan jegon lallai duk mai maki wankan jego ze kwashi takaici"
Tafaɗa tana dariya.
Turo baki ummul dake zaune rashe rashe a carfet ɗin hajja tayi wadda take ta faman zubo da hawaye kafin tace.
"Allah hajja bakiji zafi ba wallahi Shikam yaci ka mugunta shine ze haɗo ruwan da zafi"
Murmushi hajja tayi tana cewa.
"Ai ni mamaki ma abin ya bani lallai kinci sa'ar Aliko da har ya tsaya ya kula dake! wanda ƙannen shima in suna ciwo suna kuka zane su yake amman ke ai kinci sa'ar shi"
Hajja ta faɗa tana ficewa a ɗakin.
"Nikam ba wani sa'a se wahalar daya hassasa mini"
Tafaɗa tana mai shafo wajan wanda yade na mata zafin kuma zazzaɓin ma yaɗan soma sauka ba kamar ɗazu ba.
Ya gama cin abincin ya kunna TV yana kallon labarai hajja tayo sallama falon.
Fuskarshi ɗauke da murmushi yake amsawa hajja tare da cewa.
"Har kun gama?"
Murmushi hajja tayi.
"Da ƙyar muka gama wannan yarinya badai kafiya ba,duk wanda ze mata wankan jego seya shirya dambe"
Lumshe idanu yayi batare daya ce mata komai ba ya miƙe yana duba wayar shi tare da fiddo dukkan girman idanunshi waje.
"Hajja 11 ta kusa fa bara na ƙarasa gobe nake son tafiya insha Allahu amman kafin na tafi zan shigo na maki sallama"
Yafaɗa yana ƙoƙarin fita.
"Amman meya sa bazaka kwana anan ba tunda akwai ɗakuna naga an fara yayyafi"
Murmushi yayi wanda ya ƙara haska kyawun fuskarshi.
Yaɗan shafo kanshi kaɗan.
"Haba hajja ada dai na kwana amman yanzu ina magidan ci ina zan kwana gidan......."
Filo ta kwaɗo mai tana cewa.
"Ni zaka cewa haka to babarka ma nina haifeta bare kai"
Dariya yake wadda tai masa mugun kyau yana mai kallon hajja data haƙiƙance tana ta surfa masifa.
"Allah ya huci zuciyarki hajja akwai ayyukan dazanyi da system shiyasa zan koma"
Yafaɗa yana mai dena dariyar daya keyi.
"ayyo to shikenan kaje ka ma ummi sallama seka wuce"
tafaɗa tana mai mayar da hankalinta wajan tv dan hajja tana tsananin son kallo.
Ɗan haɗe ran shi yayi kaɗan tare da cewa.
"Miye haɗina da ita hajja wannan ma bada maganin arziƙin ki taci ay"
Yafaɗa yana mai ƙoƙarin ya fice.
"Aliko karka fita kaje kawa ummi sallama ai babu daɗi yarinya babu lafiya ka kasa yi mata sallama"
Babu yadda zeyi haka ya koma da baya zuwa bedroom ɗin hajja daga Bakin ƙofar ya tsaya yana kallon ta yadda take ta faman saka hannu ta cikin rigarta tana shafo wajan ciwon.
A ranshi yake ayyana wannan yarinya ta cika raki.
Kafin ya ƙarasa ciki yayi sallama wadda ta bayyana gareta.
A hankali ta amsa mai batare data dubi inda yake ba.
"Ya jikin?"
Yafaɗa kamar an masa dole.
"Da sauƙi"
A hankali tai furucin.
"Zan tafi seda safe don gobe nake son komawa garin mu"
Yafaɗa kamar baya so.
Lumshe idanu tayi kirjinta na dokawa kaɗan kaɗan tace.
"Mai yasa baza ka kwana anan ba dare yayi fa sannan ruwa ake duba kaga window"
Tafaɗa tana mai nuna masa window ɗin da hannunta.
"Kawai sena kwana anan dan baki da hankali ke koda yaushe kin fi son mu keɓe da juna salon na kwana anan ki lallaɓa ki bini ɗakin dana kwanta ai ko rashin shan maganin ki ma gulma ce dan kinsan zan zo ne shiyasa kika ƙi sha dan mu keɓe ko?"
Yawani faɗi maganar cike da rainin hankali.
Ɗimauce wa ummul tayi da jin sharrin daya lafto mata.
Shura ƙafafunta take tana faman sakin kuka ƙasa-ƙasa.
"Allah ya saka mini ni wallahi ba haka bane"
Tafaɗa cikin kuka!
Dariya ya saki mai ƙayatarwa tare da saurin ficewa daga ɗakin ya tsincin kansa cikin nishaɗi da shagwaɓar datai mashi ayan zu.
Bai tsaya wajan hajja ba yayi saurin fita waje.
Wanda hakan yayi dai dai da sanda ruwan ya kuma gocewa da tsananin ƙarfin gaske............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
Wanna shagon kayan kwalliya ko kayan Gyeran jiki zakaje kayi sayayyar aqalla Naira 32k sannan su baka kyeutar kayan 19k akan 1500?ko da kuwa sayayyarka ta Farko dasu kenan?
ORIFLEM sun bani garabasar kayan kimanin 19k💃🏽💃??💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Maza kiyi sayayyarki Dan kema ki Samu taki garabasar!wannan Garabasar zata qare a 5 ga watan nan.
Bata Qare anan ba,Kamfani yace daga nan zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne,bazaki biya kudin Register 4490 ba.yar uwa me kike jira????
Maza Danna wannan link na kasa domin Amfana da wannan Kamfanin Mai Albarka.
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
https://wa.me/message/ARQS3KWKIYKQD1
Ko Number waya
08064400588
*BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
GARKUWA WRITTER'S ASS....
*14*
Tun ma kafin yakai ga fita daga cikin gidan hajja ruwan ya gama jiƙe masa jikinshi sharkaf.
Amman sabida tsabar kafiya da taurin kai irin nashi bai juya ya koma gidan hajja kamar yadda ta bashi shawara ba haka ya shiga cikin motar duk jikinshi ya gama jiƙewa hatta ga saman kanshi ruwan ke ɗiga.
A haka ya tashi motar ya bar layin tafiya yake cikin ruwan wanda hatta fitilar motar shi seda ta dusashe sabida rashin wadatar haske sakamakon ruwan dake zuba kamar da bakin ƙwarya.
Ikon Allah kaɗai yakai Aliyu hotel ɗin daya sauka.
Anan ɗinma ruwan da ake tsulawa yafi na wanda ya baro agidan hajja horn ya danna masu gadi suka tawo aguje cikin lema suka wangale mai ƙaton gate ɗin da sauri ya shigar da hancin motar shi zuwa cikin parking lot na hotel ɗin ya jima yana saƙa yadda zeyi ya fita waje cikin wannan ruwa dubarar kiran Abokin shi nas wanda suka zo kano tare suka kuma sauka a hotel ɗin tare wannan wanda yayi mai magana a tun farkon page ɗinmu na baya, Sedai shi Nas ɗan sanda ne na farin kaya bincike shima ya kawoshi kano dan haka ma tunda suka sauka basu haɗu ba, Dan shi nas zeyi wajan sati ɗaya a kano saɓanin Aliyu daya gama aikin daya kawo shi aranar yau dan banda dalilin gidan hajja ma da tuni ya jima da wuce wa gida.
Wayarshi ya fiddo yana niman numbern nas sedai abin takaici taƙi shiga haka yayita trying amman wayar taƙi shiga tsaki! yaja mai ƙarfi tare da mayar da wayar aljihun jallabiyar yana kallon saukar ruwan ta glasess ɗin motar.
Kashe motar yayi tare da fita waje wanda nan da nan ruwan yayi mai caaa akanshi yana dukan shi.
Da sauri mai kama da gudu yake shiga ciki da gudu ya haye saman benen amman dukkan jikinshi rawar ɗari yake na rashin sabo dan tun asali Ali bayi son ruwa ya taɓashi dukan ruwa na saurin yi mai illah.
Da karkarwa yake buɗe ɗakin daya sauka yana gama buɗewa ya tura ƙofar ya shige ciki ya kunna ƙwai wayar shi ya cillah saman gado da sauri da zafin nama yake ƙwaɓe rigar jikinshi.
Ataƙaice tawul ya ɗaura ya shiga bathroom ya haɗa ruwa mai zafi yana watsa wa ajikinshi.
Wajan mintuna ashirin ya ɗiba kafin ya fito yana zabga atishawa dafe kanshi yayi a galabaice ya sauya kaya zuwa wata jallabiyar mai ruwan toka.
Wayar cikin ɗakin yayi amfani da ita ya kira ɗaya daga cikin ma'aikatan cikin hotel ɗin ya bashi umarnin ya kawo mai black coffee, Ba jimawa yaji bugun ƙofar ya buɗe ya amsa ya koma gefen gado yana kurɓar shi da zafinshi yana kammala wa ya koma bathroom yayi brush ya ɗauro alwalar kwanciya bacci.
Kwanciya yayi saman gado yana dafe kanshi wanda yake mai ciwo ga atishawar daya ke I'mta faman jerawa gaba ɗaya saman karan hancinsa yayi jajir yana fitar da gumi.
A haka wahalallan bacci ya kwashe shi wanda ko kaɗan baya jin daɗin sa..
Hawaye na zuba murmushi na sauka a saman kyakykyawar fuskarta ahaka hajja ta shigo ta tarar da ita.
Tsaye tayi akan ta tana kallon ta cike da mamaki kafin tai gyaran murya tace.
"Ummi lafiyar ki wannan wani irin shashanci ne kina kuka kina murmushi kamar sakarya?"
Hajja take mata wannan maganar bayan ta nemi guri gefen gadon ta zauna.
Turo mitsitsin bakinta tayi gaba cike da sabo da shaƙuwar da sukai da hajja tace.
"Yaya Aliyu ne"
Tafaɗa tana ƙunshe kanta cikin hijabinta.
Murmushi mai ƙayatarwa hajja tayi.
"Me Baffan yayi miki kike kuka da dariya?"
Ta cikin hijabin tace.
"Hajja inna gaya miki zaki yarda?"
Murmushi hajja tayi.
Tare da cewa.
"Haba ummi mahaifiyarki haifarki kawai tayi amman rainonki duk yana hannuna dan kin san ba da ban jarabar ubanki ba da babu yadda za'ai kibar hannuna sabida haka komai kika gayan inna gaskiya ne zan gane inma karya kike zan gane ummi haka kawai Allah ya ɗoran soyayyarki wadda bana wa jikokina dana haifi