Showing 21001 words to 24000 words out of 83661 words

Chapter 8 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11351

sannan kuma kuce kuna kan ra'ayin ku?"
Yafaɗa yana tsareta da idanun shi.
"Karka ɗora zargi kan auren ku domin aure da zargi baya yuwuwa Aliko"
Hajja ta faɗa tana mai ƙarfafa masa gwiwar sa.
Bai iya ce mata komai ba face miƙewar dayayi.
"Hajja zan tafi idan naje gida zan shaidawa abba kudai kawai ku kasance cikin shiri koda yaushe su abba zasu iya zuwa nema min auren ta"
Murmushi hajja ta saki tana mai karantar yanayin shi yayi kama da wanda yake cikin tsananin kishi tausayi da rashin sanin makama.
"Ummi zo ze tafi"
Muryar hajja ita ta fito da ummul wadda take cikin ɗakin hajja da sauri ta ƙaraso falon lokacin har ya fice daga falon da sauri domin ya tsinci kanshi da rashin son ganinta yana maijin dana sanin alƙawarin dayayi ma hajja na aurenta.
Ganin ya fita ya sanya hajja tace mata tayi sauri ta bi bayan shi tayi masa sallama.

Yana gab da buɗe ƙofar gate tai saurin cimmai ta dakata agaban shi tana mai tsare shi da idanunta dasu ka ciko da ruwan hawaye.
"Tafiya zakai kuma zaka iya yin tuƙi a haka bayan baka da lafiya?"
Tafaɗa tana tsire shi da idanunta.
Kallon ƙurullah yake mata mai cike da tarin ma'a noni da dama batare daya ɗauke idanun shi akan ta ba yace.
"Kin tilassa ma hajja kina son ta nema miki aure na? to ina so ki buɗe kunnen ki da kyau kiji ni"
Yafaɗa yana kallonta.
Jikinta ne ya tsananta rawa sam batai zaton hajja zata gaya masa ba.
"BA SON KI NAKE BA TAUSAYI NE! yes tausayin ki nake ummi kairiy zan aureki abisa wasu dalilai dana barwa kaina sedai fa ki sani koda na aure ki jinginar dake zanyi agidan mahaifa na domin matata bata raba soyayyata da kowa ba tabbas taji labarin ki zata iya halakaki dan haka ki shirya yadda zaki zauna da mahaifana domin ni bakya cikin tsarin matan dana ke so ban taɓa sonki ba sedai kina tsananin bani tausayi musamman da hajja taga gaya min koke wacece nasan in bani na taimaka na aure ki ba haka zaki ƙara komawa jagaliyar karuwan...........
"Dakata Aliyu"!!
Tayi saurin katse shi gaba ɗaya jitai komai ya fitar mata aranta.
"Mai yasa zaka min haka mai yasa kake son shiga cikin jerin maza marasa adalci? shin ƙaddara ba zane bace nina kai kaina inda kake tunani ba ƙaddara bace ko kaima kana son shiga cikin jerin wasu daga cikin ahalina da suka ƙi amsar ƙaddara ta bani da wani gata a yanzu sena Allah seku ma kai dana ɗauki soyayyar ka na ɗarsawa raina Aliyu karka zama namiji mara adalci aso! duk macen da zata kalli idanun namiji tace tana sonsa wallahi ta gama masa komai domin mace bata furta yaudara! sabida Allah ya ɗora min son ka zan zama wulaƙantacciya a wajan ka to karka aureni ka gani idan bazan yi auren ba"
Tafaɗa tana fashewa da wani irin kuka!
Dafe kanshi yayi wanda har lokacin ciwo yake masa da wani irin zafin nama ya janyota ya manne ta da jikin gate ɗin ya rungumeta da zafi zafi yake shafa gadon bayan yana jin zuciyarsa na barazanar tarwatse wa.............
*ƘAR SHEN FREE PAGE MU HAƊE A PAID PAGE*

_ME HAJJA TA GAYA MA ALIYU _ ?

_WACE IRIN ƘADDARA CE KE BIBIYAR UMMUL DA HAR TA ZAME MATA MAKAUNIYAR ƘADDARAR DATA TSALLAKE TABAR GABAN MAHAIFANTA_

_SHIN ALIYU ZE CIKA ALƘAWARIN HAJJA NA AUREN UMMUL_ ?

_SHIN BASMA MATAR ALIYU ZATA BARI YA AURI UMMUL IDAN TAJI TO YAYA MA ZAMAN ZE KASAN CE_ ?

_ALIYU IDAN YA KOMA ABUJA ZE DAWO KO BASMA ZATA ƊAUKE MAI HANKALIN SA_ ?

_WAYE ALIYU_

_WACECE UMMUL_?

_MEKE BIBIYAR RAYUWAR TA_ ?

_YAYA WANNAN RUNGUMAR ZATA KASANCE TA SO CE KOTA TAUSAYI HMMM ZAMUJI ZAMU GANI IDAN MUN SHIGA CIKIN SHAFIN KUƊI HAJIYA HANZARTA KI BIYA DOMIN AYI TAFIYAR DAKE_
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400







Wanne shagon kayan kwalliya ko kayan Gyeran jiki zakaje kayi sayayyar aqalla Naira 32k sannan su baka kyeutar kayan 19k akan 1500?ko da kuwa sayayyarka ta Farko dasu kenan?

ORIFLEM sun bani garabasar kayan kimanin 19k💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Maza kiyi sayayyarki Dan kema ki Samu taki garabasar!wannan Garabasar zata qare a 5 ga watan nan.

Bata Qare anan ba,Kamfani yace daga nan zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne,bazaki biya kudin Register 4490 ba.yar uwa me kike jira????
Maza ki garzayo domin Amfana da wannan Kamfanin Mai Albarka.
Ku Tuntubeni A wannan lambar domin yin Register ko sayan Kaya
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

17

*Wai waye Adon tafiya*

Bahaushe yace wai waye adon tafiya ina son duk wani makarancin wannan labari daya saurara ya bada lokacin sa domin karanta asalin labarin wanda nai masa laƙani da wai waye sabida karantawar ne kaɗai ze baka haske akan manufar labarin harma da saƙon dake tafe dashi.

Ummul kairi Abubakar shine asalin sunanta, malam Abubakar shine mahaifin ummul haifaffan garin kano kuma ɗan gargajiyar cikin unguwar tunga anan aka haifeshi har ya girma ya zama matashi.
Iya karatun arabiya kaɗai ya samu amman Allah bai sanya ya samu karatun zamani ba, Su uku ne ƴaƴa a wajan mahaifansu wanda tun dama suka taso mahaifinsu ya rasu mahaifiyarsu ce saura.
Malam Abubakar irin mutanan nan ne masu ɗan banzan surutu uwa uba kuma akwai shi da faɗa kamar ze ari baki tun yana ƙarami yake da wannan hali najan faɗa har zuwa girmanshi anan kusa da gidansu ya samu matar aure mai suna hadiza wadda takasance kurma amman tana ɗanji kaɗan kuma tana magana sama-sama.
Cikin hukuncin Allah Abubakar ya auri hadiza anan kusa da gidan mahaifansa yayi ginin ƙaramin gida na ƙasa dayake sauran ƴan uwan shi guda biyu duka mata ne kuma sunyi aure tuni,
Cikin hukuncin Allah zaman Abubakar da hadiza zamane na soyayyah yana fita kullum yayi aikin shi na leburanci wanda baya dawowa se yamma yaci abinci ya koma majalissa ahaka hadiza ta samu ciki wanda watan su tara cif da aure ta haifi ƴarta mace.
Zokuga murna wajan su abubakar na samun wannan ƙaruwa ranar suna yarinya taci suna Basira bayan basira hadiza ta haifi zainab bayan zainab hadiza ta haifi sakina to rayuwa na tafiya kullum nauyi ke ƙara ɗoruwa akan malam abubakar gefe ɗaya kuma baƙin cikin haihuwar ƴaƴa mata tana nausar shi.
Cikin wannan lokaci aiki yakai shi ƙiru na ginin wata makarantar kwana lokacin basira na shekara uku zainab nada shekar biyu sakina nada shekara ɗaya sabida hadiza kurma konika take yi.
Bayan tafiyar Abubakar ƙiru acan Allah ya haɗashi da wata yarinya bafulatana mai suna hassana wadda take kawo masu tallen nono inda suke aiki.abu kamar wasa Abubakar yace yana son hassana da aure.
Abokan tafiyar shi suka kada baki suka ce masa.
"Kaiko Abubakar hannun ka bai isa ya cuɗa bayan ka ba har kake jiran wani ruwan wankan?"
Buɗar bakin sa seya ce.
"Ai rayuwar duniya ƴar saka kaice komai kaga dama kayi"
Sanin halin masifar sa yasa suka ja baki sukai masa shuru.
Kafin su kammala aikin abubakar yaje har gidan su hassana waɗanda suke tagwaye wajan mahaifan su ita da ƴar uwarta hussaina.
Sosai malam jauro mahaifin hassana yayi na'am da abubakar har suka tsaida magana bayan ya koma gida ze aiko ai maganar biki.
Hakan ce ta faru domin bayan dawowar su gida yajewa da mahaifiyar shi mai suna innah maganar auren hassana sosai innah ta rufe ido take zazzaga mai masifa akan cewa.
Damme ze tarko aure bayan yasan cewar bai gama wadata iyalinshi ba sannan gidan shi duka ɗaki uku ne ɗaya na yara ɗaya nashi ɗaya na hadiza ina ze aje wata matar.
Buɗar bakinshi se yace shidai yana da ra'ayin ƙara aure ko babu komai ya sami arziƙin haihuwar ƴaƴa maza.
Murmushi innah ta sanya tare da cewa.
"Habu kenan ga talauci ga buri"
A zuciye ya tashi yabar gidan yaje gidan kawun sa yayi masa maganar shima dai kamar ta innah ɗin yayi domin faɗa yayi masa akan yadda sha'anin duniya yake tayaya hannun ka bai cuɗi bayan ka ba zaka ƙaƙalo wa kanka aure.
Haka ya tashi daga gidan kawun nashi ya nufi gidan maƙocinsa yayi masa bayanin komai wanda shiya je wajan innah ya bata baki badan taso ba ta amince aka tafi ƙiru kai kuɗin auren hassana.
Sosai suka dawo da murnar karamcin da mahaifan hassana sukai musu.
An saka aure wata uku wanda zuwa lokacin Abubakar ya gyara ɗakin sa ya mayar a mazaunin na amaryar shi wanda hadiza dan tsabar kishi jitai kamar ta sanyawa gidan wuta abinka da kurma nan da nan ta haukace ita ce harda yaji innah ta bata haƙuri ta dawo da ita.
Kowa a unguwar zagin malam habu yake sabida yadda ake ci da ƙyar agidan shi ake sha da ƙyar amman yaje ya kankamo aure.
Shikuma ya shafawa idanun shi toka yayi biris da kowa ya cigaba da hidimar shirin uren shi wanda yace hadiza in bazata zauna ba ta zube mai yaranshi tabar masa gida.
Haka hadiza tai haƙuri ta zauna ta cigaba da kula da yaranta domin tace koba komai zata zauna domin taga bayan hassana amaryar tata.
Haka kwanaki sukai ta tafiya kwanci tashi biki ya rage sauran kwana ki biyu shiri kota ina yana kan kama haka Allah ya nuna ranar ɗaurin aure wanda bayan an ɗaura aure baffan hassana ya damƙawa malam habu amanar ɗiyarsu da ƙyar aka raba hassana da hussaina wadda a rana ɗaya akai auren su ita hussaina tana nan cikin garin ƙiru ita kuma hassana tayo nan tunga gidan malam habu wajan inna aka soma kaita bayan tai mata nasiha aka wuce da ita ɗakinta.
Fafur malam habu yayi yayi da hadiza akan tazo su gaisa da hassana taƙi fitowa haka ya kaɗe babbar rigarsa yabar mata ɗakin yayi na amaryar shi bayan cin kaza da komai malam habu ya umarceta dasuyi sallar ma'aurata bayan komai na ibada ya kammala suka ja labule ihun hassana ya cika gida amman hadiza tai buris koda safe kasa fitowa tayi seda malam habun yaje ɗakinta sannan ta rufeshi da faɗa haka ya tashi yabar mata ɗakin ya koma na amarya wadda zazzaɓi ya rufeta da taimakon shi ta gyara kanta.
Sannan ya samo mata abin karin kumallo taci.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya a hankali hassana ta soma fuskantar zaman gidan malam habu da matar shi hadiza kurma wadda ƴaƴanta ke kiran da suna ummah!
Hadiza ba mutunci ƴaƴanta ba kunya.duk da ƙanƙantar su basu fasa zagin hassana ba kuma hadiza tai buris taki ɗaukar.mataki hakan yasa hassana ta tattarasu ta watsar kasancewar ta mace mai hakuri.
Haka hadiza zatai ta zagin ta a hankali ba damar ta rama sabida hadiza kurma ce koda ta zagenta ma baji zatai sosai ba.
Ta ɓangaren malam habu yana kokarin kawo garin tuwon dare wanda shi za,a ci da daddare aci da rana in yay ragowa a kwaɗa da daddare nan da nan hassana tai baƙi ta rame.
Watanta biyar ta sami ciki sedai bai kai ko ina ba ya zube, haka ta kuma samun ciki na biyu shima ya zube lamarin ya soma bawa iyayen hassana tsoro abinka da fulani nan suka dage mata da addu'a haka nan kuma ta kuma samun ciki na uku shikam seda ya ma fito amman ya zube lokacin ka dubi hassana bazaka shaidata ba sabida yadda ta rame tai baki ga talauci gashi bata gayawa mahaifanta komai kasancewar ta mace mai zurfin ciki gasu a nesa suke bare su dinga leƙo wa.
Rayuwa na tafiya shekaru naja yanzu haka hassana tana cikin shekara ta biyar da aure amman har lokacin cikinta bai samu tsayawa ba sannu a hankali sukaje asibiti akai mata daurin mahaifa wanda aka ce zata ɗan huta kafin aga mai Allah zeyi.
Dayake malam habu yana son ta yasa yake lallaɓata lokacin baya samun aikin ma sosai amman haka yake fita yayi dako domin ya samo musu abin da zasu ci.
Ita kuma hadiza tana dambu da rana na sayarwa da shinkafa da wake bayan an kwancewa hassana ɗaurin mahaifa ba jimawa ta samu ciki sosai ta dage da addu'a akan Allah ya bar mata wannan cikin don itama tana son ganin ƙwan ta aduniya, cikin hassana yana da wata bakwai Allah yayiwa innah rasuwa mahaifiyar malam habu sosai aka shiga rudun mutuwa bayan sadakar arba'in malam habu ya ɗaga gidan innah ya sayar aka raba gado inda ya samu jarin buɗe kantin saida kayan masarufi.
Lokacin da cikin hassana yakai wata tara wannan lokacin aka tada gyaran gidan innah wanda yake makotansu wanda malam habu ya sayar, ba jimawa aka tare agidan wata tsohuwa ce ta tare wadda ta shigo har gidan su hassana tai musu sallama a matsayinta na makociyar su.........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

18

Koda wannan tsohuwar ta gaishe da hadiza se hadiza tai kicin kicin da fuska lokacin tana zaune tana bada wake da shinkafa.
Tabe baki tsohuwar tayi zata miƙe ta fita sega hassana ta fito daga bayi tana ta faman yamutsa fuska.
Ganin tsohuwar a zaune amman tana ƙoƙarin tashi ya sanya ta faɗaɗa far'a tare da zubewa da ƙyar tana gaishe ta.
Tsohuwar ta faɗaɗa far'a itama tana cewa.
"Dama nice maƙociyar ku dana tare a wannan gidan na jikin gidan ku, Sunana Hajiya Hauwa amman ana cemin hajja ni ƴar nan cikin gari ce wata unguwa sabon titi ƴata ɗaya aduniya hafsatu tana aure a katsina amman aiki yakai mijinta abuja tana zaune acan da mijinta da yaranta, ita ma ta saimin wannan gidan bayan mahaifinta ya rasu dafatan zamuyi zaman mutunci atsakanin mu"
Hajjo ta faɗa cikin murna dayake tana da son mutane.

Wani irin sanyi hassana taji atake taji tana son hajjo tun da daman bata saba da kowa ba domin duk wanda zatai hurɗa dashi tofa yasan hadiza seya zame kasancewar hadiza ita ƴar unguwa ce.
"Nikuma sunana hassana ni ƴar ƙiru ce hussainata tana aure acan da yaranta uku se mahaifana aure ya kawoni nan bani da kowa anan se Allah seku ma ke daya kawo min dafatan zaki ɗauke ni matsayin ƴarki"
Hassana ta faɗa cikin raha.
"Aikam ammi ta samu ƙanwa" hajja ta faɗa tare da miƙewa ta kama hanyar soro wanda har waje seda hassana ta kaita sannan ta dawo.
Koda ta dawo gidan Basira mai shekara tara da zainab mai shekara takwas ƴaƴan hadiza sune suka hau yada mata magana.
Murmushi tayi ta rabesu ta wuce ɗakinta.
Kwanci tashi babu wuya wajan Allah yau ta kama laraba ta bawa ranar samu tsakar dare hassana ta kamu da ciwon naƙuda iya tashin hankali malam habu( baba ) ya shiga yayi zarya wajan hadiza yafi sau goma akan tazo ta taimakawa hassana amman taki daga karshe ma seta kunna rediyo.
A ɗimauce ya fita gidan hajja ya shiga buga mata ƙofar gate ɗinta cikin nutsuwa ta fito tana waye.
Da karkarwa baba yace.
"Nine Habubakar baban basira"
Bata gane ba amman haka ta buɗe mai ganin fuskar shi yasa taɗan faɗaɗa far'a tana cewa.
"Au lafiya malam habu?"
A kiɗime yake shaida mata meke tafe dashi da zafin nama hajjo ta koma ta ɗauko mayafi suka fita.
Lokacin da suka shiga gidan naƙudar takai ƙololuwa wajan kankama haka hajja ta tsaya tana bata taimako domin koda ance atafi asibiti ma lokaci ya ƙure domin kan ɗa ya kawo kai domin fitowa.
Ana kiran asubahin farko.
Yarinya ta faɗo duniya takwa tsanyara ƙara.
Wadda nan da nan ta cika gida da kuka hajja ta ɗagata tana mata addu'a kana ta naɗeta a zani bayan ta yanke mata cibiya.
Sosai hajja ta gyara ɗakin tare da ɗora ruwan zafi ƙarfe shidda hassana tai wanka da taimakon hajja ta gyarata tsaf taima jaririya wanka.
Ɗaki se tayar da ƙamshi yake hajja ta haɗe kayan jini zata wanke Allah ya jefo habiba kanwar malam habu mai binsa wadda ya aika aka kirata ita ta amshi kayan ta wanke.

Hajja bata bar gidan ba seda ƙanwar hassana tazo hussaina.
Wannan karamcin da hajjo tai musu yasa malam habu yayita mata godiya kamar ze ari baki abin har kunya ya bawa hajja
wannan shine silar daya sa malam habu yaji kaf unguwar bashida kamar hajja domin abin da taiwa matarshi ko mahaifiyar shima haka zataiwa matar tashi.

Ranar gidan yayi ta ɗaukar maƙota da ƴan uwa ƴan barka amman hadiza ko leƙe sema da daddare data sanya kiɗa da fanteka na habaicin ya zama uban mata.
Mahaifan hassana sun so ɗauketa tayi wanka agida amman hajja tace su bari tunda tana kusa zata dinga zuwa tana mata haka kuwa akai hajjo kullum da kalar kayan arziƙin da zata kawowa hassana banda farfesun data ke yo mata ta kawo mata sosai hassana da baba kejin daɗin abin arzikin hajjo.
Ranar suna na zuwa yarinya taci suna ummul-khairi sunan mahaifiyar malam habu innah data rasu wadda aka mata laƙabi da ummi.
Anyi taron suna lafiya angama lafiya mai jego tana cikin ƙoshin lafiya domin koda yaushe hajja tana aiko mata da abin arziƙi shima kuma malam habu yana iya bakin ƙoƙarin sa ta ɓangaren hadiza kuwa ta saki ranta sosai ganin hassana ta haifi mace.
Ummul yarinya ce fara mai kyau da ita tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login