Showing 54001 words to 57000 words out of 83661 words
da cewa.
"Sannu da hidima Allah yayi miki albarka kinyi matiƙar kyau"
Fari tayi da idanunta tare da ware hannunta taɗan sakosu a gefen kafaɗunshi tare da furta.
"Nagode mijina ga abincin ka can a falo na jiran ka"
Lumshe idanu yayi tare da cewa.
"Kinyi sallah de ko?"
Murmushin dake fuskarta bai gushe ba har yanzu tace masa.
"Eh nayi tun ma ɗazu"
Ta tashi tsaye ta kamo hannunshi suka fita falo.
Kujera ta ja masa ya zauna ta shiga serving ɗinshi.
Farar shinkafa ce da miyar ganda se lemon data zuba mai a cup ta ɗora spoon cikin shinkafar ta tura masa gabanshi.
Kashe mata ido ɗaya yayi tare da cewa.
"Ke kinci?"
Shagwaɓe fuska tayi tare da gyaɗa masa kai alamar "eh"!
Bisimillah yayi tare da ɗaukar spoon ya fara juya abincin.
Lomar farko yaɗan yatsina fuska sabida mugun yaji da gishirin daya yi yawa acikin abincin.
Aje spoon ɗin yayi tare da kallon ta.
Sannan a hankali ya ɗauki cup ya tsiyayi ruwa yasha tare da miƙewa yabar daining ɗin.
Sororo tayi tana bin bayan shi da kallo harya ƙarasa cikin falo ya zauna a one seater ya ɗauki remote yana serching chanel.
Ƙarasowa tayi gabanshi ta zauna a ƙasa tana bin fuskar shi da kallo tasan idan batai mashi magana ba idan zasu kwana a haka shi baze mata ba sabida rashin maganar shi.
"My Sweet man"
Tai amfani da ƙaramar murya wajan kiran sunan nashi.
Bai amsa ba, itama bata jira cewar shiba tace.
"Naga bakaci abincin ba kama taso baka kulani ba?"
Tafaɗa kamar zatayi kuka!
Seda ya ɗauki manyan lokuta bai ce mata ƙala ba sannan daga baya yace mata.
"Basmah wai akan girki munta samun matsala dake kenan? babu yadda za'ai ki girki naci a kwanciyar hankali? yanzu shi wancan yajin da kika lafta a miya ai seya kasheni, Gaskiya bazan juri rashin iya girki ba dan nagaji da siyan na restuarant shekara biyar da aure amman kusan koda yaushe sena fita sayan abinci kona ci agidan ammi, Sabida kinfi bawa aikin ki mihimmanci akan zama ki girki mai kyau ki kula da mijinki koma kina gidan idan kinyi girkin baya daɗi why basmah nagaji gaskiya"
Ya ƙarasa maganar da ɓacin rai.
Tunda ya soma maganar take bin fuskarshi da kallo wato daga jiya zuwa yau Aliyu ya sauya hali kenan jiya yayi mata cin mutunci yau ma kuma yazo yana mata idan yasan irin manyan lokutan data ɓata wajan haɗa mai wannan girkin da baze mata haka ba.
Cikin takaici tace.
"To naji nagode bazan kuma ba"
Zata miƙe yace.
"Dakata ni zaki bawa wannan amsar kamar wani sa'anki? look basma bafa zan ɗauki renin hankalin kiba, Idan har baki sauya ba wallahi zan baki mamaki and kuma daga yau na soke fita aiki ki zauna a gida kema kamar sauran mata"
Yana gama faɗin haka ya miƙe ze tashi tayi saurin riƙo rigarshi cikin kuka tace.
"Dan Allah karka min haka please ina son aikina yadda ban taɓa haihuwa ba wannan fitar ita take ɗebe min kewar yara"
Yadda take kuka kamar ranta ze fita yasa jikinsa yayi sanyi ture hannunta yayi tare da cewa.
"Naji amman daga yau babu wata fita aiki harse kin min girki kin gyaran gida nan da two weeks zan kawo mai aiki dan bazan iya zuba ido gidana kamar kango ba"
Wata zabura tai kamar mahaukaciy tayo kanshi da wani ihu! take cewa.
"Ni wallahi bana son mai aiki babu wata macen da zaka kawon gidana ko tsohuwa ko yarinya"
Wani banzan kallo ya jefa mata ya wuce bedroom ɗinsa ya datso ƙofar waya yayi dasu Ammi sannan yayi nafila yayi kwanciyar shi.
Washe gari tun wajan 7:00am ya shirya cikin black suite yayi matiƙar kyau ya fice office.
A ranar bai samu kanshi ba se dare sabida ayyukan da suka tarar masa.
Daga nan gidan Ammi ya wuce suka gaisa yayi gida.
Kusan kwana uku Aliyu ya ɗauka yana busy sabida tarin ayyukan dake gabanshi dazarar kuma ya tashi daga office seya wuce wajan Ammi yana dawowa gida seya kulle kanshi a ɗaki yana aiki akan shari'ar da zasu fara gabatarwa on monday.
Gaba ɗaya basma ta fita a hayyacinta sabida rashin kulawar da Aliyu baya bata duk ta susuce kullum seta yiwa mahaifiyarta waya tana kuka ita kuma hajiya kwana biyu ciwon ƙafa ya hanata fita wajan malaman nasu bare taji meke faruwa.
Yau kimanin kwanaki biyar da dawowar Aliyu sedai tun washe garin ranar daya dawo basu ƙara waya da Ummul ba har yanzu.
Gaba ɗaya ummul ta koma wata iri ko doguwar hira batayi koda yaushe tana tunanin Aliyu kuma tayi alƙawarin bazata kuma kiranshi ba itama zata ja ajinta irin na mata.
Amman duk da wannan ƙudirin na zuciyarta kullum setai kuka idan ta kwanta bacci tun hajja na faɗa harta zuba mata idanu.
Kusan koda yaushe ƙannenta na gidan hajja suna hira wannan ke ɗauke mata kewa itama kuma ameerah tana yawan zuwa ziyartar ta.
Har zazzaɓi seda ta kwanta na kewar Aliyu ta riga ta saka acikin ranta son Aliyu ajininta yake.
Shima kuma daga ɓangaren shi ayyuka ne sukai mashi yawa sun fara gudanar da wata shari'a ne mai zafi shiyasa ma ko a gidan shi yana ɗaki a kulle yana bincike.
Tuni Basma tayi kwanto ta bashi haƙuri ya barta ta koma wajan aikinta sedai babu wannan sakin fuskar yanzu wani irin shakkar shi take sabida yadda baya sakar mata fuska koda yaushe fuskar shi a ɗaure.
Yau ta kama friday kimanin sati guda kenan da dawowar Aliyu.
Tun wajan 8:00pm yaje gidan ammi zaune yake yana cin tuwon semo shigowar abba yasa yaɗan dakata suka gaisa.
Seda ya kammala cin sannan Abba ya dube shi tare da cewa.
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.
Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588
*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*
39
"Baffa"
Abbah ya kira sunan shi.
A nutse ya juyo tare da tattara dukkan hankalin shi wajan Abba.
Yana mai zuba mashi idanu tare da cewa.
"Na'am Abba"
Cikin nutsuwa Abba yace masa.
"Munyi magana dakai tsayin kwanaki bakwai ina du bawa koza ka kuma bi takaina akan yadda maganar ta kaya amman naji ka shuru?"
Rasa wacce maganar, sukai da Abba yayi seya fara matse yatsun shi na hannun dama yana kar kaɗa azurfar shi cike da tararrabi ya ce masa.
"Abba am so confused wacce maganar ce mukai?"
Da mamaki Abba yace.
"Kamar ya ka shiga ruɗu Baffa? maganar nema maka auren Ummul khairi mana yarinyar daka bamu labari last week daka zo"
Shaf ya ma mance da ita a rayuwar shi Ambatar sunan ta kaɗai da Abba yayi seya tsinci kanshi da nadamar yadda ya ɗauki long time bai ko kirata ba kasancewar shi mutum mai cika alƙawari ya riga yayi mata alƙawarin kira baya son ta ɗauke shi mutumin banza mai magana biyu.
"Abba wallahi na ɗan shiga busy ne a waɗannan lokutan kasan Allah na mance da maganar ta"
Yafaɗa hankalin shi kwance.
Gyara zama Abba yayi sannan yace.
"Ni bam manta ba Baffa sabida haka ranar sunday jibi kenan kawunan ka zasu je sukai kuɗi da sadakinta, Abin da yasa ma akai delay wajan kaiwar seda naɗan yi bincike ne akan yarinyar daga nan na tashi mutane uku sukaje kano can anguwar sukai min binciken halin mahaifin yarinyar dana ta kamar yadda addinin musulunci yazo da sharaɗin neman aure bincike shine first amman ance kada a zurfafa! to Alhamdulillahi ɗari bisa ɗari yarinyar ta sami sheda mai kyau ta jinƙan mahaifiyarta dan sun ƙara da cewa ma agarin taimakon mahaifiyarta agidan aikinta wannan ƙaddarar ta sameta, shikuma uban dan tsabar rashin tausayi seya koreta daga gidan to kaji baffa sabida haka ranar lahadin nan in muna da rai za,a kai sadaki da kuɗin aure mukam a kwana uku ma a shirye muke su bamu yarinya a ɗaura aure"
Dum!dum!! dum!!!
Kirjin Aliyu ya bada sautin hakan a karo na kusan uku ya share zufa mahaifi daban yake babu yadda zeyi yayi musu jayayya akan abin da suke ganin sunfi ƙarfin su nemi alfarma a wajanshi, Amman ba da ban haka ba da babu yadda za'ai ya auri ummi tausayin ta kaɗai ne maƙare a kirjinshi wanda harya ci burin taimaka mata amman ba So ba.
"Banji kace komai ba baffa?"
Abba ya faɗa yana noticing ɗin Aliyu.
"Allah ya saka da Alkairi Abba ya ƙara girma yaja kwana zan aiko da kuɗaɗan komai ɗin"
Yafaɗa kamar zece wayyo! Allah na!
Murmushi irin na manya Abba yayi tare da cewa.
"Bana buƙatar ko sisinka anan wannan ni zan maka auren gata Auren da ko bana raye zaka min Addu'a ta daban akan shi baffa yanzu bazaka gane yaran ba kona yara maka"
Murmushin yaƙe Aliyu yayi aran shi yana ayyana.
Meye ma amfanin tara mata har 2 bai gama da matsalar waccan ba ga wata, Shi ina ze kaisu sun masa yawa mace babu iya girki bare tarairaya ita de burinta akwanta da ita kullum sedai ta ɗau jaka ta fice aikinta ga wannan itama wadda batafi a raine taba zata shigo mai zata masa inba yarinta ba.
"To kaji de yadda lamarin ya kaya maganar kayan ɗakinta.........
Da sauri ya dawo daga dogon tunanin daya faɗa tare da katse abba.
"No! Abba ina da set na furnitures a kowani room a gidana so that no need a kawota da ko spoon"
Yafaɗa yana mai kokawa da nutsuwar shi.
Lokacin Ammi ta shigo falon taci ado cikin wani haɗaɗɗan brown less ɗan gasken mai kyau da tsari babu abin da ke fita ajikinta se ƙamshi.
Ammi kenan benu bakya tsufa giwar Abba, da kallo Aliyu yabi Ammi yana mamakin tsafta da kwalliyarta tamkar bata haife suba.
Da murmushi take duban Abba wanda tunda ta shigo falon yake washe baki murmushin sa ya ƙaru fiye dana ɗazu.
"Abba da baffa me ake cewa ne aka ware ni?"
Tafaɗa tana dariya.
Shima Abba dariyar yayi tare da cewa.
"Wane mutum bare kayan sa mu ai duk naki ne se yadda kikai damu hajiya hafsa giwar mata maganar bikin ɗanki muke yi ranar lahadi kamar yadda na gaya miki nake sheda masa za'a kai masa kuɗin auren"
Sosai Ammi ta saki far'a tana zuba godiya ga Allah mamaki Aliyu yake na iyayen nashi acikin su kowaye yafi wani son ƙarin auren nashi oho!
"Dama yayarsu ta wuce dubai yau kwanaki uku kenan kaga tace ranar sunday zata dawo kaga tana zuwa se a miƙa lefen kawai ko?"
Ammi ta tambayi abba.
"Eh nima hakan nace Allah dai yasa ai komai lafiya cike da narasa"
Tunda yay ƙasa da kanshi bai kuma cewa komai seda ya duba agogon hannunshi ƙarfe taran dare tayi ga basma na faman yi masa waya.
Seya miƙe tare da zube hannayen shi bisa aljihun wandon shi yana mai ce musu.
"Ni zan wuce seda safe"
Da kallo Ammi ta bisa tare da cewa.
"Ka fasa shan ruwan shayin da kace hussaina ta dafa maka?"
Girgiza kai yayi tare da ficewa daga falon.
Murmushi Abba yayi tare da cewa
"Wannan ɗan naki fa neman zamewa yake baya son auren nan na fahimta gudu nake kar mu bashi ƴar mutane ya kaita wajan matarsa su azabtar da ita"
Wani murmushi Ammi ta saki tare da cewa.
"Bana tunanin a sanyin halin baffa da haƙurin shi ze iya cutar da wata, kai dai barshi da miskilancin sa da tsare gidan sa, ni ajikina ina jin baffa yana son yarinyar nan domin inda bai sonta bazeji tausayin taba amman shi a ganinsa tausayi ne, Sedai ni ina hango wata irin kwantacciyar soyayya mai zafi a idanunshi shi kansa yana mata son da bai san yanayi bane sone wanda ake kira makahon so"
Ammi tafaɗa tana dariya.
Shima dariyar abba yayi tare da shafo fuskar ammi yana cewa.
"Su Hajjiya hafsa malamar soyayya wuce muma muje mu tuna baya"
Dariya tayi tare da wucewa daining ta haɗo mai abinci ta dire agabanshi har lokacin murmushine ɗauke a fuskar ammi.
Da wani irin speed ya ƙarasa motar shi sabida ruwan daya sauko kamar da bakin ƙwarya ashe abin da yasa basuji agidan Ammi ba sabida gidan rufin pop ne shiyasa ƙarar saukar ruwan ta ɓuya seda ya fito yaga ashe ruwane ke sauka kasancewar garine na damuna ga Abuja kowa yasanta basa rabo da zubar ruwan sama.
A gaggauce ya tada motar ya buga uban horn mai gadi ya buɗe masa ya fice basu da nisa da gidan shi tsiran layi biyar ne daman.
Seda yaje bakin gate ɗinshi sannan ya danna horn mai gadin shi ya buɗe masa ya shiga cikin gidan shi.
Ya ƙarasar da motar parking lot yayi parking tare da kasheta ya jingina kanshi da jikin seat ɗin motar tare da ɗauko wayar shi ya duba tarin miss call ɗin basma wajan guda goma.
Fita yayi daga wajan misscall ya duba time 9:30pm ya ɗan fiddo da ido cikin mamakin yadda time yaja.
A hankali yake tunanin mai yasa yarinyar nan ta share shi? bata neme shi a waya ba? kamar yadda yayta ganin kiranta last 7 days ago! yadda da dinga naci.
Wata zuciyar tace kodai ta dena son kane?
Gaban shine yaji ya faɗi.
Da ƙarfi ya furta.
"No ina ganin soyayyata mai girma cikin manyan idanuwan ta"
Hannunshi har rawa yake wajan lalubo numbern hajja rabon daya ga kira da layinta tun ranar daya kirata da daddaren nan.
Kawai tsintar hannunsa yayi da dialing number ɗin.
Ringing! tai harta katse ba'a ɗaga ba.
Still ya kuma try nan ma ba'a ɗaga ba.
Faɗuwar gabansa ce ta tsananta gumi mai ƙarfi yana keto masa tamkar babu AC Acikin motar.
Seda yayi kira sau biyar.
Abinda bai taɓa yiwa wani ba a duniya a ƙa'idar shi kira ɗaya dal yakewa mutum inka gani ka ɗaga to in baka gani ba kaga miss call ka biyo shi amman yau shine harda jera kira biyar batare daya farga ba.
Cikin baccinta takejin ƙarar wayar hajja dake kusa da ita wadda ta saita alarm da ita wanda yake farkar da ita duk ƙarfe 3:00am na dare domin tayi nafila.
Mirginawa tayi tare da buɗe manyan idanunta da suka kumbura suka tasa sabida baccin data ke, Takai duban ta ga hajja wadda taja bargo tana ta munshari alamun ta jima da yin bacci.
Itama juyawa tai tare dajan Blanket ta ƙara rufe jikinta wani baccin na sake fusgarta.
Wayar nata ringing amman nauyin bacci ya hanata ɗauka.
Seda ringing ɗin ya dameta sannan ta ɗauka idanunta rufe suke batare data san mai take faɗa sabida baccin dake cinta kuma bata san waya kira ba
Ta danna wajan ɗaya kiran.
Numfashi take saki a hankali kamar mai magagi!
Tace.
"Uhmmmm"
Tare da jan numfashi mai ƙarfi.
Da sauri Aliyu ya ɗauke wayar daga kunnen shi yana furta.
"Ya salam! wannan yarinya zata sa girmana ya zube ba ƙaramar fitinanniya bace"
A hankali ya mayar da wayar kunnen shi.
Muryar shi tayi mugun sanyi sosai yace mata.
"Bacci ake?"
Kamar a mafarki takejin muryar shi duk tunanin ta cikin mafarkin tane daya saba zuwar mata duk dare yana sakar mata tsadaddan murmushin sa.
Turo baki tayi gaba tana cewa.
"Uhhmmm ka dena kulani ka dena kirana har zazzaɓi nayi baka sani ba sedai kullum idan na kwanta kazo kaita min murmushi naita maka magana baka mayar min da amsa ba shine yau ma kazo cikin mafarkin nawa kana min magana da muryarka mai kasheni a tafkin soyayyarka"
Tafaɗa tare da sakar masa wani irin marayan kuka ƙasa ƙasa harda shesheƙa.
Jikin Aliyu wata irin kyarma ya ɗauka nan da nan numfashin sa ya fara barazanar ɗaukewa.
Wani irin murɗawa mararshi tayi atake anan mazantakar shi tai sama wani irin ƙarfi na bin ilahirin jikinsa.
Idanunshi suka rune suka koma kamar wuta har wani ruwane ke ambaliya ta cikinsu.
Hannunshi yakai ƙasan mararshi yaɗan shafo a hankali tare da cafkar laɓɓanshi na ƙasa yana tsotsa yana shafa sajenshi.
"Shiiiiiiiiii ummmmmmhhh kidena min haka ummi please kiyi shuru nine a yanzu nike maki magana ba a mafarki ba ki nutsu kiwa girman Allah ki dena min wannan kukan zaki sani ɓarnar madarata"
Yafaɗa muryarsa kamar mai yi mata raɗa.
Cikin kukan ta ware idanu taga waya maƙale a kunnenta wanda ya bata tabbaci cikin bacci ta ɗauki wayar hartai masa wannan maganar duk bata sani ba.
Se yanzu data farka taga ashe da gaske waya yake mata ba mafarki ba.
"Kinyi shuru? kin dena kukan? yanzu ina ke maki ciwon?"
Ya faɗi maganar haƙoranshi na haɗuwa da junansu kamar me shirin kamuwa da cutar zazzaɓin sanyi.
"Nifa lafiya ta lau"
Tafaɗa a sakarce.
A wahalce yace mata.
"Zan zan kiraki da safe bye"
Yafaɗi har yana haɗe maganar tashi
Jikinshi na wata irin kaɗawa ya fice a motar.
Yana xuwa falon shi basma na zaman jiranshi ta zuba uban ta gumi.
Da wani irin sauri ya ɗagata cak yayi master room da ita tun a tsakar ɗaki ya soma wurgi da kayansu yadda yake sarrafa basma kaɗai idan ka duba kasan a matiƙar haukace yake sosai tasha wuya a wajansa sabida ayau yayi mata abinda bai taɓa mata shiba a iya tsayin zamansu wata irin soyayya ya shiga gwada mata mai wuyar a fassara wadda seda ya fanshe duk wani feeling da ummul ta sakar masa ajikin basma............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.
Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu