Showing 12001 words to 15000 words out of 83661 words

Chapter 5 - BA SON TA NAKE BA complete Hausa Novel

25 Aug 2024

11355

da kashe motar ya buɗe murfin motar ya fita batare daya mata magana ba.
Ganin haka yasanya ta miƙa hannu ta buɗe side ɗinta itama ta fito tana ɗan yamutsa fuskarta kaɗan.
Hannunta ɗaya yana dai dai inda ke mata zafin ta riƙe wajan tana ɗan dannawa kaɗan.
Ganin yana tafiya ciki ya sanya tabisa da sauri ta cimmasa wanda suka jera tare seka rantse Ango ne da amarya sukazo ganin likita ahaka suka ƙarasa cikin reciption ɗin saman kujera ta zauna shikuma ya ƙarasa wajan masu bada kati.
Maganganu sukai kaɗan ya kuma dawowa wajanta hannu zube cikin aljihu murya a daƙile yace.
"Muje"
Da ƙyar taji abin da yace sabida yadda yayi amfani da ƙaramin sauti wajan fitar da maganar.
Miƙewa tayi tabishi zuwa wajan masu bada kati matar ce ta dube ta tare da cewa.
"Ƙanwata yaya sunanki dana mahaifin ki"
Tana wasa da hannunta kanta a sunkuye tace.
"Ummul khairi Abubakar"
Rubutu matar tayi akan farar takadda sannan ta miƙowa Aliyu.
"Zakaje can ka biya kuɗin ganin likita sannan ka kawo mana shaidar biyan kuɗin"
Shafa kansa yayi tare da jan tsaki marar sauti cike da takaicinta yabar wajan rai ɓace ya biya kuɗin wanda shiba biyan kuɗinne ya ɓata mai rai ba wannan zaryar data sanya shi ta ɓata lokaci ita ta sanya yaji ranshi ya ɓaci.
Haka ya dawo har lokacin tana tsaye tana kuma lura da yadda yake faman cin magani.
Takardar shedar biyan kuɗin ya bawa matar ta shigar cikin system sannan ta sanya hannu kana ta miƙo masa tare da nuna mai step ɗin bene ta bashi kwatancen office ɗin likitan.

A hankali ummul taɗan matso shi hannu na ɗan karkarwa take ƙoƙarin amsar takardar hannun nashi.
"Kaje ka zauna bara naje wajan likitan naga kamar ranka a ɓace yake"
Tafaɗa cikin kalar tausayi.

Wani kallo ya watsa mata haɗi da raɓeta ya wuce abinshi.
Tabi bayanshi da kallo yadda yake tafiya cike da kuzarin shi.
Bin bayanshi tayi sannu a hankali har zuwa saman benen daya ke komai akwai a rubuce yasan ya bai wani sha wahalar gane office ɗin ba.


Jan handle ɗin ƙofar office ɗin yayi tare da turawa ya shiga sallama a ƙasan laɓɓanshi.
Matashiyar likita ce fara mai ƙaramin jiki zaune akan kujera tana rubuce-rubuce idanunta manne da farin glass ta ɗago tare da zare glass ɗin idanunta fuska cike da murmushi ta amsa mai sallamar tashi tare da nuna mai kujerar dake kallonta.
"Bisimillah zauna"!
Ba musu ya zauna yana mai aje takardar dake hannun shi.
"Sunana Dr Fauziyya yaya akai yallaɓai?"
Tafaɗi hakan wanda yayi dai dai da sanda ummul ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama wanda dr fauza ita ta amsa mata sallamar tata.
Bai amsawa dr fauziyya abin da ta tambayeshi ba sema wayar shi daya fiddo yana dannawa cike da nutsuwa.
"Tare kuke mijin kine?"
Dr take tambayar ummul data tsaya adai dai kan Aliyu tana mai sunkuyar da kanta a ƙasa.
"Eh likita mijina ne"
Ta tsinci bakinta da faɗin hakan.
Murmushi mai sauti Aliyu ya sauke haɗi da taune ƙasan lips ɗinshi aranshi yana mamakin naci da cusa kai irin na yarinyar.
"naga matsalar ki a takardar daya bani in bazaki damu ba zan ɗan maki wasu ƴan tambayoyi?"
Dr ta faɗa tare da kallon ummul ɗin.
"Ina jin ki"
Tafaɗa murya na rawa.
"Yana yawan kusantarki da ƙarfi ne lokacin mu'amalar aure hakan ma yana janyo matsalar taɓuwar ƙugu"
Da sauri ummul tai wani irin farrrr da idanunta shiko tsitt yayi yana son yaji tata kalar rashin kunyar.
"Da katakon gado na samu raunin shi lokacin ma bai gida"
Tafaɗa cikin kunya.
Murmushi Dr tayi tare da cewa matso muga wajan.
Da ɗan sanyin jiki take jan ƙafafunta idanunta a kanshi tana son taji yaɗan fita ya basu wuri amman yayi funfurus.
Ita kuma likita sanin tace mata mijinta ne yasa bata ce ya basu wuri ba

Ita ko ummul dana sanin wannan furucin tayishi yafi sau a ƙirga.
"Ɗan kunce zanin jikinki sena duba wurin"
Murya can ƙasa tace

"Ba zani bane doguwar riga ce"
"To ɗagata sama ai mijin kine ba wani abu"
Da tsananin jin kunya ummul ta ɗage rigar santala santalan dogayen fararen cinyoyinta jawur suka bayyana safar hannu dr ta sanya tare da cafkar wajan da ummul ta nuna mata da sauri ummul ta ƙwalla wata ƙara wadda tai dai dai da sanda Aliyu yayi saurin kai duban shi gareta.................
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }

NA
*AUTAR MANYA*


HOME OF QUALITIES WRT ASS....

11


Mayun lumsassun idanunshi suka sauka a kan santala santalan cinyoyin ummul waɗanda suke jawur kamar ka taɓa jini ya fito gasu acike babu alamar rama ko bushewa a tare dasu.
Wani irin yammm zittt yaji acikin dukkan ilahirin sassan jikinsa ga wata irin baƙuwar kasala dake kawo mai cafka bai da ikon koda ɗaga yatsan hannunshi.
Tsintar kanshi yayi da saurin sada kanshi a ƙasa tare da janyo ƙasan lips ɗinshi a wahalce yana tsotsa tamkar ze cire shi. zazzafan huci yake fesarwa da sauri da sauri nan da nan idanunshi sukai wani irin ja har wani ruwane ya kwanta a saman su.

Sannu a hankali kukan ummul ke tashi acikin kunnenshi wanda tana yinshine da iyakacin gaskiyar ta domin yadda Dr ke matsar wajan data buge bada wasa take yi mata ba.
Dai dai sanda zata matsa mata saman ƙugun ummul ta cije taƙi yarda seta fara mata magiya.
"Dan Allah likita ki barni haka wallahi da zafi kin famo har inda bai yi"
Murmushi Dr fauza ta sanya na ganin sakarcin ummul wanda yake ɗauke da wata irin shagwaɓa.
Kafin a hankali ta furta.
"Haba amarya kamar ba jaruma ba pls ki bari saura ƙiris na kammala miki bazaki ji zafin ba"
Tafaɗa mata hakan cike da son bata ƙwarin gwiwa domin ta tsaya.
Noƙe kafaɗa tayi tare da cewa.
"Umm umm! nidai ki rabu dani haka wallahi har zazzaɓin wahala nakeji"
Dariya dr fauza ta sanya tare da furta.
"Gaskiya wannan amaryar kin cika raki Yallaɓai kaɗan matso ka taimaka na gyara mata wallahi ta bugu sosai barin wajan ze zame mata illah don wataƙil yama hanata tafiya idan ba'a gyara ba"
Muryar Dr fauza ta fita lokacin data ke ƙoƙarin janye hannun ummul data ɗora akan ƙugun nata.

A hankali ya ɗago da idanunshi waɗanda suka ɗan ƙanƙance kaɗan, sabida yanayin daya tsinci kanshi a halin yanzun kasance warshi mutum mai saurin shiga yanayin buƙata.
A hankali yaɗan matso kaɗan ya tsira ma fuskar ummul idanunshi wadda fuskar tata tayi wani irin ja sakamakon kukan data ci har wani gumine na zafin azaba ya jiƙa mata saman rigarta.
Yawu mai ɗaci ya haɗiye tare da tattare hannun rigarshi, Kaɗan sannu a hankali yakai hannunshi dai dai ƙugun ummul yaɗan matse kaɗan yana wani kawar da kanshi ganin hakan yasa dr ta soma gabatar da aikinta inda ta cigaba da gyara mata wajan.
Kuka sosai ummul take duk ta gama matse shi batare data san ta aikata hakan ba murya cikin kuka take furta.
"Wayyo bamu wayyo babarmu kizo zasu kashe miki ƴarki wallahi se Allah ya sakamin dukkan ku mugayene"
Abin da take faɗi kenan tana ture Aliyu daga jikinta.
Baƙaramin dauriya yake ba sabida yadda take goga mai albarkatun kirjinta a jikinshi saukar kukan ta kuma yafi kama dana wadda ake having sex da ita tana raki wannan yanayin dayake ayyanawa shine yake ƙara jefa zuciyar sa da gangar jikinsa cikin wani irin shauƙin buƙatuwa kasancewar shi namiji mai muguwar sha'awa ta gasken gaske! danshi daya rasa wannan guri gwara ya rasa abincin daze ci.
Har aka kammala ummul bata daina kuka ba dr fauza miƙewa tayi ta shiga cikin wata ƴar ƙofa tana zame safar hannunta inda shikuma ya tsinci kanshi da fisgo ummul ta zauna saman cinyarshi.
Da wata irin taɓara ta shigar da kanta tsakiyar kirjinsa tana cigaba da kukanta.
Bai iya rarrashin mace ba don ko basmah itake rarrashin sa dan haka seyayi mata shuru yana kokawa da nutsuwar shi kafin A hankali ya rankwaɓa tare da kai kanshi dai dai saitin kunnenta ya wani buga mata hucin zafin bakin shi kafin ya aro jarumtar magana.
"Haba mana pls kibar kukan tashi mutafi"
Yafaɗi maganar kamar bai da niyyar furta ta.
Bata kula shi ba sema miƙewar datai ta kama hanyar barin office ɗin kuma har lokacin kukan dai take bata dena ba.
Dr fauza ta fito hannunta ɗauke da ledar drugs ta miƙawa Aliyu tana dariya.
"Yallaɓai wannan amaryar taka ta cika raki wannan ruwan ɗumi za,a samu se a gasa wajan se a shafa shi wannan kuma tasha sau biyu a rana Allah ya sawaqe"
Kamar baze magana ba seya miƙe ya zube hannun shi guda cikin aljihun wandon shi tare da furta.
"Thanks"!
A ƙasan laɓɓanshi ya ɗauki ledar ya fice yabarta da mayen ƙamshin sa.
Lumshe idanu dr fauza tayi a matsayin ta na budurwa wadda ta jima batai aure ba kuma tana fatan samun mijin aure nan da nan taji Wannan mutumin ya burgeta ba kaɗan ba cake biron hannunta tayi tana wani irin lumshe idanunta.
Sedai akwai tsantsar izzah da taƙama a haka ta faɗa tunanin banza na wanda bai san tana yiba.

Acan gaban mota ya iske ta har lokacin kuka take bata dena ba

Bai ko dubi inda take ba ya buɗe motar ya shiga.
Ganin ya shiga ya data yana kokarin barinta a wajan yasa ta kai hannunta ɓarin mai zaman banza ta bude ta zauna har lokacin hawaye na zuba a idanunta.
Ƙarar kukan ta dame shi matiƙa ga basmah na kiranshi a waya rediyon motar ya kunna sannan ya sami zarafin ɗaga wayar basmah magana suke yana faman sakin tsadaddan murmushinsa yayi kamar ma ya mance da wanzuwar ummul a cikin motar tashi.
Wanda hakan ba ƙaramin ɓatawa ummul zuciya yayi ba dan haka ta ƙara volume na kukan ta wanda yayi matiƙar ɓatawa Aliyu ranshi.
Saurin katse kiran basmah yayi tare dajan wawan birki ya dakatar da tuƙin idanun shi duk ya fito dasu waje tare da kallonta fuska babu walwala ya furta.
"Fitar min a mota na"
Yafaɗa daɗan ƙarfi kaɗan.
Amai makon ta fita seta gyara zama tare da ƙara sautin fitar kukan nata.
Sunkuyar da kanshi yayi tare da sanya hannu ya toshe dukkan kunnuwanshi yana furta kalmar.
"Hasbinallahu wani'imal wakil,dan girman Allah ki saurara min hakan nan jina ke kaina kamar zeyi bindiga bani son hayaniya da ƙara"
Yafaɗa idanunshi sunyi wani irin ja jijiyar kanshi ta tasa tai wani irin ruɗu ruɗu wanda hakan seda yaɗan so bata tsoro.
Ganin gaskiyar maganar daya gaya mata cikin idanuwan shi yasan ya ta fara rage sautin kukan nata.
A hankali ya kunna motar ya cigaba da tafiya cike da rashin kuzari.
Aranshi yana jin tsananin tausayin yarinyar don tabbas son dake masa ya zama son maso wani ƙoshin wahala dan shikam daga basmah ya rufe ƙofar aure ko soyayya duk macen daze kula sedai tausayi badai soyayyah ba..........
ANYA KUWA?
Muje zuwa........
Littafin *BA SON TA NAKE BA* Na kuɗine akan farashin Naira #300 kacal, 0078174806 starling bank shaidar biya tanan 08142105218, Idan kuma katin Mtn zaki Turo na 400



*BA SON TA NAKE BA*🌹
{ Tausayi ne }

NA
*AUTAR MANYA*


ALHAMDULILLAHI INA TAYA ƊAUKA CIN AL'UMMAR MUSULMI MURNAR ZAGAYO WAR SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI ALLAH YASA MUN SHIGA A SA'A AMIN HAPPY ISLAMIC NE YEAR TO ALL MUSLIM UMMAH 1444.

*12*


Mayar da hankalin shi yayi ga tuƙin shi sedai ta cikin kunnen shi yana jiyo sautin fitar ajiyar zuciyarta akai akai lumshe kyawawan idanunshi yayi ya kuma waresu bisa kwalta yana jin jan ajiyar zuciyar tata har cikin ranshi.

Ba jimawa wahalallan bacci yayi gaba da ita ta langwaɓar da kanta a jikin kujerar motar tare da cusa hannunta a tsakiyar cinyoyinta kamar mai jin tsananin sanyi.

Ta wutsiyar idanu yake kallon yadda take sauke numfashi da alamun kukan data yine ya sanyata wannan baccin, sanya hannu yayi tare da ɗan ƙara ƙarfin na'urar sanyaya motar kana ya kunna rediyo ya cigaba da bin karatun alkur'ani mai girman dake tashi ta cikin rediyon daya kunnah.

Ahaka har suka ƙarasa cikin unguwar yayi parking a ƙofar gidan hajja Tare da kashe motar yayi jugum sabida rashin sanin yadda zeyi wajan tashinta daga baccin data keyi.

Wajan mintina biyar suna zaune cikin mota ganin lokaci naja yasa a hankali ya soma kiran sunanta kamar yadda ta gaya mai kuma hajja ma tagaya masa.
Murya can ƙasa kamar baya so yake furta.
"Khairy! khairy!! khairy!!! wanda seda ya kirawo har sau uku amman ummul ko gezau batayi ba sema sabon fitar numfashin dake fita ta cikin hancinta.

Tsaki yaɗan ja kaɗan aranshi yana ayyana matsalarta yawa gareta.
Sannu a hankali yakai hannun shi saman fuskarta yaɗan taɓa kumatunta kaɗan da sauri kuma ya janye hannunsa.
Tura baki tayi tana wani yamutsa fuska kamar yadda yara keyi idan suna mafarki cikin baccinsu.
Idanunshi ya tsira a saman fuskar tata yana kallon ikon Allah babu ko ƙiftawa yana mamakin yadda wani bin idan tayi abu take komawa kamar ƴar ƙaramar yarinya.

A hankali ya kuma kai hannunshi saman nata dake tsakanin cinyoyinta ɗumi yaji a saman fatar hannun wanda ya sanya yaɗan ji wani irin baƙon yanayi acikin jikinshi.
A hankali yasanya bayan hannunshi ya shafi saman fatar hannunta yana furta.
"Khairy wake up"!
Saukar sassanyar muryarshi taji acikin kunnenta tamkar cikin mafarkinta.
A hankali take buɗe kyawawan narkakkun idanunta waɗanda sukayi ɗan ja kaɗan suka kumbura sabida bacci da kuma kuka se hakan yasanya fuskarta ta ƙara cika da wani irin sahihin kyau mai shiga zuciya.

Cikin nutsuwa ta sauke ganinta a saman hannunshi daya ƙi ɗaukewa daga saman nata hannun wata irin kwantacciyar suma ce a kwance ajikin hannun nasa sannan kuma hannunshi yafi nata girma nesa ba kusa ba ahankali taɗan motsa kaɗan tana cino bakinta gaba kamar yadda take ma hajja ko bamu.
Kafin tayi wata irin hamma tare da ƙandarewa ajikin seat tana wata irin miƙa.
Da sauri ya ɗauke hannunshi a saman nata yana mai sosa kanshi da ɗayan hannunshi.
Ya wani basar tare da furta.
"Mun iso gidan hajja fitar min a mota"
Sannu a hankali ta wani juya kai tana kallon saitin windo babansu na waje yana wa yara faɗa kirjinta taji ya bada sautin dam! da karfi kwalla ta taru cikin idanunta.
"Khairey kina ɓata min lokaci na"
Wani irin mutuwa jikinta yayi ta wani kwantar da kirjinta a jikin glass ɗin motar dama ze dauwa ma yana kiran sunanta a haka tunda take bata taɓa jin wanda ya iya bawa sunanta haƙƙinshi kamar shiba.
Tsananin faɗuwar gaban ganin abbanta da kuma sanyin jikin kiran sunanta dayayi yasanya jikinta ya soma karkarwa ahankali sanyi ke ratsa saƙo da lungu na cikin gangar jikinta.
"Khairyyyyyy"
Ya kuma jan sunan a wannan karon daɗan zafin rai kaɗan.
Juyowa tayi tare da yin ƙwalƙwal da idanunta batare data iya furta mai ko kalma guda ɗaya ba se faman girgiza mai kanta data ke faman yi

"Dallah malama kimin magana ko kifita ina miki magana zaki mayar dani mahaukaci yaushe na zama abokin wasanki daga jiya zuwa yau zaki shiga rayuwata ki tarwatsan farin cikina"
Yafaɗi maganar tare da ware mata girman idanunshi masu sanya marar ji saurin nutsuwa.
"Dan Allah ka fita ka barni anan zuwa anjima babanmu ne a waje bani so ya ganni"
Tafaɗa tana wasa da yatsun hannayenta idanunta na zubar ƙwallah!!
Ɗan kallon ta yayi na mintina biyu kafin ya kawar da kanshi.
"Ni ban yarda ba ki fita kawai wani uban ne ze ƙi son yaga ƴarshi indai ba baki da gaskiya ba wato laifi kika ma mahaifanki shiyasa na ganki a hotel ko? ƙilan baya son yawon da kike ne shiyasa bakwa shiri"
Yafaɗa tare da kafe fuskarta da kallo yana son gano rashin gaskiyarta.
Rintse idanunta tayi don ko kaɗan bata son kallon daya ke mata hakan yana sanya zuciyarta tsalle tamkar zata faso ta fito mata daga kirjinta sannu a hankali ta sakar masa kyakykyawan murmushi mai ciwo tare da saurin ɓalle murfin motar ta fita.

Ya jima yana auna yanayin yarinyar kafin ya girgiza kafaɗun shi alamun su ta shafa tare da ɗaukar ledar drugs ɗin ya fice.
ƙofar karamin gida mai ginin ƙasa na kusa da gidan hajja ya ƙarasa tare da ɗan rissuna wa yana gaisar da wani dattijo fari dake faman masifa ga wasu ƙananun yara kamar ze duke su jin muryar Barrister yasan ya yaɗan sassauta tare da miƙawa Aliyu hannu suka gaisa kallon dattijon Aliyu yayi sosai wanda shigarshi ma kaɗai ta nuna talaka ne futik don babu alamar wadata atare dashi sedai akwai tsantsar kamanni atare dashi da waccan yarinyar.
Miƙewa yayi daga rissunawar tare dayi mai sallama yabar wajan wanda har lokacin dattijon bai dena masifar daya kema yaran ba.

Lokacin da ummul ta shiga gidan hajja ta tarar da wata mata fara zaune a saman kujera suna hira da hajja da ɗan sauri ummul ta ƙarasa wajan matar wadda bazata gaza shekaru 40 ba ta wani ɗane jikinta tare da sanya kuka tana furta.
"Bamu shine baki zo da wuri ba ko?"
Cikin tsananin tausayawa wannan matar da ummul ta kira da bamu take shafa kan ummul tana furta.
"Kiyi haƙuri Umminah nima ban so nakai wannan lokacin banzo gareki ba to kinsan halin gidan namu ne yanzu ma fakar idanun mutan gidan nayi na shigo"
Da sauri ummul ta ɗago tana furta.
"Aikam naga abba a waje yana sana'ar tasa wa yaran mutane"
Da alamar tsoro bamu ta ware idanu tare da furta.
"Hasbinallahu wani'imal wakil ya rabbi ka rufan asiri"
Tafaɗa tare sauri sanya hannu ta share zufar data karyo mata.
Dai dai nan Aliyu Dikko ya doko sallama cikin kamilalliyar muryarshi.
Duk suka amsa da hajja da bamu wadda ummul ke zaune ɗare ɗare saman cinyarta.
Ɗan rissunar da kanshi yayi tare da gaisar da bamu sannan ya mikowa hajja ledar tare da furta.
"Zani inda na sauka seda anjima zan dawo dan na makara a komawa gida yau"
Da sauri ya furta hakan kamar mai tsoron abin da ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login