Showing 63001 words to 66000 words out of 83661 words

Chapter 22 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11369

walwala basma tace.
"Amman wannan addu'a da Aliyu ya fara tai mana cikas wai wato ita addu'a tasirine da ita muddin zakai to se Allah ya kareka wato rana ɗaya da Aliyu yayi sakaci bai yitaba shine muka sami ƙofar shiga jikinsa, Da kuma muka sami ƙofar se muka dinga yi masa sihirin daze dinga sakaci da addu'ar shine fa har na sami damar shan kanshi har na tsayin shekaru biyar da kuma yanzu aikina ya fara saki addu'a ta ratsa jikinsa kinga komai nason zame min tarihi"

Tafaɗa tana kallon babar tata.
Numfashi hajiya binta tai tare da cewa.
"Shiyasa nace muɗan yi haƙuri da asirin haka domin idan kana wa mai addu'a asiri tamkar kana tsira allura ne jikin dutse! kinga wannan mutumin shine dutsen shi kuma asirin allura to kinga babu yadda za'ai allura ta ratsa dutse dukda ƙarfe ce ƙarshe ma sedai ta karye, Sabida haka kije kita kirsa da kisisina tun kafin ɗan sauran sihirin jikinsa ya karye gudu nake karya ma zo yace bai san yaya akai ya aureki ba shiyasa nake son mu ƙara samunta asirin namu amman wannan addu'ar tashi data mahaifanshi tai mana shamaki"

To aranar dai seda su basma da uwarta suka kira ƴan duba kusan biyar amman kaf cikinsu babu wanda ya gano mai Aliyu yake ciki kuma babu wanda ya gano auren da Aliyu zeyi bare su lalata shi.
( sun manta faɗin Allah daya ce: idan yaso abin sa babu wanda ya isa ya hana koya tokarar: idan ya nufi bawan sa dayin Abu idan aljanun duniya da mutanan duniya da duk abun da ke cikin duniya zasu taru domin su hana se Allah yace: Kullan yasibana illah makata ballahu lana: wallahi babu abin da ya isa ya cutar dakai babu! babu!! babu!!! haka ake son haƙidar dukkan mumuni ta zama ta dogaro ga Allah! babu wani abun da ya isa ya hana Allah ikon sa akan bawa haka babu wani abun da ya isa ya cutar da bawa se dai idan Allah ya so! kuma hakan yazo a cikin ƙaddarar ka kamar yadda ƙaddarar auren basma tazo cikin kundun Aliyu wanda silar sakaci da addu'a ya sanya sihirinta yayi tasiri akan shi wanda daman hakan tun fil azal fararrene a wajan Allah! ubangiji cikin iliminsa ya ƙaddara hakan zata faru tun fil azal domin ba da ban Allah yaso ba da babu yadda za'ai maƙaryatan mushirikan bokayen su basma suyi tasiri akan Aliyu )

Cikin mugun ƙudiri basma ta dawo gidanta aranar ma kusan sakinta Aliyu yayi domin koda taje ɗakinsa tana mai faɗa akan bai zo duba mahaifiyarta ba rufeta yayi da masifa daman a tunzire yake ummul ta raina shi ta ɓata masa rai to duk wannan fushi seya huce shi akan basma.

Babu yadda ta iya haka ta koma ɗakinta tana kuka!
Haka kwanakin suka ja duk babu daɗi domin tun ranar Aliyu ya tattara ya watsar da ita ko abinci baya ci agidan se agidansu ita kanta ummul ya tattara ta ya watsar shiya ma mance da cewar za'a ɗaura masu aure friday sesu baba karamine da wasu Abokanshi keta aikin tura katin ɗaurin auren.

Se Ammi data ke ta faman shirinta ana sauran kwana uku ɗaurin aure lefe ya kammala wanda ƴan ɗaurin aure zasu tafi dashi shidai Aliyu kallo ɗaya yayi ma kayan ya taɓe bakinsa Akwatuna set biyu an zuba kaya masu tsadar gaske ciki shikam yama rasa wani irin murna su Abba suke a wannan biki dasu keta ɓarin kuɗi kamar babu gobe.
Haka zalika danginsu na kano ƴan uwan Ammi dana katsina na abba da ƙannen shi duk sunzo kamar wani bikin farko duk sun cika gidan se saukewa ake ana ɗorawa.

Shi tunda yaga haka ma bai kuma zuwa gidan Ammi ba se ana i jibi ɗaurin auren Abba ya kirasa ya nuna mai shaddar daya ɗinka masu shida shi hatta hula iri ɗaya shida abba kallon shaddar yayi wadda ta lashe manyan kuɗi yayi murmushi ya ɗauka ya fita bayan yayi masa godiya wato dai wannan auren na gata za'ai masa.
*KANO*
Tuni gidan Su ummul ya ɗinke da ƴan uwan bamu dana malam habu sedai bamu tana cikin damuwar rashin kawo lefe domin yadda hadiza da muƙarrabanta keta zuba habaici da gugar zana suna cewa auren cushe ne domin ga ango nan har yau baizo ya gaida mahaifan amarya ba bare akawo lefe har kuka bamu take sabida itama zuwa wannan lokaci ta sare da cewar hajja ce kawai ta haɗa wannan auren badan ango na son ummi ba domin har yau bayan kawo kuɗi babu wani daya ɓullo daga ɓangaren angon ita kanta ummi kayan da zata saka se bamu ce ta ɗinka mata bayan sarai an san ango yana bawa amarya ƴan kuɗaɗe domin siyayyar biki amman shi wannan duk kuɗinsa da ake faɗa bai bawa ummi ko tsinke ba.
Innah hussaina ce ke tausarta tana bata misali da cewa yanzu fa ta godewa Allah daya bawa ƴar tata miji ƴammata nawa ne ke jiran irin damar ummi amman basu samu ba.
Da wannan tausar da innah hussaina kewa bamu ta samu ta saki ranta har dai take sakewa ana hidima da ita.
Waɗannan kuɗaɗe suta ware dubu ɗari acikinsu ta bawa innah hussaina da sadiya suka shiga kasuwa suka siyo kayan abincin biki na dubu hamsin dubu hamsi kuma sukai ƴar siyayyar kayan girki.
Dubu ɗari biyu cif ta bawa innah tace idan sukaje can asai wa ummi kayan gado koda babu kujeru ne.
Ta ɗauki adashin ta na dubu ɗari tai musu ɗinku nan biki da sauran siyayya.
Cikin Amincin Allah bamu ta gama duk wata hidimar siyayyar ta cikin rufin asirin Allah.
Ta ɓangaren innah hussaina kuwa babbar ƴarta maryam dake aure anan cikin gari ita kewa ummul gyaran jiki tuni fatar ummul tai wani irin kyau haskenta ya ƙara fitowa magungunan mata masu kyau masu saka matsi da ƙarin ni'ima da kashe sanyi sutake ta bawa ummul wadda suka ƙulle a ɗakin hajja tun bikin na sauran kwana biyar ummul ke amsar gyara.

Ummul har wani yalo tai dan tsabar haske gefe ɗaya mararta na wata irin kartawa sabida maganin da ake bata ƙasanta kullum jiƙe yake dan arana seta sauya pant sau uku!

Yau sauran kwana ɗaya ɗaurin auren gaba ɗaya gida ya hargitse da shirin walima wadda sadiya ta haɗa a ƙofar gida ƙarfe huɗu malama hafsat ta gabatar da lecture akan aure sadiya tai kokari wajan yin kayan walima wanda ta dinga rabawa jama'ar dasuka halarci walimar ƙarfe shidda aka gama lecture malama hafsa na tafiya Mai dj ya dasa nashi sosai ƙofar gida ya hargitse da masu rawa kamar babu gobe.
Ummul tai kyau cikin blue les ɗin da bamu ta ɗinka mata wanda taje gidan kwalliya da ƙyar azababban kyau tayi cikin kayan tana tsakiyar filin rawa ana ta mata liƙi.
Su basira da zainab da sakina ƴaƴan hadiza sune sukai shigar shadda iri ɗaya sukai kwalliya mai kyau da sauri suka shigo filin rawar suka rufe ummul da liƙi abin ya bawa kowa mamaki ita kanta ummul tai mamaki dan duk a zatonta bama zasuzo wajan ba ganin haka sadiya da kausar suka rufe su basirar suma dana su liƙin, nan fa wajan ya zama na ƴaƴan habu zallah don a junansu sukewa junansu liƙi suna rawa, Raurau idon ummul yayi se kuka! babu shiri basira ta rungumeta tana raɗa mata.
"Kibar kuka ummi mufa jininki ne wallahi umman mu bata isa ta rabamu daku ba"
Kowa a wajan mamaki yake hadiza kuwa kunyar da ƴaƴanta suka bata ita ta saka tabar wajan domin hatta shaddar jikinsu basu gaya mata sunyi ba, Sosai hadiza ta shaƙa aikwa tai ɗaki tana zage zage wata kanwarta ce tace mata.
"Yaya hadiza kibar ƴaƴan nan suyi zumuncin su dan wallahi na gama ganowa kece kike rabasu da ƴan uwansu idan ban da abinki ma wani kishi zaki da hassana! ai idan kikaji ana kishi da akwai dalili to malam habu mai zakaiwa kishi ajikinsa abu ba mamora se aikin mutuwar zuciya"
Jikin hadiza ne yayi sanyi wata nadama ta rufeta tabbas ayau taga tasirin jini wato dai duk inda aka ce jinin kane tofa bazaka tauna ƙashinsa ba koda kaci namansa yau su basira sun ɗaure mata kai, sun nuna mata cewa su ummul de ƴan uwan sune.
Tashi tayi zuwa ɗakin bamu lokacin tana zaune ita da iya hussaina suna lissafa maggi hadiza tai sallama cikin murnarta.
Haƙuri take bawa bamu akan dukkan abun da tai mata sannan tace yanzu ta gano cewar naka se naka ƴaƴanta sun bata kunya sabida haka ta janye dukkan wata masifa a zauna lafiya.
Murmushi bamu tai sannan tacewa hadiza ai daman ita bata rikonta tunda dai hadiza barta da faɗa da habaici amman bata taɓa yi mata asiri ba kuma bata taɓa yiwa ƴaƴanta asiri ba, Ko ƙaddarar data samu ummul ma ba ita ta ɗora mata ba silar aiki ne ya jefata hakan.
Sannan tace su basira sun biyata kuma sun nuna mata su ƴaƴan halak ne kuma jinin ummul tunda basu nuna bakin ciki da auren taba a yanzu tana ƙara jin ƙimar ƴaƴan a zuciyarta.
Wannan shiri ya bawa kowa mamaki hatta hajja tai murna domin da hadiza da ƴan uwanta aka cigaba da hidimar biki su basira kuma suke takewa ummul baya domin hatta kayanta sakina ce ta ɗauke ta ɓoye mata haka zalika sunwa ƙawarsu magana akan gobe zasu kai ummul tai mata kwalliyar ɗaurin aure.

Mai Dj bai tashi ba se wajan taran dare cikin gajiya ummul ta shiga gidansu rabon ta da gidan su shekara biyu kenan tun bayan barinta gidan se yau wani kuka ta danne direct ɗakin hadiza ta shiga ta zauna a bakin gadonta abinda ummul bata taɓa yiba kenan shiga ɗakin hadiza se yau.
Aiko hadiza jikinta har rawa yake ta kawo wa ummul tuwo da zafinsa anan ta zauna tana ci a hankali zuciyarta cike da fargaba yau kwana shidda Aliyu bai neme taba kode tai masa laifi ne.
Sallamar Ameera da wasu ƙawayenta yasa taɗan saki jikinta.
Gidan hajja ameera takai ƙawayen ummul nacan hotoro da suka haɗu a gidan karuwai.
Bamu ce ta shigo ɗakin hadiza ta zauna a bakin gado tana fuskan tar ummul.

Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


*KOBA SO*
*HASKE*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*RABON WANI*
*ZUMA A BAKI*
*AUREN BARE*
All in 1500 Mai so seya biya tanan 0078174806 starling bank shedar biya ta 08142105218.





Kamar yadda muka sani kamfanin oriflem yayi give wajan samar mana da kayayyaki masu inganci wanda suka hada da kayan kwalliya, kawa da Gyeran jiki,haka ma sun sauka shekaru cute da (10)wajan samar mana da supplement kuma sunyishi yadda ya dace damu.
Wellness yana aiki da dama acikin jiki wanda Inya shiga jikinka zai duba matsalar ka yayi maka maganinta.kadan daga cikin aikin da wellness keyi acikin jiki ya hada da Gyeran fata,Gashi da kuma rage Tumbi,yana kara garkuwar jiki,Yana maganin stress,yana rage cutar mantuwa,yana maganin ciwon kashi yana taimakawa wajan Infection da High B.P
Wellness Sinadarai ne dake maye gurbin abunda aka rasa wanda dan Adam ke buqata domin su taimakawa wajan gina jiki da bashi lafiya.
Wellness ya tattara Abubuwa a sarchet daya wanda ya hada da Omega 3 kafso 1,Astaxanthine and Bilberry Extract kafso 1,da Tablet na multivitamins &Minerals.
Sarchet 1500,kwali 30,000
Domin samun Naku a Tuntubeni ta wannan number 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

44


Cikin nutsuwa ta ce mata.
"Ummi ki gaya min tsakanin ki da Allah wannan yaron shiya ce yana sonki ko kuwa hajja ce ta haɗaku? sabida ni har yanzu hankalina ya gaza kwanciya ace gobe ɗaurin aure amman babu wani motsi daga dangin miji?"
Bamu ta faɗa tana mai bayyana damuwar dake cikin ranta ƙarara.
Wasa take da hannunta wanda yasha jan lalle da baƙar fulawa wanda yayi mugun kyau bana wasa ba.
Taɗan zame kallabinta haɗaɗɗan kitson da kausar tai mata ya zubo har kafaɗunta.
Ta dubi Bamu cikin sonta da ƙaunarta tace.
"Yayi min waya Bamu akan ze bani kuɗin siyayya to wayata tana hannunshi se nace zan basa account ɗin Ameera wadda ta taimaka min lokacin da baba ya koreni shine yahau faɗa wai baya son nata to ya ƙara kirana wai na rainashi nikuma ban kuma bita kanshi ba base yaci kanshi ba"
Tafaɗa tana zunɓuro bakinta gaba.
Salati Bamu ta hauyi tana tafa hannu.
Sannan ta dube ta tace.
"Ah lallai ba shakka kice wannan gaɓuntar zakije ki masa agida? yanzu ke dan gidanku haka kikaga inawa babanku? duk irin azabar dayake bani kin taɓa ganin na ɗaga mai harshe kona ƙi bin umarninsa? so kike tun kafin ki shiga gidansa gaddama ta fara haɗaku? har kika sa naita zargin bawan Allah ashe ba haka bane to wallahi bazan lamunci iskanci ba maza ki ɗauki wayar hajja gata nan naganta a hannunki ki kirasa ki basa haƙuri a gabana"

Bamu takai maganar cikin harararta.

Kuka! ummul tasa wiwi kamar wadda aka ma mutuwa har tana shure ƙafafunta cikin kukan take cewa.
"Nifa bazan kirashi ba hajja tace na dinga jan ajina so kike ajin ya tsinke yau kwana shidda bai neme niba seni mai nayi masa ni Allah ban kiran shi"
Tafaɗa tana mai kwanciya a gadon hadiza.
Ɗaka mata duka Bamu tayi wanda yasa ta zabura ta miƙe tana mai sakin ƙaƙƙarfan kuka!
"Idan baki kira shiba zan saɓa miki wannan shegen kafar kan naki insha Allahu seya sauke maki shi wato so kike tun yanzu ki tafi da ɓacin raina ko? da me zanji amman idan na faɗi na mutu seku huta"
Bamu ta faɗa cikin takaici.
Wani tsalle ummul tayi tare da rungume bamu tana cewa.
"Bazaki mutu ba babarmu wallahi kika mutu mun lalace zan kira sa kiyi haƙuri"
Tafaɗa tana kuka!
Hannunta har rawa yake ta ɗauki wayar ta lalubo numbersa ta saka speaker ta shiga kiran shi hartai ringing ta gama bai ɗauka ba.

Minti biyu suna tsaye cirko cirko ita da bamu sega kiranshi ya shigo.
Hannu na rawa ta ɗaga ta ƙaro speaker.
"Assalamu Alaikum barka da dare"
Tafaɗa muryarta cikin kuka!
Bai amsa sallamar ba se cewa yayi.
"Mi aka maki kike kuka uwar ƴan arhar hawaye?"
Kallon Bamu tayi wadda take murmushi kafin ta share hawayen ta tare da ce mashi.
"Babarmu ce tace sena kiraka na baka haƙuri gata ma"
Tana faɗa ta miƙawa bamu wayar wadda tsabar kunya kamar zata nitse.
Shiko Aliyu babu wata alkunya ya soma gaisheta cikin sakin fuska kamar ya jima da saninta.
Cikin dattako bamu tace.
"Sefa haƙuri da ummi yarinya ce Allah ya taya ka riƙo"
Murmushi ya sauke mai sauti tare da cewa.
"Karki damu mama haka ƙannena suke Nagode ƙwarai"
Sallama sukai ta miƙawa ummul wayar ita kuma ta fice tana jin ranta sayau daga jin kalamansa tasan ze riƙe mata ƴarta da amana


"Shine kika gaya mata mai ke tsakanin mu ke mai yasa baki da wayo ne? yanzu kome ma mukai bayan auren sekin faɗa? yanzu haka zakita kai mata ƙarata?"
Yafaɗa muryarsa sanyi ƙalau kamar mai jin sanyi.
"Nifa ita tace bata ga ango ba har wajan da akai walima ta ɗauka zaka zo shine na gaya mata haushi na kake ji"
Tafaɗa tana wani tura baki gaba.
Cikin sauri Aliyu yace.
"What bance bani son bidia ba? shine seda akai walimar?"
Murmushi taɗan yi tare da cewa.
"Wa'azi ne fa"
Shuru ne ya biyo bayan kafin yace.
"Ok seda safe"
Ya katse wayar.
Taɓe baki tayi tare da miƙewa ta fita gidan hajja ta wuce wanda ya cika da ƴan uwan hajja ɗakin kusa dana hajja ta shiga wanda su ameera suke ciki dasu basira wanka tayi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah ta kwanta bacci.

Tun asubahi da suka farka basu koma ba hira ce ta ɓarke wadda basu fargaba se wajan takwas sannan sadiya taje ta amso musu kayan karin kumallo.
Ƙarfe tara ummul tai wanka suka wuce gidan kwalliya ita dasu basira.

Daga can katsina ƴan uwan Abba da zasu taho ɗaurin aure suka ɗungumo cikin manyan motoci, Daga Abuja ma ɗaurin auren ya sami halartar manyan mutanen Abba.
Wanda seda Abba ya kama babban restuarent wanda za,a gudanar da reciption bayan ɗaurin aure.

Aliyu ya isa airport shida wani Abokin sa kamal, sauran abokan shi kuma daga nan katsina sun wuce suda su baba ƙarami.
Ƙarfe 11:00am jirginsu ya sauka dole seda ya kama ɗaki a hotel wanda anan yayi wanka ya haɗe cikin ɗanyar shaddar da Abba ya ɗinka masa babbar riga da ƴar ciki da hula da takalmi mai kalar hular saman kanshi.
Wani irin azababban kyau yayi tamkar ka sace shi kayita kallon shi Baba ƙarami ne ya ƙaraso a motar shi ya ɗauki Aliyu a hotel ɗin tare da kamal.
Wanda zuwa wannan lokacin tuni su abba sun jima da sauka suma har sun isa babban masallacin unguwar su ummul wanda anan za'a ɗaura auren.

Malam habu sanye cikin farar shadda bakinsa kamar gonar auduga duk irin alwashin daya ɗauka akan babu ruwansa da sha'anin bikin, bai kai ko ina ba domin yana kusa da ɗan uwansa yana kallon yadda manyan alhazan birni ke shigowa cikin masallacin gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi.

Tun daga farkon layin su ummul har ƙarshe babu masaka tsinke sabida tsabar ɗan adam ɗin dake wajan manyan motoci na alfarma ke parking mutanan Abba mutanan Aliyu da baba ƙarami ya tutturawa suke firfitowa.


Kawu usman ya firfito da akwatunan lefe ya kirawo fahad yace ya kai gidan hajja wanda hajja ta saka wasu daga cikin danginta suka shigar da akwatu nan gidan su ummul.
Nanfa kallo ya koma sabo kowa ya ruɗe da yadda ake fito da kaya daga cikin akwatunan kamar babu gobe babu abin da mutanan gidan su ummul keyi se buɗa bakin bamu ya kasa rufuwa anan ɗakin hadiza aka jere kayan lefen nan fa maƙotan dake gidan suna taya su bamu tuwon ɗaurin aure sukai ta leƙe suna ganin madarar dukiya.


Ƙarfe 12:00pm dai dai Aliyu ya shigo masallacin bayan shi abokan shine dasu baba karami gaba ɗaya kallo ya koma kan Ango shi kanshi malam habu kawai kallon surukin nashi yake cike da mamakin ina ummi ta samo wannan haɗaɗɗan mutumin.
Shuru masallacin yayi zuwa wani lokaci waliyin Aliyu kawu Abubakar ya nemi auren ummul wajan kawunta , Babu wani ja inja waliyin ummul yace ya bashi shedu suka shaida daman sadaki anjima da bayarwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login