Showing 27001 words to 30000 words out of 83661 words

Chapter 10 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11353

haƙuri amman itama mamakin taurin zuciyar hassana take domin idan ita ce bazata iya gayawa malam ɗin haka ba.
A daren ranar babu wanda ya rintsa a tsakanin malam da hassana, shi tsananin mamakin ta ya hanashi bacci ita kuma nadamar abin da taiwa mijinta uban ƴaƴanta ya hana ta bacci.
Sabida haka asubar fari ta lallaɓa zuwa tsakar gida lokacin yana alwala ze fita ta rissuna ta gaishe shi bai amsa mata ba dan haka ta cigaba da bashi haƙuri tana share hawayen ta.
Taga ɗan sassauci saman fuskar shi dan haka hankalinta yaɗan kwanta ta koma ɗaki ta tashi su ummul akan suje suyi alwala suyi sallah.
Tun wajan shidda kausar ta sanya kukan yunwa cikin faɗa hassana tace.
"Dan uban ki bani da abinci ko babu zan baki?"
Buɗar bakin kausar se cewa tayi.
"Eh Bamu ki bani babun naci"
Sautin dariya taji daga tsakar gida wadda hadiza take yinta da iya ƙarfinta tana faman sakin habaici tana cewa ƴaƴanta suzo suci abinci.
Kafin taga malam akan ta yana muzurai.
"To hassana naji dukkan batun ki najiya dan haka daga yau babu ni babu ƴaƴanki babu sabuluna bare omo abinci ma na dena baku gaki ga ƴaƴan naki nan kiyi zaman su"
Fuwwwww ya fice yabar mata ɗakin.
Hannunta ta ɗaga sama hawaye na zuba tace.
"Ya Allah ka kawo mani mafita"
Ta shafa gudar hamsin data yage ta bawa ummul tace taje ta siyo koko wanda kausar da ihsan zasu sha................
😭😭*Akwai dubban hassana a gidan miji suna fuskan tar irin haka*
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

21

A hankali ummul ta yayibo wani farin hijabi amman tsabar tsufan dayayi yasa ya koma milk colour ta sanya ajikinta.
Tare da amsar hamsin ɗin ta fita waje garin tsit sabida lokacine na sanyi ahankali take jan ƙafafunta harta ƙarasa wajan mai sayar da kokon ta tsugunna ta gaisheta haɗi da bata gudar hamsin ɗin
Juya kuɗin mai kokon take don hamsin ɗin bazata amsu ba amman tsabar tausayin yaran yasa ta amsa tare da zuba mata,kokon daya fi na kuɗinta ma yawa.
Sosai ummul tai mata godiya ta yo hanyar gida.
Adai dai ƙofar gidan hajja taga mota fara a fake wadda tun lokacin fitowarta ta farko taganta amman tsabar sauri yasa bata tsaya kallon motar ba, Allah ya bawa ummul son kallo dakatawa tai tana kallon kyan motar kamar wata ƴar ƙauye.
Sannu Ahankali ta nufi gate ɗin gidan hajja yaushe rabon data shiga gidan tun ranar datai mata fitsarin kwance yau kusan sati biyu kenan bata ƙara leƙawa ba ko hajjan tazo gidansu ɓuya take.
Tafiya take cikin gidan kamar munafuka har ta ƙarasa tsakar gidan tana gab da shiga cikin falon hajja taga namiji zaune saman kujera ƴar tsugunno yana brush.
Da sauri taja baya tana ƙifta idanu sam bata kawo zataga wani ba.
Matashin saurayine black colour kyakykyawa mai manyan idanu haɗi da kwantaccen saje daya haɗe da gemun shi jikinshi ba riga se guntun wando daya tsaya iya cinyar shi.
Kwantaccen gashine baƙi ya ƙewaye ilahirin fatar jikinsa har cinyarsa da hannunsa ga wani irin baƙin gashi a saman kirjinsa ya kwanta ya zagaye nippy ɗinsa.
Rintse idanu ummul tai jikinta yana rawa zuciyarta na bugawa dana sanin shigowa gidan hajja ya cikata.
Aguje tayi ɗakin hajja tana mai yarda kokon hannunta wanda ta fallatsawa wannan matashi ajikinsa shi sam bai ma kawo da mutum a wajan ba zafin kokon ne yasa ya ɗago da dara daran idanunsa yabita da kallo taɓe bakinsa yayi tare da wanke inda ta ɓata mai ya wuce ciki.
Dayake hajja tana ɗaki yasa ummul tabita can.
Dan haka yana shiga falon hajja bai ganta ba ya wuce ɗakin daya sauka ya shirya sauri yake sabida kar lecture ta wuce shi yazo yin wani course ne nan bayero!akan aikin shi na lauya, duka duka wata ɗaya kawai zeyi ya koma.
Ƙamshin daddaɗan turarensa yasan ya ummul ƙara maƙewa a bayan gadon hajja tana ƙifta idanu sanye yake cikin manyan kayan dasuka fito da surar kyansa na yaren hausa fulani ya zauna bakin gadon hajja suka gaisa .
Hajja ce ta nuna mai ummul wadda taƙi yarda ta haɗa idanu dashi.
"Ka ganta ita ce ƴar raino ta taimin fitsari ta gujeni"
Dariya ya saki marar sauti batare daya ce komai ba.
Ya zira hannu cikin aljihunsa ya ɗauko ƙatuwar chocolate ya bawa hajja yace ta bata.
Kana ya soma magana cikin ɗan faɗa kaɗan.
"Amman hajja wannan ƴar renon taki bata sallama sannan bata iya gaisuwa ba yakamata a koya mata"
Yana gama faɗin haka ya wuce yayi tafiyarshi bayan shi ummul tabi da kallo a haƙiƙanin gaskiya bazata ce ga kamannin saba sedai tace mai yana da faɗa yana da kyauta.
Hajja ce take dariya ta janyo ummul ta bata chocolate ɗin haɗi dayi mata faɗan rashin sallama.
Se lokacin ummul ta tuna da aiken Bamu kallon hajja tayi tare dacewa.
"Hajja bamu ce ta aikeni na siyowa ihsan koko wallahi agarin kallon wancan ƙaton na zubda"
Tafaɗa tana mai ƙoƙarin zubo da hawaye!
Hajjace ta dube ta a tsanake tace.
"Karki ƙara ce mai ƙato jikana ne sunan shi baffa! sannan kije kicin ki ɗauki taliya a kula ki kai mata sannan ki bata haƙuri"
Ƙifta idanu ummul tasoma cikin tsoro tace.
"Nikam hajja tsoro nake ji kar naje bamu tace na biyo tanan na roƙe ki"
Faɗa hajja tahau mata wanda yasan ya ta ɗauko kular ta fice.
Koda taje gidan bamu faɗa tahau yi mata kamar zata ari baki.
Kuka ummul ta sanya tana bata haƙuri da ƙyar ta amshi taliyar tare da makawa ummul worning akan kada ta ƙara biyawa ta gidan hajja da safe.
Alhamdulillahi kowa yaci taliyar ya ƙoshi harma tai saura.
Ƙarfe sha biyun rana talatu tazo domin jin yadda bamu sukai da baba aikam bayan zaman talatu hassana tana kuka tana wassafa mata halin data ke ciki.
Shawarwari talatu ta bata sannan tace mata tazo suje gidan,Data samar mata anan gaban sune can ciki.
Hassana ce ta shirya tare da barwa ummul amanar ƙannenta suka rankaya suka fita.
Sosai suka sha tafiya sabida shi gidan da zata fara aikin acan cikin unguwar yake ɓangaran masu hannu da shunin arean haka suka ƙarasa cikin layin gidane na gani na faɗa na masu hannu da shuni.
Talatu ta buga ƙofar gate mai gadi yazo ya buɗe masu.
Gaisawa sukai da talatu sanin yasan ta tana kawo wa masu gidan ƴan aiki yasa yace su zauna a saman banci domin masu gidan basu tashi ba.
Zaro idanu hassana tai cike da mamaki ƙarfe 12 amman basu farka ba amman ga mamakinta setaga talatu tace mata.
"Taso ki rakani gidan nawa aikin ki tayani kafin nan sun tashi,kinsan ita matar gidan nan ƙawar uwar ɗakina ce wadda nakewa aiki to ina kawo mata ma'aikata basa zama ne"
Ba musu hassana tabi talatu wanda layika uku suka rabasu da wannan gidan dasuka bari.
Abin mamaki talatu da kanta taje ta zubo musu abinci suka ci sannan sukai wanke wanke bayan sun gama sukaje falon matar gidan suka zauna ƴaƴan gidan sunata tsokanar talatu ahaka matar gidan tazo itama cikin barkwanci suka gaisa da talatu har tana janta itama.
Sosai abin ya bawa hassana sha'awa lallai ba kowani mai kuɗi bane yake da wulaƙanci wani zakaga yasan darajar ɗan adam gadai uwar ɗakin talatu da ƴaƴanta kamar bama su kuɗi ba sam basu da reni bare girman kai.
Tambayar talatu matar take akan hassana tas talatu ta kwashe komai ta gayawa matar.
Sosai matar ta tausayawa hassana cikin kwantar da murya tace.
"Hajiya timo bata da matsala tana da kirki xakiji daɗin ta matsalar ta ƴaƴanta ita da mijinta basa ganin laifin ƴaƴansu amman indai kika iya zama da ita xakiji daɗinta"
Sosai ta bata shawarar yadda xata zauna da uwar ɗakin nata daza'a kaita wajanta.
Har azahar suna gidan amman rabin hankalin hassana yana kan ƴaƴanta.
Seda sukai sallah sukaci abinci har talatu tai guzirin wani sannan sukai sallama uwar ɗakin talatu ta bawa hassana taliya kusan leda goma da dubu uku da sabulai.
Sosai hassana tai mata godiya suka wuce gidan da za'a kaita ɗin.

Koda suka koma wannan karon mutan gidan sun tashi babban falo ne talatu tayi sallama ciki babbar mace hakima zaune aƙasan carfet wata matashiyar yarinya na mata tausa.
Zubewa sukai suna gaisheta kadaran kada han ta amsa musu ba kamar uwar ɗakin talatu ba.
Jikin hassana seyay sanyi amman haka ta daure tana jin yadda talatu take gabatar da ita a wajan hajiya timo ɗin kamar yadda taji uwar ɗakin talatun ta faɗi sunanta.
"Kin gaya mata girki ne kawai zata yi mana zata zo 7 sabida girkin ƴan makaranta idan ta gama tai na rana tai na dare ƙarfe biyar zata tafi bani da matsala da abinci nidai sata ce ban so da ƙazanta albashinta dubu ashirin"
Ada hassana ta yanke shawarar ta fita bazata dawo ba amman jin ruwan kuɗin albashin yasa taji ta amince zata yi aikin kodan ƴaƴanta.
Washe baki talatu tayi tare da cewa.
"Godiya muke hajjaju"
Bata wani damu ba tacigaba da cewa.
"Wannan yarinyar ameerah itake wanke wanke da sharar falo waje kuma maza keyi, idan kin gama abinci ki ci anan ki ɗiba ki tafi dashi ni duk ban da damuwa matsala ɗaya ƴaƴana ba'a sasu ba'a hanasu komai zasuyi babu ruwanki gidan ubansu ne sannan koda ɗan ƙaramin sune yasaki dafa mai wani abun to kome kike sekin aje kin girka masa"
Hajjiya timo ta faɗa cike da taƙama...........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

22

Da sauri talatu ta amsa tare da cewa hajiya timo.
"In sha Allahu hajiya za'a kiyaye da girman kujerar ki"
Ta ƙare cike da fadan ci.
"Yanzu ameerah zata nuna miki store seki duba abin da babu kiyi list insha Allah gobe seki fara zuwa tun wuri"
Da sauri talatu tace.
"A,a hajiya karki damu inda hali ma yau zata fara yi muku na dare"
Ita talatu ta faɗa mata hakane sabida kwaɗayin ta samu na daren ita kuma hassana haushin talatu taji na yadda tace zatai zaman yin na dare sabida tabar ihsan ba lafiya sannan bata bar ko sisi agidan ba.
Murmushi hajiya timo tayi a karo na farko sannan tace.
"To babu damuwa ai mana tuwon semo miyar kuɓewa ameerah kaita kicin"
Tafaɗa cike da bada umarni babu yadda hassana ta iya haka tabi bayan ameerah amman ta dawo da baya tacewa talatu ta tafi mata da wannan taliyar gida wadda matar aikin talatu ta bata tace mata takaiwa sadiya ta girka dan sadiya tafi ummul girman jiki da komai.
Hakan akai talatu taiwa hajiya timo sallama wadda ta bata 2k ta tafi tana ta godiya.
Ita kuma hassana wata kwana suka miƙa tare da shiga cikin wani katafaren kicin wanda aka zuba kayan more rayuwa cikinsa ƙofar store ɗin ciki suka buɗe suka shiga babu abin da babu na kayan abinci dan haka ameerah tana nunawa hassana ta koma.
Kimantar sanwar tayi ta ɗora ruwan tuwon da zafin nama take haɗa kayan da zatai miya da taimakon ameerah hassana ta kunna gas ta ɗora tukunya sannan ta mayar da hankali akan haɗin miya cikin ƙwarewa da iya sarrafa girki ta soma gabatar da tuwon semo ɗin miyar kubewa wadda tunma kafin ta gama kamshi ya cika gidan na daddawa da kayan ɗanɗano
Wajan magariba ta sauke tuwon ta kwashe ma mutan gidan itama ta ɗibi nata dai dai kima

Miyar kuwa seda aka idar da sallar magariba ta sauke ta sabida yadda tabar ruwan ya ƙone miyar ta haɗe jikinta waje ɗaya.
Zuzzubawa tai a kula ta soma jigilar kaiwa daining ɗin dake falon.
Seda ta gyara kicin ɗin sannan ta ɗauki nata abinci taiwa ameerah sallama ta wuce gida domin bata ga ƙeyar mutan gidan ba.
Allah Allah take takai gida har tana tuntuɓe hankalinta yana kan yaranta

Lokacin data kai ƙofar gida malam habu na dawowa daga masallaci kirjinta ne ya buga amman seta nuna ko in kula ta cigaba da yunƙurin shiga cikin gidan.
Bata ko kalle shiba.
Sallama ɗauke a bakin ta sadiya wadda take jan ruwa a rijiya takwa saki gugan ya faɗa rijiyar duk akan murnar ganin mahaifiyar su ta amshi kayan kan bamu takai ɗaki tana ta mata sannu.
Wannan guga data faɗa rijiya ita ta haddasa masifa a gidan sabida basira ƴar hadixa zata ɗibi ruwa ta tarar da sadiya ta jefa guga nan ta hau cin mutunci har hadiza ta fito ta amshe har tana cewa bamu bata san daga inda ta fito ba kota fara yawon maula ne.
Toshe kunnen hassana tayi bama zakace akwai mutum agidan ba.
Alwala tai ta soma sallah sannan ta zaunar da yaranta tana tambayar su yaya suka wuni.
Sosai ummul take bata labarin irin yunwar da sukaji amman da kausar taje wajan babansu akan ya basu kuɗi su sai gari seya korota

Rufe kausar bamu tai da faɗa tana cewa bata yarda ta ƙara zuwa wajan babansu karɓar kuɗi ba tunda tasan baze basu ba

Suna idar da sallar isha'i suka ci tuwon su suka ƙoshi wannan 3k ɗin da matar aikin talatu ta bata ita ta ƙulle ta saka yaran agaba ta kaisu makarantar islamiyya ta dare gaba ɗaya a aji ɗaya aka sanya su sabida rashin ilimin da tun farko basu dashi aikwa nan ƴan aji suka fara yi masu dariya daya ke sadiya ba ƙyalle bace yasa tai musu tass nan yaran suka lafa musu.
Koda aka tashi daga makaranta suka kamo hanyar gida kuma a daren sukaita bitar karatun su, hadiza kuwa seta sami na yada habaici a tsakar gida lallai kishi kishine yana ƙoƙon zuci domin wannan ɗan sauyin da hassana ta samu se hadiza kuma ta kwana tana zubda magana a tsakar gida.
Haka garin Allah ya waye hassana ta jera yaranta agaba zuwa wata makarantar gwamnati dake can ƙasansu tunda duk sun isa zuwa hatta ihsan mai shekara bakwai.
Wajan shugaban makarantar taje tai masa bayani akan cewar zata sanya ƴaƴanta a makaranta amman yayi mata haƙurin uniform se ƙarshen wata.
Da tausayawa yace ai babu damar ɗalibi yazo makaranta babu uniform dan haka karta damu akwai daman uniform ɗin da wata ƙungiyar tallafawa marayu take aiko musu dashi duk ze basu godiya tai masa sosai a wannan rana su ummul suka shiga aji wanda ita aka kaita uku sadiya biyu kausar da ihsan ɗaya kuma babu laifi sun ɗan taɓa karatu tunda suna ji daman wajan su sakina suna biyawa a gadarance.
Daga makarantar yaran gidan aikinta ta wuce koda taje taɗan makara anan ta gamu da wata tsagerar yarinya mai suna mima

Sosai ta tsare hassana tana mata masifa akan ta shanyasu batai musu break fast da wuri ba wadda yarinyar a haife bata fi sa'ar sadiya ba.
Tuno gargadin hajjiya timo yasanya ta ƙasƙantar da kanta tana bawa ƴar cikin nata haƙuri wadda take kamar ana tunzurata.
Dama wasu ƴaƴan masu kuɗin suna da haka suna jin feeling iyayen su nada shi zazu taka kowa bare su da aka ɗaure musu gindi.
Da rawar jiki hassana ta ƙarasa kicin agaggauce tai musu abin kari sedai koda taje kai musu, watso mata wani saurayi yayi a fuska yana taɓe baki tare da cewa ya bata minti goma ta sako masa da wanda ya gaya mata a lokacin.
Cikin ɗumbin mamakin rashin kunya da tarbiyar yaran hassana ta juya zata koma dan tai mai abin da yace ɗin

Tsawa ya daka mata akan tazo ta kwashe wanda ta zubda haka ta rissunawa ƴaƴan agabansu ta kwashe ta nufi kicin.
Ranar dai hassana wunin sauke ɗora tai kuma dan iskanci baifi suyi loma biyu ba zasu ce tazo ta ɗauke kwanikan ameerah ce tace ta samu katuwar kula tana juyewa ta tafi dashi gida in ba haka bama ashara za,a zubar.
Ranar ma hassana bata koma gida ba se bayan magariba

Koda taje yaranta sunyi girkin su da wannan taliyar sunci sun wuce islamiyya ga kayan bokon sunan a ninke tsaf.
Ɗaga hannu tai tana kwarara yabo da godiya ga sarki Allah abisa canjin daya kawo musu ko a haka ma tana godiya gare shi ta fita ta dawo ta tarar da ƴaƴanta sun tafi makaranta kuma sun sami abin taɓawa lallai taji daɗin wannan canji data samu.
Alwala ta fita tayo itama ta tayar da sallah se lokacin ta sami nutsuwar cin abincin ta.
*Uwa kenan! innah uwa mafi uba koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login