Showing 36001 words to 39000 words out of 83661 words

Chapter 13 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11365

gida mai uban girma harda B.q domin ƴaƴa yensu sannan akwai ɓangaren maza sannu ahankali rayuwa na tafiya matan su abubakar na haihuwa inda ayanzu ko wannen su yana da ƴaƴa 2 mata da maza lokacin Allah ya kuma bawa hafsat ciki bayan wata tara ta haifi ɗanta ƙato kyakykyawan gaske ranar suna Ali ya mayar da sunan shi Aliyu wanda ake ce masa baffa.
Kusan a tare hafsa suka haihu da matar Kawu usman yayan Abban Aliyu Sedai Matar kawu usman ta bawa hafsa kwana uku kuma ita namiji ta haifa wanda yaci sunan muhammad amman ana ce masa baba karami.
Sannu ahankali rayuwa na tafiya shekaru na tafiya an saka Aliyu da jidda makaranta anan abuja in akai hutu Abba ya turo su katsina har ammi anan ɓangaren su zasuyi hutu su koma Aliyu bai da wani Aboki se Baba Karami, ɗan wajan kawu usman wanda suka taso kusan a tare ragowar kuma sun girmesu shiyasa su biyun suka kulle suka xama kamar uwa ɗaya uba ɗaya.

Seda Aliyu yayi kusan shekaru goma aduniya sannan ammi ta sake haifar wata macen Sarat daga sarat ta haifi shafa daga shafa ta haifi ƴan biyu hassana da hussaina waɗan da daga kansu kuma bata kara haihuwa ba ƴaƴanta shidda namiji ɗaya mata biyar, lokacin rayuwa ta sauya Tuni Alhaji Ali ya zama mai kuɗin gaske yasan manya sosai, Zuri'a kuwa tana ta ƙaruwa, ƴaƴan kawu abubakar 12 ƴaƴan kawu usman 9 ƴaƴan kawu umar 13 ƴaƴan abba ne shidda sune marasa yawa sabida shi ne bai kara aure ba amman su kowanne ya ƙara aure matan su bib biyu.


Wannan tasa wannan zuri'ar take ɗan ƙullah auren zumunci sedai su basu hana AUREN BARE ba in kana da taka a waje ka auro in kuma kana son ta gida ka aura yanzu haka jidda yayar Aliyu tana auren ɗan gidan kawu Abubakar mai suna yaya Hamza haka auratayyar take kulluwa.
Suma sauran yawanci suna auren junansu ne.
Shima baba karami ya sami aikin banki tuni bayan ya gama karatun sa inda ya auri sarat kanwar Aliyu wanda shi har wannan lokutan baida niyyar aure har seda Kawu usman yace ko rokiya za'ayi masa sedai yanayin karatunsa yasa suka hakura domin karatu yake mai matikar wahala na low.
Ya sami karatun addini mai zurfi dana boko Ali yana ɗaya daga cikin mutane masu ƙwaƙwalwa ko laifi kayi daga kwayar idanunka ze fahimta yana da sanyin hali ma'ana hali mai kyau yana da son mahaifan sa tare dayi musu biyayya bai da magana sosai yana da miskilanci yana da yawan ibada sannan yana da son ƙwallon ƙafa.
Ya kammala karatunsa na digree da master tare da phd ɗinsa duk a harkan low inda ya fito a ƙwararren lauya mai zaman kansa barrister Aliyu Ali dikko,ya soma aiki da wani alkali anan cikin garin abuja wanda seda ya sami gogewa ta tsayin shekara sannan ya sami damar buɗe nasa katafaren office ɗin sabida kowa yasan lauya mai zaman kansa bai da haɗi da gwamnati shi aiki yake da ƙashin kansa wanda in kana da wani case zaka iya ɗaukar sa amman case ɗin da bai shafi under criminal case ba domin kowa yasan criminal case yana under lauyoyin gwamnati ne sedai inma lauya mai zaman kansa ze ɗauki ragamar criminal case tofa dole seyaje wajan antomy general na hight coaut yay taking wannan case to kansa sannan ƙarar zata dawo hannunsa su yawanci lauyoyi masu zaman kansu daman sunfi tsayawa masu kuɗi case ko kamfanin nika da sauran su.


Lauyoyin gwamnati kuma suna tsaya wa akan criminal case misali kisan kai.
To duk wanda aka kashewa ɗan uwa toba case ɗin sa bane na gwamnati ne don gwamnati ce zatai taking case ɗin to coart sannan ta ɗauki lauya daga cikin lauyoyinta.
Wannan kenan


Zuri'ar su Aliyu ƴan boko ne domin ko wanne yana da rufin asirin sa sedai babu wanda ya gaji mahaifin shi don duk suna aikin gwamnati ne kama daga nurse's bankers lawyers police t.c.e dan hatta shafa kanwar Ali mai bin sarat likita ce kuma tana aiki anan abuja sedai har wannan lokacin batai aure ba kannen sa kuma ƴan biyu sune ke secondry school ya jidda yayarsa tana aiki anan wata babbar secondry a cirancin katsina tunda anan mijinta yayi mata gida, sarat matar baba karami tana aiki nan ministry of agriculture Dake Local government ɗinsu.

Tuni Abba yakai ƴan uwan sa maka yakai ammi shima kansa Aliyu yaje saudi yafi sau a ƙirga haka nan ammi ta siyawa hajja gida anan tunga ta gine mata shine na kakar su ummul data rasu baban su ummul ya sayar. babu abin da hajja ta nema ta rasa komai ammi na mata ita da jikokinta.

Aliyu ya gamu da basma matar shine a...........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400


*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

27

Office ɗinsa sun je ita da mamanta akan suna buƙatar ya tsaya musu akan ƙarar da zasu shigar ta Ƙanin mahaifin basmah wanda yayi babakere da dukiyar mahaifinta sabida yana gadarar basmah kaɗai ya haifa suma suna da gado to ita maman basmah ba wannan ne ya dameta ba, Yadda ya riƙe dukiyar baki ɗaya yaƙi basu koda ƙwandala na daga cikin gadon shiya fi damun su sabida a lokacin ma bada ban aikin da basmah take na banki ba, Da basu da yadda zasuyi su samu koda abin da zasu cine.
Lokacin da sukaje office ɗinsa babu abin da basmah take se kuka! sabida yadda rayuwar ta isheta komai ya tsaya musu cak kamar ba mahaifinta ne ada mai shagwaɓata da bata kulawa ba yanzu an wayi gari babu shi aduniya hatta gidan da suke ciki ya soma mutuwa sabida rashin wadata.
Sosai Aliyu ya tausaya musu harga Allah ya tsaya musu ne ba domin su biyashi ba domin basu da kuɗin da zasu iya ɗaukar shi a wannan lokacin ataƙaice maman basmah ta yi mai bayani akan tarihin su.

Mu ƴan asalin garin naija ne aiki ya kawo mijina nan abuja muna zaune anan gwarinfa( kusa dasu Aliyu ma kenan)mijina yana sona kamar yadda nake son shi muna zaune lafiya cikin soda kaunar juna sedai Allah baisa na haihu ba hakan tasa ƙanin mijina dake nan kusa damu shima yana aiki a wani kamfani ya takura mini har yake haɗani da sauran ƴan uwan shi akan se lallai Abban basmah ya ƙara aure kwatsam se Allah ya bani ciki na haifi yarinyata gata nan basmah munyi farin ciki matika haka na zage ina bata kulawa har takai mun sakata a makaranta bayan tai candy taje kano gidan kanwata ta shiga university ta nan bayero bayan ta kammala ta dawo gida mahaifinta ya sama mata aiki a bankin dayayi ritaya fara aikinta da wata biyu Allah yayi masa rasuwa muka tarkata naija anan aka masa suttura bayan bakwai muka dawo gida dayake duk kaddarar sa,Baya neman shawarata akai se shawarar ƙaninsa yasa ka ƙanin nashi yaƙi bamu hakkin mu hatta abin da zamuci se basmah tai albashi take siyo mana.
Tafaɗa tana gursheƙen kuka.
Sosai zuciyar Aliyu ta karye ya dinga bata haƙuri tare dayi mata alkawarin zeyi iya yinsa wajan ƙwatar mata hakkinta dana ƴarta.
Yayi ƴan rubuce rubuce ya ce musu suje ze nemi mutumin.
Bayan kwana biyu Aliyu ya kammala shari'ar dake gaban sa yabi adireshin gidan ƙanin mahaifin basmah mamaki sosai Aliyu yayi na yadda yaga mutumin dattijo mai kirki da dattako a kunyace suka gaisa mutumin ya kawo kujera fara ta roba suka gaisa.
Rasa yadda zeyi yayi masa magana yayi sabida kwarjinin da mutumin yayi masa.
A dake ya ɗauko farar takarda tare da Id card na shaidar cikakken lauya mai zaman kansa ya nuna wa kawun basmah tare da cewa.
"Cikin kwana ki biyu da suka wuce matar ɗan uwanka marigayi Alhaji Muktar ta kawo ƙarar ka akan tana son na shigar da ƙarar ka kotu na kacinye musu dukiya ita da ƴarta shin haka ne?"
Aliyu ya faɗa cikin sigar tambaya irin ta lauyoyi.
Murmushi dattijon ya saki babu wata fargaba yace.
"Au ta nan kuma hajiya binta ta ɓullo mini to samari ban hanaka kai ƙarata ba amman bara kaji wata magana hajiya binta matar ɗan uwana ce amman ko a ƙiyama bana fatan Allah ya haɗa mutum da mace irinta mace ce mai muguwar kirsa seda ta rabashi da iyayen sa hatta mahaifiyar mu ranar da zata rasu kuka take tana akira mata muktar amman bai zoba, A takaice binta seda ta sanya muktar ya rubuta sunanta dana ƴarta akan dukkan kaddararsa wallahi dai dai da farcen susa bai bari da sunan mu ƴan uwansa mu gada ba se wannan gidan dana ke ciki wanda shiya bani da kansa amman matar nan kullum idanunta akan gidan nan yake wanda hakan yasa take min barazana akan seta makani hukuma an basu saboda malamai da ƴan tsubbu sun cinye mata dukkan kaddarar data ke da ita a yanzu haka basu da komai se gidan su hajiya binta macen kirsa sunan ta kafi asiri illa data haɗa da asirin kuma tafi bom bala'i"
Dattijon ya faɗa cike da takaici.
"Burinta kullum na tashi daga wannan gida wanda shedu suka shaida muktar ya bani shi duniya da lahira na tashi na bar musu sabida bata ƙaunar kowa a ƴan uwan muntari hatta ƴarta bata nuna mata dangin mahaifinta ba"
Sosai jikin Aliyu yayi sanyi amman bai nuna wa wannan dattijon ba sema basa hannu daya yi sukai musabaha ya tashi ya tafi ko agida tunanin lamarin yake ya kasa tan tance mai gaskiya acikinsu musamman yadda matar take kuka sedai fuskar dattijo mai haiba da kamala batai masa kama.data makaryaci ba.

Bayan kwana biyu suka sake komawa office ɗin Aliyu kamar yadda yace yana buƙatar hakan wannan karon basma tai kwalliya ta baɗa turare mai masifar ƙamshi domin tunda ta koma gida take kuka akan tana son Aliyu bare data ga tsantsar kyawun da Allah ya bashi nan fa hajjiya binta aka nausa kauyen sileja wajan malaminta ta karbowa ƴarta sa'a domin itama tace ta hango hutu alherine ya kaisu office ɗinsa malamin daya bawa hajiya binta tabbacin da zarar Aliyu ya shaki kamshin angama magana wannan yasa hajja binta bawa ƴar turaren takwa makashi gaba ɗaya ya game jikinta.

Zaune suke saman banci wanda masu tsaron office ɗin suka tanadawa masu son ganin Aliyu wajan karfe goma ya ƙaraso da sauri ɗaya daga cikin ma'aikatan ya je da sauri ya amshi jakar hannunsa seda ya kammala shirinsa sannan ya umarci da a shigo dasu ciki.
Yau sabida sauri ko azkar ɗin asubahi baiyi ba wata shari'a ya gabatar har guda biyu da sassafen nan yanzu haka sauri yake yaɗan yi abin da zeyi Yayi break fast ya koma gida to kuma se wannan matar ta shigo office ɗin nasa.
Zaman su keda wuya yaji gaban sa yayi mummunar faɗuwa..............
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400

*Assalamu alaikum warahmatullah*
*Shin ke uwace?ko kuma Dalibace? Shin kin gaji da zama babu abun dake kawo maki kudi?*Ga Dama ta samu
kasancewar kasuwancin ba mai takura bane zaki iya hadashi da aykin gwamnati ko kuma wani kasuwancin👌🏽ga kuma tarin dinbin alkhairai👌🏽 ALHAMDULILLAH*

Wannan company sunanshi Oriflame, suna producing kayan gyaran jiki, turaruka, kwalliya, kula da gashi, kafafu, Supplement da sauransu....

Da Jarin 15k kacal Zaki iya fara Kasuwancinki

Ababen da zaki mora bayan kinyi register...
✔️Ribar 30% na duk abunda kika saida...
✔️Albashi karshen kowane wata (gwargwadon aykinki)
✔️ Kyautuka masu qayatarwa kowane wata(irin su designer wristwatch,bags, perfumes etc)
✔️ Kyautar kudi ta musamman (daga matsayin director zuwa sama)
✔️ Kyautar tikitin zagayawa a gida da waje

Kai da dai sauransu...Kiyi nazari akai, amma ina tabbatar miki akwai alfanu 'yar uwa....

Wani qarin Abun farinciki daga yau zuwa 10 ga watan nan Register kyeuta ne

Idan kinyi ra'ayi, yimun magana ta 08064400588


*KARKU FITAR DAN ALLAH NA KUƊI NE*

28


A kasalance yake amsa gaisuwar hajiya binta wadda tsabar kirsa taƙi bari shiya gaisheta a matsayin ta na babba harda russunawa tana sunkuyar da kai ƙasa.
Murya can ƙasa yake mata bayani kamar haka.
"Mama kuyi haƙuri da wannan dattijon ni na ɗauki nauyin baku adadin kuɗin da gidan zeyi"
Yafaɗa idanu lumshe.
Saukar kukan ta ƙasa ƙasa ke tashi tana furta.
"Shike nan kaima ya gama, Gaya maka aibuna wallahi makiri ne komi ya gaya maka ƙarya yake"
Girgiza kai yake yafara jin sarawar kai baya son kukan mace bare babba wadda zata kai ammin shi, shiya ma kasa gane mai gaskiya a tsakanin su dan haka ya ɗaga mata hannu alamar tayi shuru.
"Mama kuyi haƙuri Don Allah nidai zan baki kuɗin gida ki duba zumuncin Allah kuyi sasanci anan base ankai taiyara ba"
A wannan karon idanu ya zubawa basma wadda ta sunkuyar da kai kasa tana wasa da yatsun hannunta fuskar nan kamar tumatur amman hannayen ta baƙaƙe ƙirin alamun anci bilitin an more kenan.

Kuka hajiya binta take kamar zata shiɗe wanda tsabar makirci ne wanda sam kukan shiya danne murnar samun kudinta sabida idan tai saurin waskewa ze nuna cewar kamar tana murna da kuɗin dayace zaya bata ne kaga maganar kawun basmah zatai wa barrister tasiri amman daya ke makira ce setai kamar bata bukatar kuɗin ta cigaba da kukan ta.

Numfashi take ja da ƙarfi wanda basmah tai saurin riƙota tana cewa.
"Na shiga uku mama karfa ki bari ciwon ki ya tashi kar kema ki mutu kibi abba nifa kin fi min komai aduniya tafaɗa tana kuka!
Tausayi suka bashi dan haka seya ce suzo ya sauke su a gida shima gidansu ze wuce ƙiftawa basmah ido hajiya binta tayi wadda nan da nan ta soma zuwa mai godiyar daya ji ya shiga wani yanayi.

A hankali suka shiga motar shi lafiyayya wadda kallonta kaɗai ya kuma jefa hajiya binta da basmah halin ɗaukin ganin cimma muradin ransu.
Tafiya suke a hankali basmah na bashi kwatancen gidan su ai seya ga ma basu da wani nisa ashe tsiransu layi ka biyar da gidan su da gidan daya ke ginawa kuma layi huɗu bin kofar gidan yayi da kallo yana mamakin yadda baiga wata alama ta lalacewa a tare da gidan ba amman dayake baida magana yasa bayan ya sauke su ya zaro kuɗi rafar ƴan dubu ya bawa maman basma yana ɗan murmushi yace.
"Ai mama bama mu da nisa daku anan layin gaba nake gidan Alhaji Ali Dikko ɗan gwangila"
Zaro idanu tai a firgice sabida kowa yasan Alhaji Ali dikko shararren ɗan gwankila mai kuɗi tare da kirki da son taimakon al'ummah tabbas in ƴarta tai dacen auren ɗansa ai sun gama kuɗi.
waskewa tai tare da cewa.
"Kai yaro kasa na xaro idanu sabida ganin ɗan mafita lallai baka gado a sama ba gada kai tun usuli"
Bai ce komai ba yaja motar shi yayi gida sedai me gaba ɗaya ya kasa walwala da sukuni kasancewar sa bamai yawan magana ba, yasa tsayin kwanaki biyu babu mai gane a halin daya ke ciki sedai ammi ita kaɗai ta gane yanayin ɗan nata takwa tirke shi akan son jin matsalar sa amman yace mata babu komai.

Bayan sati ɗaya Aliyu ya kaiwa su hajiya binta kuɗin gida wanda akai masa kuɗi mai ɗan karen tsada anan ta turkeshi akan seya ci abinci amman yace a ƙoshe yake basmah kamar zatai kuka sabida yadda suka kashe kuɗinsu akan haɗin abincin wanda naman suna da tabbacin zuwan Aliyu a ranar domin yace ze kawo musu kudin.

Lemon kwakwa kaɗai yasha batare daya ci komai ba yayi musu sallama ya tafi sedai me tunanin wannan budurwa ya addabi Aliyu ko bacci ya kwanta ita yake kallo tana zuwar masa mafarkinsa babu shiri ya nemawa kansa mafitar zuwa wajan hajiya binta akan shifa yaga matar aure ranar hajiya kwana tai tanawa kanta kirarin taci dubu se ceto duk abin da sa gaba setaga bayan sa.

A hankali soyayya ta ƙulu a tsakanin Aliyu da basmah wadda zuwanta ɗaya gidan ammi ta gaisheta tana fita hassana kanwarshi ta dubi ammi tace.
"Nifa ammi wannan matar yayan batai min ba wallahi na tsani mutum mai shuru shuru asalin munafukai ne mutum sak yafi"
Ashe Aliyu na falo yana jin hassana bayan ya dawo daga raka basma ranar hassana seda tai zazzaɓin azabar duka yana huci yana cewa seya aureta yaga ɗan iskan daze takata ya barshi.
Da ido ammi ta bisa tana mamakin yadda ya doki hassana duk yadda yake son ƙannensa ko zazzaɓi suke yayta kaiwa yana komowa kenan akansu amman yau akan wadda ze aura ya xage ƙwanji yayi wa hassana dukan kawo wuƙa.

Addu'a tai masa akan Allah yasa basmah ta gari ce.
Cikin watan akaje tambayar auren basma wajan kawunta sosai su kawu usman suka yaba da dattakon mutumin wanda yayita jimantawa Aliyu auren basma amman dan kar ace bakin ciki yake yaja bakin sa yayi gum amman yasan wannan lauyan ne ke neman auren ta.

Sosai ɓangarori biyun ke shirin biki Aliyu kamar ze taka rawa dan murna komai Anty jidda ta siyo na lefe seyace bai yiba daga ƙarshe ma sarat ya tura dubai da maƙudan kuɗi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login