Showing 3001 words to 6000 words out of 83661 words

Chapter 2 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11356

kwance ta furta.
"A'a baffa bakai mini komai ba rayuwarka ce duk yadda ka tsarata hakan zaka tafi da ita naji labarin kayi tafiya zuwa kano ina maka addu'ar nasara da haske idan da hali ina mai roƙonka da ka kira Abban ka,ka shaida masa da bakin ka sannan kuma karka baro kano a wannan karon bakaje gaida Hajja ba"
Tana faɗin hakan ta datse kiran.
Kamar wani sakarai yabi wayar da kallo kafin daga bisani ya fara niman layin nata da zafin shi sedai har tai ringing ta gama Ammi bata ɗauka ba.
Zubewa yayi a ƙasan lallausan carfet ɗin.

Yana mai shafo sumar kanshi dayay mata saisaye maike Damuna? ya faɗa a bayyane.
Cikin nadama ya mike yasan bai kyautawa mahaifanshi ba, har yayi tafiya daga garinsu zuwa wani garin amman ya kasa gayawa mahaifanshi waɗanda suke a gari guda? mai yasa yayi hakan idan bai manta ba har maman basma matarshi yaje yayi ma sallama a jiya amman why beje wajan AMMI da ABBA yayi masu sallama ba sannan hajja kakarshi wadda ta haifi Ammin shi tana cikin garin kano amman sam hankalinshi bai ma kai daya je mata ba seda Ammi ta tuna masa.
Sosai ya zurfafa a tunanin lamarin shi gaba ɗaya kanshi ya kulle yama rasa mai yakamata yayi.
Da azama ya miƙe ya nufi gaban mirrow a sanyaye yake gyara jikinshi bayan yayi ma kanshi ɓarin turarukan shi masu tsada kana ya nufi wajan kayanshi shirya kanshi yayi cikin wani lallausan yadi milk colour mai aikin baƙin zare yayi wani mugun kyau kasancewar shi black beauty se kayan suka amshi jikinsa hula kalar kayan ya sanya akanshi ya ɗora black shoe a ƙafafunshi se shigar tai masa mugun kyau don ya fito a ainihin yarenshi na hausa fulani.

Da sassarfa ya ƙarasa gaban takardun ɗazu ya ɗauki guda acikinsu anan ma seda yayi tsaki tuno wannan banzar yarinyar data watsar mai dasu.
Kafin ya mike wayarshi tai ringing ya ɗauka tare da ƙaro hands free.
"*BARRISTER ALIYU ALI DIKKO* idan ka kammala ina compound na hotel ɗin ina jiran ka"
Daga cikin wayar muryar wani babban mutum ta karaɗe wayar.
Lumshe idanu yayi har zara zaran gashin idanunshi na kwanciya kana ya warasu yana mai taune ƙasan laɓɓansa cike da tarin damuwar furucin Amminsa ya furta.
"Okey give me five minutes insha Allahu gani nan"
Yafaɗa da wani irin sauri yake ƙoƙarin juyawa domin fita sedai sabon kiran mai ɗauke da sabon ringing shiya cika ɗakin
Duru-duru ya shigayi don shikam ban da wayarshi mai ƙirar iphone 13 pro max bai san da wata wayar a wajan ba,
Bin inda yake jin ringing ɗin yake harya ƙarasa dai dai gefen gadon, da sauri ya ware idanunshi kan black phone ɗin dake faman ringing wadda akai save numbern da ke kira da Sis meerah.
Ƙyam ya tsaya yana noticing kafin yayi kokarin kai hannu kai harta katse still sega wani kiran ya ƙara shigowa cikin dakiya ya sanya hannu ya ɗauka tare da danna green side don ya sami damar amsa kiran da aketa faman yi cikin wayar wanda babu ƙaƙƙauta wa da alamu duk wanda ke kiran ya dangan ci mai wayar ne.
Da sauri ya kara wayar cikin kunnenshi cikin wata irin........
*TOFA*
Ko wayar waye?
Ko waye ke kiran?
Ya zata kasance da Barrister Ali dikko.......
Muje zuwa page 4
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #500 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218








_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_



*BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }

NA
*AUTAR MANYA*


HOME OF QUALITIES WRT ASS....

004


Kwantacciyar murya mai kama data wanda ke jin bacci koya tashi daga zazzaɓi koya kejin sanyi muryar Ummul dake kwance a gefen gadon su riƙe da wayar Ameerah tana kiran layinta data ke zaton tabar wayar tane a hotel ta karaɗe cikin kunnen.
Barrister A'A Dikko.
Da sauri ya zame wayar daga cikin kunnen shi tare da ɗan tsirama numbern idanu batare daya katse kiran ba kuma bai mayar da wayar kunnen shiba sannan kuma bai yi magana ba.
"mai wayar ce please a ina zan sameta?"
Wannan furucin ummul ke faman nana tawa ta cikin wayar meerah tare da tsananin jin haushin shurun da aka mata duk zaton ta ma baza'a bata wayar tata ba sabida yadda akai mata shuru don haka cike da ƙosawa da jin haushi ta ja dogon tsaki tare da cewa.
"Koba za'a bani wayar ba dan Allah abani sim card ɗina ni waya ba damuwa ta bace"
Ta kuma faɗin hakan cike da jin haushi har tana ƙoƙarin datse kiran da sauri Ameerah ta dakatar da ita sabida fatan su' samun layin koda bazasu sami wayar ba domin layin yana da matiƙar amfani wajanta don duk numbers ɗinta akan shi tai serving.

Cike da wata irin izzah wadda a zahiri shi bai ganta ba sedai ga duk wanda zewa magana ko wanda yake tare dashi ze gane yana da ita.
Cikin wata irin dakakkiyar murya mai cike da amo! ya furta.
"Idan kinje kin koyo sallama tare da iya magana seki faɗi inda za'a kawo maki babu mace mai daraja dazatai irin abun da kikai nonses"
Ya ƙarasa faɗin hakan yana jan dogon tsaki mai ƙarfi.
Sarai ya gane muryar sedai yana kokonto a inda ya santa, Jim yayi tare da hasko fuskar yarinyar da sukai karo ɗazu dashi tabbas babu ko tam tama muryarta ce acikin wayar tsakin ya kuma ja tare da zira wayar cikin Aljihunsa yabar ɗakin yana sauri domin nufar wajan baƙon shi dake jiran sa.
Da zafi zafi yake tafiya tamkar ze tashi sama sabida sauri wanda hakan shine al'adarshi komai nashi yana yinshi da zafinshi wanda har hakan yana sanyawa wasu nai masa kallon mafaɗaci ko mai zafin rai tsananin zafin namanshi yasa bai sanya akan komai daya shafi rayuwarshi.

A harabar hotel ɗin wata haɗaɗɗiyar farar mota tai parking daga ɓarin da mutumin yayi mai kwatance kai tsaye wajan motar ya nufa wanda murfin motar duk suke a buɗe emty side ya shiga ya zauna tare da aje takardar daya ɗauka a saman cinyar sa tare dayin sallama a nutse, cikin sakin fuska sukai musabaha da mutumin wanda ze girmewa A'A sosai maganganu sukai akan shari'ar dazasu soma gabatar wa A gobe talata wanda shi Aliyu shine lauyan da mutumin ya ɗauka wanda ze kareshi a kotu wanda ya kasance lauya ne mai zaman kanshi, Tambayoyi Aliyu ke jefawa Alhaji mahmud a nutse yana bashi amsa yana rubutawa wanda hakan ya sanya suka ɗauki tsayin lokaci suna tattaunawa.


Wurgi Ummul-khairi tayi da wayar Ameera tare da sanya kuka! wanda baya mata wahalar yi.
Da sauri Ameera tai wajan wayar tare da ɗaukarta tana duba wa kota fasa mata.
"Haba ummul yaya zaki jefar min da waya kinsan wuyar dana ci wajan Alhaji kafin ya bani ita?"
Tafaɗa tare da aje wayar bisa gefen gado sannan ta tsirama ummul idanu data ke faman jan numfashi mai haɗe da kuka.
"Ni banga abin kuka ba anan wayar ce aka ce baza'a baki ba? har kike yin kuka kinga in ma baza,a baki ba share zanma bangis waya yanzu ya aiko miki da wata idan yaso gobe muje mtn shop ai maki well come back daman nasan ba lallai ki sami wayar ba duba da yadda zamani ya lalace yanzu waya ma a hannun ka nuna ka ake da makami a ƙwace to bare kuma ka yarda se mutum yaga dama yake baka wani ma baze baka ba ta tafi har abada"
Ameera takai maganar tana mai sharewa ummul hawayen dake ambaliya a saman fuskarta wadda tai jajir abin ka da farar fata.
"Nifa ba wayar ce damuwa ta ba sim card ɗina sannan kuma harda gaya min baƙar magana wai bani da daraja ko a ina yasan ban da darajar oho masa"
Tafaɗa cikin kukan takaicin baƙar maganar daya gaya matan.
ɗan jim ameerah tayi tare da kallon yadda wani hawayen ke kuma zubowa ummul cike da mamaki tace.
"Kiyi haƙuri kinsa mutane kala-kala ne ina zaton shi mutum ne mai zafi ki ƙara kiranshi ki basa haƙuri ki amshi wayarki kawai a wuce wurin"
Ameerah take kuma miƙo mata wayar a karo na biyu.
"Rabu dashi na haƙura duk da nasan dagajin muryar shi yafi ƙarfin ya riƙe min wayata sedai daga duk inda ya fito mutum ne mai taƙama da izzah"
Tafaɗa tana mai share hawayen ta batare data jira amsar ameerah ba ta cigaba.
"Nifa ameerah duk damuwata a yanzu bata wuce inda zan sake ganin mutumin ɗazu ba wallahi kirjina har zafi yake ina tausaya ma kaina ban taɓa zaton soyayya na shiga tafarar ɗaya zuciyar mutum ba"
Ta kuma share hawaye.
Sakin baki ameerah tayi tana kallonta cike da ɗunbin mamakin furucinta.
"Hmm kar dai kice wannan kukan naki bana iya baƙar maganar da kika ce mai wayarki ya faɗa maki bane har da ma tarin damuwar rashin sanin inda zaki ƙara ganin masoyin ki?"
Ameerah ta jefa mata tambayar.
Ɗago da idanunta tayi.
"Hakane ameerah ina mai so na haƙiƙa ina masa wani irin zazzafan so daga kallo ɗaya naji duk na kamu na damu na ɗimautu yaya zanyi ne damuwar waya ba komai bace domin damuwa dashi tafi damuwa da kaina bare wata abar banza waya"
Tafaɗa a haukace.
"Cool down my sister kibi komai a sannu shiɗin kinsan waye? yaya yake yana da mata? ko baya da ita ze amshi soyayyarki ko baze amsa ba mai yasa zaki sanya ma zuciyarki damuwar abin da ba lallai ki samu ba nifa a yanzu kuɗi da kayan more rayuwa sunfiye min soyayya sau dubu duk mazan dana ke hulɗa dasu babu wanda nake so fatan kawai ka hauni ka bani kuɗi a bariki kuɗi nazo nema ba soyayya ba kuma bana zaton ze soki tunda duk namijin arziki baze so auran karu......."
"Dakata Ameerah"!!
Ummu ta faɗa a haukace kamar ba ita ba.
"na shanye dukkan maganganunki amman bana shanye wannan ƙazantaccen furucin naki gareni ba karuwa ita ba halitta bace koba Allah ne ya jarabceta ba.......
"Dakata ummul akwai gyara karuwa halitta ce itama Allah ne ya halicce ta amman ba a karuwa ya halicce taba A mutum bil adam ya halitto ta sedai daga baya ƙaddarar rayuwa ta mayar ta haka wata kuma son zuciya da son duniya ya mayar ta haka wata kuma hakan cikin ƙaddararta yazo kamar ni nagaya maki ƙaddara ce ta jefoni nan toke wani dalili ne ya kawo ki nan wanda ga mahaifanki a raye amman ki kasa zama gabansu se gidan karuwai Wanda duk zamana dake kin kasa gayan dalilin zaman ki anan kin kasa gayan mai yasa kika zaɓi zaman bariki akan zaman gaban iyayenki dubeki yarinya santala mai kyau wadda zata iya tsayawa ayi gasar kyau da ita amman kash kin zaɓama kanki zaman dadiro"
Cewar ameerah cikin tsananin jin haushin ummul.wadda har yanzu taƙi sakin jiki taci arzikin jikinta duk da dandazon mazan dake rubibi akanta.
Se wani banza can daga karo dashi zata ɗaga ma kanta hankali akan shi.
"Ameerah duk naji furucin ki gareni amman ki sani hakan bai sanya naji komai ba kuma banji na tsaneki ba don kinmin halacci a rayuwa sedai akan wancan mutumin tabbas zamu iya samun matsala dake idan har zaki shiga hurumin soyayyata dashi dalilin zamana anan kuma akwai lokaci idan yaxo zakiji komai sedai idan kin gaji da zamana a kusa dake zan iya tashi daga gidan ma gaba ɗaya na matsa na baki waje, maganar karuwanci kuwa tabbas wasu da son zuciya wasu kuma ƙaddarar suce tazo da hakan sau tari wasu mutanan suna aikata kuskure ne batare da son zuciyarsu ba kamar yadda ƙaddara kan shigowa mutum batare dayay tsumin taba haka ƙaddarar soyayyar A'A ta shiga zuciyata batare dana tsammace taba kuma soyayyata dashi bata buƙatar kishiya sabida haka dukkan kalaman ki gareshi yazamana kin sanya ɗa'ar harshe cikinsu"
Tafaɗa da sauri tare da tashi tana mai kokarin nufar wajan kayansu.
Da wani irin hanzari ameerah tabi bayanta tare da rungumeta ta sanya kuka.
"Kiyi haƙuri da dukkan kalamai na dan Allah karki gujeni tsananin haushin shiga damuwarki ga wanda bai damu dake bane ya sanya na gaggaya maki magana amman zomu mu zauna nima na goyi bayanki ƴar ƙanwata
Ta janyota suka koma gado suka zauna.
Share hawayenta tai tare da kallon yatsun hannunta tana wasa dasu batare data ƙara furta komai ba.
"Babu ɗa namijin daya isa ya ganki bai ƙyasa ba komai izzarsa ina son kiyi amfani da bariki da kirsa tare da albarkatun jikin ki wajan janyo hankalinshi duk ranar da kikai ido biyu dashi ki tabbatar jikinki ya haɗu da nashi daga ranar nasan dole ya darajaki ya martabaki yakuma amshi soyayyarki ta ƙarfi da yaji"
ANYA HAKA NE?
Dayake idanun ummul rufe yake daso yasa take amsar darasin ameerah har ta aminta da hakan don yanzu yadda maza suka zama mayun mata dole in kana son jan hankalinsu seka haɗa da wannan.
Sakin ranta tayi ta cigaba da sauraran darasin ameerah mai cike da bariki tsantsa wadda ba mis.
Seda ameerah ta gama cika ummul da maganganu kamar tana da sanin ummul zata haɗu da A'A kafin tai murmushi haɗi da cewa.
"Ki saki ranki maza karɓi waya ki ƙara kiran wancan guy ɗin ya kawo mana wayarki sabida kinga akwai numbern mutanan mu ciki nima duk na damu"
Dayake Ameerah ta bata shawara akan sahibin ta yasa ba musu ta amshi wayar ta kuma danna kiran layinta.
Lokacin Barrister A'A Dikko har sun kammala magana da baƙonsa sunyi sallama tuni ya koma ɗakin daya sauka sanye yake da guntun wando yana zaune bakin gado hannunshi da black tea yana waya da basmah tana ta zabga mai shagwaɓa gaba ɗaya ta gama kashe mai jikinshi.
Jin kiran wayar daya tsinta wadda ya aje gefen gadon shi ya sanya yaɗan katse kiran basmah saninta mai zafin kishi akansa taji ƙarar wata wayar yanzu se ai gurmi.
Da ɗan sauri ya ɗauki wayar tare da karawa a kunnenshi.
"Assalamu alaikum dan Allah a ina zan amshi wayata"
Ummul ta faɗa sakamakon tirsasawar da ameerah tayi mata.
Lumshe idanu yayi haɗi da cewa.
"Ashe kin gane kuskuren da kikai a farko ok ina city star hotel room 5 amman sanin darajar ƴa mace yasa zan maki alfarma da ki bari zuwa gobe insha Allahu zan kawo maki har gida"
Yafaɗa yana ƙoƙarin kashe wayar.
"A,a nikam yau nake buƙatar wayata zanzo na amsa na hutash sheka base kazo ba"
Ƙittt! ta katse kiran tare da kallon ameera data gama sauraran maganarsu domin wayar tana hands free ne.
Ganin da sauran lokaci kafin ayi kiran sallar magarib yasa ummul tashi tsaye batare data wani tsaya dogon shiriba da hijabin datai sallar la'asar ta nufi hanyar fita hannunta riƙe da keyn motar ameerah data ɗauka domin ta iya draving
Tasan city star ɗakin ma data zauna a ɗazu yake dan haka babu wani ɓata lokaci ta fice motar ta hau tare da nufar hotel ɗin.
Shiko tsananin mamakin yarinyar ya kamashi amman dayake nan ɗin ba baƙonta bane dalilin ganin tan dayay a ɗazu yasan ya bai wani sha mamakin hakan sosai ba wayar shi ya cigaba dayi da basmah data kuma kiranshi har tsayin lokaci gaba ɗaya jikinsa ya mutu da salon shagwaɓar data ke mai ta cikin wayar.
"Please Baby zan ƙara watsa ruwa kafin ayi kiran magrib don duk kin sakar min da kasala ina jin yammmm ajikina"
Yafaɗa tare da datse kiran tashi yayi tare da nufar bathroom hannunshi dafe da hajiyarshi datake son fara harbawa.
A tsaye ya dafe bango yana sakarma kanshi ruwa yana lumshe idanun shi tsayin lokaci ya ɗauka a hakan kafin yaji ɗan sauƙin feeling ɗin dake taso mai ya ɗaura tawul ya fito a gaban mirrow ya tsaya tare da tsirama fuskarshi idanun shi dasu kai jajir.
Dai dai lokacin Ummul ta ƙaraso cikin hotel ɗin da sauri take taka step harta hau saman adai dai inda suka haɗu ta dakata kafin ta watsar da damuwar ta nufi room 5 jan handle ɗin ƙofar tayi duk zaton ta xataji ta a rufe da key amman cikin mamaki setaji ta a buɗe amman batai mamaki ba don tace mai zata zo amsar wayarta dan haka babu wani dogon tunani ta tura ƙofar ta kutsa cikin ɗakin kai tsaye.
Sallamar dake bakinta ita ta maƙale sakamon idanu biyun da sukai da wanda bata kawo ko zato ko tsammanin ganin shiba da sauri ta ƙara ware idanu a jikin madubin dakin dake hasko mata fuskarsa, mai ya kamata tayi kuka ko dariya? da wani irin sauri shawarar ameerah data bata, ta faɗo mata aranta babu wani dogon lissafi ta nufeshi da sauri wanda shikam baima san da shigowarta ba sakamon bayan daya bawa kofar da kuma tunanin daya ke faman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login