Showing 60001 words to 63000 words out of 83661 words
ni zanje wajan ƴan uwanka su ɗaura mata aure amman wallahi bazan bari kacinye waɗannan kuɗi a taru aji kunyaba kasan kai kunya gaba ka bata ba baya ba"
Hadiza ce ta fito tana mai janyo hannunsa.
Cikin kirsa tace
"Kaima dai malam kasan tsintacciyar mage bata mage meye zaka ɗaga hankalinka akan auren ƴar data shekara biyu bata gabanka waya sani ba ko seda yaron ya gama ƙwaƙwuleta kafin ya aure ta"
Tafaɗa tana mai ƙoƙarin janye shi zuwa ɗakinta.
Ai da wani sauri bamu ta fito tana mai bawa sadiya ajiyar jakar kuɗin agaban hadiza ta tsaya tare da ce mata.
"Ko da zina suke kullum da yaron, Naji daɗi daya fito ya aureta kinga zina tayi riba kenan, ta dai fi waɗanda suke kawo maza har soron ubansu aka gama watsewar kuma ba'a aure suba kuma tafi waɗanda suke gaban iyayen nasu kyan gani tunda ta zama fitila acikin gidan nan kuma insha Allah sekin ci arziƙin auren ummi ƴar baƙin cikin banza"
Bamu ta faɗa tare da komawa ɗakinta fuww kamar ba ita ba.
Sakin baki hadiza tayi tana kallon bamu wadda tai mugun bata mamaki don tunda suke bata taɓa ganin tai mata hakan ba.
"ki dena mamaki hadiza kaɗan kenan daga halin ɗan adam keko ƴarta zata je abuja dole tai mana haka"
Malam ya faɗa yana mai ficewa daga gidan.
Ita ko bamu lissafin kuɗin tayi ciff takuma lissafa abinda zatai dasu na hidimar auren ƴar tata sannan tai musu mugun ɓoye tana jiran Allah ya kawo innah hussaina taje kasuwa ita da sadiya.
Wanka ummul ta shiga bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando na pakistan kasancewar ameera ta kawo mata kayanta nacan gidan.
Tana zaune tana yanke ƙunba Hajja ta shigo ta aje mayafi tana cewa.
"Washh Allah ummi kawon ruwan sanyi mana"
Kallonta ummul tai a nutse tace mata.
"A,a dai marar sanyi hajja kinsan likitoci sun hanaki shan ruwa mai sanyi"
Firfita hajja take da hannunta tana goge zufa da mayafi sabida babu nepa ga rana yau ta fito shine yasa ake zabga mugun zafi agarin.
"Kawo min nasha ummi duk nagaji sabida zirga zirga kekuma yau bacci kika sha kamar wadda tai wani aiki"
Dariya ummul tai kurum taje ta kawo mata ruwan.
Hajja tasha sannan tace.
"To yau dai maitar ki seta koma an kawo miki kuɗi harda sadaki an tsaida magana nan da sati guda zaki tare gidan baffa sekije kita ƙunsar takaicin matarsa tunda haka kikaji kika gani, Daman nace miki ai tunda yace min ze aureki da gaske yake kuma Allah yayi ke matar shi ce"
Ƙuri tayiwa hajja da ido tana binta da kallo kamar wata sokuwa..........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.
*Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588*
*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*
42
Ta saka tafin hannunta ta tallafe kumatunta.
Wani irin yanayi ta shiga mai wuyar a fassarashi.
Wai yau ita ce aka kawo kuɗin auren ta harda sadakin ta ko a mafarki bata taɓa kawowa zata auri Aliyu ba, Lallai Allah da girman iko yake.
"Bazaki magana ba wai ummi kin min ƙuri da ido kamar shege a rabon gado?"
Hajja ta faɗa mata hakan tana kallon yanayin ta.
"To ni hajja me zance bayan kin gama min baki"
Se hawaye shaaaaaa!
Suka soma sunturi a idanunta tana saka hannu tana sharesu gaba ɗaya jikinta yayi wani irin sanyi duk babu wannan rawar kan tamkar ba ummul ba.
Tashi tayi zuwa bedroom ɗin hajja tai kwanciyar ta a kan gado tana share hawayenta hannunta dafe da saitin zuciyarta tana furta.
"Shikenan zan ƙara shiga jarrabawa ta biyu ya Allah a wannan karon kasa nice da nasara"
Tafaɗa tana share hawayenta.
Tsintar kanta tayi da jin fargaba mai yawa na kasancewa a matar Aliyu sabida hasko yanayin yadda yake nuna mata zafin kishin matar sa.
Mirginawa tayi idanunta yana kallon rufin ɗakin.
Tana hasko girman zatin kyawun Aliyu dogone mai suffar ƙarfafan maza baƙine mai ɗaukar idanu, Yana da manyan idanu masu wani irin gashi mai yawa, girarsa cunkus itama take da gashi, ga wani saje wanda ya kwanto ya haɗe da gemun sa, haka nan saman goshinsa akwai tabon sallah ataƙaice Aliyu yana da kyau mai tsayawa a zuciya.
Zare idanu tayi tana hasko yadda girman jikinsa yake tsoro ne fall ya cika zuciyarta sabida yadda ƙirar jikinsa take a murɗe tasan ba ƙaramar wuya zataci ba duk ranar daya ratsata,Kirjinta ne yake halbawa sabida tuno azabar da sameer ya gana mata se wata irin damuwa ta shigeta ta yadda zata fuskanci Aliyu a daran amarcinsu kowace mace burinta takai budurci ɗakin mijinta domin shine cikar ƙimarta sedai ita mummunar ƙaddara giftacciya tazo tayi mata shamaki da nata budurcin.
Kuka take sosai harda shashsheƙa tana jin zuciyarta na mata zafi.
Daga can falo taji hajja na magana kamar a waya sekuma taga ta shigo ɗakin tana cewa.
"Amshi ummi ga baffa"
Gabanta ne yaɗan faɗi kaɗan ta ɗago kumburarrun idanunta tana duban hajja kafin ta saka hannu ta amshi wayar a hannun hajja wadda ta juya ta fita.
A hankali ta ɗora wayar a saman kunnenta.
Huci yaɗan fesar kaɗan tare da ce mata.
"Assalamu alaiki! ina kwana"
Da sauri ta firfito da idanunta waje tasan gatse yayi mata domin dutyn ta ne bana shiba.
Ɗan zamewa tai kaɗan tare da cewa.
"Kayi haƙuri, Ina kwana"
Tafaɗa muryarta can ƙasa.
Wani irin yanayi Aliyu ya faɗa mai wuyar a fassara shi.
Daga nashi ɓangaren yaɗan gyara kwanciyar sa tare da lumshe idanunsa yana shafa saman kanshi yace mata.
"Kukan me kike na murnar zaki sami muradin zuciyarki ne kona wani abu daban?"
Ware ido tai tana wasa da yatsanta guda tare da cewa.
"Niba kuka nake ba"
Tafaɗa cikin shagwaɓa.
"Ƙarya kike kuka! kike mana oya tell me na mine?"
Ya faɗa hausarsa zam ta katsinawa.
"Nifa ba kuka nakeyi ba"
Ta kuma faɗa tana zumɓura baki
"Daɗina dake taurin kai, kuka kike akan zaki zo gidana babu budurcin ki sabida wancan yayi miki rape?"
Yafaɗa a dake.
Jikin ummul ne ya ɗauki rawa tamkar mazari!
Shuru tai masa tana faman jin yadda zuciyarta take luguden dokawa.
"Kibar kuka akan wannan, Budurci bashine ya kamata a duba ba, ƙaddarar data kauda shi ya kamata a soma duba wa ni wannan baya gabana ni bawan Allah ne ko kinzo ma bazan taɓa ko yatsanki ba burinki de ki aureni to kin aura amman bazan miki komai ba"
Yafaɗa yana wani irin nishi kaɗan kaɗan.
"Umm"
Kawai ta faɗa masa cike da mamakin sa.
"Dama ce miki zanyi dame dame zakiyi na bikin zan aiko miki da kuɗi ki nemi account dazan turo ni kinsan na gama hidimata tun a auren farko wannan kam iya ɗaurin aure zan halarta kaɗai, wannan ma kuɗin Abba ya bada aka kawo yau"
Wani haushine ya kama ummul na yadda yace wai ya gama hidimar shi tun a auren farko.
A tunzire tace.
"Aure dai aure ne koda a na huɗu ne kuma wayar bata na wajan kaba ai ina da account ɗina"
Tafaɗa kamar zatai kuka!
Ɗan murmushi ya saki yana mai shafa gemun sa.
"Au ke kina tunanin zan baki wannan wayar? to ko bana auren ki bazan baki wannan wayar ba bare ina auren ki wato na baki wayar ki koma magana da ƴan iskan samarin ku na hotel ko?"
Ya faɗa a dake da alamun duk shauƙin da yake ji ya gushe.
"A,a kayi haƙuri"
Tafaɗa tana mai janyo numfashinta sabida yadda ta karanci muryarsa ransa na tsananin ɓace ne.
"Ki turo min da acct dazan baki kuɗin yanzu"
"Bana so ka barshi"
Tafaɗa cikin sanyin ta.
"Idan na baki ki zubar, ke bafa zan ɗauki rainin hankalin mace ba ki fara saita yadda zaki shigo gidana idan ba haka ba......."
Ya wani ja ƙwafa tare da katse wayar yabarta baki sake.
Kawai daga nace ka bani wayata shikenan se cibi ya zama ƙari.
Tagumi ta rafka tare da wayar riƙe a hannunta.
Daga bisani seta aje wayar ta miƙe ta fita kicin ta shiga ta ɗora musu girkin rana shinkafa da wake da salak wanda salame ta siyo.
Turmi ta ɗauka ta fita tsakar gida tana daka yaji sadiya ta shigo gidan da sallama tana rafka buɗa.
Babu yabo babu fallasa ummul ta bawa sadiya kujerar data ke zaune ita kuma ta zauna a dakalin ƙofar tana dukan yajin bayan ta haɗa.
"Amarya bakya laifi gayu mutan Abuja sati war haka muna cin uwar sabada a layi"
Sadiya ta faɗa tana dariya.
"Umm sadiya nifa ba wata bida'a dazanyi wallahi, Kima aje cin uwar sabadarki maci a bikin ki"
Dariya sadiya tai tare da cewa
"Ai wallahi baki isa ba mude dole muyi rawa a bikinki zan ɗauko dj tun safe har dare ana kiɗa muna shanawa habawa bikin babbar yaya guda"
Murmushi ummul tayi.
Sannan tace.
"Sadiya yawan bidi'a ita ke kwashe albarkar aure nide Addu'arku nake buƙata"
Ta faɗa a sanyaye.
"Allah yasa kece tsohuwar gida amman se munyi"
Hirarsu suka cigaba dayi har ta gama dakan yajin suka shiga falon hajja anan sadiya ta zauna ummul harta kwashe abincin ta zubo musu ta zubawa hajja.
Bayan sun ƙare ci sukai sallah nanfa wata hirar ta ɓarke.
Sam ta mance da wani maganar account number daya faɗa mata.
ABUJA
Tashin sa yaje gidan Ammi suka gaisa kasancewar ranar sunday ce babu office anan yake jin maganar kai kuɗin auren shi wai harda sadaki a dole Abba ya saka shi gaba ya kira kawunan sa yayi masu godiya.
Duk da tun jiya Abba ya gaya masa maganar amman dai yadda yaji ankai ɗin ba karamin mamaki ya basa ba musamman dayaji Abba yace na saka biki next week.
Yana nan zaune Ammi ta kawo masa wani ruwa a jarka ta buɗe mai ya sha ta shafa mai a fuskar shi, Kamar wani yaro yake bin Ammi da kallo, murmushi ta sakar masa bai ce komai ba ya mike yayi musu sallama ya wuce gida.
Ranar basma bata nan tana wajan mamanta duba ƙafarta.
Tun safe ma ta tafi gidan nasu.
A falo ya zube yana mai zaro wayar sa domin kiran ummul sabida yadda wa'azin Ammi ya ratsa shi na cewar yayi wa ƴar mutane adalci.
Shine ya kirata a waya yana buƙatar ta turo account number ɗinta dayaji tana wannan kukan se jikinsa yayi mugun sanyi.
Maganar wayarta data yi masa yaji ranshi ya ɓaci sosai baya jin ze bata wannan wayar yana jin seya hallaka wayar ma gaba ɗaya.
Koda suka gama wayar a zuciye yayi ɗakinshi kayan sa daya je kano ya binciko ya ɗauko wayar ya xare sim card ɗin tare da wurgi da wayar ta doki bango ta rabe gida biyu ya saka haƙori ya taune sim card ɗin ta yadda baze moru ba ya jefar da wayar da sim card ɗin ta window.
Ya zauna a bakin gado yana rage kayan jikinshi yayi saura daga shi se shirt da gajeran wando.
Kwanciya yayi har akai azahar, sannan ya miƙe yaje yayi sallah ya dawo duk zaman gidan ya gundire shi ya saba kullum yana office yana aiki, Shiyasa some time's week end take gundirar shi sabida bai saba zaman gidan ba.
Wayar shi dake bed side drower tai ringing sunan Basma ya fito.
Ya ɗauka tare dayi mata sallama.
Muryarta shaƙe tace
"Amman sweet man fisabilillahi ka kyauta min mama bata jin daɗi amman ka kasa kirana kaji ya naje yaya jikin nata idan ada ne da kai zaka kawoni harma da gudun mawar kaita hospital amman yanzu duk ka sakarmin ragamar nike komai pls idan wani laifi nayi maka kamin afuwa karka juyan baya mijina"
Tafaɗa muryarta na rawa.
"I'm sorry basma wallahi na mance ne amman ki mata sannu idan na sami time zan shigo afuwan"
Yafaɗa muryarsa sanyi ƙalau tare da katse wayar yana mai mirginawa gefe tare da lalubo numbern hajja a karo na biyu.
Wayar na shiga ya wani ja ajiyar zuciya tare da harɗe ƙafafunsa waje ɗaya yana jin yadda wayar ke ringing amman ba'a ɗauka ba seda ta kusan katsewa sannan ummul datai saurin kaiwa ɗakin hajja da sauri tai masa sallama.
Cikin kamewa ya amsa tare da cewa.
"Ni ban isa nace ga yadda za'ai ayi ba kenan?"
Zaro ido tai kamar yana kallonta har tana dafe kirji kafin tace.
"Ya salam wani laifin na kuma to kayi haƙuri"
Lumshe idanunshi yayi kana yace.
"Bana ce ki bani acct number ba shine kika ƙi"
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Kaine ai kayi fushi, Zan kira ameera ta bani nata sena turo"
Haɗe ranshi yayi tamau tare da cewa.
"Ban amince ki tambayi wannan ba"
A zabure.tace.
"Ameera cefa toni bani da ta kowa"
Tsaki yaja tare da katse wayar yana jin zafin taurin kan yarinyar wani irin haushi ta bashi ya wurgar da wayar tare da miƙewa ya nufi falo don ya ɗan haɗa abinda zeci.
***********
Hannu na rawa basma ta kuma lalubar kiran shi a karo na biyu sedai taji wayar...............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.
Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588
*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*
43
Call waiting da alamun waya yake yi, cigaba tayi da kiran wayar shi tana jinta a haka ita kuma bata katse kiran nata ba seta barta tana shiga a hakan koda ya gama wayar seta ji ringing ɗin ya koma normal amman kuma harta ƙaraci ringing bai ɗauka ba.
Aje wayar tayi a gefen ta cike da zulumi ta dafe goshin ta ahaka hajiya binta ta fito daga bathroom tana ɗan dafe bango tana cije bakin ta.
Ta zauna a gefen basma tana kallon ta cikin nutsuwa tace mata.
"Baby meye kuma naga kin dafe goshi bakuyi magana da mijin naki ba?"
Tafaɗa da sigar tambaya.
Ɗagowa tayi tana share hawayen dake zubo mata sannan tace.
"Wallahi mama na kasa gane kan Aliyu yanzu ma nai mai waya ina masa complain akan cutarki ya katsen waya na kuma kiranshi bai ɗauka ba mama dan Allah ki wani abun akai karna rasa mijina"
Tafaɗa tana kuka!
Wata zufa hajiya binta ta share wadda take yanko mata.
Wata ashariya ta ƙunduma sannan ta dubi basma tace.
"Bani wayata na kira tsohon bokan daya fara mana aiki akan shi, kinsan tunda yayi mana wancan na farkon ban kuma komawa wajan shiba na sauya wasu, idan ya kama sena je ko a hakan ne"
Miƙo mata wayar basma tayi tare da cewa.
"Amman mama wannan ɗayan bokan da ƙawarki ta haɗamu dashi, danai masa waya yace wai aikin da mukai masa ne ya fara sakin sa yace anan kusa ma aiki baze kama shi ba kuma yace baze taɓa min kishiya ba, wallahi ba da ban wannan bokan ya gaya min Aliyu baze min kishiyaba dase nace ko wata Aliyu ya samu wadda yake so shiyasa yake min haka"
Tafaɗa tana share hawayenta.
"Sha kuruminki babu yadda za'ai fa Aliyu yayi aure ai mun masa asiri mai makulli baze taɓa buɗewa ba nidai zargina wannan shegiyar uwar tasa ita ke karya mana asiri, Amman idan batai wasa ba se a aikata ƙiyama"
Hajiya binta ta faɗa tana neman numbern bokan.
Zabura basma tayi tana kallonta.
"A,a mama nide ban da kisa please kar zunubin yayi mana yawa! nidai aimin abinda Aliyu ze dawo kamar da"
Bata kula basma ba ta cigaba da neman number wadda bugu ɗaya aka ɗauka aikuwa bokan ya kece da dariya.
"Maganar mijin ƴarki! kina son mallaka sedai baze mallaku ba domin ayar Allah tana aiki ajikinsa idan kikai gaggawar yi masa asiri tabbas abin ze juye akanki! ki bari nan da wata biyar kizo kafin lokacin zan san mai yake ciki amman yanzu komai ya toshe bana hango komai idan na cigaba da bincika shi zan ƙone nida aljanuna! Hahahahahaha, ko wancan aikin da aka muku ranar na gaya muku Addu'a ce bai yiba ya fita kuka ci sa'a akanshi"
Bokan ya faɗa yana mai kecewa da wata shu'umar dariya.
Sakatau hajiya binta tayi tare da cewa.
"To kinji mai yace shima kuma ɗayan kince yace a yanzu asiri baze ratsa Aliyu ba sabida haka, kije kiyi kirsa tafi asiri illah idan ma ta kama ki shigewa mahaifan nashi ki masu kwanto har mu samu waɗannan watanni su cika amman kafin watannin ma zan laluba ko zamu sami wanda ya fisu iya aiki"
Hajiya binta ta faɗa tana mai dukan kafaɗun ƴarta basma.
Cikin rashin