Showing 24001 words to 27000 words out of 83661 words

Chapter 9 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11347

tana jinjira take da shiga zuƙatan mutane duk faɗan babansu wanda yaran sa ke mugun tsoron sa baya hana ya dauki ummul yana jefata yana furta.
"Uwata tafi ta kowa"
Ahaka sukai arba'in suka rankaya zuwa ƙiru seda tai sati biyu ta dawo gida lokacin data dawo kuma al'amura suka sauya domin baba ya cinye jarin shagonsa baya zuwa ko ina se zaman gida talauci na saka shi cin mutunci domin hatta ƴan cinikin hadiza ma wani bin aguje yake binsu.
Da ƙyar suke sha haka zalika makarantar boko ma yace su basira zu dawo gida shi bai da kudin biyan kuɗin wata.
Ganin haka yasa hadiza ta mayar dasu da kanta.
Rayuwar gidan ta koma se a hankali ɗan tuwon da ake samu ana yi ada yanzu yafi ƙarfin su,, ummul nada wata biyar hassana ta samu ciki wanda malam habu yayita surfa masifa shifa sedai a zubar bai da abin da ze ciyar dasu kuka hassana ta sanya domin itama tafi buƙatar zubar da cikin fiye da komai sabida a yanzu ma datake da ƴa ɗaya cin cikinta na gagararta bare kuma ta kuma samun wata ƴar.
Ahaka hajja tazo ta tarar da wannan masifa wanda nan ta rufe shi da faɗa akan cewar yayi haƙuri yawan haihuwa daga gareshi ne bada ga matan ba idan har baze kauda kai ba to suma bazasu dena ɗaukar ciki ba, sabida tsananin kunyar hajja yasa yabar maganar zubar da cikin amman dai kam cin mutunci kullum yana tsakar gida yana yinsa kuma dole hadiza ta zubo mai wake da shinkafar ta na saidawa yaci.
Ummul bata isa yaye ba hassana ta yayeta hajja ta ɗauketa yarinyar bata da wani kuzari sabida shan cikin datai amman yadda hajja ta zage tana bata kayan gina jiki yasa ummu ta ciko tai kyau.
Shekarar ummul ɗaya hassana ta haifi ɗiyarta mace sadiya.
Sabida jarabar baba ko kallon sadiya baiyi ba ko ranar suna ma mahaifin hassana shiyayi hakika.
Sadiya nada shekara guda hassana ta haifi kausar daga kausar ta haifi ihsan.
ko wanne ya bawa ɗan uwan sa shekara guda abubuwa sun ma hassana yawa wadda ummul ke ce mata.
(BAMU) ma'anar shi Babarmu.
Kaf ƴaƴan babu mai iya wanke wa ɗan uwan sa pant ga yara ƙananu basu san babu ba.
Cikin haka Allah ya kawo masu allurar riga kafi anan wata nurse ta bawa hassana shawarar akan taje asibiti ai mata allurar tsarin iyali domin ta sami ta zara acikin haihuwar data yawan yi.
Ranar litinin na zuwa hassana ta goya ihsan suka tafi asibiti anan aka yo mata allurar ta dawo gida.
Abu goma da ashirin sunwa hassana caa domin mahaifin ta dake taimakonta sunyi hatsari a hanyar zamfara shida mahaifiyarta sun rasu sosai rasuwar ta kaɗa hassana nan da nan ta rame acan ta zauna har akai kwana sha huɗu kafin ta dawo gida.
Hajjah ke taimakonta ganin abin na yawa yasa ta fara ɗaura kayan miya haka baba ze rance kuɗin kuma tai magana ya ci mata zarafi.
Rayuwar gidan ta kacame yanzu hadiza ta dena kishi da bamu sabida kowa ta kan shi yake kowa fafutukar abin da ze rufawa kansa asiri yake daman hadiza ita yarant uku kuma bata kara haihuwa ba sannan kuma manya ne saɓanin bamu data ke da ƙananun yara nan da nan girma ya soma saukar mata sabida wahala ga cin mutunci baba wanda idan ya dasa cin mutunci jikinsa har rawa yake sabida talauci babu abin da baya sakawa.
Shikenan kullum yana gida ba cass ba as yana tsakanin mata yana karɓe ƴan canjin su ahaka zuciyar sa ta mutu har yamo ma baya fita aikin koya samu sedai yaci yasha ya tafi majalissa yana buɗa hanci.
Sukuwa su hassana tsabar tsoron shi yasa basa iya yi masa musu ko gardama ga dik abin da ya san yasu.
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400




*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

19


Kwanci tashi asarar mai rai tafiya na tafiya shekaru suna ja.
Yanzu haka ummul takai shekaru goma a duniya sadiya tara kausar takwas ihsan mai bakwai.
Abubuwan rayuwa sun ƙara kacamewa sabida yanayin da ake fama dashi na tsadar rayuwa, Yanzu gyaɗa Bamu take kasama ummul a bakin layi ta saida to kuma kusan koda yaushe ta kasa mata gyaɗar ita keda asara sabida ummul irin yaran nan ne masu shegen sanyi tana kai gyaɗar yaran layin ke mata wayo su cinye wani bin sadiya ke ƙwatar ta ga hajja na masifar son ta amman tsabar ƙulaƙucin uwa ya hanata zaman gidan hajja kullum tana manne da mahaifiyarta.
Ranar wata talata da daddare wata maƙociyar su mai suna talatu ta shigo gidan siyan awara wadda ummah keyi da daddare zuwanta keda wuya ta tarar da baba ya dasa kujera yana danna cin mutunci wa ummah wadda ta sunkuyar da kanta tana kuka.
Seda ya ƙare cin zarafin sa sannan ya kaɗa rigarsa ya tafi.
Daya ke shi haka yake muddin yana faɗa wa iyalansa ko baƙo ne ze shigo gidan bafa ze fasa tashin hankalin daya ke ba haka ze gama ya tashi ya barka da jin kunya.
Kallon ummah talatu tayi tare da cewa.
"Wai daman hadiza har yanzu malam habu bai dena wannan faɗan nashi ba?"
Share hawaye ummah tayi tare da cewa.
"Kedai bari talatu wallahi kullum halin malam sake ƙaruwa yake, masifar yau da ban ta gobe daban yanzu ma akan yace na bashi rancen naira ɗari ne dan na hanashi yake min wannan cin zarafin to adashi ne rancen malam wanda ba'a ɗauka ɗari hamsin nidai ya ranta yafi sau a ƙirga"
Tafaɗa cikin takaici.
Muskutawa talatu tayi tare da cewa.
"Ai mutane ke ɗorawa kansu masifar rayuwa tun farko malam habu bai da ƙarfi amman yasan ya masifar ƙara aure azuciyarsa wannan ma ya zama cutar da kai da kuma mugunta kai baka iya riƙe kan kaba ina ga mata har biyu ga yara yanzu kaf unguwa yi ake dashi ga masifa yayita zagin ƴaƴan mutane ya koma kamar taɓaɓɓe kai naka yaran babu arabi bare boko"
Talatu ta faɗa tare da ɓallo goro ta garza.
"Kedai bari kawai talatu, ai duk wanda baiji bari ba yaji hoho! inji bahaushe ada ai na ɗaga hankalina daya auro ta amman dana gane idan tazo ma ƴar gusau zata ci yasa na saki raina ai seda wadata kake kishi talatu a kullum na kwanta tunani na ɗaya a abun da zamuci da yaran nan ita kuwa haka zakiji cikin dare yaran na kukan yunwa idan tace babu se suce abasu babun suci waccan tsohuwar ke taimakon ta yau da gobe se Allah itama yanzu ba koda yau sheba"
Hadiza takai maganar da ƙarfi abinka da bebe.
Gyara zama talatu tayi cike da tausayawa tace.
"Amman hadiza kema da laifin ki tayaya naki ƴaƴan zasu ci su sha na kishiyarki suna kukan yunwa har kina bada labari cike da nishaɗi"
Talatu ta faɗa cike da rashin jin daɗi.
"Kinga talatu daya tashi ƙara auren nina ce ya ƙaro? jaraba dai irin ta namiji yawanci talakawan maza sunfi masu kuɗi jarabar son ƙara aure kana tare da matarka ɗaya ta rufin asiri ka tashi ka ƙaƙabo auren da baka da yadda zakai dashi"
Ummah ta faɗa tare da miƙewa dan ƙara zuba awarar ta a kasko.

"Haka ne hadiza sedai idan anduba ƙaddara da rabo sune lin zamin komai auren malam habu ƙaddara ce daga Allah kuma ina za'a kai waɗannan kyawawan ƴaƴan data haifa?"
Aifa jin wannan furuci yasa ummah ta fara zazzagawa talatu masifa abin ka dama da kurma ganin tana neman tara mata mutane yasa talatu tayi saurin tashi ta nufi ƙofar ɗakin hassana.
Lokacin hassana tana bawa ihsan koko wadda take ta kukan zazzaɓin daya kamata sedai rashi yasa ba'a sayo mata magani ba.

Sadiya da kausar da ummul sukuma suna cin tuwo wanda nan ma dambe suke har sadiya ta danne ummul tana ƙwaƙwular na hannunta daya ke tafita ƙarfi.
Cikin tausayawa talatu ta dubi hassana tare da cewa.
"Sannu maman kausar Allah ya kawo muku ɗauki"
Share hawaye hassana tayi tare da sakin murmushi taɗan dafe cikinta bata ce komai ba sabida yunwar data keji amman sabida yaranta basu ciba yasa ita ta haƙura ta tura musu guntun tuwon ranar da akai agidan wanda ya samu da ƙyar ya kawo rabin kwanon gari.
"Bata jin daɗi ne naga tana ta nishi?"
Talatu ta faɗa tare da taɓa jikin ihsan.
"Eh bata jin daɗi wallahi zazzaɓi ke damun ta"
Cewar hassana tare da janyo ihsan jikinta sosai.
"Zo nan ummi zokije shagon sabo ki sayo maku garin kwaki da sugar sekije wajan wancan mai allurar ki siyo mata maganin zazzaɓi"
Talatu ta faɗa tare da zaro ɗari biyu daga haɓar zaninta.
"A,a sedai sadiya ummi sanyin ta yayi yawa"
Cewar hassana tana sakin murmushi.
Tura baki ummul tayi sega hawaye yana zubo mata, Amman sabida rashin maganar ta setai shuru.
Godiya hassana tayiwa talatu kamar zata ari baki har seda talatu taji nauyi.
Bayan fitar sadiya talatu ta dubi hassana tare da cewa.
"Hassana yanzu rayuwa ta sauya munafurci yayiwa mutane yawa su bazasu taimaka maka da ƙwandala ba amman zasuyi cinikin gulmarka na dubu, Ni kin ganni nan bana jin kunyar nema kuma bana munafurcin wani abayan idanun sa kowa gulmarki yake a unguwar nan na yadda kika saki ƴaƴanki ba arabi ba boko dai dai da ummi bata saka pant sabida talauci, kuma su bazasu taso su gaya miki gaskiya ba sabida tsoron masifar bebiyar kishiyar ki"
Kuka hassana ta sanya tare da cewa.
"To talatu yaya zanyi tunda nazo garin nan bani da kowa bana hulɗa da kowa sabida gudun zuciya, Waccan tsohuwar hajja ke taimakona nikam har na gaji da hidimarta garemu,Mijina babu ta sanya shi ya zama mafaɗacin ƙarfi da yaji iyayena babu rai bare su taimaka min hussainata iyali sun mata yawa ga rasuwar mijinta to yaya zanyi da raina ƴar gyaɗar idan na soya babansu ya rance kuɗin nayi magana ya zageni tass"
Tafaɗa tare da fashewa da kuka!
Da sauri ummul ta zo ta rungumeta tana share mata hawayen ta cikin ƙuruciya take cewa.
"Ki dena kuka bamu inna girma zan siya miki mota na kaiki makka amman bani bawa baba mai miki faɗa"
( hattara iyaye maza masu cin mutunci uwa a gaban ƴaƴanta wallahi ku sani komai kayi yaro yana ƙullace da abin aran shi )
Tsananin tausayin su ya sanya talatu hawaye!
Cikin damuwa talatu tacewa hassana.........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

20


"Ki dena damuwa insha Allahu ni zan taimaka miki, Amman ina son dan Allah dan Annabi (s.a.w) kada ki nuna ni na taimake ki sanin halin mijinki ze iya ta kakkiya har gidana ya cimin zarafi ina zamana ƙalau"

Talatu ta faɗawa hassana wadda take sharewa ummul hawayen ta dake zuba kamar famfo.
Sallamar sadiya ita ta hana hassana magana da sauri ta miƙe ta ɗauko ƙatuwar silva ta karɓi kwakin ta juye ta bawa sadiya tace taje ta jiƙa musu sannan ta ɓalli magani ta bawa ihsan bakin ta yaƙi rufuwa da godiyar data kema talatu.
Sadiya ta zuba suga cikin kwakin tare da cokula tazo gaban hassana taja hannun ummul akan tazo suci.
Share hawaye ummul tayi tare da tashi taje ta ɗauko kofi ta ɗibi kwakin tare da ƙarasawa gaban hassana ta kamo hannun ta.
Muryar ta a tausashe tace mata.
"Bamu kici rabona ni naƙoshi ki daure ki dinga tsakurar abin ci koya ne kina ci, idan kika faɗi kika mutu yaya zamuyi da rayuwar mu"
Cak talatu tayi tana kallon madarar ƙaunar ƴar da uwar lallai ƴa mace rahma ce ga al'ummah.
Amman ga waɗanda basu san darajara haihuwa ba se su dinga dangana haihuwar ƴaƴa mata da bala'i musamman irin su malam habu kaiba mai kuɗi ba amman ka ɗauki tsanar duniya ka ɗorawa ƴaƴa mata, Domin takurar sa ma ga matan nasa yana da nasibi da haihuwar matan da sukai masa.
Murmushi hassana tayi tare da amsar kwakin.
Sannan tace.
"Kingan ta talatu wallahi idan ban shaba itama bazata shaba wanann jin ƙai na ummi na rasa irin son data mini"
Murmushi talatu tai.
"Sekina mata addu'a daga sharrin mutum domin naga alamun gidan nan ba ƙaunarku ake ba kar aje ai amfani da ƙaunar data ke miki a tarwatsa mata rayuwa musamman idan aka hango zata ji ƙanki"
Murmushi hassana tayi.
Bata ce komai ba domin ita bata yadda tai maganar hadiza agaban kowa duk abin da take mata dannewa take bata magana.
Cikin son ta katse wannan maganar tace.
"To ina jinki talatu wani taimako zaki min muna magana sadiya ta shigo zanyi magana kuma haɗin kwaki ya ɗauke min hankali"
Gyara zama talatu tai tare da cewa.
"Kin ganni nan ban yarda zuciyata ta mutu akan se lallai namiji ya tallafa mini ba bahaushe yace idan dama taƙi se abi ta hagu! hassana yanzu fa sekai da gaske bare ke mai ƴaƴa mata nan da shekaru kaɗan zakiji maganar aure dan haka kibar bacci kibar ƙullah gyaɗa tashi xaki ki zama mace mai kamar maza kiyi sana'ar da zata baki cida sha harma da, Kuɗin makarantar yaranki Ki cire tsoron malam habu kizo mu haɗa kai na sama miki gidan aikin dazaki tawo dana dare acan ke zakici na rana ga kuma albashin ki"
Talatu ta faɗawa hassana cike da bata ƙarfin gwiwa.
Ƙifta idanu hassana ta shiga yi wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa.
Kafin kuma tace.
"Ai talatu baze yuwu ba maganar nan kamar ƙanzon kurege ce kin san tashin hankalin baban su baze yarda na fita aikatau ba"
Tafaɗa cikin sanyin ta.
"Haba hassana ke kamar ba mace ba ai bazaki ce masa aikatau zaki ba cewa zaki abincin ƴan makaranta zaki dinga dafawa ana baki albashi"
Tiryan tiryan talatu tagama tsarawa hassana yadda zata gayawa baba wanda duk ta gamsu taiwa talatu godiya taraka ta har soro kana ita ta dawo cikin gida.
Malam habu bai dawo gida ba se sha ɗayan dare tabarma ya shinfiɗa a tsakar gida gefen shi ƙullin tsire ne yake ci seya haske tsakar gidan da fitila yadda bazaka ga mai yake ciba hassana tayi sallama can gefen sa ta zauna gidan tsitt alamar mutan gidan sunyi bacci.
Haɗe rai yayi tare da ce mata.
"Lafiya dai uwar sadiya kika zo kika tsayamin akai na saƙeƙe"
Mayar da tsinin daya tokaro mata tayi tare da cewa.
"Allah nagode masa daya sa dai ƴaƴan naka ne babu damuwa dan ka dangana ni da uwarsu"
Tafaɗi maganar a ɗan fusace domin ta fuskanci magana ya gasa mata.
"Dariya ya sheƙe da ita tare da ƙara ɗauko tsiren shi ya wulla cikin bakin shi.
"Ada nai farin cikin auren ki sabida ina kwaɗayin samun ɗa namiji daga gareki domin ko banza ya dinga taimakona wajan aiki to ƙarin bala'in kema seki kaita jero mata waɗanda babu abin da suka sani se ci da sha se kawo ƙarar gidan miji"
Yafaɗa cikin fushi.
"Malam kenan ina guje maka ranar da zakai kukan farin cikin haihuwar ƴa mace ranar zakai kukan kunya ne bana wani abu ba, sannan kuma maganar aure jaraba ce kawai irin taku ta maza kai baka ƙoshi ba baka wadata gidan kaba baka da yadda zakai da mata biyu ka tashi kai aure kuma kaine kake da ƙwan haihuwar mata bani ba domin ni bazan wa kaina ciki ba, tun farko inda nabi maganar abokan aikin ka da bazan aure kaba amman ni ina yadda da kaddarata ƙaddarar ƴaƴana ita ke zaune dani agidan nan tsananin rabo ne yasa na aure ka amman rabona da jin daɗin gidan ka tun ranar da ummi tai kwana arba'in aduniya"
Tafaɗa tana mai zubar da hawaye.
Ai seya hauro ya dinga surfa bala'i yana ɗaga muryar da har maƙota sesun jisu.
"Hassana ni kike gayawa haka? yaushe kika sha miyar birni har kikai kilewar mayar min da magana hassana?"
Ya kuma kiran sunanta yana yowa kanta kamar ze daketa.
Nan da nan zuciyar fulanin ta motsa mata ta juya harshe sabida hausarta bata fita tar tar.
Magana take mayar mai da zafi wadda ta bawa malam habu tsananin mamaki koda yake daman mai haƙuri bai iya faɗa ba.
Ganin faɗan nasu yaƙi ƙarewa yasa hadiza ta fito tana janye hassana wadda take furta.
"Malam ka sake ni nikuma bazan bar gidan ba sabida ƴaƴana zanyi zaman su mai za'ai da ƙaddararran auren ka"
Da ƙyar hadiza takai hassana ɗaki tare da bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login