Showing 57001 words to 60000 words out of 83661 words

Chapter 20 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11374

inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

40


Lokuta masu tsayi ya ɗauka kafin ya samu damar fitar da abun da ke maƙale a tare dashi.
Ya mirgina can ƙarshen gado yana sakin numfashi hannunsa dafe da kirjinsa yana shafawa sannu a hankali ya kuma mirginowa wajanta yana ƙoƙarin sakata ajikinsa.


Wata zabura tai kamar mahaukaciya tare dayin gefe ɗaya tana hucin azaba idanunta ta zaro waje tana haɗe hannayen ta waje ɗaya.
A hankali muryarta cikin kuka! take ce masa.
"Please kaiwa girman zatin Allah, Aliyu karka koma second round bangama saituwa ba nagaji sosai"
Tafaɗa tana sakar masa marayan kuka!

Girman zatin Allah ɗin data faɗa ya saka kawai ya wani janyota yana rungumeta murya a shaƙe kamar ba tashi ba yace mata.
"Na haƙura basmah girman zatin Allah yafi komai amman wallahi ban ƙoshiba ban samu yadda nake muradi ba"
Yafaɗa yana mai shafa gadon bayanta.
Kirjinta na beating da ƙarfi tai lamo a bisa jikinsa burinta ya saketa taje ta duba koyay mata rauni domin wannan lamarin abin aduba shine.

Tsayin minti talati tana manne ajikinsa kafin ya zareta a hankali ya miƙe kamar wanda ƙwai ya fashewa yayi hanyar toilet wanka yayo ya fito lokacin bata ɗakin.

Ta gudu nata ɗakin

Murmushi mai kyau ya saki tare da fara goge jikinsa ya sanya singlet da dogon farin wando ya kwanta.

Ya jima yana tunanin duniya kafin bacci ya ɗauke shi.
Bai tashiba se washe gari kasance war week end ce yasa bai fita ko ina ba yana ɗakin shi tun bayan sallar asubah yayi kwanciyar shi bai fito ba se 12 yayi break fast da tea and bread ya wuce gidan Ammi.
Anan ya ɗauki long time suna tattaunawa da ita akan tsarin bikin shide baida magana daga.
"Umh"
Se
"A'a"
Har yay la'asar anan sannan ya wuce gida ranar yaga iyayi wajan basma se nan nan take dashi ranar takasance rana mai tsayawa a zuciyarsu domin sun gudanar da soyayyah kamar babu gobe duk da shan ƙamshi da yake mata hakan bai hana shi kwasar garar taba.

Washe gari ta kama ranar lahadi tun wajan ƙarfe takwas na safiya kawu Abubakar yayi wa Abba waya akan zasu wuce kano fatan alkairi Abba yayi musu sannan yacewa Ammi ya kamata ta sanar wa da Hajja zuwan nasu kawu Abubakar.

Ba musu Ammi ta kirawo hajja a waya bayan sun gaisa ta sanar mata zuwan kawunan Aliyu akan nema masa auren yarinyar datake wajanta mai suna Ummul-Khairi.
Faɗa hajja ta somayi babu gaira babu dalili tace da yanzu sedai suka ga baƙi bayan ko sanar wa da uban yarinyar ba'ayi ba mita hajja tahau yi wadda ita ta tashi ummul daga bacci ganin Hajja ta zari mayafi ta fice yasa ummul sake jan Abun rufa ta cigaba da Baccinta.


Gidan Su ummul hajja ta shiga tana kwaɗa sallama tare da cewa.
"Ina malam garba habu ina neman ka hassana duka ku fito baƙuwa ce ta alheri"
Da sauri bamu ta yayo hijabi tayo tsakar gida tana cewa.
"A'a lale maraba da hajja ki shigo ciki mana"
Lokacin Baba shima ya fito daga ɗakinsa ido duk kwantsa da alamun daga bacci ya tashi.

Washe baki hajja tayi tare da ɗaga murya yadda hadiza zata jiyota tace.
"To hassana wannan zuwa bana zama bane na ari bakinku na ci muku albasa yanzu haka baƙi daga katsina sun tawo nemawa jikana auren Ummul-khairi shiyasa nazo sanar muku domin kutara ƴan uwan da zasu amshi sadaki"
Ai da wani gudu hadiza ta fito tsakar gidan har tana yada zanin jikinta tana cewa.
"Kur'anin Allah ba'a isaba ina zaune da ƴaƴana na mutunci basuyi aure ba se wata watsats tsiya can data gama ta zubar a titi za'azo neman auren munafurci"
Tafaɗa tana wata irin zundumo ashar!
Sakin baki hajja tayi tare da kallon hadizan kafin ta kawar da kai ta rangaɗa buɗa tana cewa.
"Mugun abu kayi bacci yace banyi ba ido na biyu! to bari kiji hadiza ni hajja hauwa bakanuwar usul jikana shine ze auri ummi da yardar Allah babu wani ɗan tsubbu daya isa ya dakatar da wannan Aure tunda rabbana yace kunfayakun! shiyasa ma na kwaza a tsakar gida domin irin ku ƴan mahaha"
Hajja ta faɗa tana cigaba da buɗa.
Itako Bamu kuka ta saki tana mai fuskantar alƙibla tana cewa.
"Allah nagode maka bani da bakin godiya gareka nagode maka rabba nagode maka rabba Allah ka ƙarawa Annabi daraja Amin, Komai nisa jifa ƙasa ze faɗi"
Bamu ta faɗa tana mai sakin ƙayataccen murmushi.
Shiko malam Habu wata dariya ya saki kamar sakarai yana cewa.
"Hajja hauwa mun gode ƙwarai da wannan abin arziƙi nagode"
Wani irin dariya hajja ta ƙara saki tare da cewa.
"A'a garba bar godiya yaro shiya ganta yace yana so bani na haɗasu ba kai nama yi maka ta bebe ban ma san randa suka haɗu ba seda yazo gidana itama tazo sannan yace ina na santa nace masa ai ɗiyata ce ummi, To kaji ɗan wajan hafsatu ne ɗiyata ta abuja yana nan lauya ne mai zaman kanshi"
Dibi dibi hadiza ta soma tana yarfe hannu tana rantse rantse su basira ƴaƴanta suka fito suka jata ɗaki rannan nasu a haɗe.
Hajja ta bisu da laƙadi'ja'akum.
Ta tofa musu ta dawo da hankalinta kan su baba wanda yake ta kokarin fita sanarwa da ƴan uwanshi waɗanda suke ƴaƴan maza zar.

"Dakata malam habu ai yanzu zuwa zakai aje a share sitroom ɗin gidana a wanke ai shinfiɗa wadda zasu zauna tunda bana aje komai a sitroom ɗin"

Bamu ce tayi ɗaki cikin sauri har tana harɗewa ta taso sadiya da kausar suka fito tsakar gidan.

Tace musu su ɗebi ruwa da tsintsiya da omo su shiga gidan hajja su gyara sitroom ɗin hajja baƙi zasu zauna waɗanda zasu kawo kuɗin,Ummi tsalle su sadiya suke haka suka wuce domin aiwatar da abin da bamu tace masu.

Sannan ta taso Ihsan ma ta bata kuɗi tace taje ta siyo, Ruwa katan uku lemo katan uku na baƙin.
Sannan ta dubi hajja tace mata.
"Bara naje gidan mai adashi na amso dubu goma wadda za'a bawa baƙin tukwici sena zo na kirawo hussainata a waya"
Jikin bamu duk rawa yake dan tsananin murna.
Buɗa hajja ta ƙara saki tana cewa.
"Babu ragagge se kasashe she ina mata kuzo kuyi koyi da halin hassana biyu kyautar Allah mace mai kama da maza jiba abin da namiji ya kamata ace yayi ita ta zage tana yi Allah yayiwa nema Albarka hassana Allah yasa sanadin auren ummi ya zama sanadin hutu agare ki"
Hajja ta ƙarasa tana zabgawa habu harara wanda yayi ƙofar gida domin nufar wajan ƴan uwan shi.
Murmushi bamu ta saki tana cewa.
"Hajja kenan ai kowace uwa tagari burinta taga ta aurar da ɗanta wanda ta haifa Allah na gode maka zuwa gobe ma zan shiga kasuwa siyayyar abin da ba'a rasa ba"

Da farin ciki hajja ta koma gidanta lokacin har su sadiya sun kammala gyaran sitroom sun goge tiles ɗin tas bayan sun wanke.
Sannan sukai shinfiɗa ta tabarma da dardumai turaren tsinke kausar ta siyo da ɗan kuɗinta na gullisuwar saidawar data ke.
Suka saka a ɗakin sannan suka rufo shi suka wuce gida.

Lokacin ihsan ta shigo da lemukan dan haka su sadiya suka taimaka mata wajan kaiwa sitroom ɗin gidan hajja ɗin.

Shiko malam habu yaje ya sanarwa da yaya a wajansa tare da amininsa maganar kawo kuɗin ummi sosai suka cika da mamakin yaushe akai neman har aka magantu yarinyar da bata gabanshi.
Shide malam habu farin cikin rabuwa da ummul yafi masa komai haka ya koma gida ya sauya kaya duk wani hidimar da namiji yake ta karɓar kuɗin auren yarshi Bamu ta gabatar wanda sana'ar data keyi ta saida mai da ita Allah ya dube ta tayi komai cikin rufin asiri wanda inda bata sana'ar da sedai a taru aji kunya ( mata sana'a tayi a daure a nemi sana'a da wata wadda tazo zata sai littafina nace mata 300 wai bata dasu sabida bata saida komai mijinta ne yake bata, kuma sunyi faɗa baze bata ba ta sani: tsananin mamakin halin mutuwar zuciyar wasu matan ya kamani: gani de bani da wasu shekaru masu tsayi a rayuwata amman kullum fafutukar neman na kaina nake domin na rufawa kaina asiri daga halin roƙo ko maula,tare da matuwar zuciya: wata tana ganin bazata iya rubutu ba wai wahala nikuma ban taɓa ganin wahalar shiba domin halak ɗina nake nema ta hanyar amfani da baiwar hannuna da tunanina wanda Allah ne ya bani ikon yin hakan Alhamdulillahi Ya Allah)

Duk budurin da ake ummi bata da labari bata ma tashi ba se wajan 12 tayo brush ta zauna tana break fast sedai tana mamakin yadda taga hajja nata kaiwa da komowa alamun girki take harta kammala ta zuba jallof ɗin taliyar a ƙaton kular abinci ta haɗe cokula da farantai tare da ƙaton fulas ɗin shayi.
Tayi waje dasu.
Wajan ƙarfe ɗayan rana manyan motoci guda biyu suka dira a ƙofar gidan hajja motocin da seda suka tsorata mutan layin sabida mata har leƙe ake dan ganin tsala tsalan motocin.
Baba ƙarami abokin Aliyu shiya janyo su kawu Abubakar, a cikin motar farko wanda Fahad ɗan kawu umar ya janyo su kawu usman da ƙannen babansu Abba a mota ta biyu su takwas ne cif mutane huɗu a motar farko mutane huɗu a ta biyu se drever's guda biyu fahad da baba karami.
Kawu Abubakar kawu usman kawu umar da ƙannen mahaifan su mutum biyar wanda ya kama su takwas kenan harsu baba karami su goma.

Baba karami ne daman yay musu jagora zuwa gidan hajja dan shi ya sani tunda sun sha zuwa da Ali, gidan.
Yanzu ma shiya nufi gidan yaja ƙofar ya shiga da sallama yana cewa.
"Ina ƴar tsohuwar kike ga na nesa sun iso"
Da murna hajja ta fito tana cewa.
"Lale mara ba da muhammadu barka da zuwa"
Dayake haka take gaya mai sunan shi na gaskiya kasancewar baba ƙarami shike auren sarat ƙanwar Aliyu mai binshi.
Cikin wasa da dariya suka gaisa da hajja tai mai iso sitroom anan ya fita ya shigo dasu kawu Abubakar hajja wadda ta gyara sosai cikin nutsuwa ta je suka gaisa da surukan nata sannan ta leƙa ƙofar gida anan taci karo da sadiya zata shigo cemata tai taje wajan babanta tace mai baƙin sun ƙaraso sadiya ta juya wadda fahad yabi da ido tun daya ga tawowar ta yake kallonta kasancewar yana jikin mota ne shi.
Seda yaga ƙarasowar hajja sannan ya je suka gaisa ya koma cikin mota.
Da rawar jiki malam Habu ya ƙarasa wajan ɗan uwanshi da abokin shi ya sanar musu zuwan baƙin.
A tare suka rankayo har sitroom ɗin hajja ba laifi kan lokacin su kawu sun sha ruwa da lemo harma wasu sun ɗan tsakuri abincin da hajja takawo masu.
Gaishe gaishe aka fara cikin girma da mutunci sannan kawu umaru ya nemawa ɗansa Aliyu auren Ummi wajan kawunta.
Malam shafi'u wanda suke ƴan maza zar da malam habu.
Babu wani ja in ja suka basu nan akai addu'a tare da miƙa kuɗin aure naira dubu ɗari biyu sadaki naira dubu ɗari wanda ya kama dubu ɗari uku ciff.
Jikin malam habu rawa ya ɗauka tun anan idon sa ya rena fata ya fara ganewa ashe haihuwar ƴaƴa mata akwai riba.
Domin harya hasko tayar da jarin tiredar sa da wannan kuɗi.
Cikin neman alfarma kawu usman yace a basu aure nan da sati biyu masu zuwa.
Dan tsabar bada kai malam habu yace shi konan da kwana uku suka ɓuƙata ma a shirye yake.
Takaicin hakan yasa abokinsa zungurinsa.
Murmushi kawun su abba ya saki yace.
"A,a ba'a haka mun dai bar shi nan da sati ɗaya mai zuwa ayi addu'a a shafa zamu koma"
To haka ta kasance akai addu'a aka shafa malam shafi'u ya kawo dubu goman bamu ya basu a matsayin tukwici amman fafur suka ƙi amsa sedai lemon da bamu ta siya da ruwa abokin malam habu ya ɗauka yakai musu mota.

Sallama sukai da Hajja suka wuce.
Cike da farin ciki.

An tsaida maganar auren ummi da Aliyu nan da sati ɗaya masu zuwa.

Malam habu yayi gidan sa da kuɗin a jakar da suka zubo, bayan ya amsa wajan abokin shi yace wa yayan sa su riƙe wannan dubu goman da bamu ta bayar ta tukwici kuji mugunta.

A tsakar gida ya dakata yana kiran bamu.
Hassana fito nan maza"

Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.



Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon
kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588





*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

41


Muryarsa ta ƙaraɗe tsakar gidan.
Cikin sauri Bamu tayo tsakar gidan sabida kiran irin kirane na ɗaga hankali.

A gabansa taja kujera ƴar tsugunno ta zauna shikuma seya nemi dakalin rijiya ya zauna wannan jaka ya ɗauko ya buɗeta bakinsa fal murna.

Zaro idanu bamu tayi tana kallon ruwan kuɗin waɗanda bata taɓa ganin irin suba tunda tazo duniya sabida bata taso agidan masu wadata ba haka nan batai aure a gidan mai wadata ba.


"Hassana ƴarki tayi goshi wato ko a tarihi ban taɓa ganin wadda tai goshin ummul-khari ba lallai ta cika ummul-khairi uwar Alkhairi duba nan duk kuɗin auren tane dana sadakin ta"
Sunkuyo wa bamu tayi tana kallon kuɗin tana ƙara zare ido ba daban hajja tace jikanta bane da seta ce sayar mata da kan ɗiya za'ayi.

Gyara zip ɗin jakar yayi tare da mayar da ita saman cinyar shi sannan yacewa bamu.
"Alhamdulillahi dukkan yabo da godiya sun tabbata ga sarki Allah, Haƙiƙa Allah shine abin godiya a ko ina kuma a koda yaushe, Sabida haka waɗannan kuɗaɗe ni zan ɗauke su na juya su na tada jarin tireda ta kinga ma dinga samun na cefane aciki"

Tunda ya soma faɗin haka bamu take kallon shi bata ce mai ƙala ba har yakai aya. sannan tace

"Haba malam ko a gidan jahilai ban taɓa jin inda akai haka ba a kuɗin aure akwai na gaisuwar iyaye akwai na kuɗin aure akwai na sadaki, Na gaisuwar iyaye shine zamu raba na kuɗin aure kuma a aje a saiwa yarinya wani abun, Na sadaki kuma haƙƙinta ne halak malak bamu da wani ƙarfi akan sa idan har ba wannan yarinya ce tace tabar mana ba, to bare ma muda bamu da ƙarfi ai kamata yayi a raba kuɗin nan asai abin da yake na dai dai na daga cikin kayan ɗaki sannan mu ware na hidimar biki tunda abun yazo gab kai a matsayin ka na uba bakai yunƙurin yi mana wani abun kuzo ku gani ba se ƙoƙarin handama da baba kere"

Tafaɗa babu wani tsoro agareta daman ance mai haƙuri bai iya faɗa ba idan ranshi ya ɓaci.
"Ikon Allah hassana ni kike gayawa waɗannan zafafan maganganun akan kuɗin auren ƴata ta halak ba shegiya ba to nacinye kuɗin ko hukuma bata isa ta karɓa ba bazan bada ko taro ba akaita gidan mijin tsirara daman ai a tsirara tazo duniya nifa burina na rabu da alaƙaƙai ko gidan mafiya ne taje muddin zata bar gabana haba ƴaƴa mata ko jidali wato bayan gama raino da ɗaukar ragama harda wani kayan ɗaki da wata hidimar shirmen biki to bazan yiba"

Buɗa bamu ta saki mai ƙarfi tana tafa hannunta tana masa dariya sannan tace.
"Alhamdulillahi daɗina da gobe saurin zuwa! yau kai da kanka kake cewa ummi ƴarka ce aini na ɗauka shegiya ce nayo cikinta a waje na shigo da ita gidan nan kai inba tsabar rashin kunya ba har kana da bakin ce musu ƴaƴanka, ka manta cemin kayi na riƙe su har abada ƴaƴana ne to Alhamdulillahi ko zan haifi ƴa mace na yar watarana zata mini rana andena binka ta sauƙi malam tunda baka da kirki wallahi kuma ka bani kuɗin nan tun kafin ajimu dakai ai wallahi ba da ban hajja tace kaje wajan amsar kuɗin ummi ba da bazan bi takan kaba ni zan samo masu karɓar mata kuɗin kuma insha Allah ummi gidan arziki zataje ba gidan mafiya ba daman nasan kwanto kayi kaga kuɗi amman wannan ƙiyayyar taka tana ƙoƙon ranka"

Bamu ta faɗa tana mai waftar jakar a hannunsa tayi ɗakinta da ita.
Zabura yayi yana mai cewa.
"Hassana kizo ki bani kuɗin auren ƴata ke wace irin shu'umar mace ce ne hassana idan baki bani kuɗinnan ba sedai ƴarki ta nemi waliyi ranar ɗaurin auren ta"

Shewa tayi tare da cewa.
"Dama ai bakai bane waliyinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login