Showing 72001 words to 75000 words out of 83661 words

Chapter 25 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11362

fito dan haka ta miƙe ta gyara gadon data kwanta ta koma ƙasan carfet ta zauna tare da rafka tagumi.
Dole ta dage da addu'a yadda ake faɗar matar Aliyu, Idan kai sakaci da addu'a seta kassara maka rayuwarka addu'a kuma makami ce ta mumini shiyasa tunda hajja ta gaya mata halin matar Aliyu ta dena bacci alarm ta saita kullum dare seta tashi tunda soyayyarsa ta ƙullu aranta bata ƙara sakaci da addu'a ba dama kuma tun can tana addu'a da wannan lamarin ya kunno kuma seta ƙara kaimi fiye da da.
Sabida harga Allah tana fatan ta zauna cikin lafiya da farin ciki agidan mijinta.
Share hawaye tai a karo na barkatai tace

"Ya rabbi kada ka ɗoran wata ƙaddarar a karo na biyu acikin rayuwata! ya Allah kar kasa nasha wahala a gidan Aliyu ya rabbi ka tauayamin kasa ƙarshen wahala kenan"
Ta faɗa tana share hawayenta lokacin Ammi ta turo ƙofar ta shigo da sauri Ummul ta share hawayenta sosai ta gyara tare da ɗan kallon Ammi farar mace tas mai dattako mai kamala da nutsuwa.
Sallama Ammi tayi da sauri Ummul ta amsa tare da ɗanyin ƙasa da kanta tana cewa.
"Sannu da zuwa Umma ina kwana an tashi lafiya?"
Ummul ta faɗa a rarrabe.
A bakin gado ammi ta zauna tare da cewa.
"Kema ƴata ce kada ki sake cemin umma ammi zaki ce kamar yadda ƴan uwanki suke faɗa"

Ammi ta faɗawa ummul.
Sannan cikin kulawa tace mata.
"Ki kwantar da hankalin ki ummul khairi kada halin baffa ya dame ki nidda mahaifin sa muna da sanin komai na ƙaddarar data same ki hakan ce ma tasa muka ce ya aureki domin yayi jahadi kuma insha Allah zamu tsaya wajan amsar maki haƙƙin ki"
Taja fasali sannan ta ɗora.
"Zaki ɗan kwana biyu anan kafin ki tare agidan mijin ki ina son Dan Allah ki dage da addu'a ummul khairi sabida matar sa shu'uma ce bana gaya maki hakan dan kije ki raina taba a,a na gaya maki hakan ne don karki sake ki bata yarda domin zata iya cutar dake duk da bana zaton ma tasan da wannan aure"
Dum dum! gaban ummul ya buga wato matarsa bata san da auren suba to meke nan?
Katse tunaninta ammi tayi tare da ce mata.
"Seda bana zaton zeƙi gaya mata domin baffa jarumi ne ko ada can da giyar asirinta ke ɗiban sa bai bata fuskar raini ba bare yanzu nake tunanin ayar Allah ta kassara wannan sihirin na jikinsa"
Wani gumi ummul ta share duk da uban AC ɗin dake tashi a ɗakin sannan tace.
"Insha Allahu Ammi dama hajja ta gaya min komai"
Murmushi Ammi tai tare da cewa.
"Maza shiga kiyi wanka ga yayarki nan Zata kawo maki kaya yau zasu wuce ba'anan suke aure ba"
A hankali ta yunƙura ta tashi ta shiga toilet ruwa mai ɗumi ta haɗa ta fara wanke jikinta bata wani jima ba ta fito.
Zaune ta tarar da farar matashiyar mace mai sakin fuska.Cikin nutsuwa ummul ta gaishe da anty jidda sannan anty jidda ta bata wasu riga da skirt sabbi da undies tace ta shirya.
Kana ta juya ta bata waje koda ta sanya kayan sunyi mata cif kamar an gwada ta zama tai a gefen gado kafin anty jidda ta kuma dawowa da ɗan kwando a hannunta.
Ta kalli ummul sannan tace mata.
"Sunana jidda nice yayar mijinki ni bana suruka dake ummul ke ƙanwata ce ga kayan gyara nan ammi ta sanya an tawo maki dasu daga katsina"
Nan ta dinga fito mata dasu tana nuna mata yadda zatai amfani dasu wasu har kunyar bayanin ta dinga ji tana gama yi mata bayanin su hassana suka kawo mata break fast.
Bayan fitar su ta janyo flask ɗin tea ta haɗa tana sha tana kallon agogon dake ɗakin ƙarfe 11:40am amman har yanzu Aliyu bai shigo ba kamar ya mance da matar sa tana gidan! jitai shayin ya fitar mata aranta.
Tsirama cup ɗin idanu tai tana kallo da alamun tunani ta shiga.

A gurguje yayi wanka ya shirya cikin farin yadi bai sa hula ba seya sanya baƙin takalmi ya fesa turare ya ɗauki wayarsa ya kunna sannan ya fita 11:00am wata mahaukaciyar yunwa yakeji ya nufi ɗakin basma ya tarar da key da fushi ya fita daga gidan ya nufi gidansu.
Falon Ammi ba kowa da alamun duk suna ɗakunan su dan ba'a break da wuri agidan ammi.
Yana ƙoƙarin shiga part ɗin Abba yaga hassana ta fito daga kicin ta zube da kaishe sa.
Kamar ya tambayeta tace

"Tana kusa da ɗakinmu"
Ta faɗa mashi da sauri tai hanyar ɗakin ammi.
Shafa sumar kanshi yay tare da nufar hanyar ɗakin data ke ɗin...........

Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400

*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.


Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

49


Cikin nutsuwa ya murɗa handle ɗin ƙofar ya buɗe ya shiga bakin sa ɗauke da sallama sanyin Ac tare da ƙamshin turaren ɗakin ya mamaye hancin sa, Lumshe manyan idanunshi yayi tare da warasu akan ta, sallama kusan uku yayi a jere amman babu wadda ta amsa mai tsira mata ido yayi daga nesa alamu sun nuna tana cikin tsananin tunani mai zurfi.

Da sassarfa ya ƙarasa inda take ya zauna a gefen gado inda ita kuma tana ƙasa a gaban kayan break ta tsirawa cup ɗin tea idanu batare data sha shiba.

Gyaran murya yayi tare da cewa.
"Yaya kwanan baƙon waje?"
A hankali taji saukar sassayan muryar shi tare da wani irin daddaɗan ƙamshin turaren shi daya cika ɗakin.

Ɗan gyara zamanta tai sosai tana mamakin how long time data ɗauka tana tunani da har ya shigo bata jishi ba.
"Na shigo ina ta sallama baki amsa ba har na zauna baki sani ba hope dai ba wani abun ke damun kiba?"
Ta kuma jin dirin maganar shi.
Anan ma bata basa amsa ba se shurun daya biyo baya.

Ɗan zamewa yayi daga saman gadon ya koma kusa da ita ya zauna suka jera a zaman nasu.
Kamo hannunta yayi zuwa cikin nashi da sauri ta doke nasan tare daja baya kaɗan tana watso masa wata shegiyar harara!
Sunkuyar da kanshi yayi a ƙasa ya jima a haka kafin ya ɗago fuskar shi a tamke yake duban ta.
Murya a kausashe yace mata.
"Wannan wani irin sakar cine? Tunda na shigo ina maki magana kinmin banza bamma sami arziƙin gaisuwa ba sannan na taɓa hannunki kamar wani dodo kinja baya"
Yafaɗa idanunsa yana mai kaɗawa kaɗan.

Bata ce mai komai ba ta ɗora hannunta a ƙasan carfet tana wasa dashi hakan yayi mugun ƙular da Aliyu ba zato taji caraf ya damƙota ya riƙe hannunta tamau riƙon tsauri riƙon data ji mugun zafin sa.

Ƙoƙarin saka masa ƙara take yayi saurin sanya ɗayan hannun nashi ya rufe mata bakinta.
"Shit ni karki taran mutane"
Ya faɗi maganar da ƙaramin sauti.
Ɗorata yayi a saman cinyar sa ya juyo da fuskarta daf da tasa.
Kallon ta yake sosai har seda taji ta tsargu tayi saurin yin ƙasa da kanta domin bazata jure wannan kallon nashi bai kama dana mayu ba.
Cikin cool voice yace mata.
"Ni sa'an rainin kine ummi yau she ne kika rainani haka? ina maki magana kina jina kika min banza?"

A mai makon tai masa magana seta hau hawaye shaaa kamar an buɗe famfom.
"Ya salam mai nayi maki? har ga Allah bana son ingan ki cikin damuwa domin amana ce Allah ya bani baki da kowa anan daga Allah seni sekuma mahaifana please idan laifi nayi maki Allah ya baki haƙuri"
Yafaɗa muryarshi naɗan rawa kaɗan.
Wani irin shock ummul tai wai yau ita wannan ɗan zafin kan yake bawa haƙuri to me hakan yake nufi?
Muryarta laushi ƙalau tace masa.
"Tun jiya ka sauke ni kamar wata ƴar tsana kai tafiyan ka yau ɗin ma baka zoba duba lokaci?"
Tai masa nuni da agogon dake manne a bangon ɗakin.

"Nidai nace kiyi haƙuri ai sannu bata karya wuya inji bahaushe na amshi laifin nawa"
Yafaɗa yana mai manna kanta acikin kirjinsa wani irin sanyi mai haɗe da kamshi ne suka ziyarci hancin ummul lumshe ido tai tana mai kuma lafewa ajikinsa tana jin dama su dauwa ma ahaka.
Ada tana masa kallon murɗaɗɗan mutum amman a yanzu seta ji ƙimar shi da sonshi acikin zuciyarta fiye dana da domin shiɗin ya kasance mutum nagari mai wa soyayya adalci duk da yadda yayi mata jiya bata ji daɗi ba amman yadda yau yazo yana kwantar mata da kai yana lallaɓata yana nuna bata da kowa agarin se shi setaji komai ya wuce harga zuciyarta domin inda wani namijin ne bama zebi ta kanta ba.

"Kinci abinci ga tea ɗinnan baki ma taɓa shiba? mai zaki ci?"
Taji muryarsa a cikin kunnenta har yana ɗan fesa mata numfashi.
Miƙewa tayi ajikinsa tai flate tare da sanya hannayen ta bisa ƙugunshi ta cusa kanta cikin kirjinshi taƙi basa amsa.
Wani wahalallan numfashi ya sauke yana jin yadda kirjinta ya kwanta a saman Cinyarsa.
Ya Allah wannan yarinya zata kassarani.
Yafaɗa cikin ransa.
Hannunshi ya ɗora a bayanta yaɗan matsa kaɗan wani zullo tai tare da sauka daga saman cinyar tashi tana dariya tana gyara ɗaurin ɗan kwalinta.
Jajayen idanunshi ya zuba mata tare da miƙo mata hannayen shi batare daya iya furta komai ba.
Baya take ja kaɗan harta miƙe tsaye.
"Ka taso muje mu gaishe dasu Abba rana tana kuma yi"
Tafaɗi maganar a tsorace.
Miƙewa shima yayi tsaye yana gyara rigarshi wadda taɗan ɗaga kaɗan sabida feeling ɗin daya ziyarce shi.
A hankali ya tako gabanta.
Ya ɗora hannunshi a ƙafaɗunta yayi mata rumfa da faffaɗan kirjinshi ya mannata da karfi zare ido tai batai aune ba taji ya tura su saman gadon ɗakin ya kwanta a samanta.
Kokawa take da numfashinta sabida yadda ya zuba mata dukkan nauyinsa a jikinta.
Muryarta a shaƙe tace.
"Dan Allah ka bari ka ɗagani nauyi kayi min girma"
Bai kulata ba sema ɗora bakinsa dayay a kan nata ya shiga kissing lips ɗinta a hankali ya ɗora hannunshi a saman kirjinta ta saman rigar yake wasa dasu.
Wani irin wasannin ma'aurata ya shiga gwada mata wanda kwanyar kanta ta gaza ɗaukar su tun tana numfashi da ƙyar har tazo tana mai kukan shagwaɓa.
Seda yaɗan rage zafi da ita sannan ya ɗagata yana dariya tare da sanya harshe yana lashe mata hawayen yana tsokanarta raguwa babu abin da akai amman take kuka.
Duk da bai furta mata kalmar so ba amman a yadda ya gwada mata a yanzu gaskiya ya nuna tana da girma da daraja a wajansa.

Tsaye ya miƙe yana gyara botir ɗin rigar shi.
Yaɗan dubeta wadda tai laƙwas ta kasa motsi.
"Ki tashi muje ko sekinyi wanka?"
Da sauri ta miƙe taɗan zabura tasan wani wanka yake nufi kafin taɗan tura bakinta gaba kaɗan ta ɗaura ɗankwalinta tare da mayafinta.
Ta ɗan gyara bedshirt ɗin tare da yin gaba ta barshi a tsaye.
Murmushi ya sauke tare da bin bayanta a falo ta tsaya tana jiran shi harya ƙaraso ya kama hannunta.tai saurin ture shi.
Taja baya.
Bai ce mata komai ba yayi gaba abinsa tana binshi a baya.
Falon Abba suka shiga.
Dattijo ne mai kama da Aliyu sak hatta bakar fatar shi ashe irin ta mahaifinsa ce don ko kaɗan bai yi kama da.ammi ba.
Zaune yake saman kujera one seater yana karatun jarida.
Sallamar su tasa ya aje jaridar yana ƙawata fuskar shi da murmushi tare da cewa.
"Har kin tashi kenan Ƴata sannu"
Wata kunya ce ta kama ummul tai saurin xubewa tana gaishe dashi wanda yana amsa mata cikin sakin fuska.
Tama rasa waya fi karamci a tsakanin uwa da uba ga Aliyu mutane ne masu matikar karamci wa ɗan adam.
Shima gaishe da Abba yayi a nutse.
"Lafiya lau baffa yaya iyalin naka dafatan kuna lafiya"
Sosa kanshi yayi tare da cewa.
"Lafiya kalau Abba dama nazo ne mu wuce da Ummi can gidan nata..............

Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.


Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588


*50*


Da sauri ummul ta kalle shi wanda yayi mirsisi kamar bai san irin kallon data ke masa ba.
Murmushi Abba yayi tare da cewa.
"Kai da kace zata yi sati biyu anan kuma yaya zaka zo da maganar tarewa tun yanzu bayan ko gama shiri bakai ba"
Da sauri ya tari numfashin Abba tare da cewa.
"A,a Abba nikam na gama komai yau zanzo mu wuce da daddare"
Lokacin Ammi ta shigo falon tai matiƙar mamakin ganin Aliyu zaune gaban Abba duk da Hassana tace mata yayansu ya shigo tai zaton yana ɗakin matar sane.
Zama tayi a gefen Abba da sauri Aliyu ya sada kai yana gaishe ta kafin Abba ya soma magana.
"Tofa kinga yaron ki wai yace ze wuce da matarsa ya gama shirin sa"
Haɗe rai Ammi tayi tare da cewa.
"Ba yanzu ba, Ya bari har ta kammala sati biyun daya ɗiba mata"
Shafo kanshi yayi tare da furta ammi zata kashe shi acikin zuciyarsa sannan yace.
"Ammi nagama komai please ki barta ta tare a ɗakin mijin ta nan ne rufin asirin ta"
Ita dai ummul ƙasa tayi da kanta muryarta sanyi ƙalau tace.
"Dan Allah Ammi ki barni anan gidan nikam nafi son wajanki"
Wata uwar harara ya ɓalla mata yana ƙwafa aranshi kafin yayi kalar tausayi ya dubi Abba.
"Please Abbana karka bi tasu Ammi yau ummi ta tare agidanta sabida na kammala shirina"
Dariya Abba yayi tare da cewa.
"Iko se Allah kaida kake cewa baka son ta tausayin ta kake sannan kazo kuma kana ƴar murya tun kafin aje ko ina"
Da sauri Ammi tace.
"Ai daɗina da gobe saurin zuwa Abban su daman mai nagaya maka?"
Turɓune fuska yayi batare daya kuma magana ba da alamun ƴan zuciyar sun motsa.
Ita ko Ummul yadda Ammi tayi yayi mugun yi mata daɗi wato har iyayenshi ma sun san ba son ta yake ba tausayin ta yake lallai ma.

Kallon Ammi Abba yayi tare da haɗe hannayenshi biyu cikin kwantar da kai yace.
"Muna barar amaryarmu ayi hakuri abashi matarsa dan Allah badan shiba"
Murmushi Ammi tayi tare da cewa.
"Gata gashi nan inta ga zata tare to Shikenan amman dai kasan kayi son kai wallahi"
Murmushi shima abban yayi tare da cewa.
"To ai ƴata bazata ƙi bin umarnin mijin taba kai baffa anjima kaɗan kazo ka ɗauki matarka Allah ya baku zaman lafiya"
Daɗine ya kama shi kamar yayi tsalle amman a fili seya kame yana watsa wa ummul wani kallon ƙasan ido aransa yana cewa kaida matarka se kai laushi kafin abaka ita.

"To Amman fa naga kamar bata zo da kayan sawar taba"
Cewar Ammi.
Da sauri yace.
"No problem zan saya mata wasu ai"
Wata irin kunya ce ta kama ummul kamar ta nutse na yadda Aliyu ke nuna rawar jiki akan tarewar ta agaban iyayen shi babu ko kunya.
"Allah yayi maku albarka ka kaita wajan su saratu yau zasu wuce sekuyi sallama ummi kijirani a ɗakina"
Cewar Ammi.
Godiya tai masu kana ta miƙe yabi bayanta daya ke tasan ɗakin Ammi bata jirashi ba sabida yadda ya bata kunya haka ta shiga suka gaisa dasu a mutunce shima ya shigo suka gaisa sannan suka fita wanda driver ze kaisu airport.
Zama tayi a ɗakin Ammi tare dasu shafa'atu da ƴan biyu shikuma yabi bayan su anty jidda.

Seda suka je wajan Abba suka kuma sallama sannan suka wuce parking space suka shiga mota driver ya jasu zuwa airport shi kuma Aliyu ya wuce Office ɗinsa duk da yau sunday amman ze ɗan cike wasu takardu ne.

A falon Abba Ammi ta dube shi tace.
"Ai wato naso wannan yarinya bata tare yanzu ba harse baffa yazo yana min kuka da idanun shi akan soyayyarta sannan zan bashi ita Amman yanzu idan ta tare ze ganta ne a ɓagas har yayi mata wulaƙanci".

Murmushi Abba yayi wato su dai mata tunanin su ɗaya ne koda sun tsufa tofa babu wani hankali kamar na namiji.
Sannan yace mata.
"Hafsatu kenan ke a ganinki rashin tarewar yarinyar nan kamar shine cinyewarku to bari kiji ni a tunanina tariyar wannan yarinyar ɗakinta shine masalaha domin ta hakanne ze warware dukkan ƙullin matar sa sannan shima baffan anan ze gane waya ke so acikin su wannan yarinyar zata zama kamar garkuwace gare shi"
Yaja fasali kana ya ɗora.
"Haƙiƙa baffa bai taɓa soyayya a rayuwar shiba haka zalika bai san mene soba domin matarshi ta hanyar shirka suka bi suka tusa soyayyarta azuciyarsa ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login