Showing 75001 words to 78000 words out of 83661 words
kuma wannan yarinyar kinsan Allah ita baffa yake so amman rashinta a kusa dashi yasa ya kasa tan tance meke faruwa dashi domin da zarar soyayyarta ta kunna shi idan yaje gida yaga waccan matar tashi seya juye soyayyar tasa akan ta hakan yasa zakiga bai fiye zafafa wa akan wannan ɗin ba amman da zarar ta tare yana ganinta tana sauke mai wasu nauyi na aure to daga lokacin ze fara farkawa daga mafarkin auren matar sa ta fari dayayi har yaji komai na dawo masa daki daki kamar yadda ada zafin sihiri yasa ya makance akan zaɓin matar aure"
Abba ya kare maganar cike da nutsuwa.
Jimm Ammi tayi kafin tace.
"Kuma fa haka ne tabbas tunanin ka shine dai dai to Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba yasa ta tare lafiya cikin aminci Amin"
Hira suka ɗan taɓa da Abba kafin ta miƙe tayi ɓangaren ta.
Samun su tai zaune dasu hassana suna ta hira ummul ta saki jikinta suna ta labarai.
Sosai take dariya lokacin da hassana take bata labarin dukan da baffa yayi mata akan matar shi.
Shigowar ammi yasa taɗan tsagaita.
Kallon Su hassana ammi tayi tare da cewa.
"Ƙarfe ɗaya saura baku ɗora abinci ba waye ze maku girkin?"
Dayake duk kuɗin Alhaji Ali yaransa mata suke girki da gyaran gida ƴan aiki kuma suyi na harabar waje.
Shagwaɓewa hassana tayi sannan tace.
"Ammi jiya fa nina yi sannan yau ma ninai break ita ya shafa da hussaina basu yi komai ba"
A hasale shafa tace.
"Dan gidanku dame zanji da fita aiki hospital koda girkin ku kuda kuke hutu baza kuyi ba seni"
Hussaina ma ta cafke tana cewa.
"Nifa Ammi marata kemin ciwo shiyasa ban yi ba"
Tsabar takaicine yasa hassana fashewa da kuka tana cewa ita aka tsana a gidan
Sosai suka bawa ummul dariya seta tuno yadda suke da sadiya agida.
"Toya isa ni xan tashi nayi da kaina tunda babu wanda zeyi"
Jin ammi ta faɗi hakan yasa ummul tace.
"Ammi duk na hutarsu ni zan shiga nai muku domin babu abin da ban iya ba"
Dariya shafa'atu tayi tare da cewa.
"Lalala inji balarabe bazaki wahalar wa da yaya jiki ba mude zamuyi kici"
Rufe fuska ummul tai cike da jin kunya inda ammi tace.
"Su zasu yi ke zauna saman gado zan baki abu ne"
Hakan yasa suka tashi suka bar ɗakin wani kwanon silba ammi ta ɗauko ta buɗe shi ta miƙawa ummul zuma ce aciki da sauran su dabino.
Tace ta shanye babu musu ta amsa ta kafa a bakinta sedai baurin ciki ya hanata haɗiya gashi tana jin kunyar ammi bazata iya yi mata musu ba.
Haka dai ta shanye tas.
Sannan ta ƙara bata wata jarka mai tsumin maganin sanyi aciki tace ta shanye a wannan karon da kyar ta shanye wannan tsumin duk cikinta ya cika wata kwalba ta bata tace mata.
"wannan zaki dinga shafawa ajikin ki da daddare humra ce mai kyau sauran kayan kuma yayarku tai maki bayani ko? babu lokaci naso a sati biyun nan munyi gyara sosai to wannan anacen ya kafe amman waɗannan ma zasuyi maki aiki sosai"
Ita dai ummul bata fahimci komai ba amman dai ahaka taiwa ammi godiya.
Fita ammi tayi minti goma se gata ɗauke da wata ƴar ƙaramar kula ta miƙawa ummul tare da cewa.
"Maza ki cinye ƴan shila ne aure aka dafa da magani amman karki tauna kashin kidai ci tsokar kisha romon su"
Godiya taiwa ammi tare da yin bisimillah ta soma ci A hankali ammi take bata shawarwari akan tsafta girki tare da biyayyar aure.
Sannan ta horeta data riƙe addu'a kartai sakaci dayin ta.
A haka harta kammala ta mike zata fita da kular ammi ta hanata da kanta ta fitar kafin ta dawo ummul.tayo alwalar axahar ta tayar da sallah bayan ta idar wannan sanyin ac ɗin ɗakin tare da mutuwar jikin da maganin ya sanyata wani wawan bacci ya kwashe ta ammi nata mata magana akan ta tashi ta hau gado amman ina baccin ta yayi nisa.
Ƙarfe 11 na rana hajiya binta ta fita daga gidan ta bayan sunyi waya da basma motar naija ta hau bayan ta sauka ta sami ta ƙauyen da bokan yake tafiya ce yita manta uwa tun kana tafiya da marmari har seka ƙosa amman haka ta daure harta ƙarasa garin sannan ta sauka a motar ta sami mashin ta hau dan ƙarasawa wajan bokan..........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.
*51*
Ba ƙaramar wahala tasha ba kafin ta ƙarasa wani ɗan ƙauye inda anan bukkar bokan nata take layi ne a wajan sa na bala'i zama tai tare da tsaida mai mashin ɗin ta ƙara masa kuɗi akan ya zauna ya koma da ita bakin hanyar da zata sami motar da zata fidda ita daga yankin baki ɗaya.
Se wajan rana layi ya zo kanta da baya take shiga tana karanta wasu surkulle irin na mashirikai kafin ta ƙarasa gaban bokan tai wata irin dira tana masa kirari.
Baƙin gabjejen ƙaton mutum mai ƙatun ƙatun ɗin idanu jajir dasu hancin sa mai kama da zubin na samudawa kansa cunkus da suma idan ka dube shi baza kace masa bil adam ba.
Wata irin dariya ya saki wadda ta amsa dukkan wajan kafin yayi sama da hannunsa wata jar tukunya ta bayyana a tsakiyar tafin hannun nashi ya direta a gaban hajiya binta babu komai acikin jar tukunyar se jini.
Muryarsa mai tsananin ƙara ya furta
"Leƙo da kanki kiyi kallo"
Da sauri ta leƙa cikin tukunyar wanda taga wani irin haske na gaurayeta yana nashe jinin hasken sama yake yowa har ya haske masu fuskar su da sauri bokan yayi wurgi da tukunyar yana zufa.
Wata ashar ya maka tare da cewa.
"Na gaya miki kin kasa yarda wannan hasken na addu'a ne yanzu sauran kaɗan ya kashen idanu baƙaƙen aljanu sunce muddin za,a ƙara bincika wannan yaron tofa zasu tashi daga wajena domin bazasu ƙone ba sabida haka bazan iya aikin kiba a wannan karon yafi ƙarfina kuma duk inda xakije bafa zakuyi nasarar gano komai ba"
Wata irin zufa hajja binta ke gogewa idanunta yayi wani irin ja cike da tsananin son zuciya irin na waɗanda son duniya ya rufe masu idanu tace.
"Yanzu boka meye abin yi? bana son yarinya ta tai boranci gidan mijinta kamar yadda ka gamamin da mahaifinta shima ina son ka gamamin dashi ina son sahihiyar mallaka tunda kace baze taɓa yi mata kishiya ba"
Wata dariya ya kece da ita kafin yace.
"Baze taɓa mata kishiya ba idan har kinga mijin ƴarki ya sadu da wata macen to uwarsa ce! kin taɓa ganin ɗa ya sadu da uwarsa?"
Tai saurin girgiza kai tana cewa.
"A,a boka ban taɓa ganin ɗan daya sadu da uwarsa ba sedai a jinsin dambobi ma'ana ɗan akuya"
Dariya! ya kuma yi kafin yace.
"To hakan ce zata kasance idan har kika ga surukinki yayi aure to uwar sa ya aura babu shi babu aure"
Yafaɗa yana dariyar hauka.
Itama dariyar tai kafin tace to Boka godiya nake.
Wata ƙara yayi tare da karanto wasu irin yaruka wasu kwalabe guda biyu suka faɗo hannun sa.
Ya miƙo mata yace.
"Lallai lallai yau ƴarki ta cusa maganin cikin kwalbannan a gabanta kuma ta tabbata yayi auratayya da ita a yau hmm idan har ya kusance ta ayau tofa babu shi babu Kallon koda wata macen ma kuma baze ƙara kallon mace a mace ba sedai namiji ɗan uwan sa ita kaɗai ce zeta kallo a mace wannan maganin sunan sa koda ta kwana ma'ana sabida ƴammata masu kawo farmaki"
Sabida tsabar murna hajja binta harda tsalle kana ta kunce jaka zata ciro kuɗi.
Lasar bakinsa yayi yana kallon ta dajan idanunsa tare da cewa.
"Kin san tun wancan aikin danai maki ma ban amshi kuɗi ba"
Dayake shine yayi mata aikin farko wanda basma ta auri Aliyu.
Gabanta ne ya faɗi sabida azabar data sha a wancan aikin shine ma yasa ta sauya akala taƙi komowa wajan sa bada ban ta ɓaci bama yanzu da bazata zoba to duk inda taje bata samun aiki mai kyau kamar nashi.
"Ina nufin zaki juyan bayanki Aljani ya sadu dake"
Wa'iyazu billahi luwaɗi fa kenan wanda a yanzu shine ya zama ruwan dare wanda wasu bokayen keyi da matan da suka je neman waraka a wajan su.
Babu yadda ta iya haka ta miƙe tabi bayan sa zuwa wani ɗaki mai duhu ta cire kayanta baki ɗaya boka ya sadu da ita ta baya yana ta sunbatu a ƙaryarsa wai aljanine ( wa'iyazu billahi Allah ka rabamu da taɓewa )
Ya shuɗe lokuta masu tsayi yana sukuwa a bayanta kafin ya gamsu ya rabu da ita ta sanya tufa ta baro ɗakin tana cije baki sabida ko a wancan karon ma ba ƙaramar wuya taci ba kafin duburarta ta koma ta rufe to wannan karon ma duburar tata a buɗe take tana shan iska haka ta saka kayan ta fita da magungunan tana jin indai zasu sami Aliyu komai mai sauƙine.
Kafin ta dawo gida har zazzaɓin wuya ya rufeta jikinta fal ciwo ta sauka a gidanta wajan magariba tai wanka tana tura hannunta bayanta abin mamaki baki ɗaya hannun ya shige cikin duburar tata zare ido tai tana tsoron kar wata masifar ta sameta sabida duburar ta riga data buɗe sosai.
Amman sabida taurin zuciya haka ta sauya kaya babu tunanin sallah ta nufi gidan ƴar tata sosai suka ƙulle a ɗaki suna ta sheƙa dariyar cin nasara.
Ta bawa basma kwalaban sukai sallama ta nufi gidanta.
Da murna basma ta tsala wanka tazo ta cusa wannan maganin tana zaman jiran Aliyu.
Bai sami kanshi ba se bayan sallar isha'i bayan yayi sallah ya wuce yahuza suya na nan abuja yayi musu takeaway ya nufo gidan Ammi.
Har ummul ta soma bacci sabida jikinta a mace yake tunda tasha waɗannan magungunan ga ciwon mara haka Ammi tace ta tashi mijinta yazo.
Ta yafa mayafin doguwar rigar data saka datai wanka falon abba suka je sukai masa sallama ya ɗauko kuɗi masu yawa ya bawa ummul ita kuma Ammi ta bata ƙananun kaya cikin akwati sannan sukai sallama suka shiga mota.
Har suka je gida babu wanda yayi magana acikin su sosai ummul ta yaba da tsarin gidan Aliyu duk da bai kai na iyayen sa kyau ba da ƙafar dama ta shiga ta karanto addu'a kana ta luntsuma cikin haɗaɗɗan falon wanda yaji manyan royal chair haɗi da wani irin carfet mai kyau ga labulaye na alfarma se TV ƙatuwa daga can nesa kuma daining area.
Hanyar ɗakinsa ya nufa ledojin dayay siyayya suna hannunshi da sauri tabi bayan shi hannunta ɗauke da akwatun da ammi ta bata.
Ƙaton ɗakine mai ɗauke da saitin gado da wadrobe da madubi dukka farare tas.
Aje leda ɗaya yayi tare da ɗaukar ɗaya ya fita batare dayayi mata magana ba ɗakin basma yaje tana sallah ya aje mata ledar tare da komowa ɗakinsa ya rufe kofar ya bar key ajikinta.
Kayanshi ya shiga cirewa ummul tai ƙasa da kanta harya gama ya daura tawul ya shiga wanka.
Kafin ya fito tai kwanciyarta a saman gadon duk ta cure waje ɗaya.
Seda ya shafa cream tare da turare sannan ya shirya tsaf kana ya dube ta
"Taso muyi sallah"
A dake yayi maganar ba ƙarfi ajikinta ta mike ta shiga bayin sa ta ɗauro alwala shiya jasu sallar nafila raka'a biyu ya jima yana addu'a kafin ya dafa goshinta ya karanto addu'a tare dayin masu fatan alkairi.
Ya tambayeta ta iya wankan tsarki da kuma sauran tambayoyi akan addininta Babu musu ta bashi amsar dukkan tambayoyin sa.
Yaji matiƙar daɗin hakan sabida haka, Bai ce mata komai ba ya tashi ya bude ƙofar ya fita falon ba kowa ya je kicin ya ɗauko plate and Cup ya dawo ya zazzage kazar dake ta turiri acikin plate ɗin tare da tsiyayo yoghurt acikin cup ya matsa gabanta.
A hankali yake yagar farar tsokar kazar yana saka mata abakinta tana ci kaɗan yana bata yoghurt ɗin harta matsar da kanta alamun ta koshi sannan shima yaci.
Ta miƙe ta wanko bakinta tazo bakin gado ta zauna shima seda ya kammala sannan ya shiga toilet minti biyu ya fito tare da nufar bakin wadrobe ya tube rigarsa yay saura daga shi se guntun wando babu ko singlet ƙaƙƙarfar surar shi ta cikakkun maza ta bayyana.
Kashe ƙwan ɗakin yayi tare da nufowa gabanta.
Ya miƙar da ita tsaye ya zuge zip ɗin rigarta yay wurgi da rigar,tai saura daga ita se under wears.
Ya nufi saman bed da ita wata irin runguma yayi mata yana mai ɗora harshensa saman dokin wuyanta yana lasa.
Sannu A hankali yake sarrafata cikin wata irin zaƙuwa jikin ummul ne ya ɗauki rawa nan da nan ta fara haɗe jikinta waje ɗaya tana sakin kuka.
Sosai ta fara gunjin kuka sabida abin da sameer yayi mata shiya faɗo mata aranta.
Shiko babu ji babu gani yake wasa da duk inda yaci karo acikin jikinta musamman kirjinta wanda har ya gaji da azabar matsar Aliyu, Lokacin daya keson yaje fadar ta a lokacin taƙi bashi haɗin kai sema curewar datai jikinta na karkarwa tana yarfe hannu tana girgiza masa kai.
Jikinsa na wata irin tsuma yake furta.
"Haba fulani ta please karki min haka zan mutu idan ban yi ba"
Kuka take yana shanye mata hawayen da harshen sa, kafin a hankali ya kamo tattausan laɓɓanta ya shiga tsotsa hannayen sa zube a kirjinta yana matsasu a hankali ya soma gigita ta tana wata irin miƙa ajikinsa sannu A hankali ya fara addu'a Cikin rawar jiki ya haɗe da ita suka zama abu ɗaya.
Wannan sirrin na ma'aurata ne dan haka naja masu labule.
Ya jima yana abu ɗaya kafin ya sami cikakkiyar gamsuwa shikam baiji wata ƙofa da zata nuna masa an mata fyaɗe ba dan haka ya janyo ta yana shafa bayanta yana gaya mata maganganu masu daɗi.
Saɓar ta yayi a kafaɗa ya nufi toilet suka tsarkake jikinsu kana ya kuma ɗaukota suka dawo seda ya sauya zanin gado sannan ya kwantar da ita shima ya kwanta yaja masu abin rufa nan da nan bacci ya ɗauke su mai daɗin gaske........
Cikin sauri basma ta idar da sallar, ta ƙara ɗauko sauran maganin wajan boka ta cusa sannan ta sauya kaya zuwa wasu ƙananu masu fidda surar jiki ta ƙara zuba uban turare ajikinta ta ɗauko ledar daya aje mata ta ɗora a saman frij ɗinta dake ɗakinta kana ta nufi nasa ɗakin tana yauƙi............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.
Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588
*52*
Ta ƙarasa gaban bedroom ɗin Aliyu ta tura ƙofar taji ta a rufe setai murmushi taja handle ɗin ƙofar setaji ta gam komawa tai zuwa saman daining ta ɗauko spare key sedai data zira dan ta buɗe ƙofar taji alamun da wani keyn ajiki.
Jikin ta ne ya hau rawa gumi na tsatstsafo mata nan da nan gaban ta ya soma faɗuwa ta shiga zare idanu.
Zubewa tai anan wajan hawaye na takaici na zubo mata kafin ta miƙe ta nufi nata ɗakin wayar ta dake yashe a saman gado ta ɗauka ta shiga kiran layin mamanta.
Hajja binta wadda take zaune tai goho sabida har zuwa lokacin bayanta a buɗe yake se iska ke shiga da fita cikinsa ita ta ɗauki wayar tare da cewa.
"Yaya akai kuma?"
Kuka basma ta sanya mata tare da cewa.
"Mama naje ɗakin Aliyu naji sa a rufe kuma harda saka key kuma na riga na saka wannan ɗan matsin"
Wata dira hajja binta tai daga saman gadon tare da cewa.
"Na shiga uku ni binta mai kiki cewa basma ke wace irin banza ce kinsan wuyar dana ci kafin na amso wannan maganin? ko kinsan sharaɗin da boka ya baki akan amfani dashi akan ki gani kwance duburata taƙi komawa dai dai sabida bala'in saduwar dayay dani ta baya wannan duk bai daman ba muddin buƙatata zata biya"
Kuka basma take wurjanjan tana cewa.
"Mama ni ban san yaya zanyi ba ni kaina maganin ya soma zubamin ƙaiƙayi agabana"
Sharaf hajja binta ta zauna a gadon ta tana wani irin gumi hankalin ta a tashe tana ƙoƙarin yin magana ƙawarta hajjiya falmata ta shigo ɗakin wadda taiwa waya akan bata jin daɗi tun ɗazu akan dole taima basma sallama akan cewar zata neme ta.
Gaisawa sukai da hajja falmata kafin hajja falmata tace.
"Maman basma naga kina ta kirana lafiya duk na tawo hankalina tashe"
Muskutawa hajja binta tayi tare da share zufa tare da cewa.
"Hmm hajiya falmata ina cikin matsalafa" nan ta kwashe komai ta gayawa ƙawar tata aminiyar ta wadda ada tare suke yawon bin bokayen da ita.
Cikin nutsuwa hajja falmata ta soma salati tare da cewa.
"Hajiya binta daman har yau baki dawo daga hanyar ƴan duba mashirikan Allah ba? maƙaryatan mutane masu son ɓatar da ɗan adam?.wallahi ni na ɗauka tuni kin bar wannan layin Ashe baki dena zuwa ba nikam na tuba kuma na gyara laifuka na daman akan kishiyata nake zuwa yanzu kuma naje na nemi yafiyarta mun dai daita babu ni babu sake bin bokaye nai asarar kuɗina abanza"
Taja fasali ta cigaba.
"Hajiya binta ki tuba tun kafin lokaci ya ƙure miki kisa ƴarki ta nemi gafarar mijinta wallahi yanzu tun a duniya Allah