Showing 33001 words to 36000 words out of 83661 words
sallah.
Bayan ta idar da sallah bamu ta dube ta.
"Ummi dan Allah idan kinje gidan nan ki kula da kanki sosai nima na kusan komawa aikina"
Cikin murmushi tace.
"Niko shiga falon su bana yi ko sallah ma a bayan gidan nake bamu ina mai aiki ai bani da damar zaƙewa agidan da ba namu ba"
Albarka ta sanya mata da sanyin jiki ta shirya ta ɗauki kofin kokonta tasha sannan tai musu sallama ta fita.
Seda ta biya ta gidan hajja tana mata waƙa tana cewa hajjata najima ban zoba aguje ta fita daga gidan sanin hajja zata iya tsayar da ita.
Seda ta fita waje ta gyara tafiyarta wadda take yinta kamar bazata taka ƙasaba dan tsabar yanga wadda hakan ajinin ta take.
Bayan ta ƙarasa gidan kicin ta wuce ta soma haɗa wa mutan gidan abin kari ƙarfe goma mutan gidan sun halarci daining area dan haka a nutse ta soma kaiwa da komowa a tsakanin kicin da daining sosai Sameer ya kafe ummul da idanu wanda bai da sana'a ko acan turan se bin matan turawa kuma mima tana gayawa mahaifansu awaya amman basu dauki abin da mahimmanci ba
Ita kanta ummul ta tsargu da kallon nasa dan haka seta hade ranta tamau ta cigaba da jerawa harta gama ta wuce kicin ta zauna taci nata.
Tana zaune a kicin tai shuru sabida yau ameerah bata nan wai taje gidan su.
Kawai sejin mutum tayi akan ta ya wani tsaya da sauri ta ɗago tana furta addu'a cikin bakinta murmushi ya saki na yaudara tare da ce mata.
Ta dafo masa coffee takawo masa ɗakinsa.
A tsorace ummul ta amsa da to sannan ta ɗora masa ruwan coffe ɗin amman dik bata jin dadin yadda ya tsaya akan ta yana wani kallonta da ƙananun idanun sa.
Koda ta gama seta juya domin tambayarsa a fulas za,a zuba mai ko a kofi sedai wayam baya nan se wani daga cikin yaran gidan daya leƙo yace mata wai ya samir yace takai masa coffe ɗakinsa.
Yaron ne yayi mata kwatancen ɗakin sameer wanda ba'a cikin falon iyayen yake ba acan baya yake haka ta ɗauka ta tafi duk bata jin daɗin yanayin
Koda ta ƙarasa bakin kofar ɗakinsa tsayawa tai ta buga daya zo ya bude mata seya juya.
Se kawai ta dire mai a bakin kofar zata juya ta koma taji ya janyo hannunta kallon shi tai daga shi se tawul ya mayar da kofar ya rufe ya maƙureta da bango yana bin idanunta da kallo muryar sa ce ta doki kunnenta.
"Beauty ina son ki pls ki bani zumar ki na ɗan ɗana ni kuma nai miki alkawarin kawo muku karshen talaucin ku"
Koda take da ƙananun shekaru tasan haɗuwar namiji da mace haramun ne don haka seta ce.
"Allah yayi min tsari da iskanci kuma talauci baka isa ka fitar damu cikin saba se dai Allah"
Tafaɗa tare da tofa masa yawu saman fuskarsa.
Haushin hakan yasa yace.
"Shikenan baki da rabo kuma yanzu zanyi yadda naso dake kuma inga uban daya isa yace min domme"
Yana gama faɗin haka ya kamo bakinta ya fara tsotsa duk yadda ummi takai da duka da yaƙushi batai nasara ba kuka take tana dukan sa amman sameer bai sarara mataba seda ya kaita gadon sa daya sha gyara idanunsa rufe da son ɓatancin ga ƴar talaka ya soma rabata da kayan jikinta lokacin numfashin ta ya ɗauke amman sabida wahalar data sha haka numfashin ya dawo dan azaba lokacin mai afukuwa ta afku sameer ya raba ummul.da budurcin ta, ta hanyar yi mata fyaɗe!!!
Babu abin da take se kuka da ƙyar take iya ɗaga hannayen ta, dan tsananin azaba jini nabin ƙafafunta dan tsabar rashin imani haka ya fito daga wanka yana rera waƙa sabida yana kallonta a lataka marar galihu ya yiwa banxa.
Da sanyin jiki ta zira kayanta sedai ta kasa tashi se kuka wanda babu hawaye ahaka samir ya tsallake ta babu ko waige ummul ta wanzu a ɗakin har zuwa duhun almuru babu wani ma ceci se Allah da kuka ta yunƙura takai bakin ƙofa a daddafe ta fita harabar gidan tana wa gidan kallon tsana tare da Allah wadai da tarbiyar iyayen gidan waɗanda basa bincikar mai ƴaƴansu suke ciki.
Tana gab da fita daga gate ɗin ta hango hassana tare da sadiya agigice suke tafiya kamar a tashin hankali suke.
Dakatawa tai har suka ƙaraso wajanta lokacin tsananin zugin ƙasanta ya hanata tafiya.
Da sauri bamu take bin ummul da kallo tana cewa.
"Lafiya kike kuka ummi? tun ɗazu hankalina ya gaza kwanciya?
Sedai duba data kai ga ƙasan ɗiyar tata yasa ta zabura ta daka tsalle tayo kanta cikin ruɗu take furta.
"Ya Allah ka farkar dani daga wannan mummunan mafarki ummi waye yayi miki haka ko jinin al'adarki ne yazo?"
Sedai yadda ummul ke kuka yasa Hassana itama tasaka kuka tana jijjigata tana tambayarta.
Cikin ruɗu tsoro zulumi ummul ke wassafawa uwarta komai na abin da ya faru tana kuka! kamar zata shiɗe
Zubewa Hassana tayi a ƙasan wajan tana wani kuka mai tsuma zuciya sadiya kuwa tama kasa kataɓus
A haukace hassana ta fisgo ummi suka nufi cikin gidan hankali kwance suka tarar da samir da mahaifan sa suna shan ice cream a falo.
"Ke ummi ina kika tafi kin san sarai yarana basa jure yunwa ni akan hakan zan iya sallamarku akawon wasu"
Cewar hajiya timo tana faɗi a zafafe
"Dakata hajiya kafin nan seki fara tambayar wannan sakaran ɗan naki marar imani awar sa nawa akan ƴata yana hakke mata? bayan tsananin wuyar data ci ajiya tana haɗa musu abincin dawowa daga turai?"
Bamu tafaɗa tana kuka kafin ta ƙara cewa.
"Ki tambaye shi gashinan yayi wa ƴata fyaɗe bata jiba bata gani ba sabida yana taƙama da suna da kuɗi?.mu kuma kuna da Allah dan haka wallahi bazan yarda ba se inda ƙarfina ya ƙare"
Tafaɗa tana kuka!
"Dama momy na ce miki yaya iskanci....."
Bata bari mima takai ba ta daka mata tsawa tare da kallon hassana tace.
"To yaro yaga kayan marmari yana son taɓawa ai dole ya taɓa koya ji daɗi dan haka duk inda zaki kai ki kai ai mune hukuma ubansa yana da kuɗin daze iya da wanda ya fiku ma ba kuba"
Lokacin yayi dai dai da fitowar mai gidan shikam dariya ma ya saka tare da watsowa bamu damin ƴan dubu tare da cewa.
"Akaita asibiti inma da ciki a kawo mana ita mu rena muna buƙata nikam talaka kamar ledar pure water yake awajena my son in baka koshiba kamata ku ƙara"
Wannan karon a zuciye sadiya tace
"Tirr da halin akuyoyin mahaifa kamarku,kuma da sannu se kun girbi abin da kuka shuka kaikuma kaje in sha Allahu Allah baze barka ba ɗan bunsuru kawai dan kun dauki talaka ba abakin komai ba yasa kuke furta haka mukam.bamu da karfi sena Allah kuma ze mana sakayya domin baya bacci"
Sadiya tana kaiwa haka taja hannun Bamu da ummul suka bar gidan
Da taimakon sadiya dana bamu aka kai ummi gida.
A sace suka shigar da ita gidan bamu na kuka ta ɗora mata ruwan wanka sedai lokacin da zata kirata dan ta shiga bayi ta gyara jikinta kafin su san matakin ɗauka malam habu ya fada dakin don kiran sadiya kallo guda yayiwa ƙafafun ummi ya saki labulan ya tsaya a tsakar gida yana faɗin
"Ni za'a kawowa bariki acikin gidana basira zainab sakina da suke manya basu ɗauko min abin kunya ba seke ummi maxa kika fara bi aka lalataki haka?"
Gaban bamu ne ya faɗi da sauri tace.
"Malam ɗan gidan dana ke aikine ya haike mata daman wanka zatai muzo musan matakin ɗauka"
Tafaɗa duk jikinta na rawa.
"Allahu akbar inji mai kiran sallah?.da wa za,a ɗauki matakin bayan nace miki daman na bar miki su uban wa yasa ki kaita can gidan aikin har su far mata to wallahi ba'a gidana ba jiya jiya nagama tsinewa ƴar gidan hamisu dana ganta a motar.wani sannan kuma yau aga ƴata ta kawon abin kunya gidana ke ummi zoki wuce kibar mini gidana wallahi bazan rike kiba ban dau wannan kaddarar ba"
Yafaɗa da ɗaga murya.wanda hakan yasa hadiza faɗuwa daga kujera dan tsabar dariya.
"wallahi malam bazata bar gidan nan ba kai wani irin uba ne in ta bar nan ina zata?"
cewar bamu tana kuka!
"Ta shiga bariki dama dasu tai kala dama yarinya marar kunya marar ganin ƙimata ke kaɗai ta sani wallahi bazata kwanar min agida ba in kuma kika bita dai dai da soro ban yafe miki ba akuma bakin auren ki"
Yafaɗa a gadarance.
Lokacin ummul ta fito tana kuka tana cije bakinta.
"Ko a tarihi ban taɓa ganin uba kamar kaba baba zan mar maka gidan ka amman burinka baze cika ba domin bazanje bariki ba zan fita da ƙafar dama da addu'ar uwa zanje domin ɗaukar fansa! Bamu karki biyoni akan rayuwata kaɗai bazanso kibar gidan nan ba sabida tarbiyar ƙannena amman komin daran daɗewa zan dawo gareki da alkairi mai yawa"
Tana faɗin haka tabar gidan tana kuka!
Ranar acikin ɗakin su ummi babu wanda ya rintsa kuma a washe gari magana ta cika unguwa ummi tai ciki tabar gida kuji sharri! kuma ba kowa ya fitar da maganar ba se hadiza dan takaici malam habu kasa fita waje yayi hajja kuwa kuka ta saka sosai tare da faɗan mai yasa ummi bataje gidanta ba ita da zata riketa.
Wannan shine dalilin barin ummi gida wadda kaddarar fyaɗe da rashin ɗaukar ƙaddarar mahaifinta tasa tabar gaban mahaifanta
Koda takai titi ciwon zazzaɓi ya rufeta lokacin wata matashiyar budurwa tazo wucewa a mota ita da wani saurayi ganin ummul a titi a yashe kamar tana numfashi da kyar yasa ta umarci namijin daya tsaya da sauri ta fito tazo ta taimakawa ummi ta shigar da ita mota hotoro suka isa da taimakon namijin da macen ummi ta fito a motar gidane kamar na karuwai suka shiga koda suka kai ɗakin ummi ta sume agigice wannan budurwa ta dubi namijin.
"BB kamar fyaɗe aka ma wannan yarinyar fa to yaya zamuyi kasan asibiti basa amsar waɗanda aka ma fyaɗe fa seda shedar ƴan sanda"
Murmushi saurayin yayi tare da cewa.
"Akwai abokina ɗan sanda zan sanar masa komai inya so se muji yaya zata kasance"
Murmushi ta saki tare da cewa.
"Nidai bb bar wannan kawai yadda zamuyi mu kaita asibiti a matsayin kaine mijinta daran farkon kune kayi ganganci kaga a haka ma xan iya gyara ta sedai nafi son mu sami shaidar asibiti na gangancin da aka mata sabida gaba koda buƙatar hakan ze taso dan dai wannan yayi kama da fyaɗe to kaga kuma idan police muka kai wallahi se an ɗan samu jan lokaci"
Tafaɗa tana ɗan jimanta abin.
"No ke nama manta ashe fa su police ɗinne basa amsar case ɗin fyaɗe har se sun tabbatar da shaidar likita na cewar fyaɗe akai dan haka mukaita na ƙwarai clinic muyi.musu bayani na gaskiya akan fyaɗe akai mata muka tsince Ta inyaso in suka bamu shedar koda gaba xata buƙaci shedar kinga tana da ita a hannunta"
Da wannan suka ɗauki ummi a mota suka kaita asibitin sukaiwa likitan bayani yadda ze gamsu nurse aka kira aka shigar da ita ɗakin duba marasa lafiya taimakon gaggawa aka bata har da ɗinki sannan aka mata allurai.
Se wajan washe gari ummul ta farka da kuka tana kiran bamu, wannan saurayin da wannan budurwar suke bata haƙuri sannan budurwar mai suna amira ita ta haɗa mata ruwa ta shiga wanka wannan saurayin ya kawo mata kayan sakawa ta sanya se da taɗan ci abinci dr ya shigo ƴan tambayoyi yayi mata tana basa amsa tana kuka.
"Ko kina son kai ƙara kotu in yaso ni zan tsaya miki?"
Cewar dr ɗin
Girgiza kai tayi tare da share hawayenta ta amshi takardar wadda itace evidance ɗinta na fyaɗen da samir yayi mata ta adana ta wajan yamma aka sallamesu bayan likita ya bata magunguna.
Tun daga nan rayuwar ummul.ta koma gidan ameerah wadda take zaune agidan karuwai, tsayin shekara biyu BB wannan saurayin na nacin son ummi yana kashe mata mugayen kudi amman ita baya gabanta kuma tunda ta tafi, sau ɗaya ta taɓa zuwa gidan hajja ta kawowa bamu kudi bata ma bar kowa ya ganta ba ta koma, akwai ranar data raka ameera wani hotel royal star zasu fito sukai karo da sameer sedai shi bai gane taba ita kuma ta gane shi tun daga nan take yawan ziyartar hotel ɗin harma ta kama ɗaki ta zauna don ganin gilmawar sameer dan ta shirya mai wani makirci na mata shiyasa take sanya kananun kaya sosai take komawa kamar karuwa inzata zo sedai har lokacin Allah bai haɗa suba maza ko ta ina na son ummi amman ita tai alkawarin bazatai zina ba sedai ba lallai wasu su gane hakan ba kasancewarta tana zaune a gidan karuwai.
Ko ranar dat hadu ma da Aliyu taje farautar Samir ne tana waige ta bige Aliyu batare data sani ba.
Wannan ne yasa taji ta kamu da son Aliyu zazzaɓin damuwar son shi yasa tacewa ameerah ta kawota gidan hajja tai kwana biyu inta warware ta dawo to ashe hajja kakar Aliyu ce ko yaya zata kasan ce agaba?
Wannan shine tarihin ummul.khairi.
*WANENE ALIYU* ?
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400
*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*
Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....
Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki
Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje
Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....
Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne
Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588
*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*
26
Alhaji Ali Dikko..............
Haifaffen Jahar katsina ɗane a wajan malam muhammad Asalin dikkon da yake amfani da ita laƙanine na jaharsa.
Alhaji Ali shine ɗa na huɗu kuma ƙarami a wajan mahaifin shi malam muhammad da mahaifiyar shi saratu akwai Yayyinsa, Abubakar se usman se umar se shi Ali.
Allah bai sa saratu mahaifiyar su ta taɓa haihuwar mace ba sun taso cikin rufin asirin Allah amman dai baza'ace musu masu kuɗi ba sedai agidan malam muhammad akwai cida sha da suttura.
Sunyi karatun Arabic dana boko sedai na boko bamai zurfiba ne iyakacin su abubakar diploma se suka, koma kasuwa wajan mahaifin su wanda yake kasuwar dabbobi yana saida wa.
Shikuma Ali ya sami damar haɗa digree ɗinsa, sedai halin da rayuwar tamu ke ciki da kuma yadda ƙasar tamu ta zama na se kana da wane kasan wane zaka sami aiki yasa Ali Ya Faɗa harkar gine gine shi bai je kasuwa ba kwangila yake amsa ta gini idan ya kammala sedai ya baka makullin gidan ka, Da wannan sana'a ya samu ɗaukaka sosai sunan shi yakai inda bai tunani ba yana karɓar ginin shaguna tafi tafi har makarantu duk yana ginawa wanda ya sami hanyar amsar ginin makarantun gwamnati daga wajan wani abokinsa daga haka arziki da sauyin rayuwa ya fara zuwar musu
Lokaci Ɗaya Abubakar da usman da umar sukai aure kuma a shekarar da sukai aure Allah yayiwa mahaifin su rasuwa.
Sosai ahalin suka shiga halin jimamin rashin.
Komai yana tafiya yadda ya kamata dan su kansu su Abubakar suna samu sosai da harkokin su haka zalika shima Ali yana samu atashi sana'ar lokacin dayakai minzalin aure mahaifiyar shi ta takura akan seya fidda matar aure koda a dangin sune sedai kawai yayi murmushi batare daya bawa maganar mahimmanci ba, Ahaka Allah ya cillashi kano yin wani ginin kamfani wanda ya sami kwangilar shi anan Allah ya haɗashi da Hafsatu ɗiyar hajja yabawa da halinta na kirki da nutsuwa da tarbiya yasa yay sha'awar auren ta hafsatu ita kaɗai ce wajan mahaifiyarta da mahaifinta wanda tun tana karama ma mahaifin nata ya rasu,Ali bai bar kano ba seda yaje wajan kanin mahaifin hafsatu lokacin yana raye yayi tambaya akan yana son auren ta babu wata matsala kanin mahaifin hafsatu ya aminta da Ali wanda shikuma bayan ya gama aikin daya kawoshi ya koma katsina anan yake shaidawa mahaifiyar shi ya sami macen aure babu jimawa su Abubakar sukaje kano nemawa ƙaninsu auren hafsatu wanda ba'a wani saka lokaci mai tsahoba akasha biki hafsat ta tare gidan mijinta anan kusa da yayinsa inda mahaifinsu ya saya musu ƙaton fili yace kowa inze aure ya yanka ya gina domin baya son su rabu da junansu.
Zaman hafsatu da matan yayin ta se son barka domin kansu ya haɗu babu gulma bar munafurci sannan yaransu na xuwa gidan hafsatu su wuni dayake ko wanne ya haifi ɗa ɗaya a lokacin kuma maza ne .
Rayuwar zuri'ar gwanin shawa'a sabida haɗin kai gakuma ilimi da iyayensu suka tsaya musu akai.
Sannu Ahankali Ali ya soma fita aiki abuja na wasu gidaje da gwamnatin taraiya take ginawa na ma'aikata duba ƙwazo da nagartar aikinsa yasa gwamnatin dake ci a wannan lokacin take yawan bashi gayyatar gine gine ahankali Alhaji Ali dikko ya tattara ya koma abuja da zama shida hafsa mai tsohon ciki a gidan haya ya soma zama kafin komai ya dai daita masa.
Ba jimawa hafsatu ta haihu inda ta sami ƴa mace aka sanya mata sunan hajja hauwa'u ( jidda) farin ciki a wannan family kamar me wanda jidda nada kwanaki 40 hafsat tazo ganin ƴan uwa Allah yayiwa maman Ali rasuwa mutuwar data girgiza wannan Alhali.
Sannu Ahankali Ali ya fara rushe gidajen yayinsa ya haɗe dana mahaifiyarsa dana sa ya soma gina musu ƙaton gida mai sassa da dama domin iyalansu daga can abujan ma harya buɗe office ya zuba ma'aikata sabida masu zuwa neman yayi musu aiki sannan a hankali ya fara ginin gidansa anan wata anguwa mai suna gwarinfa.
Gida mai kyau ya gina wadatacce, Daga ɓangaren nasu ma ya gina musu katon