Showing 132001 words to 135000 words out of 144575 words

Chapter 45 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

32173

abunda ke cikinta , idan kukayi sake da damar jinin nan yazo duniya tabbas abunda ke  Boye zai fito fili tana kammala zancenta ta  bace batare da ta basu damar sake yin wata maganar ba. Shiru sukai gabaki d ayan su kowa yana tunanin mafita , a zuciye wacce ake wa la kabi da Abar kauna ta mike , bazai sabuba, dole cikin nan ya zube idan ba haka ba gabaki d ayansu sai na kashe su har lahira, bazai taba bari burina ya salwanta ba, bazai taba faruwa ginin da na fara tsawan shekaru ya rugeje ba dole nayi wani abu, wannan karan da kaina zanyi yakin, da kaina zan fuskanceta , itama bata jira cewar suba ta  bace , gabaki dayan su sunji dadin kalamanta, shiyasa tana fita suka fara jinjina mata daman duk cikinsu tafi kowa hatsabibanci, tunda tace zatayi toh tabbas zatayi din kamar yarda tace .

~&?~&?~&?~&?~&?~&?~&?
~&?~&?~&?~&?~&?
~&?~&?~&?
~&?

Kallansa tayi ganin yanda fuskarsa take a had e, a hankali ta furta  am sorry,sweetheart  , bece mata komai ba sai kyakkyawar fuskarta da ya cigaba da kallo kamar yasamu TV. Tunda zaki ya dora bindigarsa akan Tj, wani irin gudawa ya kwace wa Tj, sai wari da sutar da yake matsewa ce ta fito, ba shi da ka nuna wa bindigar ba, gabaki d aya kusan Tsure wa yan makarantar sukai ganin abunda ya dauke musu kai kamar a film, kowa tanbayar da yake yiwa kansa meyasa balaraben can yaje wajan Tahee, suma su zuky wani irin gumine ya fara tsats tsako musu , tun ba azo kansu ba jikinsu rawa yake . Saida ya gama kare mata kallo yadda yakeso kafun ya furta  are you ok , kanta ta d aga masa kafin ta sakar masa murmushin da yake sanya ya masa zuciya , duk da ransa abace yake hakan be hana yaji bacin ransa kaso mafi yawa tafiya ba Amma duk da hakan be nuna mata ba, dauke kansa yayi kafin ya riko hannunta guda d aya , gabaki d aya wani irin mube musu hanya sojojin sukai kafun su sara masu, a hankali yake tafiya da ita hannunsa d aya cikin nata,ba dalibai ba hatta malam suma sakin baki sukai ganin wani irin kyawu da sukai musu, ganin sun kusa karasa wa cikin motar ne yasa zaki bugawa Tj kan bindiga dayasa Jini fara zuvowa , wani irin kara Tj ya saki gabaki d aya ya daburce, bude mata mota king yayi da kanshi, kafun ya zagaya inda Zaki ya bude masa yashiga, babu Wanda ya kalla acikin malaman har me makarantar da yake basa hakuri, tsoransama karya sa a kulle masa makaranta. Shima zaki cikin motar suka shiga kafun gabaki d aya ragowar sojojin su tafi su tsaka motar king a tsakiya subar wajan, banda mota da aka bar sojoji guda biyar , suna ganin bace war motar king d aya ya zabgawa TJ mari kai dan iska ko ya furta kafin ya umar ta akawo masa ragowar abokan Tj din, su musty har Anfara kuka tun ba aje ko ina ba, hatta yan untouchable sai da yasa aka kawo masa, be mari matan ba sai wankin ba daki yasaka sukai, kamar zasuyi Hauka haka suka wanke bandakin , tsabar mugunta babu ta kalmi yasa suka shiga haka suka saka kafafuwansu a ciki, gabaki d aya toilet din makarantar yasa su wanke har su Tj din da yake tafiya a kwale sabida kashin da yayi a wando, duk da Anzo daukar su basu bari sun tafi ba sai da yasa su tsallan kwado da zaman kujera, tun student nanan har aka tafi aka barsu , yawanci student Allah shikara suke musu dan kowa ya san halinsu, saida sojojin nan suka tabbatar bazata moruba kafun su bar makarantar bayan wani horon punishment din da suka da aka yiwa su Tj , da Sauri kuwa me makarantar yayi na am dan yasan wanene king, baya magana biyu, dama shima ya gaji da ba kin halinsu da suke kokarin sawa a kulle masa ba shiri, da rarrafe su TJ suka soma tafiya sabida yanda kafarsu tayi tsami ko motsata basasan yi gabaki d aya ko wannansu fuskarsa ta jike da hawaye, su musty sai faman tsinewa Tj da su Ruky suke.

****** Tunda suka shiga cikin mota be ce Mata komai ba sai hannunta guda d aya da yake murzawa a hankali, d an d ago da idanuwanta tayi ta kallesa ganin ya dauke kansa yasata matsowa kusa dashi sosai, dan short din unique labulen da ya karesu ta gyara kafun ta danyi dage Daidai kunnansa  My love  , ta furta cikin wani irin salo, lumshe idanuwansa yayi duk da wani irin abu da yaji ya taso masa amma sai da ya danne ya shareta, kara dagowa tayi akaro na biyu amaimakon tayi masa magana sai ta Dan ciji kunnansa kadan, da wani irin shock ya kalleta, ido daya ta kashe masa kafun ta dan marairaice masa fuska Daidai lokacin da zaki yayi parking . Door din mota ya bude mata, suka nufi part dinsu har yanxu hannunsa yana cikin nata. Har suka shiga cikin daki be ce mata komai ba , saida ya tabbatar tayi wanka , yasata cin abinci , duk yanda taso yi masa magana yaki bata damar hakan, ruko hannunsa tayi cikin nata  Am sorry  , kallanta kawai yayi kafun ya lumshe mata ido har yanxu bece mata komai ba, ko karin tashi yake tayi saurin d anewa kan cinyarsa  Am sorry babyna, ni banasan wannan shirun naka , kana so shima babyn mu yayi fushi? Ta karasa tana dora hannunsa akan cikinta, lumshe idanuwansa yayi kafin ya kara rungumeta a jikinsa,  you won t be going to school for now , okay? Tasan ransa zai baci daman, bata yi masa musu ba ta d aga masa kai, food din tayi serving dinshi, dakanta tayi feeding baby dinta  are you upset? Cewar king , yalwataccen murmushi ta sakar masa kafun ta cusa hannunta kan lallausan gashin kansa tana wasa dashi me yasa zanyi fishi da sweetheart d ina?,Am not angry , how are you feeling, do you need anything  , da Sauri ta daga masa kai alamar eh, inasan choki choki, goruba, taura sai magarya , kai ya jinjina mata  zansa a duba miki a super market  , dariya ce ta kwace mata wai super market,pillow d aya ta dauka ta buga masa zata gudu yayi saurin rukota, cakulkulu ya fara yi mata tana dariya  no please na dena , na dena please  , tahee take fada , ganin tana kokarin kwarewa ne yasa ya lafa da iya mata cakulkulun, hira ta fara yi masa, yana sauraronta har lokacin sallahr la asar yayi ya tafi masallaci.

Karfe 8:40pm ihsan ta kawowa Tahee abinci wai inji ummey, duk yanda Tahee tayi da ita akan ta zauna ta ki zama ta gudu,Sabida kwata kwata bataso king yazo ya tarar da ita a part din. Tana bud ewa taga kafiyayyiyar masa da miyan Taushe da yaji man shanu,ya wunta ne ya tsinke shiyasa bata jira king ba ta dakko plate ta soma cin abin cinta. Sosai taji masan saida taji ta Ko shine ta ajje ragowar masan tana maida nunfashi, ta mike da nufin komawa kawai taji juwa na neman kada ita da Sauri ta koma ta zauna, sai da ta kara kusan mintuna 10 a zaune kafun ta mike da niyar ta shi, kulle war da cikinta yayine yasa ta sakin karar azaba kafun ta rike cikin nata tana ambatan sunan Allah, kara kulle wa cikinta yayi da yafi na farko a zaba,  ya Allah cikina , Nunfashinta ne yake kokarin futa daga jikinta sabida wani irin azaba da tajii a cikin ta , take a wajan Jini ya fara bin kafarta, kara Tahee ta saka  Jini,jini,jini ta kuma sakin gigitacciyar kara, banko  kofar da akai ne yasa ta d ago kanta a wahala , Wanda ta ganine yasa ta fashewa ta kuka ta yanke jiki ta fadi, da wani irin masifaffen sauri king ya  karasa inda take be tsaya bata lokaci ba ya d auketa kamar baby bayan ya lullu be mata jikinta sai cikin motor , ga baki d aya ya rud e ,zaki zaiyi driving king ya hana tare da kar  bar mu motar, idanuwansa har sun fara canza wa a kausashe ya furta  kar Wanda ya sani a cikin gida , duk Wanda yazo neman ta mun d an fita ne  yana kammala zan cansa ya ja motar cikin matsiyacin gudu sai asibitin NAHYAN.
GIDAN AUNTY

07041879581 ( mss Lee =ؖ?)

Book 1

PAGE 68

Direct yana shiga cikin asibitin ta baya yayi parking, da Sauri ya daukota ganin yanda jinin da yake zuba a jikinta har yanxu be tsaya ba, office dinsa na sama ya hau kai tsaye bayan ya bada umarnin a kira masa Dr Maryam, tunda kafun ta karaso ya tsayar da jinin, tana zuwa be jira ta cewar ta ba suka fara aikin duba Tahee , gabaki d aya fuskarsa tayi jawur jijiyoyin kansa sun tashi, cikin ikon Allah suka gano matsalar, tare da d aure mata mahaifa sabida yanda wajan yayi rauni, saida ya tabbatar komai yayi settling kafun ya sauke a jiyar zuciya , test d in da ya umarci Dr maryam tayi masa ne ta kawo masa , akan gadon sa dake cikin dakin office d in take , a hankali ya kara murza hannunta cikin nashi kafun ya sauke idanuwansa kan kyakkyawar fuskarta da yi fayau da ita, hannunsa d aya ya d ora kan cikin ta yana shafawa a hankali , cikin ranshi kuma wani irin tafasa ransa yake, gabaki d aya jijiyoyin kansa sun mike tsaye , launin idanuwansa sun sauya daga ainahin kalar su zuwa wani kalar launin ja daban, be san wanene yake gangancin ta ba masa ciki ba , shikansa be san Wana irin hukunci zai yiwa Wanda yake  ko karin salwantar masa da ciki,sunan Allah ya fara nanatawa aransa ganin yanda ransa yake  kara baci , yana dad e a zaunan da yake yana karanto duk adduar da tazo masa rai kafun ya fara yiwa Tahee addua itama .

Agogon hannunsa ya duba almost past 10, allurar baccin da yayi mata har yanxu be sake taba , Sabida ba  karamin jigata tayi ba , Sabida maganin da akai anfani dashi ba karamun illane dashi ba da kai tsaye yake kisa, forehead d inta ya sun bata  am really sorry Angel  , kafun ya dakko phone d inshi,a haroon ya kira a waya, cikin wata irin zabura haroon ta sakko daga kan gado ganin kiran King abunda bai ta ba faruwa ba , safa da marwa ya fara gumi har ya fara tsatstsafo masa , yana d aga kiran tunkan ya fara bawa king hakuri ya ji saukar muryarsa,  Number ihsan , kittt ya kashe wayar tasa, tazo idanuwa haroon yayi, Allah yasa yarannan ba lefi sukai ba, gudun karya yi wani kuskuren yasa yayi saurin tura masa number ihsan ba  bata lokaci.

Daidai lokacin da king ya kira number ihsan , a Daidai lokacin ne ta fito daga part d in ammeey zata koma part d insu, sabuwar number da ta ganine yasa ta share kiran kamar katta d aga , sai wani zuciyar ya ce mata ta d aga , tun kafin ayi magana zuciyarta ta soma dukan uku uku,  where are you  , taji saukar muryar king, da mugun sauri ta cire wayar a kunnanta kafun ta mayar murya na rawa ta furta  na fito ne zan koma part d in mu  ,shiru yayi kamar baze ce komai ba sai kuma taji saukar muryarsa  wanene ya kawo mata abinci , ta gane Tahee yake b
Nufi shiyasa tayi saurin bashi amsa  Ummey ce tace na kawo mata , wani irin harbawa zuciyarsa yayi , besan lokacin da ya furta  wacce ummeyn itama amsa ta bashi da  ummeynka  yanxu kam runtse idanuwansa yayi, me Hakan ke nufin , ummey, no , kusan 2 minutes be ce komai ba ta d auka ya kashe , itama har zata kashe cikin wata iriyar murya ya furta , kije ki bawa zaki kwanukan abincin, and ki gyara wajan, don t said anything to anyone ko wanene , okay  , da Sauri ta furta  insha Allahu yaya ,. Cikin sauri sauri ta nufi part d insa zuciyar ta har ta fara bugawa itama , tana shiga ta tarar da uban Jinin da Tahee ta zubar, a mugun rud e take bin wajan da kallo ga abincin da ummey ta bata . Da Sauri ta d akko jakar zuba abinci ta had a kayan abincin , Kafun ta kaiwa zaki dake waje , tana dawowa Jinin ta fara gyarawa kafun ta gyara falon, har yanxu zuciyarta be dena bugawa ba , fatan ta Allah yasa Tahee lapiya take. Saida ta tabbatar komai ya gyaru kafun ta kulle musu part d in ta nufi nasu duk jikinta yayi sanyi.

Duk wannan abun da yake faruwa babu Wanda ya sani a cikin gidan, zaki na kawo masa kayan abincin yasa akan bin cika masa su, tabbas kuwa a cikin su maganin yake , wani irin zazzafan zazza bine ya fara kamata , gabaki d aya ya rasa Wana irin tunanin zaiyi , yana ganin kiran Ukti amma ya kasa d aukan kiran nata, sai bin Tahee yake da kallo ,har yanxu ya kasa gasgatawa, yana cikin tunanin da ya fad a Tahee ta soma mutsu mutsu da ido, har ta ware kumburarrun idanuwanta kan kyakkyawar fuskarsa da ya du kar  kasa  sweetheart  ta furta a hankali kamar me rad a , da Sauri ya d ago rinannun idanuwansa da suka canza kala, cikin sauri ya  karaso inda take  are you okay  , shima ya furta mata kamar me rad a , kanta kawai ta girgiza masa alamar eh, ahankali ya furta  Am sorry  , rufe masa baki tayi da tafin hannunta  Ni bakayi mun lefun komai ba , Babyn mu? Ta tanbayeshi duk da shakkar tanbayar da tayi masa , kallanta yayi for second kafun ya furta  he s safe too ajiyar zuciya ta sauke da har shi da yake kusa da ita sai da yaji,duk da bata da wani  karfi sosai a jikinta akan me hana ta kamo hannunsa ba tana shafa gefen fuskarsa  wannan face d in fa ta canza ba haka na santa ba  , rungumeta kawai king yayi a jikinsa ya kasa magana jiya ke kansa kamar zai tar watse, har sai da ya samu nutsuwar da yake bu kata kafun ya raba jikinsu  Sleep !! Okay  , da d an mamaki Tahee ta kallesa tasan dai nan ba gidan su bane duk da  kamshin da ya karad e ko ina na d akin hakan be hana ta jin wari asibiti ba,  bazan iya bacci ba , bana san warin asibitin nan kamar zan yi amai , but har yanxu jikinki ba kwari ,  Dagaske nake yanxu bana jin ciwon komai , inna cigaba da shakar warin asibitin zan iya amai fa  ta fad a tana  karasa turo masa  karamin bakinta , kansa kawai ya jinjina mata kafun ya temaka mata har zuwa cikin motar yana ri ke da hannunta, saida ya tsaya a ocean basket yayi mata order d in abunda zataci kafun su koma gida . Bai zaunar da ita a kasa ba da kansa ya d auketa ta cikin lifter ya kai ta master bedroom dinsa , sai da ya tabbatar tayi wanka kafun ya fara bata abuncin da suka taho dashi, duk yanda take ce masa ta  koshi saida ya sata ci kafun ya bata wani magani ta sha , ba jimawa bacci ya d auketa. Tunanin abunda ya faru yake har yanxu ya kafada fita daga cikin kansa , ga wani irin lafiyayyan ciwan kai da ya haifar masa , duk yanda ya so runtsawa abun gagara yayi sai wajan 2:40 kafun bacci  barawo ya sace shi.

Ana kiran sallahr asuba ya farka , sabida tsananin yanda kansa yake ciwo bai je masallaci ba yau a gida yayi sallahn shi ganin Tahee na kokarin saka damuwa a ranta ne yasa shi cire komai ya mayar dashi gefe dan kansa ya fara kula da ita , tun daga kan abincin da zataci , da kanshi yake fita ya kar bo mata order d in duk abunda take so ko ya kira ihsan ta girka mata. Kwana biyu da rashin lapiyar ta jikinta har ya murmure ta dawo normal sai wani ci kowa da ta karayi na musamman , Tunda abunnan ya faru Tahee bata ta ba kawo wa ranta cewa ummey ta mata abu ba , duk da tasan tana gama cin abinci cikinta ya fara mata ciwo , ga Tamar dar king your husband da take samu har yanxu, ta  bangaran king shima har yanxu be ce komai ba akai ba , amma ga baki d aya mood d insa ya sauya , wani irin miskilanci ne ya  kara shigarsa , Tahee ce kadai ke iya controlling kayanta .

Karfe 3:02 biyu Tahee ta nufi part d in dada ganin kwana biyu bata le kasu ba kuma har yanxu basu san abunda ya faru ba, Tana shiga kuwa dada na damun fura, cikin washe baki ta karaso wajan dadan,  Nazo a Daidai kenan , yau zansha furan dada  , murmushi dada ta sakar mata  kamar kinsan kuwa ke nake damawa , wancan tanbad ad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login