Showing 30001 words to 33000 words out of 83661 words

Chapter 11 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11349

uban yayi sarki ina miƙa gaisuwa ta ga duk wata macen data amsa suna na uwa mai tarbiya da sadaukar wa domin inganta rayuwar ƴaƴan ta* 😭😭😭😭


Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

23


Bayan taci abinci ta ɗan kwanta abin ka da jikin talaka tuni bacci yayi awon gaba da ita sama-sama cikin baccin ta taji tashin maganganu masu kama da faɗa acikin tsakar gidan nasu muryar hadiza ce ke tashi tana cewa.
"Kaga malam baka isa kazo ka sakani agaba nida yarana ba ita matar so ka barta da auren ka aka tana fita tun safe bata dawowa se dare ai baka taɓa bita kanta ba duk abin duniyar data ke shigowa dashi bata baka takai yaranta makaranta suna ɗaga mana kai, seni daka raina zaka saka agaba ɗan cinikin danai ka rance idan na hana ka hauni da cin zarafi wallahi wannan mutuwar zuciya ta wasu mazan hausawan tana cutar su"
Tashi hassana tayi tsam daga kwanciyar ta zauna sosai ta fara jin maganar malam shi kuma.
"Ke hadiza dakata ke har kina da bakin cemin mai matacciyar zuciya kin manta da taimaka miki nayi na aureki sabida kurmantar ki babu mai zuwa wajanki seni dana ɗauki lalura, Kuma hassana da kike maganarta ai nagaya mata cewa itace uban yanzu nina zare hannuna akan ta ita da yaranta ayi dai mugani in ruwan ido ze dafa shinkafa"
Yafaɗa cikin ɗaga murya.
"Ahayye! shagali to ai bari kaji da namiji irin ka malam gwara zawarci kai to meye marabarka da gawa agidan nan mai kake mana maika tsinana mana ka kashe zuciyarka a banza kaiba musaki ba,ko ita hassanar da kake tutuya kabar mata yaranta ai ba wata uwar kake tsinana musu ba yara da ran ubansu amman suna yawo kamar marayu sabida mutuwar zuciyar mahaifin su........
Tas!!!
Ya wanke hadiza da mari hannunsa yana rawa yake ce mata.
"Ki fita a idanuna hadiza in kika ƙara magana sena sake ki! kuma bazan baki ƴaƴanki ba suyi bara tunda ubansu mai mutuwar zuciya ne"
Yafaɗi haka kuma ya tsugunna ya kwashe ƴan canjinta tas yayi ficewar sa tukubar mai tsire.
Zaman ƴan bori hadiza tayi a tsakar gidan tana rusa kuka!
Ƴaƴanta da suke laɓe a ɗaki suka fito suka cicciɓeta sukai ɗaki da ita.
Abin duniya duk yayiwa hadiza yawa gaba ɗaya komai ya fice mata akanta ga jarabar babansu basira ga takaicin sauyin da hassana ta samu a kwana biyu.
Duk abin da sukai hassana tana jinsu bata ko tanka ba, bare ta fito har wajan tara yaranta suka dawo daga makaranta abinci ta zuba musu suka ci tana tambayarsu wuninsu har sukai bacci.

Wajan sha ɗayan dare malam habu ya shigo gidan aɗakin sa ya yada zango, Tunda dama gidan ɗakuna uku ne to matan ke zuwa ɗakinsa ranar girkinsu subar ƴaƴan su a ɗakunan su.
Ita dama hassana ta jima rabon ta da miji tun bayan cin mutuncin dayayi mata itama seta fita daga harkan shi sam ta nuna baya gabanta.

Malam habu zamansa keda wuya a ɗakin ya haska fitilar sa ya bude ledar naman yaci ya yarda ledar yasha ruwa tashi yayi zuwa ɗakin hassana daga bakin ƙofa ya tsaya tare da cewa

"Duk matar data ke ƙaura cewa mijinta kwana take mala'ikun rahma na tsine mata"
Gyara zama hassana tayi tare da cewa

"Idan ya kirata taƙi zuwa ba! in bai kirata bafa? sannan shi namijin daze gasa iyalinshi fa? wanda baya da nakasa ajikinshi se a zuciyar shi mai ƙarfi da lafiyar nema amman dan tsananin cutar kai ya kashe zuciyarsa a gindin matan sa yake ci yake sha ya mayar da ƴaƴan sa marayu?.shi wannan mutumin yaya ze dubi Allah da mala'ikun sa?"
Tafaɗa babu ko shakka.
"Hassana karki nunan halin ba ƙauye idan yaci miyar birni wallahi idan baki taso ba sena shigo nai miki tsirara gaban ƴaƴanki na karɓi haƙƙina"
Sanin halin tijarar sa yasa jikin hassana yayi sanyi.
Ta miƙe tana hawaye tabi bayanshi zuwa ɗakinsa wanda duk ya haɗa dauɗa dama ita ke mai gyara yanzu kwa ta dena.
A wannan dare seda malam habu ya fidda maitar sa akan hassana bai sarara mata ba se asubahi

Koda ta fita daga ɗakin kuka take sosai na rashin adalcin mijinta banɗaki taje tayi wanka.
Koda ta fito buɗa taji na tashi hadiza na yada magana.
"Wallahi anji kunya dan tsabar rashin zuciya mutum yace yabar miki ƴaƴanki amman sabida jaraba da baƙin naci seda kika bishi ganin munyi faɗa dashi"
Alokacin hassana ta ɗibi ruwan awala tare da cewa.
"Daɗin tama ba zina nayi ba" zina itace abin kunya to raya sunna nai mijina yana ta shimin albarka kinga kwa na sami lada"
Tana faɗar haka ta fara alwalar bayan ta gama ta wuce ɗakinta ta tada ummul da sadiya da kausar sannan ta soma gabatar da sallah

Bayan sun idar ruwan wanka suka ɗora yana tafasa suka shiga wanka da kanta ta ɗumama musu sauran abincin jiya suka ci ragowar malam dake tsaye bakin ƙofa yace abashi yaci.
Cikin mamaki hassana take kallon shi babu ko kunya ya karɓe sauran abincin buɗar bakin ummul tace.
"Allah bamu dana san shize ci dase na zubar shibai bamu ba kin samo ze wani ce ze ci"
Tafaɗa cikin haushi.
Duka bamu takai mata tare da cewa

"Nikam ban san yadda akai kika tsani mahaifin kiba ina rabaki da wannan uba ubane fa"
Hawaye ta zubo tare da cewa.
"Tun ranar daya fara zagin mahaifan ki naji bana son shi wallahi bamu ina ga bashine mahaifin muba"
Duka ta rufe ummul dashi sosai ta nuna mata ɓacin ranta na furucin data ma mahaifinta.
Ranar da kuka ummul ta fita makaranta ko a hanya da malam ya ganta ya tawo da sauri dama shi duk cikin yaran shi yafi son ta sedai ita sam ko sakar mai fuska batai haka zalika su kausar ma tsoron sa suke ji sabida tsabar yadda sukaga yana masifa........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

24


Cikin so da ƙaunar ta yace.
"Uwata tafi ta kowa waye ya taɓaki?"
Ya kamo hannunta yana saka ɗayan hannun sa yana goge mata hawayen dake zubo mata.
Wata kalar harara ta zuba mai ta fincike hannunta tayi gaba.
Sadiya ce take binta abaya tana mata faɗa kamar haka.
"Haba ummi ubanmu ne fa duk abin da ze mana bazamu biyasa haihuwar dayayi mana ba"
Da tarin takaici ta juyo gaban sadiya tace.
"Seki gaya min tunda aka haife mu abin da yata ɓa tsinana mana in ban da ma neman kashe mana uwa daya keyi wallahi kinji na rantse duk ranar danai kuɗi sena ɗauke uwata daga wannan baƙin gidan"
Tafaɗa a tunzure tare da fisgar hannun ihsan sukai gaba.
Dama mai haƙuri idan ya tashi bai da daɗin kai.

Itama hassana shirin fita aiki tai amman can ƙasan zuciyarta tana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar ƴar ta akan ubanta.
Abin mamaki koda ta fito zata tafi yau malam yana zaune akan bancin mai rake daya ganta bai mata wannan kallon tsanar ba sema tashi dayayi yana cewa.
"Ƴan biyu kyautar Allah tawa uwar sadiya da kausar"
Ya kuma riƙo mata ledar kayanta ya sakata agaba se surutai yake na rashin kan gado.
Aranta kuma mamaki take lallai mutuwar zuciya masifa ce seta mayar da mutum mahaukacin ƙarfi da yaji.
Seda ya kaita har bakin layin sannan ya koma.
Aikam zata shiga layin ta hango talatu suka gaisa sosai.
"Wa nake hangoki dashi ɗazu kamar babansu?"
Cewar talatu cikin barkwanci
"I wallahi shine ya rakoni"
Hassana ta bawa talatu amsa kai tsaye
Wata shegiyar dariya talatu ta sanya tare da cewa.
"Iko se lillahi wato shidai malam habu ya zama ƙadangare mai bin ledar manja oh"
Tafaɗa tare da kuma cewa hassana.
"Toni na wuce mu wuni lafiya"
Tsaf hassana ta gane magana ta gasawa malam habu amman seta danne sabida bahaushe yace tsuntsun daya ja ruwa shi ruwan kan doka!
Itama gidan aikin nata ta wuce yau ma wai yaran gidan zasuyi partyn gama makaranta.
Tunda taje take tilar aikin kaji waɗanda suyar su zatai bayan ta kammala.
Ba ita ta sami kanta ba se magariba tayi sallah ta haɗa karonta tayo gida da uban nama don kai da ƙafa ma seda ta ciko wata baƙar ƙatuwar leda.
A bin mamaki malam yana waje yana ta sintiri aiko daya hangota ya wani saki ƙayataccen murmushi tare da amso ledar hannunta suka shiga gida atare.
Ɓuɗa hadiza ta sanya tana cewa.
"Oh ni dije ALLAH wadaron naka ya lalace wai mazan zamani nakasassun maza"!
Babu wanda ya kulata haka malam ya raka hassana har ɗakinta wanda ummul ta biyoshi da harara!
Ƙaton kwano hassana ta ɗauka ta zuba mai jallof ɗin taliyar data yo tare da soyayyan naman ta bawa kausar tace akai masa.
Dan tura haushi agaban hadiza ya amsa ya zauna ya buɗe yana ci yana dariya yana yada magana ita namiji mai zaman banza.
Jimm kaɗan ihsan ta fito hannunta ɗauke da wani kwanon ta mikowa basira tace mata.
"Yaya wai gashi inji bamu"
Basira tasaka hannu zata karɓa hadiza ta tungure kwanon ya faɗi abincin ya zube ƙasa.
"Dan ubanki ku mayu ne? me zaki da abincin da baki san daga inda ya fito ba?"
Hadiza ta faɗa da ƙarfi yadda bamu zata ji.
Cikin sauri bamu tacewa ummul taje ta kirawo ihsan buɗar bakin ummul tace.
" Bamu kullum inna ga umma fa dariya take min kuma taita kallona shine na gayawa hajja se hajja tace na dena zuwa wajanta karta cinye ni da baki da idanun ta"
Tafaɗa kamar zatai kuka!
"Kul karki kuma faɗar haka ummi kinji kita lahau'la insha Allah bata isa tai miki komai ba"
Sadiya tasa taje ta kirawo ihsan.
Shiko malam habu wata dariya ya saka tare da tattare naman da hadiza ta zubar ya ƙara akan nashi tare da cewa.
"Hassada cinikin matsiyaci"
Yayi ɗakinsa da ƙarfi hadiza ta ɗaga murya tace.
"Mutuwar zuciya masifar jiki"
Ta faɗa cikin takaici tayi ɗakinta.
A wannan daran ma seda malam habu ya buƙaci hassana.
***********
Kwanci tashi asarar mai rai yanzu haka hassana takai kusan shekaru huɗu agidan aikinta tama shiga ta biyar kuma sosai take samun canji ackin rayuwarta data yaranta waɗanda suka murje sukai.kyau nan da nan masassaƙin budurci ya soma bayyana a jikin ummul dama abinka da kyakykyawa har maza sun fara biyota da kuka take ƙarasowa gida lokacin suna jss3 ita da sadiya kausar jss 1 ihsan aji shidda.
Ta ɓangaren islamiyya kuwa tuni sunyi wajan izif 30 suna bada hadda sosai rayuwarsu ta canja sanadin aikin hassana wanda hatta malam shima yana cin arzikin aikin sedai duk ranar da ƴan cin mutuncin suka motsa tofa seya taɓa

Sam hassana bata kula shi sabida bata ma yinin gidan kusan kullum tana gidan aikinta.
Kuma ko can gidan aikin nata ma aikin gabanta takeyi ta iya da kanta sabida ta fuskanci mutan gidan suna jin kai da kuɗinsu sun ɗauki talaka banxa wofi rayuwarsu data yaransu kaɗai suka sani jin daɗinta ma wannan mima da yayanta Samir sun tafi london karatu se anyi hutu suke dawowa wani bin ma basa dawowa hutun dama kuma duk ciki sunfi bata matsala.
Sauran yaran basu kaisu girma ba da alamu sune manya agidan kuma su iyayensu suka fiso sannan uwa uba sam basa ganin mutuncin kowa hatta mahaifansu basu isa dasu ba.
Dama ƙiri ƙiri hajiya timo tace mata su sunɗauki talakane kawai wahalalle mai aiki da gaɓarsa abiya shi dan haka karta yadda ta ɓatawa ƴaƴan su rai don akan ƴaƴansu zasu iya komai wannan tasa hassana take kama kanta sosai babu ruwanta da kowa.
Acikin gidan iyaka cinta aikin ta ta kammala tayo gida abinta tana saka rai da cewar komai na Allah ne kuma bawa baya yanke tsammanin rahma daga ubangijin sa.
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

25


Kwanaki na tafiya lokaci naja dama haka rayuwar duniya take kwanci tashi asarar mai rai.
Komai yana tafiyarwa hassana dai dai misali don wannan aikin nata ya toshe mata wasu kafafan da dama acikin rayuwarta daman bahaushe yace babu nakash she se ka sash she.
To hakan take domin hatta malam habu yana ƙaruwa da wannan aikin na hassana.
Wadda sam bata da wata matsala da gidan aikin nata face ta rashin sanin darajar ɗan adam

Lokaci na tafiya yanzu haka su ummul sun zana jarrabawar filesimen wadda idan ana aji uku a sakandire ake zanata.
Sabida haka bayan sun zana ita da sadiya se suka fara zaman gida sabida hutun da aka basu na sati biyar lokacinne kuma hassana ta fara laulayi wanda yayi matiƙar firgitata domin ta ɗauka tayi bankwana da haihuwa daga kan ihsan sabida kusan shekarar ihasan goma sha ɗaya aduniya samun wannan ciki yasa hassana fita daga hayyacinta domin komai ya zamo sedai tayi shi batare da zafin nama ba.
Hakan ce tasa sadiya ke taimakonta agida da wasu ayyukan ita kuma ummul take tafiya gidan aikin ta tana mata aikin.
Ranar da ummul ta fara zuwa gidan aikin hajjiya timo tayi mamaki sosai na yadda taga yarinya ƙarama ta zage tana ta aiki bata sha mamaki ba seda ummul tai girki ranar kowa santi ya dingayi

Kuma ita bata ma kaiwa lokacin da hassana take kaiwa sabida tana da saurin aiki tana gamawa zata haɗo kayanta tsaf tayo gida.
Haka rayuwar ta cigaba har sanda su ummul suka koma makaranta cikin hukuncin Allah suka shiga ss1 ita ankaita sciense class ita kuma sadiya art class.
Kuma ahaka ummul take tafiya gidan aikin Hassana ƙarfe shidda bakwai ta gama abin karyawa ta wuce makaranta tabar kayan ta anan tana dawowa daga boko ta wuce tacan ta ɗora na rana wajan ƙarfe biyar ma ta gama tayo gida tana dawowa gida tai wanka taci abinci ta wuce islamiyya.
Sosai hassana ke tausayin ummi sabida yarinyar duka duka a lokacin batafi shekaru goma sha biyar ba sedai akwaita da garin jikin girma daka ganta zaka ɗauka takai shekaru sha takwas.
Sabida yadda masassakin budurci ya sassakata nono ya cika kirjinta dama tun tana 14 ta fara jinin al'ada kuma bamai matsalar ciwon mara bane ba.
Cikin hassana yakai wata tara ta haifi ɗanta namiji zokuga farin ciki wajan malam habu wanda ko hakika baiyi ba seda kudinta tayi ba jimawa da haihuwar taje akai mata allurar tsarin iyali dan wannan cikin ma tace a lalura ta same shi Allah yayi ze taka ƙasa.
Ɗa yaci sunan mahaifinta Ɗalhatu amman anace masa hanif saboda karantawa.
Lokacin su ummul suka fara zana jarrabar shiga ss2 bayan sun kare akai musu wanda daga sun koma zasu shiga aji biyar.
Lokacin Hassana tana wankan jegon Hanif wanda tace insha Allah tana arba'in zata karɓi aikin ta sabida gabatowar saukar su ummul tana son ummul ta zauna ta nutsu tai ta bitar karatunta.

Yau ta kama asabar tun safe ummul take mursu akatifa hannunta dafe da kirjinta.
"Ummi karna kuma magana a karo na uku".
Cewar bamu wadda take ta faman tashin ummul akan tai sallah taƙi.
Turo baki tayi gaba tare da cewa.
"Bamu zan fa tashi kaina ke ciwo jiya mun sha aiki agidan can ƴaƴan gidan sun dawo daga ƙasar waje sun gama karatun su"
Tafaɗa tare da tashi tabar katifar ta nufi tsakar gida tayo alwala tazo ta tayar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login