Showing 114001 words to 117000 words out of 144575 words

Chapter 39 - GIDAN AUNTY BOOK 1 cmpt by Mss Lee

miss lee   

28 Jun 2024

32163

gaggawa yayi musu wankan tare da dakkota kamar wata baby, kaya kawai ya saka sai turare tare da nufar masallaci, itama sallar tayi har sai da ta jira isha i , tana idar da sallah ta fashe da kuka ,ko a mafarki bata taba kawo Waranta zatayi farinciki ba , duk da bata cire rahama daga rahamar ubangijiba, kukan abu biyu take yi, Allah ya bata mijin da yake santa ba tare da yayi laa kari da wani na kasu na jikinta ba,ya kaunaceta, ya sota, ya taimaketa alokacin da take neman temaka,tabbas ta cika me sa a , oummanta da taheenta kullum tana musu addua Allah ya bayyanasu, tasan bawa baya wucewa kaddararsa , har yanxu bata karaya ba wata rana zata gansu, gudun karya dawo ya ganta a hakane yasa tayi sauri ta wanke fuskarta tare da gyarata , light food ta hada masa , lafiyyayen Dankali tayi masa da yaji zogale da kifi gabaki d aya part din ya kare da kamshin abincin. Yana dawowa kai tsaye kitchen ya nufa shima, a jikin kofa ya tsaya ganin tana gyara wajan da ta bata, ganin bata kula da zuwansa bane yasashi takowa a hankali ya rungumeta ta baya, zatayi ihu kenan ya rufe mata baki matsoraciya kawai ajiyar zuciya ta sauke  ka bani tsoro sorry dear, me kike a kitchen kinsan ciwanki har yanxu be warke ba kauda kanta tayi kafun ta furta  ni lapiya ta kalau , murmushi ya saki me sauti kafun ya furta , shikenan ki shirya anjima zan baki baby baya taja tare da fara yarfa hannunta daya  ban warke ba fa uhm uhm kin ce mun fa lapiyar ki kalau, karamin bakinta ta turo masa kadan  ni wasa nake  , uhmm this your lips ko unmm  ai be karasa ba tayi saurin barin kitchen , sai da tayi nesa dashi kafun ta furta  your food is ready  , uhmmm  my baby is on his way baby , ya fada a zuciya tare da bin bayanta, tun kafun ta fara serving dinshi kamshin abincin ya cika masa hanci, da kanta ta bashi a baki kamar yanda ya bukata, sosai ya yaba da amincin sabida yanda yaji dadin girkin, yana ci yana sa mata albarka, saida ya kammala cin abincin kafin ya bata tukwicin dalleliyar prado sabuwa baka kiran me shegen kyau, farin cikin da take ciki ya kasa misaltuna , ta rasa me zatace, Godiya zata fara yi masa ya dakatar da ita ,bata gama shiga shock din motar ba sakamon papers din da ya bata, fara dubawa tayi amma bata fahimci komai ba sai kallansa da tayi, ware su yayi zuwa gida biyu, gabaki d aya gift dinta da aka bata na biki ya nuna mata, tun daga kan takardun jirginta, da mall dinta , da gida da motocin da ta samu, suman zaune tahee tayi ta kasa kwakkwaran motsi kamar a mafarki this one is for your studies , Monday zaki fara zuwa school insha Allah & & & ..


****
Ayi hakuri da mss lee kwana biyu >?q?>?y?
GIDAN AUNTY

Mss Lee =ؖ?
07041879581

BOOK 1
Page 60=ؖ?

She was so speechless, gabaki d aya ta kasa magana, ji take komai kamar a mafarki yake zuwar mata, bata san lokacin data rungumeshi ba tana sakin wani saban kuka me taba zuciya , ta rasa wani irin farinciki zatayi,sai kara rungumesa da tayi so very tight, murmushi ya saki yana hugging din ta back shima, a hankali ya fara shafa bayanta alamun rarrashi, it s ok , banasan wannan kukan please  ,ya fada a hankali, duk da ta jishi hakan besa ta dena kukan ba sai ma kara masa karfi da tayi, ganin kukan ba me karewa bane ya hade bakinsu waje d aya, bata hanashi kusan mintuna biyu kafin ya janye bakinta yana kallan yanda fuskarta ta baci da hawaye, tissue ya dauke ya fara goge mata hawayen amma duk da hakan ta kasa tsayar dashi, i don t like , stop it ok , girgiza masa kai tayi a hankali zata bude baki ya dakatar da ita, don t even start it, banaso  , magana zata karayi ya girgiza mata kai tare da langwabar da Kai kadan  dady want to sleep , murmushi ne ya subuce mata, ta saki dariya kadan, Allah ya albarkaci rayuwanka, yasa ka fi haka,Allah ya cika maka burinka na duniya da lahira,Allah yasa ka gama da duniya lapiya , yanda ka sani farinciki Allah ya baka masu saka farin ciki fiye da haka  , batayi auneba sai ji tayi yayi sama da ita , da paper din hannunta,direct upstairs ya nufa da ita, be sauketa a ko ina ba sai akan wani bed me shegen kyau, daki ne babba a second floor sai faman tashin kamshi yake,takardun kuma ya sa mata cikin wani lock me anfani da turn print,  dare yayi, we have to sleep  , sai yanxu wani tsoro ya bayyana a fuskarta ganin zasu kwana waje daya , amma duk da hakan tana kokarin danneshi,dan tayi alkawari bazata taba hanashi a bunda yake so ba, ya na shiga toilet ta fashe da wani saban kukan farin ciki,dama oumma da taheer sunanan, nasan da sunfi kowa farin ciki da koma wata makaranta, cikin sauri kuma tayi istigfari tana goge idanuwanta gudun karya fito ya ganta tana kuka, ko da ya yafito kallo daya yayi mata yau dauke kansa, itama tashi tayi tashiga wankan, kayan da zata saka ta fara tunani tunda bata taba kwana a cikin dakin ba, tana fitowa taga wata red din Riga a ninke tare da yar karamar paper , wear it please  , tana daga rigan ta zaro ido waje sabida ganin ba ta inda jikinta zai rufu a cikin, rigar tayi shara shara da yawa sosai sai wani dan siririn pant, duba wardrobe din Wajan tayi taga duk manyan kayana ne a wajan babu ta yarda zata sasu yasata yin shahada ta saka kayan, ita kanta saida taji kunyar kanta sabida yanda jikinta yayi mugun fitowa,ganin bazata iya shiga cikin bedroom din ba ysa tayi zamanta a cikin dressing room din.

A bangaran king kuwa tana shiga , ya dauki wayarsa da aka turo masa abu ta cikin email, abunda aka rubuto ya karanta kafun ya dauki wani number yayi kiranta, ringing 1 aka daga wayar kamar ana jiran tsammaninta tun tuni, bai amsa gaisuwar da na wayar yake masa ba sai ma tanbayar da ya jefo masa  ansamo details din inda suke , banji me akace masa ba tsawan mintuna biyar kafun ya furta  duk inda suke a binciko su, few days kawai na baku , yana kammala zan cansa ya kashe wayar, abun hannunsa dake yawo ya dan kalla, me harafin M and T, abunda suka faru tsawan shekarune suka shiga yawo a kansa, take a wajan wani masifaffen ciwon kai ya kamasa, ya dade yana addua kafun ciwon kan ya lafa masa a hankali, lokaci ya kalla ganin har yanxu bata fito bane yasa shi bin bayanta, a hankali ya tura kofar, tana zaune kan wata kujera bacci ya dauketa, kallan yanda rigar ta fito da ainahin jikinta yayi kafun ya saki wani murmushi me kayatarwa, sosai ya ke bin surar jikinta da wani irin mayataccen kallo, ganin abunda yake san dannewa yana kokarin ta somasa ne yasashi saurin kauda ido, tare da daukarta a hankali, a zabure ta ware idanuwanta , kafun tayi saurin kullesu ganin rigar dake jikinta tana kara kankame jikinta, bece mata komai ba har ya kwantar da ita kan fadon, da wani irin mugun sauri ta kashe Wutar dakin tayi saura lamp,dariya ce taso kamasa da har saida murmushi ya bayyana a fuskarsa duk da kasancewar da duhu, gefen gadon ya zauna tare da jawo ta jikinsa, kokarin zame jikin ta take sanyi amma ya kara kankame ta, ouchhh da sauri ya kalleta ganin yanda take runtse ido, duk da a duhu duke , ciwo na , ta fada a hankali, am sorry bari na duba wajan , kafun ya kai karshen zancen sa ta dora hannayenta biyu akan bakinsa Dan bata bukatar jin karshen maganarsa, ok am sorry ,bazan karayi ba sai wajan ya warke ,ok , ya fada yana dora kanta akan kirjinsa, aziyar zuciya tahee ta fara sauke lokacin da yake shafa mata baya, sleep tight, I love you  , ya fada yana kara rungumeta, same  ta fada a hankali duk da batayi tunanin zai jiba,  I won t force you!!!!!! But Inaso nasan soyayyar da kike mun dan dagowa tayi ta kallesa kafun ta kara dora kanta akan kirzinsa batare da tace komai ba, shima be damu da tayi maganan ba shiyasa ya cigaba da shafa bayan ta,bata dau dogon lokaci ba wani daddadan bacci me shegen dadi ya dauketa, ajiyar zuciya king ya sauke yana kara gyara mata kwanciyarta  I love you to the moon and back sweetheart  , ya fada tare da sunbatar goshinta,addua yayi musu kafin shima wani bacci me dadin gaske ya daukesa.

>???>???>???>???>???>???

After 5 days, wata iriyar soyayya king yake nunawa tahee me tsayawa arai, tun yan gidan basu fuskanta ba har kowa yagane irin soyayyar da yake mata, a tsakanin su abeeey da ummey kuwa baza ace ga Wanda yafi nuna farincikinsaba, ummey har da kuka dan ganin d anta ya fara samun farincikin da ta dade take biri ya samu, ammey ma sosai take jin dadin ganin yanda son dinta ya fara dawowa kamar rayuwarsa ta da, dada kullum cikin sa masa addua take Allah ya kawo mata jikokinta nan kusa, duk lokacin da ta fada hakan kuwa sai dai ya kalleta amma har cikin zuciyar sa yanajin dadin adduar, a fili kuwa sai dai ya dauke mata kai, sau da dama saida tace munafurci dai babu kyau Allah yasa ba jaraka kake zuwa kana yiwa yarinya ba. A cikin yan kwanakin nan kuwa wata iriyar shakuwace ta shiga tsakanin ta dasu ihsan duk da kasancewar sun dan girmeta, amma hakan be hana su ki girmamata ba a matsayinta na matar yan su, sau da dama indai basu da lectures toh suna ban garantane, wani lokaci kuma a part din su dada suke zamansu, duk tsawan kwanakin nan bata ganin amrah da basma, duk da yawancin lokaci ta naji su ihsan na maganar zaman dakin da take yi yanxu musamman da taji motsun king ko me take bari take ta gudu inda bazai ganta ba,ta bangaran basma ma ta koma gidan wata aunt dinta acewarta zatayi mata kwana biyu ne itama, babu Wanda ya hanata, kwafa kwai tayi ita kadai Tasan abunda ke cikin ranta, a cikin kwana biyar din nan small mom da mahma kowa ya koma gida suma, gabaki d aya family din babu Wanda beyi missing Dinsu ba, rigimar da zoya tasa akan zata bi small mom ne yasa itama aka tafi da ita, yanxu gidan ya rage saura su kadai.

Yau ya kasance Saturday, Daidai da saura kwana biyu tahee ta fara zuwa makaranta. tana zaune kan 2 sitter cikin shigar kananan kayan da ya sabar mata, dan karamin plate din fruit ne a hannunta take yankawa ,lokaci zuwa lokaci tana sashi a bakinta, tun bayan tafiyar kulu take zaune akan 2 sitter din bayan bacci da ta dade tanayi akan, ringing din wayartane ya mayar da ita cikin dogon tunanin da ta fada, private number ne babu suna kwata kwata a jiki, gabantane yayi wani irin wawan faduwa, sabida mafarka da take yawanyi akan kiran, kamar karta daga sai kuma wani bangare na zuciyar ta ya bata goyan daga kiran, cikin sallama ta daga kiran , bata karasa sallamar tata ba sabida wani gigitacciyar karar da yasa tayi saurin cire wayar a kunnanta na yan sakanni kafun ta mayar da wayar a hankali, wani irin dariya mara dadin ji aka dauke dashi me ban tsoro kafun cikin hade rai taji an soma magana  Ba a mun taurin mai, duk Wanda yayi kokarin bujurewa umarnina ina kashe sa kamar sauran ne, kwanaki kadan na baki ki kashe mun mujin ki, dan jinin jikinsa mallakina ne ni kadai, idan kikai sabanin hakan kuwa ki tabbatar da samun gawarwakin mahaifiyarki da dan uwanki dan zan musu kisa irin kisan wulakanci ne , na turo miki sako ki duba  kitt aka kashe wayar, TAHEE da ke zaune duk launin idanuwanta sun canza zuba launin ja me ban tsoro, wani irin tsikar jikintane taji yana tashi a jikin, cikin sauri ta bude private number din da babu suna ko daya a ciki, KILLED YOUR HUSBAND  wani irin gigitacciyar kara ta saki tare da jefar da wayar, gabaki d aya launin idanuwanta sun canza zuwa launin ja, girgiza kai ta somayi kafun tayi ball da wani tanbuwal din glass me shegen kau, fashewar sa yayi Daidai lokacin da king ya bude kofar, da mugun sauri ya shigo falon,inda take ya nufa, cikin wata iriyar murya me amo ta dakatar dashi,  me nayi musu, me nayi musu,kaje ka kashe su dukansu bana san su mugayene, da mamaki king yake kallanta ya rasa gane me take nufi shiyasa yayi yin kurin zuwa wajanta, wani gigitaccen ihu tahee ta saka, launukan idanuwanta na kara canza wa , cikin wata siririyar murya ta furta  sun kashe mun NONNA,SUSAN, SUN KASHE MUN SIF DINA, Nima sun kashe ni , ka fada mun Menene laifin mu da suke san hallakamu  , kallo daya king yayi mata ya fahimci ba taheen sa bace, fuskarsa ya hade kicin kicin ba alamar fara a yace kalleni , amaimakon ta kallesan sai ta kuma dukar da kanta kasa, cikin gigitacciyar tsawa ya furta kalli cikin idona ynxu  , fashewa da kuka tayi tana girgiza kanta , ganin hakan yasashi yin taku daya, a mugun zabure tahee ta danki wukar da take ynxu apple da ita& .

GIDAN AUNTY
07041879581

BOOK 1
Page 61

Tsayawa yayi a inda yake gabaki d aya hankalinsa ya gama tashi ganin ta da wuka a hannunta, kalaman dazu take ta kara maimaitawa,gyada mata kai yayi shima  ok zamu rama muma amma bani wukar nan tukunna , kin bashi wukar tahee tayi saima fashewa da wani saban kukan tayi, jikinshi har rawa yake dan ya gane ba ita kadai ce ba, tsoransa karsu cutar da ita, sunan dazu da ta kira ne ya fado masa kafun ya kalli yanda take faman hada gumi duk da sanyin Ac dake fitowa, bayanta ya kalla kafun ya furta  NONNA , da sauri ta juya tana sakin wukar hannunta, yana gani ta juya taku biyu yayi ya damki Dan tsan hannunta, kara ta sakar masa sai faman fusge fusge take ita kadai, wata iriyar gigitacciyar tsawa ya daka mata yana hade fuskarsa kamar bashi ba,  ki nutsu , ya furta cikin kausashshiyar murya , nutsuwar kuwa tayi tana sun kunyar da kanta,  ya sunanki  , shiru tayi tana kara sunkuyar dakanta,  karki bari na sake maimaita tawa  , cikin shashsheka ta furta  sunana LOLA , dan kallanta yayi jin tayi magana da wata iriyar murya wacece ke , me yasa kika shiga jikin mata ta , yanxu ma shiru tayi masa, bece komai ba kafun a cikin dan daga murya yayi Bismillah, rawa jikinta ya fara , ah ah zanyi magana ka bari dan Allah  ta fada cikin rikicewa, banza yayi mata kafun ya fara karatun alkuranin, yanxu kam ihu ta sa masa tana rokonsa karya konata, zaunar da ita yayi kan kujera har yanxu hannunsa na rike da nata kafun ya dakko wani bottle water da ke gefensa ya ajje mata a gabanta, da sauri ta saka hannu zata dauka ya matsar da ruwa nesa da ita  ruwa , ruwa  ta fara fada ,  zakisha , ya furta , bata jira ba ta amsa masa da Sauri zan baki ruwa idan kin gama amsamun tanbayoyina, sabanin hakan kuma zan ko????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
na kine  , wacece ke, me yasa kika shiga jikin matata , cikin wata iriyar murya ta fara kuka ,  ba cutar da ita nake ba, te makonta nake, suna san Kasheta ne kamar yanda suka kashe mun ahalina shiru yayi na yan sakanni kafun cikin kausashshiyar murya ya furta  Menene hadinki da matata, sannan menene alakar ku da matata da zaki shiga jikinta , ina bata kariyane kamar yanda Nima ta taba temakona a lokacin baya,ni ba muguwa bace, suna harin rayuwar tane , su wanene da mugun firgici ta kallesa , zasu kasheta kamar yanda suka kashe shi, bazan iya va ,wani irin rawa jikinta ya fara, ruwa !!ruwa!! , ruwan ya dakko kamar yanda ta bukata amma be bata ba, banasan jin wannan tatsuniyar taki, kar na sake ganin ki a jikin matata, idan va haka ba zan konaki da ayoyin uban giji, ki gaggauta fita daga jikin matata yanxun nan ,kanta ta daga masa tana rike makoqwaranta, ruwan ya mika bata da mugun sauri ta fara sha, saida shanye duka kafin ta fara sakin ajiyar zuciya, zan fita daga jikinta, Kai ma nagode da yanda kake kular mun da ita,nasan kana kula da ita amma ka nunkashi sabida kokarin kasheta da suke yi, ganin komai nasu ya fara lalacewa,ka kula da ita  , tana gama fadar hakan tahee tayi atshawa me karfin gaske,kafun ta sulale ta fado kan king da yayi saurin tarota, cikin zafin nama ya dauke tare da kaita cikin bedroom, kallan yanda take bacci peacefully yayi, kokarin kawar da tunanin yun kurin kashe masa mata da akace yake, iska ya furzar a hankali kafin ya furta  it s a lie . System dinsa ya dauka bayan ya canza kayan jikin sa, ya jima yana operating a kanta,lokaci zuwa lokaci yana kara dubata duk da yana kusa da ita, kiran sallah la asar ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login