Showing 18001 words to 21000 words out of 83661 words

Chapter 7 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11352

uwarsu"
Hajja ta ƙare tana dariya.
"Hajja wallahi ban san mai yasa na damu da yaya Aliyu ba tun ma kafin nasan jikan kine naji ina son shi dan Allah hajja ki roƙe shi ya soni"
Tafaɗa tana dunƙule wa waje ɗaya.
Murmushin dake saman fuskar hajja bai gushe ba ta furta.
"Kema kinsan baffa baze ce yana son ki tafarar ɗaya ba sedai muyi masa shigar sauri"
A razane ta ɗago tana kallon hajja dake jefa goro cikin bakinta.
Murya can ƙasa cike da ruɗani ta furta.
"Daman nima nayi wauta nasan ba kowani namijine ze dubi girman ƙaddara ta ya aure ni ba, Dan Allah hajja gaya min hanyar da zanbi domin na kankare faitin dake bibiyata kodan Aliyu ya zama mallakina?"
Tafaɗa tana kuka!
Jan yota jikinta hajja tayi tana shafa gadon bayanta.
"Ummi ba ina jifanki da baƙar magana bane ko ɗaya ni sema daɗin dana ji da kika ce kina son jinina kuma koda kowa ya gujeki wallahi ni bazan gujeki ba! idan har hafsatu ɗiyata ce ta halak! Aliyu ɗanta ne na halak to baya da mata seke ummi wannan karon zanyi masa shigar sauri sedai ko kaɗan bana tunanin Aliyu ze soki sedai yayi maki son tausayi sabida matar shi shu'umar mace ce, sedai kuma ko wace mace akwai tata kalar kirsar ban san taki baiwar ba wataƙil da ita ki janyo shi jikinki"
Hajjah takai maganar tana kokarin miƙewa.
"Hajja na haƙura dashi, Ina tsoron kishiya domin naga zahiri akan Bamu dan Allah hajja karma ki gaya ma Ammi tai masa dole akan ya aure ni bana son yadda mukai zaman boranci agidanmu agidan miji ma na mai maita"
Tafaɗa tana sakin kuka tare da cusa kanta tsakanin kafaɗun hajjah.
"Aifa tunda kika furta kina son jikana sefa kin aure shi rufe bakin ki babu maiji bare ya gani zamuyi abun mu cikin sauƙi"
Hajja takai tana dariya.
Turo baki tayi tare da sakin hajja ta koma gado ta kwanta.
Hajja ce ta fice a ɗakin tana furta.
"Munafuka kyayi kya gama"
Dariya ummul ta sanya tana rufe idanunta bata taɓa zaton komai zezo mata cikin sauƙi ba, Tabbas hajjah mai son ta ce.
Shiko Aliyu koda ze yanka ta gunduwa gunduwa tana son shi zata zauna a haka.
Da wannan tunani bacci mai daɗi ya kwasheta wanda ta jima bata sami irin shiba.
Koda asubahi ma da ƙyar Hajja ta tayar da ita sabida nannauyan baccin daya ci ƙarfinta.
Acikin sujjadar sallarta sosai ta dage tana jaddada neman zaɓin Allah a tsakaninta ita da Aliyu.
Sabida acikin kwana biyun data san shi taji kaf duniya acikin maza masoyan ta bata da gwani azuciyarta kamarshi.
Anan zaune tayi azkar ta miƙe tahau gyarawa hajja ɗakin seda ta kammala sannan ta wuce kicin.
Da kanta take sarrafa abin break fast wanda ta kammala komai tsaf ta jere a center table bayan ta baɗe ɗakin da haɗaɗɗan turaren wuta mai azabar ƙamshi.

Bata da kaya agidan hajja ko ɗaya sabida haka datai wanka seta aika gidansu wajan sadiya ƙanwarta mai bi mata ta amso doguwar rigar atamfa wadda ta matse ta gam

Ta gama komai taci kwalliyar jiran shi tana ta turo baki hajja ta shigo da kallo ta bita aranta tana ayyana lallai iska na wahalar da mai kayan kara.
"Hajja ki kira wayan shi mana harfa 10 ta kusa najishi shuru"
Ta faɗa babu kunya.
Tafa hannu hajja ta hau yi tana.
Cewa.
"Yau naga abin da yafi ƙarfina ni binta wai ummi bazaki hankali ba nikam zan wa hansatu waya akan dole ma a tursasa ɗannan ya aureki karki mace mana"
Shura ƙafafu take tana dariya.
"Amman hajja kika cewa ammi ina son shi zataji wani iri fa"
Tafaɗa tana ƙifta idanu.
"Dama kawai zan nemi auren ne a matsayina na wadda ta isa dashi ummi ina son ki auri baffa kodan ki kawo ƙarshen gwamnatin matar shi marar mutunci na tabbata mahaifiyar shi taji wannan batu zatai matiƙar murnar data xarta tawa,sanan kuma auren baffa ba abu ne mai sauƙi ba dama dole sedai ta silar haɗi amman in dan kanshi ne baze taɓa furta yana son ƙarin aure ba, sabida soyayyar daya ke yiwa matar shi"
Hajja ta faɗa tare da miƙowa ummul wayarta.
Amsa tayi hannu na karkarwa ta nemo numbern sa da aka rubuta.
ALIKO............

Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


Wanne shagon kayan kwalliya ko kayan Gyeran jiki zakaje kayi sayayyar aqalla Naira 32k sannan su baka kyeutar kayan 19k akan 1500?ko da kuwa sayayyarka ta Farko dasu kenan?

ORIFLEM sun bani garabasar kayan kimanin 19k💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Maza kiyi sayayyarki Dan kema ki Samu taki garabasar!wannan Garabasar zata qare a 5 ga watan nan.

Bata Qare anan ba,Kamfani yace daga nan zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne,bazaki biya kudin Register 4490 ba.yar uwa me kike jira????
Maza ki garzayo domin Amfana da wannan Kamfanin Mai Albarka.
Ku Tuntubeni A wannan lambar domin yin Register ko sayan Kaya
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
08064400588



*BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }

NA
*AUTAR MANYA*


GARKUWA WRITTER'S ASS....

*15*


Ta shiga kira wadda seda ta kusan katsewa kafin Aliyu dake kwance saman sallayar dayayi sallar asubah ya ɗauka.
Muryar shi can ƙasa yayi sallama da sauri ummul ta ɗauke wayar daga saman kunnenta sabida yadda taji hucin numfashin sa ya daki zuciyarta.
"Kiyi magana mana ummi karfa kuɗina su ƙare cewar hajja"
Lumshe idanu tayi tare da mayar da wayar saman kunnenta muryar ta na rawa ta furta.
"Amin wa'alaikas salam ina kwana?"
Daga ɓarin Aliyu wanda ke kwance tun da yayi sallar asubahi sabida zafin murar data kamashi ya lumshe manyan idanunshi dasuka ƙan ƙance sabida azabar sarawar kai dake damunshi ya furta.
"Lafiya"
Shuru ya biyo baya.
"Shike nan?"
Taji saukar muryar shi cikin kunnenta.
Ƙifta idanuwa ta shiga yi kafin tace.
"Dama break fast hajja ta haɗa maka kuma tajika shuru koka wuce ne garin ku?"
Tafaɗa a rarrabe tana wasa da yatsan hannunta guda.
Murmushi ya sauke kaɗan yana auna rainin hankalinta wai hajja amman seya basar tare da cewa.
"Ban riga da na tafi ba sabida na kwana da zazzaɓi amman haka nan zan wuce"
Zaro idanu tayi waje tana ji kamar tai tsun tsuwa gare shi cike da ruɗani ta furta.
"Dama ai seda aka ce maka karka fita a ruwan nan shine ka fita ai gaya nan ka kwana da mashash shara"
Lumshe idanu yayi yana sauraran sassanyar muryarta tana magana kamar da sa'anta.
Muryarta ce ta kuma karaɗe mai dodon kunnen shi inda ta kuma cewa.
"Ga hajja zata maka sannu"
Bata jira ba ta miƙawa hajja wadda ta daskare a tsaye tana kallon rashin kunyar ƴaƴan wannan zamani.
Ta amshi wayar tana furta.


"Aliko kai nakeji kana baka da lafiya?"
Daga kwancen daya ke yayi ɗan murmushi a karo na barkatai tare da cewa.
"I Hajjah kinga ruwan jiya fa yayi mani mugun duka!"
Yafaɗa yana dafe saman kanshi.
Daga ɓangaren hajja tace.
"Ai daman kafar kanka Aliko seda nace akwai ɗaki anan ka kwana kaƙi yan zu dai ka zo kaci abinci anan kasha magani"
Murmushi ya sauke mai sauti tare da cewa.
"To hajja zan lallaɓo na zo amman kisa ma min shayin citta"
Yafaɗa tare da katse wayar.
Hajja mita tahau yi na daman tasan tun yana ƙarami baya son ruwa shine ya shiga ga ciwon shi mai naci.
Ita dai ummul da ido take bin hajja tana auna yadda hajja ke tsananin son jikan nata sabida yadda taga duk hankalinta ya tashi.

Da ƙyar yana rangaji ya ƙarasa wajan trolly bag ɗinsa ya fiddo da wasu haɗaɗɗun ƙananun kaya rigar fara ce ƙal mai gajeran hannu se baƙin wando ya sanya su ajikinsa waɗanda sukai mai tsananin kyau suka amshi kalar fatar shi mai tsananin sulɓi da kyawun gani.
Ya ƙarasa gaban mirrow ya fesa turare key ya ɗauka da phone ɗinshi ya kulle ɗakin ya fita.
Kiciɓis sukai da Nas wanda yaketa sauri shima daga gani fita zeyi sukai musabaha suka jera atare suna ɗan tattaunawa har zuwa gaban motocinsu kowa ya shiga cikin tasa suka kama hanyar gate.
Tuƙi yake da ƙyar da kuma taurin zuciya wayar shi ta ɗauki ringing ganin numbern Abbah yasan ya yaɗan rage gudun tare da katsewa ya kirawo shi.
Gaisawa sukai Abba yayi kamar bai san Aliyu yayi tafiya ba, shima sabida tsabar kunya bai iya cewa abban yana kano ba haka sukai sallama A ɓangaren abba yana wa yaron nashi addu'a akan Allah ya sauya mai lamarin shi da alkairi.

Zurfafa yayi da tunani bayan sun gama waya da abbah na yadda a yanzu sam baya kula da mahaifan shi duk da Abba nada kuɗin daya fi nashi amman ai suna da hakki akanshi sau tari koda ya fito daga office idan yayi niyyar shiga gidan Ammi su gaisa seyaji ya shafa'a seyayi gida suna gari guda seyayi wata baije yagan su ba.
Tsananin damuwar daya shiga ta ƙauracewa mahaifanshi daya ke a kwanakin nan se hakan ya ƙara mai ciwon kai wanda kafin yakai gidan hajja ko gani ma da ƙyar yake yi Allah ne kawai ya ƙaddara ze isa gidan hajja lafiya.
A galabaice yayi parking yana dafe kai ya isa bakin gate ya buga salame dake wanke-wanke a tsakar gidan ta wanke hannunta da ruwa ta isa ta buɗe masa tana ganin shi ta russuna tana gaishe dashi wanda da hannu ya amsa mata tare da raɓeta ya wuce ciki.

Ƙasa-ƙasa yayi sallama acikin falon yana mai zubewa saman three seater ya miƙe ƙafafunshi akai hannu ɗaya dafe da kanshi.
Da sauri ummul dake zaune tai tagumi ta ɗago tana amsa sallamar shi wadda seda tai ta maza kafin ta fahimci abin da ya furta.
Ganin shi a kwance ya sanya gabanta faɗuwa da sauri ta ƙarasa bedroom tana kiran hajja sedai kash ta mance fa ashe bayan hajja ta gama mitar ta fita ta siyo mai magani wanda ta bar mata sallahun idan yazo ta sauke shayin data ɗora mai a kicin ta zuba a cup ta kai masa.
Hakan yasa ta juya kicin ta haɗo mai abincin data ɗauke ɗazu takai kicin ta aje sabida rashin zuwan da bai akan lokaci ba, A tire ta haɗo komai ta zo gabanshi ta aje a nutse.
Ido ta zuba mai tana kallon saman fuskarshi wadda idanunsa suke lumshe harya faɗa ma sabida yadda baya jin daɗi.
Kamar zatayi mai kuka ta furta.
"Sannu ka sauko kasha tea ɗin na sirka maka dan karka ƙone da zafi"
Idan ya tanka mata to kujerar daya ke kai ta tanka.
Sake matsowa tayi dai dai saitin kanshi.
Tsintar kanta tayi da ɗauke hannunshi daya ɗora saman kanshi ta mayar da gurbi da nata hannun.
Da sauri ta janye tana ɗan zare idanunta waje.
"Wai zafi kamar wuta sannu"
Ta faɗa nan ma bai magana ba.
Ta shi tayi har tana harɗewa abin tausayi( kai soyayyar bala'i ce )
Ta nufi toilet ɗin hajja ruwa mai sanyi ta taro a bawo ta saka tawul ƙarami ta fito.
A gaban shi ta aje jikinta se rawa yake ta sanya hannu cikin ruwan ta matse tawul ɗin taɗan matsa kaɗan ta yadda bazasu haɗe ba ta ɗora mai tawul ɗin akan shi tana goga mai.
Bakinta yaƙi mutuwa har lokacin sannu take faman zuba mai kamar zata ari baki.
Seda ta taɓa kan taji babu zafin sannan takai bawon ta dawo ta zauna gabanshi tayi tagumi.
A haka salame ta dinga shigewa tana jera kwanuka a kicin harta gama aikinta tai mata sallama ta wuce.
Seda hajja tai wajan mintuna ashirin kafin ta dawo gidan tana ta masifar wai mai chamist ɗin ya riƙe mata canji boska ta siyo mai maganin ciwon kai.
Ta zube a ƙasan carfet tare da zame gyalen ta tana cewa.
"Ummi ɗauko ruwa a firji yasha maganin"
Kamar wadda ƙwai ya fashewa ta miƙe ta ɗauko ruwa marar sanyi tazo ta miƙawa hajja tare da cewa.
"Hajja ai bai ci komai ba"
Salati hajja ta hau yi.
"Haba Aliko kai daman a zahiri ma baka fiye son kaci abinci ba bare kana ciwo tashi zakai kaci abinci ga maganin nan na siyo maka kasha dan Allah karka je gida da sauran lalura"
Tausayi tsohuwar ta bashi na yadda duk ta damu.
Sannu ahankali ya yunƙura yana cije bakin shi ya zauna sosai idanun shi ƙurr akan ummul............

Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



Wanne shagon kayan kwalliya ko kayan Gyeran jiki zakaje kayi sayayyar aqalla Naira 32k sannan su baka kyeutar kayan 19k akan 1500?ko da kuwa sayayyarka ta Farko dasu kenan?

ORIFLEM sun bani garabasar kayan kimanin 19k💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Maza kiyi sayayyarki Dan kema ki Samu taki garabasar!wannan Garabasar zata qare a 5 ga watan nan.

Bata Qare anan ba,Kamfani yace daga nan zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne,bazaki biya kudin Register 4490 ba.yar uwa me kike jira????
Maza ki garzayo domin Amfana da wannan Kamfanin Mai Albarka.
Ku Tuntubeni A wannan lambar domin yin Register ko sayan Kaya
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
08064400588


*BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }

NA
*AUTAR MANYA*


*16*


Lumshe idanun nashi yayi tare da ɗaukesu daga kallonta tsananin tausayin yarinyar yana ratsa dukkan sassan jikinshi.
Tabbas inda yana da hali daya taimaki zuciyarta ya sadata da abin da take muradi.
A hankali ya sauko zuwa ƙasan karfet.
Da sauri ita kuma ummul ta matsa can nesa dashi janyo try ɗin abincin tayi tare da ɗaukar plate ta zuzzuba masa wainar ƙwai da soyayyan dankali se miyar hanta da albasa wadda take ta tashin ƙamshi se kunun gyaɗa daya sha madara.
Ta zuba mai wadatattu ta tura mai gabanshi.
Cikin nutsuwa ta miƙe tare da nufar ɗakin hajja dan ta basu waje.
Seda yaga ta ƙulewa ganinshi sannan ya ɗauke kanshi daga hanyar data wuce ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya da sauri ya janyo plate ɗin ya ɗora spoon ya soma kai lomar abincin bakinshi wani irin daɗi ya mamaye bakinshi.
Murmushi hajja tayi tare da cewa.
"Aliko tun da ummi ta tashi kake bin ta da kallo kodai ƴar gida zakuyi?"
Bai daina cin abincin nashi ba kuma bai bata amsa ba har seda yaci mai ɗan dama sannan ya ture abincin daga gabanshi ya ɗauki ruwa yasha kaɗan.
Sannan yayi hamdala ga sarki Allah.
A nutse ya dubi hajja yace.
"Hajja wani irin magana kike haka? kinsan a wani hali na fara ganinta? hajja ko kaɗan bana son ta, Ban taɓa jin sonta araina ba Hajja BA SON TA NAKE BA TAUSAYI NE! kaɗai narke acikin zuciyata tare da tarin ruɗu kala-kala tabbas ganin yarinyar nan agidan nan ya sakani a shakku na yadda a farko na ganta a hotel sannan na dawo na ganta agidan nan duk da na shaida ƴar can gidan ce to amman mai ya kaita hotel? dik da ni lamarin wani bai shafeni ba dan bana ɗora idanuna akan abin da bai shafeni ba amman wannan ya tsaya min araina"

Ya faɗa yana mayar da numfashi sama sama alamun baya jin daɗi ajikinshi.
Ga mamakin shi hajja batai wani acting daze nuna taji mamakin maganar daya faɗa ba na cewar yaga ummul a hotel sema murmushin data cigaba dayi wanda bai gushe gareta ba.
"Aliko banyi mamaki dan kace kaga ummi a hotel ba amman tabbas nina san iskanci baze kai ummi can ba sedai ɗaukar fansa wadda rayuwarta da hakan ta taso! makauniyar ƙaddara mai ɗauke da ƙalubalan rayuwa sune ummul aba'isin ɗin jefa yarinya ƙarama cikin garari dan Allah Aliko idan na baka labarin ummi ka taimaki rayuwarta ka amshi soyayyarta ka aure ta ko hakan zesa wannan tausayin ya juye ya zama so! ada nayi niyyar biyo maka ta bayan gida sena ga kuma cewar gwarama ayi mai yuwuwa"
Hajja ta ƙarashe maganar da ƙarfin gwiwar ta.

Jin kanshi yake kamar ze tarwatse tayaya da idanunsa yaga yarinya acikin hotel sannan har hajja tazo tana bada shaida akan cewa wai ba iskanci taje ba!
Shafa kanshi yayi tare da cewa.
"Hajja hotel matattara ce ta mutane kala kala kowanne kuma akwai abin da ya kaishi cikin sa sedai ita a yadda na ganta a shigar dana ganta a yanayin dana ganta hajja na shiga shakku"
Ya faɗa murya can ƙasa.
Murmushi hajja ta kuma yi kana ta fara magana.
"Aliko ummi ba iskanci taje yi hotel ba ka nutsu ka cire zargi cikin zuciyarka fatana kayi min alƙawari muddin na baka labarin ummi zaka taimake ta?.zaka aure ta?"
Hajja ta faɗa tana share hawayen fuskarta.
Jinjina kai ya shiga yi idanun shi ƙurr a fuskar hajja.
Murmushi ta sauke tare da fara bashi labarin kamar haka.....................................
Tunda ta fara magana yake kallon ta tsigar jikinsa na wata irin tashi gaba ɗaya idanunshi ya kaɗa yayi wani irin jajir jikinsa na wata irin rawa.
Dafe kanshi yayi yana juyawa wani irin rauni ya mamaye ilahirin jikinsa.
Hajja ta ƙare tana sakin kuka!
Da sauri ya matso gaban tsohuwar ya rungumeta shima yana jin inda yana da hali dayayi kukan.
Amman daya ke namijin duniya ne seya dake seda ya tabbatar hajja ta dena kukan sannan ya koma da baya yana fesar da zazzafan numfashi.
"Hajja an kai shekara nawa kuma mai yasa baki shaida min ba?"
Cikin mayar da ajiyar zuciya hajja tace.
"Za'a kai shekaru biyu lokacin kayi aure kasan tun da kai aure shekara biyar baka taɓa zuwa nan ba tayaya zakaji?"
Jinjina kai yayi tare da matse yatsun hannunsa suka ce ƙas! sau uku sannan ya dubi hajja da nutswar sa da kamewarsa yace.
"Karki damu hajja zan taimake ta amman hajja inda kin gayawa su ammi maganar nan da kin ɓata lamarin ai sabida ba kowa ne ze fuskanci abin ba kamar yadda na gaya miki na ganta a hotel inna gayawa su ammi abba baze yadda ba ina son wannan maganar su tsaya a iya mu please har na kammala shirina"
Yayi maganar yana nuna mata iyakacin gaskiyar shi acikin idanunshi.
"To yaya alƙawarin mu?"
Ta tafaɗa tana kallon shi.
"Yana nan hajja zan aure ta kodan na kare martabar ta domin ni har yanzu ina hangen abin da baku hanga ba tayaya shekara har biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login